Showing 408001 words to 411000 words out of 413917 words

Chapter 137 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2696

ku Wan jira"

Ta amsa mashi da toh, rejecting call din ya yi, ya shiga tuntu6ar layin Chief, almost 5 times tana ringing bai yi picking ba, ana shidda ne ya ci sa'a Chief ya Waga kiran..

"Yalla6ai mun yi ba?i, Anila ce tare da Benazir, Wlh bansan da zuwansu ba saboda basu faWamin ba, sai dai kawai ta kira a waya ta fadamin suna a bakin gate an hanasu shigowa, wlh da nasan da zuwan da bazan bari suzo ba, amma na ji Anila tace matsalace ta kawo su."

Koda jin wannan maganar Chief Win ya ce zai yi magana a basu iznin shigowa ciki.

Godiya Taj ya yi masa bayan sun yi sallama, ya zura wayar Cikin aljihun jallabiyar sa.

A hankali Motar Dr Shureim ta karaso cikin parking space, bayan ya tsayar da ita. suka fito daga ciki, kallon kallo Benazir da Anila suka jefawa junan su.

"Yaya Shureim ko zaka jira mu anan?" Benazir ce ta yi maganar saboda basa son su shiga dashi ba don komai ba sai don kada su ?etare iyakarsu ga kuma gargadin da aka yi masu.

"Ba damuwa, ku shiga zan jira ku, but pls kada ku daWe."

Amsa mashi su ka yi da toh kafin suka nufi main door na falo, suna ?arasawa ?ofar ta zuge suka shiga bakinsu Wauke da sallama, wani sanyayyan sanyin Ac ne na daban ya ratsa fatar jikinsu har wani lumshe idanu suka yi.

Time da suka buWe idanun nasu kaitsaye suka sauka akan Taj dake a zaune kan Sofa ya nutsu yana jiran ?arasowarsu, Ba zaka ta6a gane yaji rauni a cinyarsa ba saboda ya lullu6eta da jallabiyar jikinshi, Sofa Win ma da?yar ya samu ya yi dubarar da ya zauna akanta, da Wayar ?afarsa me lafiyan ya tura wheelchair din ta koma tsakankanin sofas saboda baya son su ganta.

Ta wutsiyar idanunshi ya ke hangosu yayin da suke nufo shi.

Anila ta yi mamakin ganinsa bayan ya ce mata basa nan ashe yana nan, komi yasa ya boye mata da farko? Ta ayyana a cikin ranta.

Har saida suka ?araso kafin ya Wan Wago da niyyar ya kallesu karaf idanun shi suka shiga cikin na Benazir, har saida ya Wan ji gaban shi ya faWi saboda kyan da ta yi ma shi, amma da yake namijin duniya ne sai ya haWe rai tare da kawar da idanun shi.

Murmushi Anila ta yi kafin ta gaishe shi ya amsa mata fuskar shi asake.

Cikin sanyin murya Benazir ta gaishe da shi a da?ile ya amsa mata..

"Ku zauna."

A kan Sofa mai mazaunin mutun uku suka zauna suna fuskantar shi....

Gaza jurewa Benazir tayi idanunta cike tab da ?walla ta ambaci sunan shi"Taj!" Shiru bai tanka mata ba..

"Nasan har yanzu fushi kake dani, amma meyasa idan na kira baka picking? Har sa?o na tura maka akan ka taimaka ka haWani da Unaisah saboda idan na kira bana samun layinta amma kwata kwata ba response..."

Hannu ya Waga mata tuni ta haWiye maganarta, "Dama wannan ne abun da ya kawo ku?"

?asa-?asa da murya Anila ta raWa mata "pls ki aje wannan maganar gefe, ki yi ha?uri mu yi abinda ya kawo mu, kinga da?yar muka samu aka bamu damar shigowa ciki." Jinjina mata kai ta yi alamar ta gamsu.

Mayar da dubanta ta yi akan Taj, "Dama issue ne akan yar aikin gidan mu Ana data 6ace yau wata Uku kenan."

Jin wannan maganar Yasa Taj ya maida hankali akan Aneelerh.

