Showing 333001 words to 336000 words out of 413917 words

Chapter 112 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2700

shi ba sai wannan karanS'

Sun riga da sun gama tsara komai, tafiya kadai ta rage masu amma daddynsa na neman Ya kwafsa mashi.

Wayarsa dake acikin Trouser pocket dinsa sai ringing takeyi, yasan bai wuci na hannun damansa ne ke nemansa ba.

Kifa kan shi yayi, jikin Sofa wani irin sarawan Ciwon kai Yake Ji, Ji yayi bazai Iya bari damar nan ta wuce shi ba, Shi kadai ne zai bada Umarni su tafi kai farmakin nan In har basu ji daga gare shi ba, gaba daya plan dinsu zai lalace.

Yana tsaka da tunanin nan kwatsam lokaci Waya ya fara Jin wani irin matsanancin bacci na neman yaci karfin shi lokaci daya ya zare idanun shi cike da tashin hankali Ya ke duban Cup din da daddynsa Ya bashi Yasha cofee yunkurawa yayi da wata irin kasala Ya nufi kofar dakin Yaja handle din Yana kokarin bude ta sai dai ga mamakin shi Ya datse kofar ta waje, Kuma dole saida fingerprint Win daddynsa ko na mommynsa za'a iya unlocking Winta, tashin hankalin da ba asaka masa Rana.

Gwiwowin ?afafunsa ne suka sage, wata irin juwa ta Webe shi gaba Waya Ya kife kan floor kamar wanda yasha giya takai mashi karo bai ta6a zaton daddynsa zaiyi masa haka ba, dama saida boyayyan mutumin nan yace mashi kada ya yarda da kowa saboda kowa zai Iya cutar da shi a halin Yanzu da alamun kamshin gaskiya amaganar shi.

Still bai daina kokarin mikewa ba, dakyar Ya zaro wayar shi daga trouser pocket dinsa, yanata faman kiciniyar bude idanunshi dake lumshewa, dakyar Ya lalubo layin Mommynsa Ya danna mata Call, cikin sa'a tayi picking.

"My baby boy, how are you"?

Kokari yake ya buWe labbansa sai dai yayi masa nauyi, kamar harshen shi ya karye, dakyar ya iya furta"mom... myyy ... in.. Ina a resting home din dad... he locked me in his master suite...I can't open the door...I need your help...come quickly, Mommy."

yana faWan hakan wayar ta sulbe daga hannun shi.

Yana jiyo muryarta da karfi take ambaton"hello Hello, Owais! Kana ji na? Me ka yi masa ne?

Kalmar karshe da kunnansa su ka ji ta furta kafin kiran Ya katse, bai ?ara sanin inda kan shi Ya ke ba..

(TASHIN HANKALIN DA BA'A SAKA MASHI RANA>??S')

__________________________________
'?

Yayin Da Chief Owais ke a gar?ame Cikin Wakin Mai girma sharafuddeen, acan Gidansa kuwa ?arfe biyar na maraice dai dai ba ?ari, Dankara dankaran Motocin suka fara shararowa Cikin gidan, kamar a filin daga, Wasu irin Dakarun Sojojine Majiya karfi, masu kirar samudawa, sunyi tsayuwar jarumtaka kan motocin, gaba dayansu Army Combat Uniform ne a jikin su, baka iya ganin fatar su saboda ta ko'ina sun rufe jikin su with protective gear, kowan nansu yana sanye da helmet(hular kwano) Bayan motocin sun yi Parking, cikin zafin nama sojojin dake akan motocin suka diddiro tare da bubbbuWe Cardoors din, U.s Armies ne su ka fito kowan nan su yana a sanye da kayan ya?i sun shirya tsaf.

Ta glass door din Falo, Big guy ya hango su, shima harya kammala shirinsa cikin Isod Combat Uniform.

Wata irin damuwace ta bayyana akan fuskarshi Ganin har su commender james sun karaso amma chief bai dawo daga Villa ba, Ya riga daya san halin turawa basu wasa da lokaci, kuma basa sa6a al?awari, In har suka ji Chief bai nan Bazasu ji dadi ba, zasu ga kamar ba'a Wauki abun da mahimmanci ba ne.

