Showing 375001 words to 378000 words out of 413917 words

Chapter 126 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4571

tea ta fara bashi Ya shanye duka kafin ta dauki fork ta soma nannado noodles tana tura mashi abaki yana ci.


sam bata lura da Halin da Aneelerh take aciki ba, sai surutu takeyi tana fadin"Aunty Aneelerh ba zaki ci bane,? Shiru taji bata amsa bata ba, juyowa ta danyi tare da le?a fuskar ta, gabanta ne ya faWi ganin tsantsar damuwa akan fuskarta, idanunta sun kaWa jawur.

Da karfi zahra ta furta"Aunty Aneelerh"! Firgigit tayi tare da kallonta razanar da tayi yasa Zahra jin fargaba.

Adabarbarce ta furta"am...um...zahra.. Har kin sa mashi kayan..." a ruWe zahra ke kallon ta duk tabi tasha jinin jikinta..

"Aunty Aneelerh, Lafiyarki kuwa? Kinga yadda idanunki suka kumbura, kumatunki sun yi ja, kamar kinyi kuka, gaba daya ma kin sauya min kwata kwata babu nutsuwa atare dake"

dakyar ta daidaita nutsuwarta cikin sanyin murya tace"bakomai wlh, lafiyana lou, kawai tunanin duniya ne..." girgiza kai zahra tayi"wlh kallo daya mutun zaiyi maki ya fahimci baki cikin nutsuwarki, auntyna in akwai abunda ke damunki, ki fadamin dan Allah sai mu nemi mafita a tare..."

murmushi ta danyi"Zahra ki yarda kawai babu komai" gyaWa kai tayi"shikenan, ga noodles din nan ki ci pls, kada ki zauna da yunwa ni zan tafi gurin aiki har na kusa yin late"


"Nagode da kulawarki zahra, ki kula min da kanki" tana murmushi tace"kema haka" kar6ar junaid anila tay don taci gaba da ba shi abincin.

Zahra Harta kusa ficewa daga dakin ta tsinkayi muryar Aneelerh"Uncle na nan ne"? Zahra bata kawo komai aranta ba tace"Eh, yana nan dakinsa"

"Okay, " fuce wa zahra tayi daga dakin..

Bayan tafiyar zahra, da rabin awa ta fito Hannunta dauke da baby junaid ta nufi dining area, tunkafin ta karasa ta hango mutanan gidan gaba daya sun hallara akan dining chairs zahra ce kadai babu atare da su.

tsayar da idanunta tayi akan Uncle dan iya daya hakimce kan kujera Ya ?wama wani uban glases akan idanunsa, Ya tasa farfesun yan ciki shake da plate sai sharbar romo ya ke yi kamar ?aramin yaro, yanayin fuskarta ne ya canza zuwa matu?ar bacin rai, fusata, da tsantsar tsana Aranta ta furta Mugu bashi da kama, Cike da rashin kuzari ta karasa cikin girmamawa ta gaishe da su da fara'a suka amsa mata, mami ta mika hannu ta kar6i junaid ta zaunar da shi kan laps dinta nan fa ya fara zuba mata shagwa6a.

Tun da ta zauna mami ta yi serving dinta duk cokali daya idan tay sai ta dago ta kalle shi gabanta sai faduwa yakeyi, hakanan yaji kamar Ana kallonsa yana kokarin dagowa tay saurin kawar da idanunta, a dabarbarce ta shiga tura chips abakinta, Mayar da kansa yai ganin ba abunda ya zata bane.

"Aunty Anila ya maganar komawar Junaid School ne? Tun da yaji sau?i ya kamata amaida shi, karatu yana ta wuce shi"

"Zahrama ta tambayeni dazu, in sha Allah sati mai zuwa zai koma"

Mahboob Yace"Allah Yakaimu lafiya" ta amsa da ameen

Junaid dake zaune saman Laps din mami tana bashi abinci tuni ya haWe fuskar shi muryarshi da shawaga6a yace"Allah ni bazan koma ba, dodo zai Wauke ni in naje.." dariya su ka yi Abie yace"jikana mai abun ban mamaki! Wani irin dodo ana zaman lafiya"? Yana faman zumbura baki yace"wanda Ya kashe..." a firgice Anila tay sauri katse shi da karfi ta furta"junaid! Ya isa haka, kamanta abunda na fada maka" da sauri ya rufe bakinsa da tafin hannunsa, dariya su ka yi inka cire Uncle Waya wanda hankalinsa kwata kwata baya akan su, Anila kam Ajiyar zuciya ta sauke ganin ba su Wago komai ba sun maida abun wasa, agogon hannunsa ya duba kafin ya mike Abie yace"har za'a fita"?