Dakatawa ta Wan yi ganin kuku ya nufo su hannun shi ru?e da wooden tray na fruit da cool drinks ya ajiye masu kan table, bayan ya tafi Aneelerh ta cigaba da zayyana masa komai da ya faru har izuwa kan videon da ta gani...." tunkafin ta kai ?arshen zancen yanayin fuskar Taj ya sauya zuwa tsantsar mamaki, tashin hankali da kuma ruWani...

"Zan iya ganin Videon??"

Da sauri tace "Eh," Ta faWa tare da zaro wayar daga cikin handbag dinta ta shiga pressing dinta, bayan ta kunna masa video ta mi?e taje gaban shi ta mi?a ma shi.

Bayan ya kar6a, lokaci Waya hankalinsa ya tashi matu?a, saboda tsabar girgiza da kidima duk da sanyin A.c din falon saida ya fara zubda gumin zufa lamarin ya Waure masa kai, Lallai sun zo da case mai girma, abun da ya Wan jefa shi a rudani a bayanin Ana ya fahimci shi Uncle Win Anila matsafine kuma abun da yake yi ma Ana yayi kamanceceniya da cin zarafin da Elders su ke yi wa prisoners a lokacin da suke yin jinin al'ada.

A dabarbarce ya furta, "Anila dama Ana tana nan?"

Idanunta cike tab da ?walla tace, "Eh, atare da ita muka dawo gidan Uncle din"

Jinjina kanshi ya yi Idanunshi sun kaWa sun Wan yi ja,

"Ku sha lemun" Ya faWa yana nuna masu drinks din..

Mi?a hannu Anila tayi ta dauki Juice ta tsiyaya masu a glass cups, saboda dadin da ya yi masu kusan duka suka shanye..

"Tanimu Ja'afar Falgore, inkiya ?an-iya shine full name na uncle dinki ko?"

Ya tambaya yana kallon Anila, Jinjina mashi kai ta yi alamar eh, a ransa ya furta karen yan siyasa zai aikata fiye da hakan, ya ?arashe zancen zucin nashi tare da aje wayar Ana a gefen sa.

Har ya zaro waya zai dannawa Chief kira maganar Anila ta dakatar da shi...,

"Benazir na ji kin yi shiru baki ce komai ba? ba zaki fada masa abunda ke faruwa dake ba?"

Cikin karyayyar murya ta wanda ke shirin saka kuka tace,"Ba ki ga ko kallona bai son yi ba, Even if I tell him, he won't take me seriously."

A hankali Taj ya dubi Benazir da tayi maganar, idanuwansu suka shiga cikin na juna, da sauri ta kawar da nata idanun gefe Waya.

"Ina sauraronki! FaWamin me ke damunki?" Wani sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta jin ya kula ta, aikuwa ta gyara zama ta fara labarta masa abun da ke faruwa da ita, nutsuwa ya yi yana sauraronta, dan dakatawa ta Wan yi tana haki kamar wadda tasha gudu.

Da hannu ya nuna mata Mineral water,"Ki sha" da sauri ta dauka ta Wan kur6a.

Bayan ta ajiye taci gaba da bashi labari..

*bari mu koma baya don jin meya faru a ranar da Benazir ta dawo daga gidansu Anila bayan ta fada mata komai dangane da batansu Angel harta kulle kanta a daki, a ?arshe da aka bude dakin aka iske ta kwance a ?asa rabin jikinta a cikin toilet=?G?*


Bayan da ta gama shan kukanta tamkar ranta zai fita, lokaci Waya ta fara Jin azababben ciwon kirji, tana jiyo bugun kofar da suke yi mata haWi da yi mata magiya akan ta bude amma ta?i saboda bata son ganin kowa a kusa da ita, a kan floor ta kwanta tana cigaba da sharar ?walla.

"Pls idan kina saurarena ki tashi ki kunna karatun alkur'ani kada ki kwana a haka, yakamata ki yi hada nafila..." Muryar Dr Shureim ta jiyo acikin kunnanta.


Da?yar ta iya tattara ?arfin da ya yi saura a jikinta ta mike ta nufi toilet don tayi alwala kamar yadda Dr Shureim ya shawarce ta.

A gaban sink ta tsaya tare da kunna faucet, ta soma yin alwalar sai dai gaba Waya hankalinta baya a tare da ita, ta lula duniyar tunanin ina zata ga Taj da ?arta? Tana tsaka da yin alwalar hasken electric bulb din dake a saman ceilling ya fara wasa ya kawo ya dauke, bata kawo komai aranta ba ta yi tsammanin electricity din gidan ne ya samu matsala, hakan yasa taci gaba da yin alwalarta.

