Showing 123001 words to 126000 words out of 413917 words

Chapter 42 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4559

Wauka kamar kina agidanku ne, don na fahimci kamar kin takura"
Murmushi Zeenatu tayi har dimples dinta suka lotsa,
"Ina su Maminku ina fata duk suna lafiya" cikin kulawa tayi Maganar tana kallon benazir"
"Suna nan lafiya, sunce mu gaishe daku, taso mu zo tare amma tace sai zuwa na gaba",
Murmushi Mami tayi "Allah Ya kawo ta Lafiya in ma batazo ba ni na fidda lokaci inje gidan naku"

Shiru sukayi na wani lokaci, kowa da abunda Yake sa?awa aranshi, Benazir ta ?osa su ke6e da Aneelerh don su ?ara jajantama junansu.
Fitowa daga kitchen Ana tayi hannunta Wauke da tray na kayan abincin da suka shirya masu har zata gifta ta Wan dakata tare da kallon ba?in nasu karaf idanunta suka sauka akan fuskar benazir, tsabar kiWima da ganin Benazir ?iris Ya rage ta saki kayan abincin hannunta Jikinta Ya hau bari da sauri takai abincin Dining ta nufo su, gaba Waya ta zube kan carpet tana ambaton sunan Benazir,

Kusan atare suka Wago suna kallonta duk tabi ta ruWe muryarta na rawa take faWin "Aunty Benazir! Kece? Ko dai makuwa nayi ne?"
Hawaye ne suka ciko idon benazir bakomai Ya faWo mata aranta ba face Irin azabtarwar da tayi ma yar'uwar Ana mai aikin gidanta Janet taci azaba a hannunta in tai mata laifi hada duka take haWa mata,
Cike da jin kunyar Ana tace"Ni ce Ana, ba makuwa kikai ba, fatan na same ki lafiya? Ina yar uwarki janet"
Matse ?walla Ana tayi "Allah Sarki Aunty Benazir Ina nan lafiyalou, Janet tana a Jos tare da Esther ni kaWai ce anan, Aunty Benazir Ina kika shiga tsawon lokaci bamu ji Wuriyarki ba..."
Kafin benazir ta bata amsa Aneelerh tayi saurin tarar numfashinta da cewa "Ana kije ki ?arasa shirya masu abincin, zanyi maki bayanin komai" ta faWi hakanne saboda bata son ana tayi maganar 6acewar su Angel gudun kada Benazir taji hankalinta Ya tashi,

"Kada ki damu, zuwa anjima kafin mu tafi zan nemeki..." amsawa Ana tayi da toh, Jiki asanyaye ta mi?e tana tafiya tana waiwayon su Benazir tana mamakin Matashiyar da suka zo da ita, aranta ta ayyana watakil itace Yar uncle Winsu da taji ance zasu zo da ita...har sai da ta shige kitchen tukunna ta daina kallon su,

Mi?ewa Aneelerh tayi tare da kallon Benazir tace "mu shiga daga ciki",
Mami tace "kuyi me? Ba zaki bari su ci abinci ba, salon ki cika ta da surutu"
"Ba daWewa zamu yi ba Yanzu zamu fito"
Ummi tace"ke ko an daWe ba'a haWu ba, tana son su Wan ke6e ne ay firar yaushe rabo",
mi?ewa Benazir tayi suka nufi bedroom Winta hannunsu cikin na juna,

"Shureim ya'yanka nawa Yanzu" sunnar dakai ?asa yai jin tambayar da Mami tayi masa,
Dariya tayi "dan Allah kada kace min bakai aureba"
Cike da jin kunyarta Yace "banyi ba Mami, amma nakusa in sha Allah" tayi mamakin jin maganarsa gashi har ya fara manyanta baiyi aureba koda Yake komai sai Allah Ya nufa,
"Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa" amsa mata su kai da ameen,
Shigowa Ana tayi "Mami na gama shirya abincin"
Mami tace"toh, ku tashi mu ?arasa Ciki" Dr Shureim Yace"Alhamdulillah, bana Jin yunwa sai dai ko Zeenatu in zata ci"
Ma?e kafaWa Zeenatu tayi "nima bana jin yunwar ay naci abinci agida" yadda tai maganar yaso basu dariya har sun gane shagwa6a66iyace
"Ha?uri zukuyi ku tashi muje, Nasan baza'a rasa space a cikin ku ba ko ruwan zumunci ne ku sha" lalla6a su Ummi tayi har dai suka mi?e suka bi su Mami zuwa dining..