Uncle yace" Yau hutu nake har gobe ina gida" Ya fada tare da juyawa ya nufi bedroom dinsa.

Mami tace"wai nikam Ina zahra ne? Ko har an tafi aikin"?

Ummi tace"eh tun dazu ta wuce, tazo tayi min magana cikin bacci naji ta" ummi tace"nima kam naso naji ta tana knocking yau fitar wuri akayi kenan, Abie Yace"zahra badai hankali ba, bata iya tafiya aiki batare dabi kowannan mu tayi mashi sallama ba" Mahboon yace"dama tayine don afada" dariya sukayi, Ummi tace"na fahimci kana kishi kaji an yabi zahra" ta6e baki yayi Anila dake kallonsu daya bayan daya wani irin tausayin su ne Ya kamata.


A Obie Estate kuwa, Yau shirye shiryen Tarbar baba Obie su ke yi, kasantuwar yau ne ranar da zasu dawo daga Lagos, maids din gidan tun safe suka fara gudanar da aikinsu.

Tsaye take a gaban dressing mirror tana Wan jujjuya jikin ta, wani hadadden Saree ta sanya launin ja mai adon duwatsu sai sheki suke, yayi bala'en yi mata kyau kamar amarya, ta zuba adon Zabba da awarwaro a hannayen ta, ga wasu jerin gemstone necklaces a wuyanta masu daukar ido, ta saki doguwar sumar kanta a abayanta baka wulik sai sheki take, A hankali take kokarin gyara Earrings din dake a kunnanta, yayin da idanunta ke kallon cikin madubin, Ita kanta ta yaba da haWuwarta, Sareen jikinta ya nadu sosai ya zauna mata, Wan light makeup tay akan fuskarta tayi kyau, daddaWan ?amshin turarenta dana bakhhoor burner din data Kunna Ya gauraye iskar Wakin da wani irin kamshi mai dadin shaka.

Murmushi ta dan saki har dimple dinta Ya lotsa, ta fito sak ba'indiyarta ta usili, wani irin annurin farin ciki ne ya bayyana akan fuskarta, bakomaine yasa ta farin ciki ba face murnar dawowar Pravin Jiya sunsha waya da shi yana fada mata irin kewarta da yai yace mata ta shirya mashi kanta don idan ya dawo sai ya fanshe kwanakin da baya nan.

Cikin harshen indianci ta furta"Ina jiran ?arasowarka my lovely husbad"

ta faWa tana yar dariya.

High heels ta Wauko ta zura a kafafunta ta fito ta nufi kitchen don ta duba masu aikin gidan.

*HAJIYA SARATU*


Tana a kwance kan katafariyar bedmatress dinta tayi nisa a baccin ta, Ta wawware kafafuwanta daya tay dama daya tay hagu sai jan minshari takeyi, Sleeping gown ce a jikin ta, zanen kitson da ke akanta ya kara fiddo da kyawun fuskarta duk da babu annuri akanta.


Iphone dinta dake ajiye saitin kunnanta ce ta fara ruri da karfi sautin ya addabi kunnanta, har saida ta fara kokarin farka cikin magagin bacci da bacin rai ta dinga katse kiran almost 4 times a na hudu ne ta fusgo wayar ta kara kunne rai a6ace ta furta"wai wanene ke son takura mini ne"?

"Jatuminki ne" ras taji gabanta Ya fadi jin muryar baba Obie, a rude ta zabura ta mi?e fuskarta ya amutse cike da jin nauyin furucin da tay sam takasa magana saboda kunya.

Murya na rawa ta furta"baba i'm sorry, wlh bansan na furta ba, Kiran wayarka ne ma ya tashe ni daga bacci bansan kai bane ka kira..."

bata kare maganar ba ya katse ta"Auta Ko da bani bane abun da kikai ya dace? Idan abokan aikin ki ne fa"?