Bata yi aune ba, unexpectedly glass din madubin da take fuskanta ya fara tsattsagewa, a razane ta ?ura ido tana kallon abun mamakin gani take kamar idanunta ne ke nuna mata ba dai dai ba, dama bata a cikin hayyacinta damuwa ta fara zautar da ita, mi?a hannu ta yi da niyar ta shafa madubin don ta tabbatarwa kanta abunda take gani gaske ne ko ?arya kwatsam! madubin ya tarwatse da kan shi glass din ya zubo kan floor, har ta kware baki zata fasa ?ara ta ji an fusgo hannuwanta izuwa cikin madubin, ta ?arfi da yaji ake kokarin janta cikin shi, fashewa ta yi da matsanancin kuka na tashin hankali ta dinga yan buge-buge tana ?o?arin kufcewa yayin da hannayen da suka rurruke nata suka ja kusan rabin jikinta cikin madubin, daddagewa tayi da iya ?arfinta na ?arshe ta shiga karanta ayatul kursiyu bata kaiga direta ba ta ji an wurgo da ita gaba Waya gangar jikinta ta dawo cikin toilet Win kanta ya daki floor, A zabure ta mi?e ta watsa a guje ta nufi ?ofa sai dai me? Kafin ta ?arasa ?iiiii taji kofar ta datse kanta, fasa ?ara ta yi da ?arfi take ambaton sunan Yaya shyureim dana Mommyn su don su kawo mata a gaji, bugun kofar ta dinga yi kamar zata 6alle ta, gurnanin mutun ta jiyo a bayanta jiyowar da zata yi keda wuya tayi arba da wani gabjejejn mutun ?a??arfa jikinshi sanye da ba?a?en kaya ya rufe ko'ina na jikin shi, zazzare mashi idanu ta yi kamar mai fama da farfaWiya ta dinga farfari zuciyarta na bugawa da tsananin fargaba ta dinga sambatu tana fadin, "Na shiga Uku!!! Wanene kai? Wallahi kada ka ta6a ni, kada ka matso kusa dani, zan ?ona ka da ayar Allah..., bata ?are maganar ba ya Waura gabjejen tafin hannunsa kan wuyanta ya dam?e shi ya jata tana kuka da yan buge-buge ya nufi bathtube da ita, wani irin ruwan zafi ne ya kwararo ta cikin faucet har tiriri yake yi kamar za'a zabka kaza haka ya soma ?o?arin tura kanta cikin ruwan, wanda hucinsa kaWai bala'e ne tsaf zai ?ona fatar mutun, fashewa tayi da kuka tana ihu ga bleeding da hancinta ya fara yi,

Sai yakushin hannunshi take yi don ya saketa, yana gab da zai tsumbula kanta cikin ruwan, ta furta wata addu'ar neman tsari da Dr Shureim ya koya mata, wallahi ko second ba a ?ara ba mutumin ya 6ace 6aat hasken toilet din ya daidaita, madubin ma ya maida kansa yadda yake, hannunta dafe da wuyanta dake mata raWaWi take kallon Ikon Allah, Wato addu'a tayi a rayuwa musamman in kayi imani ba tare da kokwanto ba, ganin ya 6ace yasa ta zabura aguje ta nufi kofar toilet Win ta dinga bugunta da?yar ta samu ?ofar ta buWe sai dai kafin ta fuce wani irin jiri ya Webeta gaba Waya ta yanke jiki ta faWi yaraf har goshinta ya fashe sakamakon dakar floor da kanta ya yi.

Hankalin Anila dana Taj ba ?aramin tashi ya yi ba, Sun yi matu?ar girgiza da jin abunda ke faruwa da Benazir.

"Kin taba faWa ma wani?" ?aga kai ta yi,"Eh, Yaya Shureim ne kadai ya sani, amma ban faWa masa na ranar dana shiga toilet ba saboda ban farfado cikin hayyacina ba.

Cike da al'ajabi yake Wan jinjina kanshi yayin da zuciyarshi ta cika fam da tashin hankali, Komai da suka faWa yayi shige da case din da suke aiki akai, yanzu ya fara yarda da abunda Anila ta faWa masa akan Benazir.

