Showing 303001 words to 306000 words out of 413917 words

Chapter 102 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4478

ne addu'arki muke bukata ba damuwarki ba.."

"Toh daddy, zan daina, amma pls ka fadamin date da zaku tafi na maka alkawarin bazan sanar da kowa ba"

Aranshi ya ayyana ay ko da zan fada ma kowa Unaisah bazan fada maki ba, ni nasan me zai biyo baya in kikaji, rigima zaki sa sai mun tafi da ke ..

"Daddy ka yi shiru"

"Unaisah, Chief Yana kallon mu, kuma shi Ya hana asanar da kowa, kuma mun yi mashi al?awarin zamu ruke amana, kinga bai kamata in zama mutun na farko da zanci amanar shi ba, amma ki ?ara hakuri zan nemi izni daga gurin shi In har Ya amince zan sanar da ke"

yamutsa fuska tayi tamkar zata sanya kuka tace"ran nan ma haka ka ce min zaka yi mi shi magana akan in biku amma baka yi masa ba"

Shiru yayi bai tanka mata ba, ta fahimci wayou ya ke yi mata gashi takasa tunkarar Chief din da maganar wani irin nauyinsa ta ke ji.

Agogon Hannunsa ya duba karfe goma na dare, Wagowa yayi tare da kallon Chief, Wanda Hankalinsa ke akan Phone dinsa da yake daddanawa..

Har saida suka fara gajiya da jiran sheikah Imam, A kalla sun shafe mintuna talatin Cuf, Wasu daga cikin Prisoners har sun fara bacci.

A lokacin da basuyi tsammani ba, sai ga sheikh Imam Ya fito daga dakin batare da Danish ba, tunkafin ya karaso su ka lura da yanayin damuwar dake akan fuskarshi, nan take suka fahimci ba ay nasara ba...

Har ya zauna ba su daina kallon shi ba, yayi shiru babu walwala akan fuskarsa

"Baba an dace kuwa"? Kallon chief yayi tare da girgiza mashi kai yace"ban ta6a yi ma wani Wan adam da'awa irin wadda nayi mashi ba, kuma da wuya inyi har in gama mutun baiji imani ya shige shi koda bai musuluntan ba, amma banaso hakan Ya dame ku, kowa ni dan adam da irin tashi Jarabawar, wani har ya mutu baiyi imani da Allah ba, amma fa kada ku yanke kauna da shi, idan Allah yaso shi da rahama koda da numfashi na karshe ne in Allah ya nufa sai kuga ya furta kalmatusshahada..." bai ?are maganar ba, Unaisah ta mike da gudu ta bar falon, gaba daya suka bita da kallo har ta 6ace ma ganin su.

Suma sauran yan uwan nata, kuka suka kamayi, shiekh imam ne yayi masu nasiha mai tsuma zuciya harya samu ya shawo kan su,

Kafin tafiyarshi, sai da Ya ?arfafa masu Chief gwiwa, Ya jima agidan har wuraren karfe sha daya kafin yayi masu sallama ya tafi.

Bayan tafiyar shi, Taj Yace suje su kwanta, jikin kowan nan su asanyaye suka mike ko sallama ba su yi ma su ba, kowa ya nufi Wakin shi Ummi ma ta yi ma su sallama ta nufi nata Wakin.

(After two days da zuwan Sheikh imam, Bayan kwana biyu)


Yau tunda sanyin safiya, kiran Taj ya farkar da Ummi tana tsaka da yin baccin ta, bayan ta daga sun gaisa Yace Ta shirya su Unaisah, tare da ita kanta, yana son su kawo ziyara part dinsa gurin Danejo, Ummi taji dadi dama Ta gaji da zama guri daya tafi son tana Wan yawata.

Batare da 6ata Lokaci ba, taje dakunansu ta tada su daga bacci ta isar masu da sakon Boss, duk da halin da damuwar da suke a ciki hakan bai hanasu jin dadin zasu je part din daddy taj ba, Unaisace kadai Hankalinta bai kwanta da zancen zuwansu part din daddynta, saboda ranta yana bata yau ne kwanan watan da zasu je kai farmaki, shiyasa akayi masu wayau don a kawar masu da tunanin su, aikuwa ko brush batayi ba, wankan ma ta kasa yi, A karkashin gado ta boye kanta duk don kada tabisu.

"Sister! sis! Where are You, Mun fa shirya, ke kadai muke jira" muryoyin su Batool tajiyo a cikin kunnanta, shiru tayi bata amsa masu ba.