"Baba ka gane mana, daga bacci na tashi, ban gama wartsakewa ba"


"Pravin bai fada maki yau zamu dawo bane"? Yamutsa fuska tay"ya fada min"?

"Shi ne kuma kike ta baccin asara, ba zaki tashi kije ki gyara kanki ba"?

HaWe rai ta yi "baba wani irin gyara kuma"?

sautin dariyar shi tajiyo"its Okay, yanzu haka muna akan hanyar zuwa airport"


"Okay, zan zo in tarbe ku, Yanzu zan shirya Allah ya kawo ku lafiya" ya amsa mata da Ameen kafin sukai sallama.

Saukowa tay daga gadon tana ?u?uni kan maganar gyara da baba obie yai mata.

"Haba Akan me zan takura kaina, Gyara ya wuce mutun Ya dawo ya iske iyalinsa daya bari cikin koshi lafiya, Nifa ba baiwar Namiji bace ehe.." ta ?arashe kukunin tare da bude toilet door ta shige.


Lokacin da ta ?araso Kitchen din kamshin abinci ne ya daki hancin ta har can cikin makoshinta kamshin ya ratsa.

Sam basu lura da zuwanta ba, gaba daya Hankulansu na akan girke girken da sukeyi.

Gyaran muryar da tay masu"Aikinku na kyau" atare suka dube ta, kamar yau suka fara ganinta tayi masu kyau, murmushi suka saki tare da gaishe da ita cikin girmamawa, da fara ta amsa masu.

"Ya kamata kuyi sauri ku kammala, sun kusa karasowa"

Sofia tace"in sha Allah kafin su karaso zamuyi kokari mu gama"
Hajjaty tace"yanzu dame dame ku ka kammala"? Safa ce ta lissafa mata.

"Okay, naji kince hada dambun Nama, pls Ki dan zuba min shi tare da juice, wlh yunwa nake ji" ta fada tana shafa cikin ta, dariya sukai cikin raha tana lura da satar kallonta da sukeyi tasan da wuya in basuyi gulmarta ba kamar ko ta sani gulmace ke cin su.

Bayan Safa ta zuba mata dambun naman a plate ta haWo mata da glass na juice a kan madaidaicin tray ta daura mata tare da muka mata tasa hannu ta kar6a tare da yi mata godiya ta juya ta fuce.

fitarta keda wuya Abla tace"wannan gayu haka hajjaty, Kamar wadda zataje gasar kyau"? Ta fada baki asake, sofia tace"ni dai wlh tana burgeni, inason mace mai tsafta da iya daukar wanka, amma abunda bangane ba Wa takeyi ma kwalliya ne? Naga dai ba wani guri take zuwa ba kullum tana a gida"

"Kun cika sa ido, Nifa bansan gulma wlh, naga dai ba yau ta fara yin kwalliya ba" safa ta fada tana jifarta da harara.

"Ba yau ta saba ba amma na yau yasha banban, yau fa baba Obie da pravin zasu dawo meyasa zata ca6a adon nan sai kace wadda zata tarbi Mijinta, ko dai hajiya saratu batay gayun nan ba bana tunanin ma ta tashi daga bacci, sai ita zakakka abun nata na nema ya wuce gona da iri ya kamata ta tsaya a matsayinta na yar aiki" Ta kare maganar tana hura hanci
Fashewa sukayi da dariya..
"Pls Ya isa haka Sofia, nasan meke damunki, Bakin cikine da hassada, Saboda kinga hajjaty Allah ya zuba mata ruwan kyau gashi tafi ki matsayi shiyasa kike kishin ta"

tsoki Sofia taja"Allah ya kiyaye inyi mata hassada Ni kawai na fara zargin akwai wanda takeso ta mallaka agidan nan shiyasa take caba ado nan don taja hankalin sa, In kuwa hakan ta faru mu zamu zama bayinta, kuna gani dai haka Harriet ta aure Sir mubarak to wai mu ko bamu da farin jini ne a gurin mazan family din nan" ..fashewa sukayi da dariya.

