Showing 327001 words to 330000 words out of 413917 words

Chapter 110 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4538

kada jawur ta dube shi

Wani irin ciwon kaine Ya far mata...
Cikin disasshiyar murya tace"daddy, kada ka raba ni da Danish, zan iya rasa raina.."


Kwata kawata baya son tana fadin zata rasa ranta akan Danish, Ranshi baci yake kamar ya hadiyi zuciya, kuma yana akan bakanshi bazai janye ba.


"I'll think about it, Yanzu bana son duk wani abu da zai Waga hankalinki, kwanciyar hankalinki nakeso..." hankalin ta ya Wan kwanta, gani take kamar daddynta zai duba mata ne.

"Amma daddy, baka son Danish ko"? Girgiza mata kai yai"Ina son shi Unaisah, Kuma ina jin tausayin rayuwar shi, maganganun da kikaji nayi Wazu rainane Ya 6aci bawai don ina nufin hakan ba, ni kawai banaso kina sakar mashi jikin ki ne"

cikin kwantar da murya ya faWa.

Ruko hannun shi tayi a cikin nata"daddy pls ka min alkawarin ba zaka raba ni da shi ba"!

Dafe kai yai da tafin hannun shi, ji yake kamar ya kifa mata mari saboda haushin da yake ji in ta ambaci sunan Danish

"Kina so In amince ma Soyayyarku?In kuma ba shi damar Auren ki"? jin wannan maganar daga bakin daddyn nata yasa ta mi?e zaune cike da zumudi tace"Eh daddy..."

Numfasawa yayi kafin yace"Zan baki Umarni, If you do what I say, I promise to fulfill your dream of marrying your choice".

gabanta ne ya Wan faWi duk da batasan umarni da zai bata ba, taji fargaba sosai..

"Daddy, wani irin Umarni ne? Ka faWa min in sha Allah zan yi maka biyayya" ta faWa cike da jin fargaban amsar da zai bata..

Ido cikin ido su ke kallon jun.

"ki bashi Umarnin, ya yi mana jagora zuwa Gidan Kurkukun ?addara..."

wata irin razananniyar faduwar gaba taji, kamar zata zauce ta daddafe kanta da tafukanta dama saida ranta ya ayyana mata abun da zai umarce ta da tay...

"Inaso in tabbatar da kaunar da ya ke yi maki, ta hakanne zan gane shin jarumtakarsa takai in mallaka mashi lu'u lu'u na?

ya faWa yana kallon idanunta da suka rune zuwa Jajawur kamar Jan gauta.

Cikin shesshekar kuka tace"daddy, pls ka bani wani umarnin daban, wannan is too hard for me! I can't force him I don't wanna put his life in danger"


Kwata kwata babu annuri akan fuskarshi, ya haWe rai sosai saboda yana son ta Wauki maganar shi serious

"Unaisah, karna kuskura na ?ara ji kin furta kalmar kada ki jefa rayuwarsa cikin hadari! Ke ba musulma bace? Ba kiyi imani da Allah ba? Ko baki yarda da ?addara ba? Ko kuwa ?arancin tawakkali ne ke damunki"? Runtse idanunta tayi tana jin wani iri yanayi a zuciyarta mara dadi

"Ba haka nasanki ba Unaisah! Kin canza min! Ina zuciyar imaninki take? na fahimci so ne ke nema ya rufe maki ido, Unaisah kin manta mummunar ?addarar data rabamu? Kin ta6a tunanin zaki ku6uta daga kurkukun ?addara? Kin ta6a tunanin zamu sake haWuwa? Ikon wanene yin hakan"?

In a weak voice tace"Allah"

"Toh inaso ki sanya ma ranki, duk wani abu da zai faru da shi mu?addari ne daga Allah, tun zuwan shi kurkukun kaddara bazai hana Allah ya jarabce shi da wata ?addarar ba, har kwarama yaje can yayi jahadi gurin ceton rayuka...."

nasiha ya cigaba dayi mata tun bata fahimtar shi har ta fara yin amanna da maganar shi...

"Daddy, ni damuwana he's not a muslim, banson ya mutu batare daya kar6i kalmatusshada ba"

ta faWa hawaye na bin fuskarta...

Ruko hannayenta yayi acikin nashi ya ru?e su gam kafin yace"In sha Allah zai musulunta Unaisah, idan sheikh imam yazo zamu nemi taimakon sa"

"Amma daddy, nima ina neman alfarma agurinka"!