Can tajiyo muryar Ummi tana fadin"Unaisah Ina kika shiga ne? Kun duba toilet Winta kuwa"? Ta fada tana kokarin tura kofar toilet dinta, koda Ummi ta buWe kofar ta shiga ciki bata ga kowa ba, tayi mamakin ganin babu ita a ciki, rufe kofar tayi, tare da kallon su, sunyi tsaitsaye.

"Aunty ummi ki kira daddyn nata, Muji idan taje can Win" acewar Sajeed

Waya ta zaro daga Cikin Yar purse Winta, ta danna ma Taj kira almost 3 times tana kira baya shiga har ta gaji ta hakura da kiran nashi..

"Mu tafi, may be tana can din" fitowarsu keda wuya daga dakin sai ga big guy ya shigo part din su

Kaitsaye idanun shi suka sauka akan Ummi, from head to toe Yabi ta da kallo, fitted gown ce a jikinta ta material launin ash colour kamar ajikinta aka dinka kayan, ta kashe daurin dankwalinta sai Wan gyalen data yarfa a kafadarta, ko makeup batayi ba amma tayi matukar jan hankalin shi.

Gaba daya sunyi mamakin kallon da big guy keyi ma Auntyn ummin nasu, ita sam bata lura ba da fara'a tace"Gm Sir, ya gajiyar aiki? dakyar ya haWiye abunda ke ransa Yace"lafiyalou Ummi, Ina zuwa haka"? Ya tambaya kamar baisan da plan din su ba

"Zamuje kai ziyara a Part din Daddyn Unaisah" murmushin gefen fuska Ya sakar ta, kafin Ya dubi prisoners.

"Guys, Kunyi kyau, Muje na raka ku part din nasa" ya fada tare da nuna masu hanya, su ka yi gaba shi kuma Yajera da Ummi cikin nutsuwa suke yin tafiya.

"Kinyi mini kyau, badan Ina busy ba, da na daukeki mun fita yawan buWe ido"

"Banyi zaton kana Kula mata ba.." ta fada tare da kallon shi..

Murmushin gefen fuska yayi"nima fa banajin magana, tubabbe ne, daga baya na shiryu silar Owais.."

"Allah sarki Chief, Mutumin kirki, har kasa na kara jin kaunar shi saboda shi din na dabanne samun irin shi da wahala" still fuskarshi da murmushi yace"That's why I'm proud of him..."

"Kasan wani abu"? Girgiza mata kai yai saikin faWa

"najima ina yi maka kallon sani, hatta muryarka tayi min kama data wani mutumina Allah, kuma kun Wanyi kama da shi"

"Zan iya sanin sunanshi"?

"A'a, bana faWi, amma ka fadamin sunan Family dinka"

Yar dariya yayi yana binta da wani shu'umin kallo, kamshin turarenta duk ya kashe mashi kuzarin shi musamam Yadda qugunta ke gogar nashi ba karamin tsuma shi take ba..

"Wayau zaki min Ummi, Ke kin ki faWamin sunan mutumin naki sai ni zan fada maki sunan family ina, bazai yiwuwa ba Allah"

Murmushi tayi"na yarda kowa ya ruke nashi, amma kai ba hausa bane zalla ko? Cos kayi kama da ruwa biyu" Waga mata gira yayi.

"Meye Full name Winka"?

har ya buWe baki zaiyi magana Muryar Sarah Ta katse su"Aunty Ummi, ke muke jira fa" Gaba daya sun shagala sunata fira sam sun manta da su, har sun karasa bakin kofar part din...

Karasowa sukayi, big guy ya kwankwasa kofar, almost 3 times kafin suka ji motsin bude kofar ta ciki

Taj Ne Ya fito Jikin shi sanye da kakinsa Yana ganinsu ya saki fuskar shi da fara'a suka gaisa da juna cikin girmamawa.


"Bismillah Ku shiga, madam Tana a ciki tana jiran ku..." murmushi suka saki gaba dayan su, har sun fara shiga ciki Taj ya lura babu Angel acikin su..

Da sauri Yace"Ina ita Unaisah din"?

Ummi tace"wlh bamu ganta ba, mun duba ko'ina har cikin toilet dinsu, mun yi zaton ta riga mu karasowa ne"

Big guy yace"ni banma lura babu ita a cikin su ba, sai yanzu da kayi maganar nan.." fuskar Taj A yamutse Yace"ku shiga daga ciki, Bari naje na dubota" ya fada tare da kallon Big guy"muje" sai da ya fara kallon ummi Yai mata waving kafin Yabi bayan Taj, suna fitowa daga falon,yayi locking door din dama da biyu suka turo su nan.