"Duniya tayi maku dadi, wato Na lura gaba daya kun manta da marwa" acewar Abla, Atare suka hada baki gurin furta Alah sarki marwa ko awani hali take? Safa tace"jiya nayi waya da innarsu ta fada min jikin nata da sauki har ta fara kokarin yin magana"
Sofia tace"baiwar Allah tadaiji jiki sosai, Alah ya bata lafiya, ko ta samu ta dawo bakin aikin ta, In sha Allah nima da anjima zan kira inji ya jikin nata"

_____________________________________
'?

A hankali take tafiya cikin takun dattako, wata hadaddiyar egyptian abaya ce a jikinta mai tsadar gaske, tay rolling head scarf, yayin da Idanunta ke amanne da farin glases, Ko hoda b????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? !ata shafa ba amma ba ?aramin kyau ta yi ba, hannunta daya na a ruke da purse dinta, ga wani daddadan fragrance dinta dake tashi.

Har zata gifta idanunta suka hango mata hajjaty, wani uban burki ta ci ganin yadda ta caba ado kamar wata amarya.

"Ke zonan" ta fada da Waga murya, hajjaty bata san da zamanta ba, har takusa shiga part dinsu na maids ta tsinkayi muryar Hajiya saratu rass taji gabanta Ya fadi arude ta juya tana kallon ta, da hannu tay mata alamar tazo.

Hankalinta ya tashi don tasan kiran hajiya saratu ba alkhairi bane.
Jiki asanyaye Ta nufe ta aranta tana ta ambaton la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin.
Koda ta karasa nesa da ita ta tsaya cikin sanyin murya tace"gani aunty saratu" harara ta galla mata har saida tasha jinin jikinta.

"Uban wa kikai ma wannan adon"? sunkuyar da kanta kasa tay, aranta ta furta"mijinki nayi mawa, a fili kuma tace"Aunty, kamar dai yau kika fara ganin nayi kwalliya"? Ji tay kamar ta kwasa mata mari saboda fusata"karki kuskura ki kara kirana da sunan aunty, in banda munafurci sai da kika saisaici ranar da kikasan mijina da baba zasu dawo tukunna kika caba adon nan ko? A cikin su wa kikai mawa"? Ta fada tana cije lips dinta hadi da matsowa kusa da hajjaty, jikinta sai kerma yake tray din hannunta kamar zai kife kasa, Cikin rawar murya tace"Allah shine shaidata, Ni banyi kwalliyar nan don daya daga cikinsu ba, nayi ne saboda in burge kaina" idanunta cike tab da kwalla ta kare maganar.

Da hannu hajiya saratu ta cafko pallu din sareen data laga kan kafadarta..

Ta soma goge mata kwalliyar fuskarta ran hajjaty ya 6aci sosai duk ta cabe mata kwalliyarta.

Murmushin mugunta hajiya saratu ta saki da alama ta manta da abunda hajiya laura ta fada mata"Idan kin koma Waki, Ki cire sareen nan, Yau nafi son naganki cikin uniform na ma'aikatan gidan nan fatan kin fahimce ni" jinjina mata kai tay"Toh"
"Yawwa zaki iya tafiya" har zata juya ta kuma kiranta
Da yatsa ta nuna tray din hannunta"meye a ciki"?
Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"dambun nama ne"
"Samun wuri, Wato ke har kin riga masu gidan dandana girki ko? Ta fada tare da kai hannu ta buWe plate din Ta duma hannu ta dibi dambun naman ta tura abaki tana tauna, bakinta a cunkushe tace"kafin in dawo kisa a shirya min Lunch dina, komai da aka dafa za'a zuba min.." ta fada tare da kara dumbuzar dambun naman ta tura abaki, kafin ta dauki Juice ta kur6a, duk hajjaty tana atsaye tana kallonta.

Tsoki taja"duk na bata hannuna da maiko ni da zanje airport tarbo mijina" cikin sanyin murya hajjaty tace"yakamata ki wanke" ta fada tare da nuna mata Sink din dake a kusa da in da suke.

harara ta galla mata"nifa komi zakiyi ba zaki taba burgeni ba.."

Ta fada tare da zaro hanky daga purse dinta ta mutsustsuke hannun dashi duk don kada hajjaty taji dadin ta bi shawarar ta, juyawa tayi ta nufi hanyar fita daga falon.