A 6angarensu Benazir bayan sun shiga Waki da Aneelerh, cike da zumuWi suka zauna daga gefen gado
Sai faman bin juna da kallo suke yi kamar yau suka fada haWuwa
"Kinga yadda kika canza? Kin ?ara girma kinyi kyau abunki, bani labari bayan kin tafi ina kika faWa"?
Numfasawa tay kafin tace"Wani bawan Allah ne Ya taimaki Rayuwata, Mutumin kirki, Wan family Win Obinna nasan ba zaki rasa saninsa ba, sunan shi Zaki Mubarak Obinna A ?asar Canada Yake..." gaba Waya Benazir ta bata labarin Yadda suka haWu da zaki a Abuja bayan ta gudu daga jos da yadda harya taimaketa suka bar kasar atare..
Jinjina kai Aneelerh tayi har cikin ranta taji dadi da rayuwar benazir bata wula?anta ba,

"Koma wanene Yayi miki wannan aika aikar in sha Allah sai yaga sakayya, tun agidan duniya, anso a cutar da rayuwarki, da yake Allah ba azzalumin bawansa bane cikin ikonsa kin faWa hannu nagari",

"Ni inda nagode ma Allah, ban tafi da tsohon ciki na ba, da bansan a Ina zan haife shi ba, ba rabon ?ata tasha wahala wlh banyi zaton zata rayu ba, inaji ina gani nabarta a kwamin wanka tana kuka tana kallona..." kuka ne Ya ci karfinta da sauri Aneelerh ta fara lallashinta
"Ni damuwana wanene yake kokarin ganin ya rabani da dangina? Me na masa Aneelerh? Nasan bana jin magana tun a ?uruciyata inada jan faWa da masifa, mutane da dama na sanya su ciwon kai har da masuyi min mummunan fata amma wallahi ban ta6a zaton za'a samu wanda zaiyi min asiri, to waini me nayi masu haka??" idanunta jawur ta faWa.

Dafa kafadarta Aneelerh tayi"in sha Allah duk wani mai nemanki da sharri kanshi zai koma, ubangiji Allah Ya tona asirin su"
"Ameen Aneelerh nagode sosai da kulawarki agareni, ni wlh banyi zaton zaku kar6e ni hannu biyu idan na dawo ba, ko gida da zan dawo nayi fargaban haWuwa da su Daddy amma saina ga kowa Yana murnar gani na ba ?aramin daWi naji ba, yanzu damuwana Waya shine mijina da ?ata ina matu?ar jin shakkarsu saboda nasan da wuya su kar6eni hannu biyu kamar yadda kukai min..."

"Meyasa zaki ce haka? ay su sai sun fi kowa murnar ganinki"
Girgiza kai tay"ba zaki gane ba Aneelerh, bayan tafiyata lokacin ina agidan zaki, kwatsam wata rana saiga sa?on saki daga Taj hakan Ya tabbatarmin da yaji haushin abun da na masa" da mamaki Aneelerh tace"kina nufin bake kika nemi saki daga wurinsa ba?"
?aga mata kai tay alamar eh, shiru Aneelerh tayi jikinta Ya ?ara mutuwa lakwas saboda taj da kanshi Ya ta6a faWa mata Benazir ta tura masa text message tana neman ya saketa, to kenan wanene Ya shirya wannan tuggun?" Ta jafe ma kanta tambayar da bata da amsarta,

Ru?o hannayenta Benazir tayi a cikin nata ta dam?e su sosai cikin sanyin murya tace "Dan Allah Aneelerh ki taimaka min Inason yin magana da tajuddeen, naji kince baki da layin da Yake amfani da shi, tun da suna a tare da mijinki dan Allah ki kira Uzair Win sai mu yi magana da shi..." Rass Aneelerh taji gabanta Ya faWi, tuni ta nemi nutsuwarta ta rasa, batasan taya zata shawo kan Benazir ba sam ta manta da jiya ta faWa mata hada mijinta suna a South Korea,