Kusan sau Hamsin Yana danna mashi Call baiyi picking ba, Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, cike da takaici ya furta"Ya salam,! Chief Ina ka shiga! Pls kada ka 6ata mana shirin mu, dan Allah ka Waga kirana, bana so mutanan nan suga gazawar mu"

ya faWa idanun shi akan screen Win wayar shi dake ru?e a hannun shi..
Layin Boss Ya danna ma Kira, bayan yayi picking Ya ce"boss, akwai matsala fa" on the other hand Taj Ya furta"meya faru Omar"?

"Chief Har yanzu bai dawo ba, Ina ta kira wayarsa baya picking, gashi har tawagar su commender sun karaso..."

Hankali atashe Boss Yace"Ya salam, Yanzu ya zamuyi Omar? Ko dai zaka jaraba kiran daddynsa"

"Har layin daddyn nasa na kira baya shiga"

"To ka jaraba kiran layin mommynsa watakil aci sa'a ta Waga"

"Okay, zan jaraba, but pls kuma Ya kamata ku fito Yanzu" ya amsa mashi da toh kafin Ya katse kiran

Yana kokarin kiran Gimbiya malikat Sai ga sako Ya shigo wayar shi da bakuwar number..

BuWe sakon yayi tare da karantawa

_Omar, I won't be able to come; inform every team of fighters. I have canceled the attack_

(Omar, bazan samu damar zuwa ba, Ka sanar da kowace tawaga ta maya?an, Na soke kai farmakin)

Tsabar bacin rai, tuni idanun big guy sun kaWa jajur, kamar zai fashe da kuka baima san sa'adda Ya jefar da wayar Ta fada kan sofa.

jiri Yaji Yana niyar dibar shi adaddafe ya zauna kan sofa, adai dai Lokacin, yaji Motsin BuWe kofar main Falon, zumbur Ya mi?e Yai saurin daidaita nutsuwar shi don kada su gane wani abu...

Waya bayan Waya suka soma shugowa falon, dakyar Ya kakaro murmushi kan fuskarshi ya nufe su da sauri suka sara ma junansu, a mutunce suka gaisa da juna..

Cikin harshen turanci Commender James yace"Omar me kuke Jira ne? Naga banga sauran ba, Ina Chief Yake"?

Fuskarshi da matsananciyar damuwa kamar mara gaskiya sam Ya kasa bude baki Ya basu amsa saboda nauyin maganar da zai furta masu

gaba daya sun fahimci kamar akwai wani abu dake damun shi

"Omar kayi shiru bakace komai ba, Ina Chief dinne"? Yawu mai Waci Ya haWiya, adabarbarce Ya furta"Am..sir.. dama dazu ne daddynsa Ya kira awaya yana son ganin shi, Har yanzu dai bai dawo ba, shi muke jira"

Yamutsa fuska Commender James Yayi da alama ranshi Ya 6aci bai dai ce komai ba.

"Pls mu shuga daga ciki" ya fada tare da nuna masu Cikin falon..

Girgiza kai Commender Yayi"ba zama ya kawo mu ba, bamu da lokacin da zamu 6ata, ka kira Chief kace mashi Yazo Mu tafi"

"Na kira layin shi baya shiga"

"Me hakan ke nufi"? Ya tambaya yana kallon Big guy.

Kafin Ya furta Kalma sai ga Boss Ya na saukowa Down daga second floor, jikinshi sanye da kakin yakinsa karasowa yayi tare da sarah masu commender suma suka sara mashi.

kallon big guy yayi

"Har yanzu baka same shi ba"?
Jinjina mashi kai yai alamar eh..
Cike da damuwa Taj Ya dubi su commender"sir, pls ku ?ara hakuri, watakil wani Uzirinne Ya ruke shi, idan ba damuwa mu shiga daga ciki"

"Taj kuyi kokari ku nemo Chief, idan ba haka ba zamu rasa damar da muke da ita"

ya fada tare da kallon yan tawagarsa"mu je" bin bayan shi su ka yi a kan sofas suka zauna.

ya rage saura Taj da big guy atsaye suna fuskantan juna sam sun kasa magana duk basu ji dadi ba.


"chief bai kyauta mana ba, Ni dama saida raina ya bani da wuya mukai farmakin nan lafiya batare da an samu matsala ba" rai aWan bace Yai maganar.

Kafin Taj Ya furta kalma, wayar Big guy Ta fara ruri, da sauri Ya duba screen din tamkar zai fashe da kuka Ya dubi Taj"mun shiga Uku, General ne ke kira, may be Suma sun shirya tawagar su"

"Omar, ka kwantar da hankalinka, In sha Allah, komai zaifi daidai, Yanzu ka Waga kaji me zaice maka"!