Bin falon su ka yi da kallo, jin shiru matar gidan bata fito ba, ummi tace mu zauna mu jira ta.."

da sauri kowannansu ya samu guri kan Sofas suka zauna.

Badajimawa ba, sautin takalamanta Ya karade kunnuwansu, kusan atare suka kalleta yayin da take saukowa down, ta dauki wankan abaya ba?a, tayi rolling akanta.

jinjina kai ummi tayi aranta ta furta masha Allah.

Sallama tayi masu, kamar tana jin shakkarsu, har yanzu bata saba da mutane ba..

A wayance Ummi ta mike tare da ruko hannayen Danejo Acikin nata, ta sakar mata murmushi"sannu madam, fatan mun same ku lafiya.." sai faman rarraba idanu takeyi akansu Rubina
Dakyar ta firta"lafiyalou"

Ummi tace"kamar baki gane su wanene ba, Ko dai Mijin naki bai fada maki zuwan mu bane" sai lokaci tayi murmushi"wlh ya fadamin, na shafa'a ne, da yake banganku tare da ?artawa ba shiyasa na Wan ruWe amma yanzu nagane ku" Hugging Winta Ummi tayi, Kafin suka zauna kusa da juna.

Da sauri Prisoners suka gaishe da ita.

Da fara'a tace"tabarakallahu ahsanul khalikin, Kune Yan uwan Angel Win? Atare suka amsa mata da eh

"Masha Allah Jinsin kyawawa Naji dadin haWuwa daku, amma Ina Unaisah Win take"?

Ummi tace"bata karasa shiryawa bane, shiyasa muka tafo, amma dadynta Yaje ya taho da ita"

"Ke ce mommynsu ne"? Yar dariya ummi tayi"kina nufin wadda ta haife su? Daga mata kai tay, dariya ta kumayi kafin tace"kin iya zolaya, ni ina zan iya haifan wadannan har su goma sha, ko nayi maki kama da matar aure ne"?

Ta tambaya tana kallonta, murmushi Danejo tayi"A'a amma dagaske baki ta6a yin aure ba"?

Waga mata gira ummi tay, waro idanu waje Danejo tayi da mamaki tace"tab lallai, aradun Allah da a rigarmu kike da tuni Kin aje tatta6a kunne, Ko kina so ko bakisho dole ay maki aure" tuntsirewa sukayi da dariya gaba dayansu, hausarta ba karamin nishadi ta basu ba, kana jin maganarta zaka gane bafullatanar daji ce.

Sai dadi takeji ganin yadda ta sanya su nishadi

Maimakon ta dauko masu abunsha, sai ta kama basu labarin haWuwar ta da Taj, har zuwanta birni da irin wautar da tadinga yi mashi, sunci dariya kamar zasuyi kuka.

Ta za?e sai zuba takeyi masu kamar aku, Har saida Parveen ta gaji da zuba na mazurai taji shiru bata kawo masu abinci ba, gashi ko breakfast basuyi ba suka taho

Hannunta dafe da cikinta tace"Aunty Danejo, mufa Yunwa muke ji, bamu ci komai ba muka taho" dan zaro ido ummi tayi tana kallonta, sarai parveen taga kallon da ummi tayi mata amma saita kawar da idonta gefe.

Mikewa Danejo tayi"i'm really sorry, na cika ku da surutu, kunsan mutumin dake zama cikin kadaici in ya samu abokin fira komai ma mantawa yakeyi, kuma fa tun dazu Nayi maku girki tunda daddyn angel ya sanar dani zuwanku..."

har ta fara tafiya ta juyo tare da kallon su"wa zai bini kitchen din mu dauko kayan abincin"? Da sauri Parveen da Yasmeen suka mike atare suka nufi kitchen.

Ajiyar zuciya sajeed Ya sauke tare da kallon aunty umminsu yace"da farko dana ganta kyakkyawa nayi zaton miskila ce ashe ta iya dan banzan surutu" dariya ummi tayi tana fadin"Pls kadaina maganar nan kada taji ka, amma fa kamar ka shiga zuciyata, Nima nayi zaton hakan"

Jemimah tace"gulma haramun, Allah In tadawo saina fada mata abunda kuka ce" Harara sajeed Ya galla mata"dako Kin ci na jaki Allah, Yar sa ido kawai" gatsina mashi hanci tayi tare da hararar shi, Ya janyo throw pillow Ya Wan buga mata akanta.