Chief ya kira bayan ya yi picking gaba daya ya fayyace masa abun da su Aneelarh suka sanar da shi, tashin farko ya ce wannan babban al'amari ne, kuma ya ji dadin zuwan su, in ba damuwa su jira shi ya dawo yana son yin magana da su.

?agowa ya yi tare da kallon su Aneelerh, "Ya bu?aci yana son magana daku, zaku iya jira har lokacin da zai dawo?"

Aneeleerh ta ce, "Ba damuwa zamu jira shi"

FaWa mashi ya yi kafin su ka yi sallama ya aje wayar gefen ta Ana...

"Naga baku sha fruit din ba," Ya Wan tambaya idanunsa akan Benazir dake ta kallon shi..

"Ni wlh hankalina kwata kwata ba a kwance yake ba, bana jin cin komai"

"Look Aneelerh, Ki kwantar da hankalin ki, tun da har ku ka yi dubarar tuntu6armu in sha Allah komai zai tafi dai dai" jinjina kai ta yi ..

"Ina su Unaisah ne?" Benazir ce ta tambaya

"Suna a daki" ya bata amsa batare da ya dubeta ba...

"Zan iya ganin ta" girgiza mata kai ya yi"A'a!"

"Meyasa? pls Taj, almost one month ban ji muryar ?ata ba? Dan Allah meyasa ka ke yi min haka? Laifin da na yi maka tsakanina da kai ne, banga dalilin da zaisa ka shiga tsakanina da ?ata ba, saboda ni na yi wahalar na?udarta na kuma haifa maka ita..." ranta a 6ace ta yi maganar tana aika masa da harara.

"Sau nawa kina yun?urin zubar da cikin nata don kada ya 6ata maki shape?"

Bai ?are maganar ba Anila ta yi saurin furta, "Dan Allah Taj ku daina, ba girman ku bane, bai kamata aji maganar nan daga bakin ka ba, Benazir koda da son ranta ta gudu tabar Unaisah amma ai tayi nadama ko? Allah ma muna yi masa laifi ya yafe mana yakamata kaima ka yafe mata."

Murmushin gefen fuska ya Wan saki, "Ni zolayarta nake yi, amma komai ya wuce awurina, sannan ni ba hanata Unaisah na ke yi ba, tayi rashin lafiyane har kwantar da ita asibiti saida aka yi, bana so na Waga maki hankali ne shiyasa ko kin kira bana Wagawa ....."

Bai ?are maganar ba sakamakon kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji"un da Benazir ta furta tare da mi?ewa tana yarfa hannu ta furta "Meke damunta ne? Wani irin ciwo ne ta yi? Don Allah ka haWa ni da ita! Dama saida na ji a raina wani abu na faruwa da ita, har mafarkinta nake yi ashe bata da lafiya...." Ta faWa har hawaye sun zubo kan fuskarta,

Da damuwa akan fuskar Anila ta ce, "Taj, meke damun Unaisah ne? Meyasa baka sanar dani ba?"

"Calm down your mind, Unaisah ta ji sau?i yanzu, bari na kirata ku gaisa."

Ya faWa tare da Waukar wayarsa yana ?o?arin danna mata kira Unexpectedly suka jiyo shesshekar kukanta!

Kusan a tare suka kai duban su gare ta, tana a tsaye jikinta sanye da Satin fitted gown black colour tabi shape dinta, bata Waure sumar kanta ba,ta sake ta har mid back dinta, ?afafunta na sanye da highhill masu Wan banzan tsini....

Jikinta sai kerma yake yi kamar mazari, yayin da idanunta dake fitar da hawaye ta tsayar da su akan Benazir, ashe tunda Taj da Benazir suka fara sa'insa ta fito daga daki kaitsaye maganganunsu suka sauka acikin kunnanta.

"Daughter meyasa kike kuka? Ko jikin ne?" Da damuwa akan fuskar Taj ya tambaya.....

Da index finger Winta ta nuna Benazir,

"Dama kece mahaifiyata wadda ta haifeni a wulakance! ta barni a cikin kwamin wanka sannan ta gudu ta tafi ta barni! Dagaske kece Aunty Benazir?"