Binta da kallo Hajjaty tayi har ta bace ma ganinta, murmushi ta saki ta danyi mamaki da ta ci abun hannunta musamman a kwanakin nan data lura kamar batason ko hanya su hada, tabbas ta bata mata rai amma har yau Allah bai sanya mata tsanarta ba, Ita dai tana so su dinga mutunci da juna.


Juyawa tayi jiki asanyaye ta nufi dakinta.

kaitsaye hajiya saratu ta nufi hamshakiyar motarta, a hanzarce Officern da zaiyi driving dinta yai hanzarin bude mata cardoor har ta zura kai zata shiga muryar Twins ta katse mata hanzarin ta"Mommy" gently ta juyo tare da kallonsu, yayin da suke fitowa daga Entry hall sun dauki wankan suit kamar a turai.

Murmushi ta sakar masu, Suna karasowa ta haWa su duka tayi hugging dinsu gwanin ban sha'awa..

Bayan sun gaishe da ita ta amsa masu tare da cewa"my twins Ina zuwa haka? Yau dai ba aiki na sani ko za'a fita yawon bude ido ne" zaid yace"No, daddy ya fada mata time da jirginsu zai karaso shiyasa muka shirya don muje tarbo su"

"Kunyi tunani mai kyau, Nima yanzu haka airport din zanje, me zai hana mu shiga mota dina"

Bayan sun shiga suka sanyata tsakiya suna zaune a gefe da gefenta.


Sai da motarsu ta haura kan titi kafin ta dubi zayn"ya zahra? Two days ban tuntube ta ba, amma nasan kai kana waya da ita"

yamutsa fuska yai a dakile ya furta"may be tana lafiya" wani kallo ta wurga mashi"oh baka da tabbaci ma? Thats mean baka kiranta awaya"!


"No ba haka bane mommy, Kinsan yanayin aikina bakasafai nake samun lokacin yin waya ba" girgiza kai tay"banji dadi ba, yakamata kana bata kulawa zayn, nan bada jimawa ba zata zama matarka" daure fuska yai, zaid sai faman kunshe dariya yakeyi..

"Mommy hannunki kamshin nama yakeyi ko hancina ne" Ya fada tare da ruko hannunta Yakai saitin hancin shi yana shinshinawa.

"Kai Zayn Allah ya wadaran naka ya lalace, ka cika sa ido" ta fada tare da dago purse din hannunta, ta kwala mashi akai" dariya suka sanya gaba dayansu da alama dai suna acikin farin ciki.

__________Hajjaty___________


Bayan da ta dawo daki, zama tayi daga gefen gadonta, ta ajiye din akan table din gabanta, A tsanake ta fara cin dambun naman fuskarta dauke da murmushi wato abunda hajiya saratu tay yabata dariya, aranta ta ayyana in da ni muguwace kamar yadda kike fadi wlh da abinci kadai zan iya kashe ki saratu.

Wayarta ce ta soma ringing, tayi azan Pravin ne cike da zumudi ta janyo wayar daga kan pillow ganin ba pravin bane yasa murnar ta koma ciki amma taji dadi data ga kiran daga kayin marwa ne.

Picking call din tay tare da kara wayar a kunnnata.

"Ina wuni inna, ya jikin marwan"? Bata kare maganar ba, Muryar Marwa ta katse ta da cewa"Aunty Hajjaty Nice marwa dakai na"

Da mamaki ta furta"Wai dagaske Marwa kece? Allahu akhbar amma natayaki murna naji dadi da bakinki Ya bude Marwa Ya jikin naki"

"Da sauki, yatsun hannayena ma sun warke har abinci Ina ci dakaina" tsantsar farin ciki ne Ya cika hajjaty"Alhamdulillah Ya Allah mungode maka, Allah ya kara maki Lafiya marwa, Allah ya kara tsare ki daga sharrin Aljanu".

"Ameen aunty, nagode da kulawarki agare ni" shiru sukayi na dan wani lokaci kafin hajjaty tace"kinji kwana biyu ban kira na tambayi lafiyarki ba, wlh na shiga busy ne amma kina araina, bari na hada ki da su Abla ku gaisa" har ta yunkura zata mike Marwa tay saurin katse mata hanzarinta"Aunty akwai wani abu da nake son

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0