Azeeza tace"Aunty Ummi, wai itace maman angel ne? Wadda Ta gudu tabarta acikin kwamin wanka" waro idanu waje sukayi

Batool tace"ke fa baki gane komai, Kin manta bafullatar dajin da Angel ta bamu labarinta? Wadda ta tsinceta acikin ruwa.." ta faWa tana kokarin fahimtar da ita can tace"Yanzu na gane ta" ummi dake kallonsu a hankali ta sauke idanunta kan Deeja, data daura kanta saman kafadar Haris, hannunsu ruke cikin na juna tun zuwansu basuyi magana ba, aranta ta ayyana"Mun baro romeo da juliet agida, ga kuma layla da majnoon"

Fitowar su Danejo daga kitchen ne Ya katse firarsu, kowan nan su ruke da farantai shake da kayan abinci , akan rug suka ajiyesu,

kowannansu ya sauko kan rug din suka kewaye farantan,tun da kamshin abincin ya daki hancinsu suka fara hadiyar yawu

Har sun fara Cin abincin, Batool tace"ba zamu jira Unaisah ba"? Ummi tace"nima dai naji shiru bata karaso ba"danejo tace"kada ku damu, itama na ajiye mata abincin ta, duk lokacin data karaso sai taci"

daga haka ba su kara magana ba, Kowa ya maida hankali kan abincin da yake ci da alama yayi masu dadi, su parveen ba baka sai kunne, Hannu baka hannu kurya, kwata kwata bata Iya bakunta ba. Ummi har alama tayi mata da ido donta daina loma amma ta wani basar kamar bata ganta ba

Danejo ko sai fadi take kuci ku koshi in ma bai isheku ba, akwai saura abincin dana aje mana..

_________________________________=ؔ?

Around ?arfe 2 na rana da matsakaicin gudu motocin su suka kunno kai Cikin Villa din..

Su biyune zaune a back seat din Motar Chief, babu mai magana a cikin su, sunyi shiru daga gani ba karamar gajiya suka kwaso ba ..

Gently yake daddana wayar hannun sa, yana kokarin kiran daddy dinsa sai ga kiran shi ya shigo, yayi mamaki kamar yasan shi yake shirin kira..

Picking call Win yayi tare da kara wayar a kunnansa yana niyar yi mashi sallama miryar Mai girma sharafudden Ta katse masa hanzarinsa"Owais Inason ganinka Yanzun nan..." har saida gabansa yadan fadi da jin yanayin muryar daddyn nasa.


"Am...daddy, Ina fata lafiya" bai kare maganar ba Yace"idan kazo zaka ji koma menene" daga haka Ya katse Kiran

Lamarin Ya daure mashi kai! Bai ta6a jin muryar daddynsa cikin fushi irin Na yau ba, fatan shi Allah Yasa ba wani abun bane ya taso.

A hankali Ya dubi Danish dake a hakimce kan seat, Ya langwa6e kan shi, Idanun shi suna a lumshe kamar ma bacci ne yayi awon gaba da shi.

"My Boy, Bacci kake Yi"? Cikin kunnanshi ya tsinkayi muryar chief a wahalce ya buWe rinannun idanun shi batare daya iya furta kalma ba.

Adaidai Lokacin Motocin suka yi parking, agent Ya buWe masu cardoors Win. .

Atare suka fito, adai dai lokacin Taj da big guy sun fito daga motarsu..

Gaba daya suka maida Hankali akan Chief da Danish..

"Daddy Ya kira ni yanzu a mota, Yace Yana son gani na, zan tafi.." ya fada yana kallon su

"Pls take care of my baby boy, he's very tired and needs your care. Ensure he bathes, eats, and then goes to bed and rests before the time is full..."

yamutsa fuska Omar yayi kasa kasa da murya ya furta"sai kace wani jinjiri, kowa ma agajiye yake ay"

"Magana kake yi ne"? Chief ne ya fada yana kallon shi, Girgiza kai yayi"a'a," ya fada tare da kallon Danish baima san yanayi ba, hankalin shi baya atare da su..

"Sir, Allah ya dawo mana dakai lafiya, agaishe mana da mutanan gidan" amsa masu yai da ameen Kafin Ya koma cikin motar, basu bar gurinba, har saida motar chief ta 6ace na ganin su.