"Wace alfarma"?

"Ku tafi dani, Nima ina son in bada gudummuwata..." waro idanu waje yayi aranshi ya ayyana bazai yiwu ba, amma a fili sai yace"Zan yi magana da chief, kinsan dokar aikinsu babu mace, amma in har ya amince zamu tafi dake" ajiyar zuciya ta Wan sauke, fatanta Allah yasa Chief ya amince mata, dalilin dayasa ta za6i tabisu saboda abu biyu, na farko don ta kashe Jan wuya, duk da batasan wanene shi ba, kuma batasan ko yana Waya daga cikin members na kurkukun ?addara ba, sai dai taji aranta dakyar in ba ya cikin Elders, abu na biyu donta ba Danish kariya, koda Ajali zai riske shi, toh su mutu atare zaifi mata kwanciyar hankali.

Kiraye kirayen Sallar isha'i da aka fara yi ne, yasa Taj mi?ewa ya dube ta"zan tafi, kiyi kokarin aiwatar da umarnina, in sha Allah silar biyayyar da zakiyi min, ba zaki ta6a danasani ba, saima ya zama silar farin cikin ki na har abada" cikin sanyin murya tace "in sha Allah daddy, zanyi masa magana, duk yadda mukai zan sanar dakai"

"Gobe da safe, in tashi da labari mai dadi" jinjina mashi kai tay

Mi?a mata hannu yayi da sauri ta sauko daga kan gadon ya rungumota, yana ?ara lallashinta da bata baki har saida ya tabbatar taji hudubarshi kafin su ka yi sallama da juna kamar karsu rabu..

_________________________________
'?

Idan muka koma bangaren Benazir sam ta kasa walwala, maganganun Zaki sun tsaya mata arai, sun hana ta sukuni gani take kamar batayi masa adalci ba, tayi kuka sosai har zazza6i saida ya lullu6eta, Wlh Yabata tausayi bata ta6a ganin rauninsa ba sai awannan lokacin, yayi mata taimakon da har abada bazata ta6a mantawa da shi ba, ya bata lokacin shi! Ya bata kulawarshi! Ya bata ci da sha Da suturu harma da aikin yi, ya kuma ruketa agidan sa na tsawon shekara goma sha bakwai bai ta6a goranta mata ba, sun shaku da juna, ya zama tamkar uba agare ta!

babu wanda yasan wani abu dangane da zuwan Zaki, daga Ita sai Alhaji musa suka san da maganar, fatanta Allah yasa kada Uncle musa yayi ma Daddynta maganar don batason duk wani abu da zai da?ile maganar komawarta dakin Mijin ta, taso taji daga bakin uncle me Zaki ya fada masu sai dai takasa ma tunkarar shi saboda bata son taji abunda zai hana runtsawa.

Har kiran Layin Zaki tayi don ta kara bashi hakuri amma kwata kwata kiran baya shiga..

Tunani ta somayi me zatayi don ta saka mashi?

Zuciyarta ta bata amsa da cewa me zai hana ta hada shi da Aneelerh! aranta kuma ta ayyana zaiyi wuya su sasanta cos zaki bazai kara gangancin fadawa tarkon son macen da kaddara ta rabata da mijinta, kamar dai ita =???

_________________________________
'?

Har wuraren ?arfe shaWaya na dare bata runtsa ba, saboda matsananciyar damuwar data addabi zuciyarta, sai faman juyi takeyi kan matress kamar me fama da ciwon ciki, maganganun daddynta dana Salsabeel ne suka dinga dawo mata cikin kwalwar kanta, bata san ya zatayi ba, bata da wata mafita daya wuce ta amsa bukatarsu sai dai tana jin tsoron tayi silar jefa rayuwar man dinta a cikin haWari amma idan ta tuna burin da take da shi na kashe jan wuya, da kuma nasihar daddynta sai taji kamar ana kara mata kwarin gwiwarta.

*CHIEF OWAIS*

Bacci ya ?auracewa Idanun shi, Ina zai sa ran shi yaji dadi? chief irin mutanan nan ne waWanda idan suka kwallafa rai ga abu suka saka buri da naci da komai in har ba su ga sun Cimma nasara ba to fa hankalin su bazai ta6a kwanciya ba..

Ya ?untata kanshi Ya hana zuciyar shi sukuni, baisan taya zai 6ullowa lamarin ba, Danish Yana nema Ya zamar ma shi ciwon kai...