"Kinyi shiru baki ce min komai" ta faWa idanunta acikin na Aneelerh, farat Waya ta fahimci wani abu daga yanayin da ta nuna, Wani irin kwarjini Benazir tayi mata muryarta da inda inda ta shiga faWin "am..umm..bani da layin shima uzair...au wayarshi ta lalace zan ce....." bata ?are maganar ba ta katse ta da cewa "Kada kiyi min karya Aneelerh ba halinki bane, dan Allah ki faWamin gaskiya ni dama najima ina kokwanton maganar mami, daga baya sai da raina ya bani akwai wani abu da take boyemin don itama lokacin dana tambayeta lambar Taj tunda nasan bata rasata ba kamar da suka bayyana man cewa suke kula da yarinyata lokacin dana dawo amman sai ta nuna man basu da lambarshi ta inda yake, tun nan na fara shakkun maganar ta tunda ko don saboda yarinyar tawa ai ya kamata ace suna da lambar tashi da suke magana, kawai ki faWamin in da akwae wani abu nayi maki alkawarin bazan tada hankalina ba, boyemin bashi da amfani tunda duk min daren daWewa zanji ne kuma bazan ji daWin ?in sanar man da kuka yi ba...."
Jinjina kai Aneelerh tayi tuni taji ?walla ta cika idanunta don har yanzu zuciyarta da ciwon abun,
Numfashi taja kafin ta fara bata labarin abun da Ya faru na 6acewar su Tajudeen,
Tsabar tashin hankali Yasa Benazir saukowa daga zaunan da take a gefen gadon ta dawo kan floor dirshan ta Waura hannayenta biyu asaman kanta muryarta cike da tashin hankali take faWin "INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJU'UN! INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJU'UN......" Misalta tashin hankalin da zuciyarta ta fuskanta ba abune mai sau?i ba, Idanunta sun kaWa jawur facial muscle dinta har kerma take gaba Waya jikinta ya Wau wani irin mahaukacin zafi kamar mai fama da zazza6i sai kerma take,
Dafa kafaWarta Aneelerh tayi muryarta a raunace ta furta "Innallaha ma'assabirin Iya abun da zan iya furta maki kenan, abun da Ya faru Ya riga daya faru Benazir, illa iyaka mu cigaba dayi masu addu'a ubangiji Allah Ya bayyanar mana da su tunda har Yanzu babu labarin suna araye ko sun mutu,
Cikin shesshekar kuka Benazir take faWin "nashiga uku Aneelerh! Meke faruwa da rayuwata ne? Da farko An rabani da dangina hakan bai isa ba sai da akayi silar da ?ata da mijina suka 6ace! Wai wanene ke bibiyar rayuwarmu ne? Uban me muka masa...." jin Yadda take Waga Murya Yasa Aneelerh saurin toshe mata baki da tafin hannunta gudun kada su Mami su jiyota....
A ?arshe ma sai ta rungumeta saboda ta samu relief Win abunda ke damunta
Allah kaWai Yasan tafarfasar da zuciyarta keyi mata kamar numfashinta zai Wauke bakomai take tunawa ba face fuskar Taj dana yarta Unaisah yanzu shikenan ta rasa su?
Gunjin kuka taci gaba da yi, kwantar mata da hankali Aneelerh ta shiga yi, suna haka Mami ta shigo ganin halin da suke ciki yasa ta nufosu da sauri tana tambayar lafiya mike faruwa ne ta gan su haka da alamun tashin hankali, zama tayi a bakin gadon ta dafa kafaWar Benazir tana faWin "mike faruwa ne na gan ki cikin wannan halin??" Aneelerh ce dake ?walla ta faWi mata dalilin shigarta halin, yanayin damuwa ne ya bayyana akan fuskar Mami tace ma Aneelerh tunda bata sani ba ai da bata sanar mata ba, shiru Aneelerh tayi cikin kuka Benazir tace "Mami nice na matsa mata ta sanar man, 6oye mani baida amfani don koda yaushe ina sa ran haWuwa dasu ashe ba rabo, an raba ni da mijina da kuma ?ata, Mami suwaye waWannan azzaluman da suka tarwatsa kan iyalin mu, mi mukai masu ne don Allah" gaba Waya ta gama karya masu da zukatansu itama Mami har idanunta sun ciko da ?wallan, rarrashinta ta shiga yi tana karfafa mata gwuiwa kan inda rabo sai suga sun bayyana tunda har yanzu ba'a da tabbacin ko sun mutu har ta bata misali da ita yadda ta 6ace 6at ba'asan ina take ba tsawon lokaci gashi yanzu Allah ya bayyanar masu da ita don haka ba abunda zasu yi sai suci gaba da yin Addu'a, a tare suka cigaba da rarrashinta har saida suka ga ta Wan samu nutsuwa Mami tace ta taso suje taci abinci dama shi ta shigo tayi mata magana, idanunta sunyi jawur ta girgiza mata kai kafin cikin disashshiyar murya tace bazata iya cin wani abu ba a yanzu, dole Mami ta ?yaleta Benazir Win ta bu?aci shiga toilet da sauri Aneelerh ta mi?e tana nuna mata toilet Win ta mi?e jiki ba ?wari ta shiga, bayan shigarta Mami ta mi?e cike da tausayinsu ta fita, wanko fuskarta tayi bayan ta fito akan gadon aneelerh ta kwanta kamar ba laka a jikin ta, tsananin tausayinta duk Ya kama Aneelerh tana ta kallonta, bayan wani lokaci ta mi?e taje ta kawo mata abinci da juice don tasha tace mata bazata iya cin komai ba, lalla6ata tay dakyar ta samu tasha juice Win, shiru sukai can Benazir din tace "Ina yaronki? Naga bangan shi ba? Ina abie?"