Picking call din yayi tare da kara wayar a kunnanshi bayan sun gaisa
General Noah Yace"Ya ake ciki ne? Na kira layin chief baiyi picking ba, Already mun shirya tawagar Sojojin mu, Umarnin shi kadai suke jira"

yamutsa fuska big guy yayi, da ido Taj yake karfafa mashi gwiwa dakyar Ya furta"Sir, nan badajimawa ba, zakuji daga gare mu" daga haka su ka yi sallama.

Dagowa yayi tare da kallon Taj" hmm kasan meya faru"? Girgiza kai Taj yayi

"Chief ya turo min message, na boye ne saboda inajin nauyin in furta, amma chief Ya soke kai farmakin ayau"

wani irin faduwa gaban Taj yaji arude Ya firta"tayaya hakan zai yiwu Omar? Anya kuwa ka karanta sakon da kyau"


Mika mashi wayar yayi don ya karanta da kanshi bayan ya kammala karantawa Ya kalli Omar"ka yarda Chief ne ya rubuta sakon nan? Girgiza kai Omar yayi"ina kokwanto wlh, saboda Chief kaifi Wayane baya sa6a alkawari in ba wani kakkauran dalilinne zai hana shi zuwa ba, bayan haka meyasa bai turo min sakon da layin shi ba"? Boss yace"uhum ni nasani ay, Allah kadai yasan meke faruwa, gaskiya ?wara muje villa din.."

Da sauri Omar Yaje ya sanar da su commender cewa zasuje Villa donsu ga meya tsayar da Chief, commender Yace suyi kokari kada a bata lokaci.

gudu gudu sauri sauri suka fito daga Falon da karfi Big guy Ya kwaWawa Jami'an dake akusa da parking space Kira Yace su buWe masu mota, agaggauce jami'an suka bude, Taj ne ya fara shiga big guy na kokarin shiga, ba zato ba tsammani, saiga Motar Chief ta kunno kai cikin gidan da gudun gaske kamar zata tashi sama.

wata irin nauyayyar ajiyar zuciya Big guy ya sauke.

"Boss Ga chief din nan" da sauri boss Ya fito daga motar suka nufi motar Chief, motar Na tsayawa Big guy ya buWe mashi car door din, kaitsaye idanunsu suka shiga cikin na juna, Ya jigata ba kadan ba.

Huggin dinsa Yayi kamar zasu koma mutun Waya a kalla big guy ya sauke ajiyar zuciya yafi sau uku..


"Ka tada min hankali Owais, meyasa ka dade? Ina ta kiran layinka baya shiga" ya fada tare da dago da kan shi har saida yadanji gabanshi ya fadi ganin yanayin fuskar Chief sam babu walwala kamar wanda yayi jinya.


Hatta boss Yasha jinin jikinshi da ganin yanayin nasa.

"Wani abu ya faru ne? arude Ya fada Yana kallon shi
Baya Jin zai iya sanar dasu abun da daddynsa yayi mashi.

dakyar ya iya shanye damuwarshi Ya kakaro walwala kan fuskarshi kafin Yace"bakomai, lafiyana lou, bacci ne ya dauke ni acan, kuma na sanya wayar a silent batare da sanina ba" badan sun yarda da maganar ba suka amince.

boss Yace"Sir mu shiga daga Ciki, tawagar su commender sun karaso, Suna a falo suna jiranka, bayan haka tawagar sojojin nigeria suma sun shirya, gaba dayanmu Umarninka muke jira..." numfasawa yayi kafin ya furta"okay Danish da salsabeel fa? Suma sun shirya"?


"Eh, duk sun shirya" ajiyar zuciya ya sauke.

Bayan sun shiga Gidan, atsaitsaye Ya gaisa da su Commender kafin Ya nufi bedroom dinsa, don Ya shirya...

(Tayaya akai Chief Ya ku6uta daga tarkon da Mahaifinsa Ya Wana masa"?)

Bayan da ya kira Mommynsa awaya, ba'a fi minti biyar ba, sai ga hamshakiyar motarsu ta shigo a parking space security din dake driving dinsu yayi parking, A hanzarce Gimbiya Malikat ta fito daga mazaunin baya na motar, Jikinta sanye da tsadaddiyar Lafaya lace, hadadden shade din data sanyawa idanunta ba karamin kawatasu yayi ba, takalman kafarta kadai abun kallo ne, tana tafiya p.a Winta na take mata baya, wata katuwar mace karkarfa, Jikinta sanye da Suit, tasha kitson zane akanta.