Yayin da yake wannan tunanin safa da marwa yake a tsakar bedroom Winsa, boxer short ne kaWai a jikin shi, fuskarshi a yamitse ba annuri..

Jefi jefi in damuwar ta addabe shi tafin hannunsa yake cusa cikin sumar kanshi ya yamutse ta kamar Wan mahaukaci wani lokaci da karfi ya ke bugun iska da hannayen shi.

Phone ringing dinsa ne ya katse hanzarin shi, kamar bazai duba mai kira ba, zuciyarshi ta takura mashi akan ya duba, juyawa yayi a sukwane cikin rashin kuzari ya dauko wayar dake aje kan mirror chair, yayi mamakin ganin almost 16 missed calls, picking call din yayi tare da kare wayar a kunnan shi yai shiru yana jiran jin me zaice


"Owais, ya ake ciki game da kai farmakin?..."

"Only a few days remain"


"Ko zaka Iya faWamin menene shirin ku a yanzu ni kuma zan ?arfafa maku gwiwa"

Har yanzu bai yarda da mutumin ba, shi mugu bashi da kama, zai iya bayyana ta suffar mutanan kirki don ya shiga jikin mutun...

"I'm sorry to say, bazan iya faWa maka ba, in har dagaske kana son taimakona ba dole sai kaji me muke shiryawa ba"

"Hakane, Ka faWi gaskiya, Owais, shawarar da zan baku shi ne, Ku sanya malaman addini su tayaku addu'a, sannan ku ma iyayenku magana su tayaku da addu'a, ku kuma yawaita sadaka ga marayu da mabu?ata suma su tayaku da addu'a, ku nemi kariya daga wurin Allah, in sha Allah badai mutun da Aljan ba sai Allah...." bai ta6a jin 6oyayyan mutumin ya burge shi irin na yau ba yaji dadin shawarwarinsa

Har ya buWe baki zai yi mashi godiya yaji Wuff yai rejecting call din..


Hakanan Yaji Yana ra'ayin ganin Unaisah, wall clock Ya kalla ?arfe 11 na dare, yasan i war haka tayi bacci


Jaraba kiran layinta yayi, tana fara ringing ta yi picking yayi mamaki bai zata zata Waga ba ..

Kara wayar yayi a kunnan shi yama rasa me zai ce mata.

Sanyayyar muryartace ta ratsa kunnanta

"Barka da dare chief, ka wuni lafiya"?

"Why are you still not sleeping"

"I woke up for the night prayer" yaji dadin jin hakan

"Okay, if you dont mind I want you to bring me the girl's backpack"

"Toh" rejecting call Win yayi, sai da yayi unclocking Win kofarsa don ta samu damar shigowa, kafin ya shiga bathroom don yayi wanka.

Saukowa tayi daga kan gadon ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta ta cikin madubin.

Silk Pyjama ne a jikinta, riga da wando launin blue sky, rigar tana da dogon hannu sun yi matu?ar yi mata kyau.

Lallausar Curly hair dinta tabi da kallo, duk Ya har gitse saboda rashin kwanciyar hankali ta manta when last tayi fixing dinsa.

Fragrance set ta Wauko ta feshe ko'ina na jikinta da shi, cikin kankanin lokaci daddadan kamshin turarenta ya buWe Wakin

ta Wauko veil ta yafa ma kanta kafin ta saka flat shoe a kafarta.

Back pack din ta dauko, ta daurata kan mattress, ta curo wasiyar da Unaizah ta bata guda biyu ta boye su cikin diary Winta, don bata jin zata iya rabuwa da su tunda kamar amana ta bata, tafison ta dam?a ma iyayenta da hannunta.

Goya jakar tayi abayanta, ta fito daga Wakin, gidan shiru babu kowa a falon alamar duk sunyi bacci adakunansu..

Bata nufi ko'ina ba sai Wakin Chief, tana ?arasa bakin kofar takai hannu zatayi knocking sai taji ?ofar ta fara kokarin buWe kanta ta Wanyi mamaki

Almost 3 times tana yin sallama ba'a amsa mata ba, ta kutsa kai ta shiga ciki, bata ga kowa ba, sai dai taji sautin safkar ruwa daga toilet dinsa, wurga ido tayi tare da kallon glass wall din toilet nasa yayi duhu sama ka dai take iya gani..