"Bayanan sun tafi unguwa tare da Mahboob ?anin Zahra, su abie suma basa nan amma nasan zuwa anjima kaWan zasu dawo gidan"
"Allah Ya dawo da su lafiya" amsa mata tayi da Ameen daga haka bata ?ara magana ba har bacci Ya Wan dauke ta a Wakin.

____________________Chief

Around 5 na marece Ya fito daga Gym room Winsa, daga shi sai short ba?i a jikinsa, Ya haWa uban gumi zufa ta ko'ina take tsatstsafo masa, Hannunsa Waya ru?e da short towel da yake goge gumin jikinsa,

Bathroom Ya shiga, within 15 mins Ya fito daga wanka ya nufi walk-in closet dinsa cikin kankanin lokaci Ya kimtsa cikin suit navy blue sunyi bala'en Yi mashi kyau da alama zai fita wani wuri ne, hadaddiyar agogon hannunsa sai salki take, kafafunsa na sanye da hadaddun leather shoe ta ko'ina kamshin turarensa Ya karaWe Wakin,

Wayarsa ce ta fara ruri ya Wauko tare da duba sunan mai kiran sa, hidding number ce nan take Ya gane mutumin nan ne daya saba yi mashi kiran sirri,

Picking call din Yayi tare da kara wayar a kunne,

"Naji daWi da ka fara yadda da maganata, Yanzu Ya rage naka Owais kai kokari wurin gano su wanene miyagun dake a family Winka tunkafin lokaci Ya ?ure maka"

"Sai yaushe ne zaka bayyana min kanka? Ina son sanin Wanene kai?And how did you know everything that's happening with my fam?

Sautin dariyar mutumince ta cika masa kunnansa "sanin wanene ni bai da amfani, idan kuma ka damu da son sanin wanene to ka fara kawo ?arshen miyagun dake a cikin zuri'arku" runtse ido Chief Owais yai har cikin ranshi bai son jin Ya ambaci miyagu a family dinsa zuciyarsa karaya ta ke yi kalmar bata masa dadi,

Rai a6ace yace "babu miyagu a family dina, ka kiyaye kalamanka," dariya mutumin yayi "shiyasa nake jin tausayin ka Owais saboda ka yarda da kowa na family Winka, me zai faru a ranar da ka gane gaskiyar da nake kokarin ganar da kai" a fusace Ya daka masa tsawa baima tsaya ya ?arasa jin zancen mutumin ba Ya wurgar da wayar kan Gadonsa, Yana faman fitar da huci Ya furta "bazai ta6a yiwuwa ba, na yarda da family dina, babu bata gari a cikin su...." Yana a cikin wannan Halin Wayarsa ta sake Yin ringing, Ko kallonta baiyi ba a zaton shi mutuminne Ya ?ara Kiransa shiyasa bai kulata ba,

Jiki amace Ya zauna kan couch gaba Waya Ya rasa sukuninsa zuciyarsa sam bata masa dadi,

Wayarsa sai faman ringing take da zarar kiran Ya katse wani Yake shigowa,

Runtse idanunsa yayi bakomai Yake hangowa ba face fuskar Daddynsa data Uncles dinsa kai harma da Kakansa mutanan kirki masu Daraja a idon duniya, abune mawuyaci ya gasgata maganar mutumin in har ba gani yayi a zahirance ba, to wai wa akeso Ya zarga a cikin su? hakan ma bazai ta6a yiwuwa ba, wannan rashin imanin badai a family Winsa ba, sai dai wani baren dake a cikin su,