Cikin takun qasaita take tafiya, yanayin fuskarta sam babu walwala, saboda Hankalin ta ya tashi da jin abunda Owais Ya fada mata.

Kaitsaye suka Nufi master suite din Mai girma sharafudden.

Abakin kofar Room Win suka dakata da yin tafiya, Gently ta Waura Thumb Winta akan Biometric scanner Win dake jikin handle din kofar, nan take kofar tayi Unclocking Win kanta...

Juyawa tayi tare da kallon P.a Winta, abunka ga masu Izza a jini, da ido tayi mata alamar ta tsaya anan, with respect ta amsa mata da okay ma'am..

shigarta keda wuya kofar tayi locking kanta..

?akin tabi da kallo, kwatsam idanunta suka hango mata shi kwance kan floor kamar matacce kwata kwata baya motsi.

Numfashin shi ne kadai ke fita.. Hankalinta yayi mugun tashi, a sukwane ta zare shade din dake akan fuskarta..cikin sauri ta nufe shi ta zukunna agabanshi ta sanya hannayenta biyu ta dago da kanshi ta kwantar saman laps Winta.

shasshafa fuskarshi tayi muryarta na rawa ta furta"My son! Lafiya ka kwanta kan floor kamar wani mara gata? Meke damunka ne? Owais kana Ji na kuwa?

tariyo maganar da sukayi awaya tayi lokaci Waya zuciyarta, ta raya mata ba baccin lafiya yakeyi ba, saboda yanayinsa yafi kama da na wanda yasha kwayar maye.

a hankali ta kwantar da kan nashi kan floor, ta mike tare da kai idonta kan coffee table din dake a seating area.

Cups ta gani biyu akai, matsawa tayi gaban table din, ta dudduba cups Win, ita dai bata ga komai ba har ta juya zata koma wurinshi kwatsam idonta ya hango mata packet na pills daga gefen table din kiris ya rage ya shige karkashin sa.


Yatsun hannunta na kerma ta dauki packet din ta soma karanta rubutun dake a jikin shi zaro ido tayi saboda ta gane sleeping pills ne.


Hankalinta ya tashi ba kadan ba! tamkar zata fashe da kuka ta furta"why Owais! Why! Me ya hadaka da maganin bacci mai hadarin gaske.." juyawa tayi tare da kallon shi bawan Allah baimasan inda kanshi yake ba..

fitowa tayi daga dakin hannunta ruke da fakitin, P.a na ganinta tay saurin russina mata..

"Duba min maganin nan" ta fada tare da mika mata roban

"Inaso akawo min antidote dinsa Yanzun nan.."

Jinjina mata kai p.a tay, tare da juyowa ta bar gurin, tana atsaye tana jiran ta, badajimawa ba saigata ta dawo hannunta ruke da Injection ta mi?a mata.

Tasa hannu ta kar6a, tare da juyowa ta koma Wakin, kasancewar tana da ilmin abun bata sha wahala ba, bayan ta kamma yi mashi allurar.

Zama tayi gefen shi, tana kallon shi, zuciyarta cike fal da tunin meya faru tsakanin shi da mahaifin shi..

Tsawon mintuna ashirin, Ya fara zubda gumi a jikin shi, kamar an yayyafa mashi ruwa, yatsun hannunsa dana kafafunsa suka fara kerma kamar wanda sanyi ya kama, ajiyar zuciya ta fara saki ganin ya fara dawowa hayyacin shi...a hankali ya bude idanunshi wadanda suka kaWa jawur ya kurawa ceilling din dakin ido kamar ya manta da abunda ya faru.

"Owais,"

jin muryar Mommynasa yasa shi saurin kai idonshi gare ta..wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, da kyar ya tattara karfin jikinshi Ya samu ya mike tare da matsawa kusa da ita, cikin sauri ta rungumoshi kan kirjinta, hannunta daya acikin sumar kan shi..

"My son, are you Okay? ta fada cikin kulawa.


Jinjina mata kai yai alamar eh, bata kara tanka mashi ba, yayi shiru yana faman jan numfashi har saida Ya ?arasa wartsakewa Ya dawo hayyacin shi kafin ta tambayeshi dangane da kwayar maganin baccin daya sha!

"Kai nake sauraro Owais, ka daga min hankalina, kuma meya hadaka da daddynka, dayaja harya kulle ka adakin sa"?

ta fada tana kallon fuskarshi, still bai dago daga jikinta ba.