Gajiya tayi da tsayuwa, ga wata kasala da take ji, wasa wasa ta fara gyangyaWin bacci, har ta saki backpack din hannunta ta fadi kan floor ba tare data lura ba..


Lokacin daya fito waist dinshi Waure da towel fari kyal, fatar shi tayi freshi danshin ruwa ya ji?ata...yana kokarin Waga kafa ya nufi dressing mirror ba zato ba tsammani ya hango mutun kwance kan rug kamar an jefar da ita a gurin ta baje sai sharar bacci take yi, ga backpack Winta yashe gefe Waya...

Yayi mamaki cos bai tsammaci zai iske ta adakin ba, ya daisan ya cire security din kofar, abun da ya fi daure mashi kai ta yadda bacci yayi awon gaba da ita akan rug dinsa, kamar wadda tasha kwaya..

Walking slowly ya nufi rug din Ya zu?unna daga gabanta, ya nutsu yana kallonta, yanayin yadda take fitar da numfashi cikin nutsu kirjinta na sama da kasa ba karamin tafiya tayi da imaninsa ba, kamar jinjira la66anta sai kerma suke.

Sai yanzu yayi tunani me ya hanata bacci da wuri? tabbas akwai damuwa aranta wanda silar hakan ta kuntata kanta ta hana idanunta bacci shiyasa da tazo dakinshi baccin yaci karfinta har yai awon gaba da ita batare da sanin ta ba..

Baya jin zai iya tada ta daga baccin, bai shirya katse mata jin dadin ta ba, baccin da takeyi sauki ne agare ta.

Yanke shawarar canza mata gurin kwanciya yayi, A hankali ya sanya hannayen shi biyu ya tallabota ya dago da ita tare da mi?ewa Ya nufi katafaren gadon shi da ita, kusan itace mace ta farko da zata kwanta akan shi,

A tsakiyar mattress din Ya shimfidar da ita, duk da baccin da takeyi hakan bai hanata jin dadin sauyin gurin kwanciyar da akayi mata ba, numfashinta har canzawa yayi, lallausan duvet Winsa ya janyo ya lullu6e ta shi har zuwa kan kirjinta, kasa janye idanun shi yayi daga kallon ta gaba Waya ya shagala da kallon kyakkyawar sexy face dinta wani irin yanayi ya fara ji a jikin shi hakan yasa shi saurin mi?ewa Yabar gaban gadon, badan bai yarda da tsoron Allahn shi ba sai don gujewa sharrin shaidan...

Can cikin bacci kunnuwanta suka soma jiyo mata daddaWar kira'ar karatul qur'anin shi, kamar amafarki take sauraron karatun a lokaci yana zaune kan darduma jikinshi sanye da farar jallabiya, raba dare yayi yana kai kukansa gurin Allah, bayan ya kammala ya buWe kur'ani yacigaba da karantawa.

Yana tsaka da karatun, tayi wani kwakkwaran juyi cikin bacci ta dinga mirgino kiris Ya rage ta kundumo ?asa, yana gani yai hanzarin mi?ewa yai saurin tallabota da hannayen shi biyu..

Zu?unnawa yayi gaban gadon ya bi ta da kallo, ganin kamar tana kokarin buWe idanunta, biji biji ta fara ganin kamar mutun a kusa da ita aranta ta ayyana anya ba mafarki take ba"?

Murya na rawa ta furta"Batool" shiru ba'a amsa mata ba

"Aunty ummi" still ba amsa mata ba

"Sajeed" nan ma shiru ba'a amsamata ba

Murza idanunta tayi da yatsunta, don ta samu damar ganin wanene...wani irin faduwar gaba taji lokacin da idanunta suka washe ganinta ya dawo normal, kokwanto ta farayi anya Chief ne? Ko dai mafarki ta ke ba? Taya za'ai chief ya shigo dakin su"? Kwata kwata ta manta abun da ya faru.

Tunani tayi ko Danish ne ya koma mata Chief,

Cikin disasshiyar murya ta furta"Danish"

Jin shiru bai amsa mata ba, yasa ta fara kokarin mi?ewa da wata irin kasala a jikin ta, zama tayi tare da jingina bayanta jikin headboard.