Knocking kofarsa akai, nan take alert ya shigo masa, kamar bazai tashi ba, a kasalance Ya mi?e Ya nufi wayar Ya danna unclock slowly ?ofar ta buWe, bai kai idonsa ga mai shigowa ba hankalinsa na akan missed calls din da akai masa daga delivery man na Companynsu, tunawa da sa?on Hateem yasa shi saurin dannawa mutumin kiran bayan yai picking suka gaisa ya sanar dashi sa?one Ya kawo masa tun Wazu Ya shigo jami'ae sun hana shi ?arasowa ciki,

"Okey, Gani nan zuwa" ya furta,

Sauke wayar yayi daga kunnansa
Juyawar da zaiyi ke da wuya karaf idanunsa suka sauka akan ?afafunta dake asanye cikin highhill, sam ya manta da izni daya bada na ashigo dakinsa,

Tun daga ?asa Ya fara kallonta har Ya sauke idanunsa kan fuskarta, ganin kallon da yake yi mata ne yasa tai saurin cewa "naga kana waya shiyasa ban yi magana ba" muryarta ba ?aramin sanyaya masa zuciya tayi ba sai yaji kamar yasha pain reliever ne,
Kallo Waya da unaisah tayi masa sai da ta fahimci wani abu na damunsa,

"Ina wuni,"

Lumshe idanunsa yai muryarsa da sanyi ya furta "lafiyalou,"

"Idan akwai wani aiki da zan maka ka faWa min"

"Okey" ya faWa tare da kallon bedroom dinsa "ki gyara min Wakin but karki takura kanki" amsa mashi tayi da toh, Fucewa yai daga Wakin Ya barta ita kadai wani irin dadi taji, sai da ta 6ata lokaci wurin sha?ar kamshin turarensa daya cika dakin kafin ta fara gyara mashi gadon shi,

A sitting room dinshi Yasa aka shigo mashi da Wan sakon, da sallama Ya shigo hannunsa ru?e da wata katuwar shopping bag mai Wauke da logo na Obie tech,

"Barka da warhaka Yalla6ai, fatan na same ka lafiya" yana daga zaune kan sectional sofa Ya amsa mashi da barka da zuwa,

"Yawwa Sir, ga sa?on" da hannu Ya nuna masa gaban sofa Win da Yake mutumin Ya ?arasa Ya sauke jakar kayan Kafin sukai sallama Ya juya ya fuce,

Ko minti biyar ba ayi ba wani senior agent Ya shigo sitting room Win hannunsa ru?e da mug din coffee, cikin girmamawa ya gaishe da shi kafin Ya Waura masa cup din kan table din gabansa,

Da hannu ya nuna masa shopping bag din "fito min da kayan dake a ciki"

"Okey sir" zu?unnawa yayi agaban Jakar Ya fara zaro Apple laptop sabuwa gal, tare da phone box na Iphone 15pro max, A hankali Ya Waura su kan rug din gaban sofa din kafin ya ?arasa curo sauran kayan, Apple ipad da headphone tare da watch box and eyeglass case" bayan ya kammala curo su, chief Ya Wan jinjina kansa kafin yace da shi ya maida su ciki ya amsa mashi da Okey Sir, mayar da su ciki yay sannan Ya mi?e Ya sarah mashi da hannu yay mashi alamar yaje ya juya ya fuce,

Har cikin ranshi Yaji dadin kyautar da Hateem yayi ma yaron kaya masu kyau da tsada, aransa ya ayyana zaiyi amfani da wannan damar wurin ganin Yaja shi a jiki,

Cup Win Ya dauka Ya fara kurbar coffee a halin Yanzu Baya bu?atar kowa a kusa da shi shiyasa Ya ke6e kansa don Ya samu damar Yin nazari,

A 6angaren Unaisah dake gyara masa bedroom dinsa, har ta gama da gadon ta dawo gaban dressing mirror Winsa tana jera masa perfumes Win yayi amfani dasu,

Tunkafin tagama take Jin kamar faWuwar gaba, kamar ance ta Wago ta kalli madubin kwatsam idanunta suka sauka akan shi, Rasss! taji gabanta ya faWi, a matu?ar firgice ta juyo tana kallon shi ya harWe hannayensa kan ?irjinsa fuskarsa kamar wanda aka aiko

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0