Cikin disasshiyar murya ya furta"mommy, zanyi maki bayani, amma ba yanzu ba, pls ki kwantar da hankalinki, ba abunda ya faru tsakanina da shi..."

fuskarta ayamutse tace"meyasa bazaka fadamin yanzu ba"?


A gajiye ya girgiza kanshi"mommy, tafiya zanyi, abokan aikina suna jira na, I don't want to lose the opportunity I have, In har banje ba, all our plan will be ruined"

gefen fuskarshi ta shafa da hannunta"shikenan, Na fahimce ka, bazan matsa maka ba, nasan yanayin aikinku, amma pls, ka kula mun da kanka Owais..." lumshe idanunshi yayi tare da jinjina mata kai, ya ruko hannayenta biyu acikin nashi"mommy, Ina barar addu'arki, nasan kinayi min, amma kwanakin nan ina bukatar ?ari akan wadda kike yi min, bama ni kadai ba, hada abokan aikina .." cikin sanyin murya tace"in sha Allah Owais, zanyi maka addu'a, ay bana mantawa dakai, amma kayi ma daddynka magana akan yayi maka addu'a ?

girgiza kai yayi"a'a mommy, nafi bukatar taki, in har kikayi min kamar yayi minne, and pls, bana so daddy yasan kin bude min dakin nan, kiyi min hanyar da zan fita daga gidan nan batare da wani ya ganni ba..."

ta Wan rude da jin abunda Yace amma sai bata kawo komai aranta ba, saboda ta yarda da Wan nata da kanta tayi mashi hanyar barin gidan batare da security officers din da mahaifinsa yasa tsaron gidan sun tuhume su ba.

Kunji yadda akai Chief Ya ku6uta daga tarkon daddynsa
'?


Fitowar Chief daga Part dinsa tayi daidai da fitowar Danish Da Salsabeel.

Gaba Waya Hankulan U.s Army din Ya dawo kan shi, yayi matu?ar jan hankalinsu yadda kasan Diamond a sararin samaniya saboda kyan da yayi Cikin shigar Isod Combat Uniform, Ya rufe fuskar shi da Mask, hadaddiyar sumar kan shi ya daure ta da head ties jelar gashin ta sauka agadon bayansa.

?afafuwansa suna asanye da wasu hadaddun Combat boots ko a kakin yakin bakomai ya sanya ba babu protective gear saboda baya bukatar su.

har ya sauko down basu daina bin shi da kallo ba, tun da Allah ya halicce su basu ta6a ganin Matashin sarauyin da kakin Yaki su kayi ma kyau irin Danish ba ya fita daban acikin su, ya fito a suffar jarumtakarsa, sadaukin namiji mai ji da karfin sa..

Kallo Waya big guy yai masa ya kau da kai gefe, taj kuwa sai da yadan sha jinin jikin shi aranshi ya ayyana ba mace ba ko namiji ya kallesa sai ya burge shi, ina ma amfanin kyau irin nashi ba ilmi wannan ay masifa ne bakaramar 6arna zaiyi ba, a ganinsa kyawun shi ne ke ruWar Unaisah da kuma tausayinsa shiyasa ta ke nema ta zauce akan son shi.

A hankalin Salsabeel Ya ruko hannun Danish acikin nashi.

Bayan sun karasa saukowa down U.s Armies suka fara zuzuta kyawun da kakin su ka yi mashi hatta chief sai da ya yaba, gaba daya suka dunguma zuwa harabar ajiye motocin gidan.

abun daya 6ata ma big guy rai Yana niyar ya shiga Motar da chief zai hau Chief ya ja hannun Danish suka shiga motar, Yaji zafin hakan sai dai Ya hakura Ya shiga Motarsu Taj.

bayan us armies din sun shisshiga motocinsu, da gudun gaske suka fuce daga Estate din saboda Lokaci.

A cikin Mota Chief Ya kira Sheikha Mujeeda, Aransa yana Allah Allah ta Waga Yasan ba ta daga kira in ba an fara tura mata sakon neman izni ba amma cikin ikon Allah tayi picking yadan yi mamaki amma da ya tuna maganar da sukai akan Danish sai ya gane dalilin dayasa ta daga kiransa bayan sun gaisa yace mata Wanta na barar addu'arta zasu yi wani aiki mai hadarin gaske.

yanayin muryarta da damuwa tace In sha Allah zanyi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login