Rai a matu?ar 6ace ta faWa da tsiwa tana fitar da numfashi mai huci.

"Ki amsa min tambayata??" Ta faWa tana zare mata gray eyes dinta...

Tsabar ruWu da tashin hankali ya hana Benazir furta kalma, wani irin shakkarta take ji....

"Shirun da kika yi ya tabbatarmin da abunda kunnuwana suka jiye min."

Ta faWa tare da maida kallonta akan Aunty Aneelerh cikin jin ?unar rai ta ce,"Aunty Aneelerh, I know you won't lie to me tell me, who is she?"

Yawu Aneelerh ta haWiya ?utt, cikin sanyin murya ta ce,"Pls Unaisah, zo ki zauna za mu yi maki bayanin komai..."

Fashewa tayi da kuka tare da girgiza kanta, "Daddy, Aunty Aneelerh meyasa kuka 6oyemin cewa itace matar nan data gudu ta barni? Kuka sani na je nayi jinyarta a asibiti, bayan kunsan irin tsanar da tayi mini, bata taba sona ba, wallahi dana san kece bazan taba yin jinyarki ba koda zaki rasa ranki ne" with a burning heart ta faWa tana aika mata harara.

"Why didn't you kill me at birth if you couldn't care for me? You left me in the bathtub and abandoned me for years, You never thought to return and check on the child you left behind!, wlh hakkina kaWai bazai bari ki gama da duniya lafiya ba...."

Bata ?are maganar ba sakamakon tsawar da Aunty Aneelerh ta doka mata, "Unaisah ya isa! Ya isa haka!! Har yanzu ita mahaifiyar kice, karna kuskura na ?ara jin kin gaya mata maganganu marasa daWi"

Fashewa da kuka Benazir tayi, baiwar Allah tama rasa ina zata tsoma ranta taji dadi.

"This woman will never be my mother! I don't like her, I hate her, I don't want to see her, You're heartless and don't deserve to be called a mother! Dan Allah na ro?e ki ki fuce daga gidan nan in har ba so kike ni in bar maki gidan ba"

Cike da takaici Taj ya dafe forehead Winsa da tafinsa, dama saida yayi fargaban zuwan ranar nan, shi yasan za'a rina saboda Unaisah ta ?ullaci Benazir aranta, haushinta take ji sosai, tsanar ta samo asali ne tun daga kuruciyarta.

Bata saurari kowannan su ba ta juya a zafafe ta nufi kofar dakinsu, da gudu Benazir tabi bayanta ta kai hannu tare da ru?o hannun rigarta, aikuwa cikin fushi Unaisah Win ta bangajeta har saida ta yi taga taga zata faWi, cikin sauri Aneelerh da ta biyo bayanta tayi saurin tallabota.

Rushewa ta yi da matsanancin kuka tana fadin wai ?ar da ta haifa ce ta ke gaya mata magana kamar zata doke ta? "My own daughter calls me heartless! Na shiga Uku Aneelerh ta tsaneni bata son ganina! Wayyo Aneelerh zuciyata zafi ta ke yi min..."

Gaba Waya hankalinsu ya tashi da abunda Unaisah ta yi, abun da ya ?ara ?ona ma Benazir rai yadda Taj ya yi banza da su ko motsawa baiyi ba daga kan kujerar da yake balle ma harta sa ran zai taimaka mata su shawo kan Unaisah, tayi masa mummunar fahimta, batasan lalurace ta hana shi mi?ewa ba, dama da haushin shi aranta saboda tasan shine ya cusa ma Unaisah tsanarta acikin zuciyarta shiyasa harta ?ullaceta arai in bashi Win da ya fada mata ba, Uzair da Aneelerh ba zasu ta6a tona mata asiri a gurin Unaisah ba dole sai in a wurin Taj ta ji.

Bawan Allah Taj damuwa ce ?arara akan fuskarshi, kwata kwata bai ji daWin abun da Unaisah ta yi mata ba.

"Aneelerh, Ku dawo ku zauna, ku barni da Unaisah, zanyi magana da ita."

Rai a6ace Benazir ta nufe shi kamar zata doke shi ta dam?i gaban jallabiyar shi da hannyenta biyu tana huci ta ce, "You caused everything Taj, I hope you're happy now, kaine ka cusawa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login