"Kin tashi lafiya"? sexy voice dinsa ce ta ratsa kunnanta, firgigit ta ware idanunta sosai akan fuskar shi wani irin faduwar gaba taji, a rude ta kalli bedroom din sai yanzu ta gane adakin wa take..nan take ta tariyo abunda ya faru daren jiya bayan ta zo dakin shi bacci yaci karfinta adakin shi...tsabar rudu jikinta na kakarwa ta zabura zata sauko daga kan gadon ai kuwa gaba Waya jiri ya kwasheta kiris ya rage ta kifa kasa da sauri Chief Ya janyota ta fado kan laps dinsa, wata irin kunyace ta kamata, ta runtse idanunta la66anta na kerma tace"i'm really sorry, I didn't know I fell asleep in your room dan Allah ka yi ha?uri ka yafe mini"

?amshin turarenshi ya hana ta ?arasa maganar saboda ratsa makoshinta da yayi.

Batai aune ba taji numfashin shi na kokawa da nata numfashin

Jin shiru bata ji move dinsa ba yasa ta Wan kyalla ido Waya don ta ga wani hali yake ciki

Unexpectedly suka haWa ido cikin na juna, sam ta kasa runtse idanunta..

gani take kamar amafarki wai yau gata ga chief, ya Wauketa kamar yar jinjira..bakomai take tunawa ba face maganganun daddynta, duk da bai fito fili ya faWa mata wanene mijin da yayi mata ba, taji aranta Chief ne, kuma tabbas taga abunda yake kokarin ankarar da ita, Chief ya haWa komai da zaisa mace ta so shi.

Matsawo yayi da fuskarshi saitin tata, har tsinin hancinsu ya gogi na juna anata wautar tayi azaton kiss zai mata abaki, gaba Waya tabi ta dabarbarce kamar wadda electric shock ya kama, ?ayataccen murmushi ya sakar mata har dimples dinsa ya lotsa aransa ya yi mamakin kamun kanta cos yadda mata ke hauka a kanshi da wata ce ta samu kusancin nan da shi tuni zata ?waye masa.

Ya riga da ya fahimci me zuciyarta ke raya mata..

A hankali ya sauke ta kan floor din. da sauri ta mi?e tare da sunnar dakanta kasa.

Veil dinta dake ajiye kan gadon shi ya dauko ya yafa mata akai tare da naWe mata shi.

"Thank you.." tafiya tasoma yi zata bar dakin ya dakatar da ita"ban gama magana da ke ba" tsayawa tayi tare da juyowa ta dube shi

Zama yayi gefen gadonshi, da yatsan shi Ya nuna mata backpack din data kawo ma shi

"BuWe min jakar" da sauri ta dawo ta zukunna ta bude backpack din..

"Ki curo komai dake aciki" ta amsa mashi da toh, bayan ta kammala curo kayan dake a cikin jakar ta jerasu kan floor.

"Ki buWe min textbooks din, Inason ganin meke a cikin su.."zama tayi dirshan kafin ta fara bude shafukansu harta kammala Ya rage saura Diary din Unaizah..

"Zaki iya karanta min" Waga mashi kai tayi alamar eh a gogo ya kalla saura rabin awa afara kiran sallah asubahi.

Kasa kunne yayi yana sauraronta, yayin da idanunshi ke akan tausasan pinkish lips dinta ta za?e sai karanta mishi takeyi da zazza?ar muryarta.

Kafin ta kammala karantawa tuni idanunta sun cicciko tab da kwalla, saboda akwai chapters na rayuwar Unaizah da suka ta6a zuciyarta, duk wani abu daya faru da ita mai dadi ko mara dadi sai da ta rubutashi.

shi kanshi chief dake sauraronta zuciyarshi ta karaya da jin irin rayuwar sharholiyar da yarinyar tayi tare da iyayenta batare da sun tsawatar mata ba, saima suka bada gudummuwar gur6ata rayuwarta, hakan na nufin dama cen mahaifinta ya sadaukar da ita shiyasa ya wulakanta rayuwarta ya hana tasan addinin shi don kada Allah ya tuhumeshi aranar gobe kiyama saboda shi jaki ne.

Cikin shesshekar kuka tace"na gama karantawa"

Mika mata hannu yayi ta bashi diary Winta, shafin farko ya duba shi anan yaci karo da corners na hotuna guda uku babu biyu sai Waya daya rage na Unaizah.

A cikin zuciya ya karanta sunayen dake akasan gidan hoton

_My lovely dad, Red Neck, and my first love, my momma, and me, Unaizah, Yar gidan daddy_

ya shafe mintuna Yana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0