"Guy ina zuwa, Ka manta amanar da Chief Ya bamu"? Da zolaya ya fada yana kallon shi, a lokacin Danish Har yayi gaba abun shi..

Harara Ya galla mashi"Ya 6ata min rai, tarairayar da yakeyi masa tayi yawa sai kace wani jinjiri? Bai da magana sai ta Danish..." Yar dariya Taj yayi"wlh Omar Ka fara bani tsoro! Bana tunanin ko matar da zaka aura zaka yi kishinta makamancin wanda kakeyi ma Chief, kai dai bakaso kowa ya ra6e shi, bazan manta farkon zamana agidan nan ba, kiri kiri Ka fara jin haushina saboda kyautatamin da chief Yakeyi, naci wuyarka kafin muka saba da juna.."

kayataccen murmushi Big guy yayi"ba zaka gane ba Taj, duk yadda zanyi maka bayani ba lallai ka fahimce ni ba, wlh ina tsananin kaunar chief son shi nake, fiye da yadda nakeson kowa nawa, nifa ji nake dama mu Twins ne ni da shi..."

Wan zaro idanun yayi maganar Omar ta bashi mamaki"nifa wlh ban ta6a zaton kai mataimakinsa bane saida na fara kar6ar training na isod, nayi mamki cos kamar Wan aikinsa baka gajiya dayi masa hidima" yar dariya Big guy yai"kauna ce kawai, shima yayi fama dani akan indaina amma nakiya sbd banaso wani ya samu kusanci da shi."

Murmushi Taj yayi" Allah yabar kauna tsakaninka Da Chief, Allah yasa mutuwace kadai zata rabaku"

ya kar6e da cewa"ita ma mutuwar bana fata ta rabamu, nafison ta dauke mu atare ni da shi"

murmushi Taj yayi bakomai ya fado mashi arai ba face Wan uwansa kuma amininsa Ozair, har abada bazai samu abokin da zai maye masa gurbinsa ba.

tuni Yaji Kwalla ta cike idanunsa a fakaice Ya share Hawayen don kada Omar Ya gani raba hanya su ka yi da Omar, Ya nufi part din chief don Ya cika Umarnin sa na ba Danish Kulawa.

A lokacin Danish Har Ya shiga bathroom, Koda ya shigo bedroom dinsa bai iske shi ba, landline din kitchen ya kira ya isar da sakon su kawo ma Danish lunch dinsa.

Yana katse kiran saiga kiran Ummi Ya shigo Layinsa, Picking call din yayi tare da kara wayar a kunnansa.


"Boss, Har yanzu Unaisah batazo ba, har jaraba kiran layinta nayi amma akashe, kuma naga kofar falon anyi locking Winta already.."

dafe kai yayi da hannu Waya sam Ya sha'fa'a da batun Unaisah..

"Ummi, i'm really sorry, dazu mantawa nayi wlh, amma yanzu zan dubota"

"Okay, sai naji daga gare ka"

Rejecting call din yayi, Cikin sauri ya fito daga dakin Danish, Ya nufi Bedroom dinsu shigarshi Keda wuya adai dai lokacin Tana kokarin fitowa daga karkashin gado ashe tun bata fito ba, anan bacci yayi awon gaba da ita sai yanzu ta farka.

Wani irin burki Yaci Yana kallonta cike da mamaki, Yarinya ta zama kamar aljana, kwata kwata bata lura da shi ba, dakyar take jan numfashi saboda zazza6in dake nema yafi karfin ta, ga wata matsiyaciyar Yunwa da take ji, Sleeping Gown Win jikinta tayi squeezing, Kamar yadda sumar kanta ta yamutse.

Gyaran Muryar da yayi mata ne, Yasa tay firgigit Ta juyo ta fuskance shi da idanunta wadanda suka ?ankance...

Wani irin faduwar gaba taji, girgiza kai taj yayi"Unaisah, Irin Rayuwar da kika zaba ma kanki kenan? Bakya jin maganata Unaisah, soyayya ta rufe maki Ido kinbi duk kin hana kanki kwnaciyar hankali" jikinta na kerma ta girgiza mashi kai batare data Iya furta kalma ba

A faWace Yace"Zoki wuce Kibi Yan uwanki, tun safe suke ta jiranki"

Make mashi kafaWa tayi cikin disasshiyar murya ta furta"daddy, ni bazan bi su ba,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0