Showing 90001 words to 93000 words out of 413917 words

Chapter 31 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4507

data Isa ta tunkaresu muddin Yana atare da su, rashin baccin da baiyi ba shine Yaja har muka gaza tunkarar su, lokacin da baccin Ya Wauke shi munyi nasarar yi mashi abunda zai dawo gare mu sai dai wani abun al ajabi ya ku6uta daga hannunmu Ya koma ma gangar jikin shi_

Kamar yadda suka ce tun tarihin kafuwar kurkukun ?addara ba'a ta6a samun prisoners da suka tsira ba sai akan su, kuma ba kowa bace sila face ?addarar kurkuku, da ace unaisah ba ta kasance a gidan kurkukun ba, wallahi Danish bazai ta6a yun?urin taimaka ma wani don ya gudu daga cikin sa ba shiyasa bai ta6a taimakon su Deeja ba bayan yana da hanyar da zai iya fitar da su.

Salsabeel Ya ci ba?ar wahala wurin Wawainiya da su Hibba, babu wanda bai ji jiki ba a cikin su, saboda yankin da su ka faWo a dajin babu ko kayan marmari da mutun zai sha, yasha jaraba yin amfani da sihirinsa don ya sawwa?a masu wahalar amma abun ya faska, Saida ta kai ga ciyawa su ke ci ko su ci ganye don suyi maganin yunwar cikinsu, ga Deeja ba hankali tun da tafarfaWo sambatu takeyi shi kuma Mubeen wasu irin marurai ne masu masifar zafi suka mamaye fatar jikin shi, kullum sai yayi hauka kamar zai rasa ransa saboda raWadin azaba, ga uwar rana dake ?walo masu ta ko'ina ba sauki, ga damuwar rashin yan uwansu sunyi kuka tamkar zasu kashe kawunansu, ba?in cikin da suka ?unsa baya misaltuwa, hakika salsabeel yayi namijin kokari wurin ganin Ya basu kulawa duk da wani lokacin abun nema yake yafi ?arfinsa, gaba Waya sun jigata sun sha wahala, babban tashin hankalinsu miyagun halittun daji dake kawo masu farmaki, kusan kullum ne sai Salsabeel Ya zubda jinin shi wurin faWa da su.

Satin su Waya acikin dajin suna shan ba?ar azabar rayuwa, acikin rana ta takwas suna cikin tafiya agalabaice sunata yi ma Salsabeel kukan yunwa suke ji ma?oshinsu zafi yake yi masu ruwa zasu sha bawan Allah Ya rasa ya zaiyi da su, da gudu Ya nufi Cikin dajin yana neman inda zai samo musu ruwa tun yana tafiya da kuzarinsa har ?afafuwan sa suka fara sagewa sai da yagama shan wahala bai samu ruwan ba yana kan hanyar komawa wurinsu kwatsam ya faWa wani yanki na dajin ba zato ba tsammani ya hango gungun Sojojin ?asar Ghana da suke yin atisayen horaswa a dajin, da gudu ya tunkare su kamar mahaukaci haka suka ganshi Ya faWo masu, har sun saita shi da bindigu ya zube kan gwiwowinshi ya fara rokon su akan su taimaka mashi da ruwan sha, gaba Waya sojojin suka kewaye shi hannunsu ru?e da bindigu saboda basu yarda da shi ba, sunyi tunanin wani mugunne shiyasa basu bashi taimakon daya bu?ataba, tsawa suka fara daka mashi suna tambayar shi wanene shi? Meyake yi a cikin dajin, sam ya kasa ba su amsa, kwatsam ana haka sai ga su mubeen sun watso da gudu iya ?arfinsu suna neman shi wata dabbar daji ce ta biyo su aguje, a gaggauce sojojin suka harbeta da bindiga tun kafin su ?araso nan take suka tarwatsa kan dabbar ta faWi ?asa tana birgima, ai koda sojojin suka ga prisoners sanye da jajayen kaya masu numbers a jikinsu sai suka fara zargin salsabeel ne Yayi garkuwa da su tun da shi ne babba acikin su kuma jikin shi akwai zanan tattoo, wanda alama ce ta tambarin wata ?ungiya, ba su tsaya bata lokaci ba suka Waure Salsabeel da igiya tamau, su Mubeen sunata kuka suna rokonsu su ?yale masu Wan uwansu amman ko ta kansu sojojin ba su bi ba, gaba Waya suka sanya su a bayan motarsu ta sojoji, ba su nufi ko'ina da su ba sai cikin ?asar Ghana.

Bayan isar su, A headquarter suka ru?e salsabeel wurinsu, su kuma su Hibba Asibiti suka mi?a su ganin muggan raunin dake a jikin su, babu irin bugun da sojojin nan basuyi ma Salsabeel ba don ya faWa masu me yakai shi daji tare da ?ananun yara amma ya?i faWa masu, sai ce masu yai bazai iya tuna komai daya faruwa da shi ba, ya faWi hakanne saboda bai yarda da sojojin ba yasan ma koya faWa masu gaskiya ba lallai su yarda ba, A ?alla ya shafe kwana uku a hannun sojojin kafin ya faWa masu cewa su ?an nigeria ne, iya abunda zai iya tunawa kenan a rayuwarsa, ba su sake shi ba har sai da su rubina dake a Asibiti suka samu lafiya sunata tambayar ina Wan uwansu Salsabeel tukunna sojojin suka gane cewa ba mugu ba ne, ba su tsaya 6ata lokaci ba don sun fahimci al'amarin su babba ne ba kamar rahoton da Asibiti suka bayar, hakan yasa suka tuntu6i hukumar sojin Nigeria don su sanar da su dangane da yaran inyaso sai su mi?a case Win wurin su.

Lokacin da sa?on Ya riski su Sir Mubarak, bayan ya duba duka bayanan yaran, nan take ya yanke shawarar kiran chief owais don ya sanar da shi zancen case Win saboda yafi dace wa da hukumar Isod, su yakamata case din yaran ya kasance a hannun su saboda abune da ya shafi 6angaren bincike.

Chief Owais yayi farin ciki lokacin da Sir Mubarak ya sanar da shi, dama a lokacin sunata faman bincike kan yadda zasu gano Unaisah, daga shi har taj sunyi tsammanin cikin yaran zasu ga Angel, sai dai ko da sukaje Ghana suka dubasu babu ita aciki, aranar da sukaje basu kwana ba, sai da suka haWa yaran gaba Waya tare da Salsabeel suka tafi da su a privet jet din chief suka shigo Nigeria....

Bayan komai Ya lafa, Sun sama masu gidan da zasu zauna, basu fara bincikar su ba don sun lura da ba'a hayyacinsu suke ba, sai dai suna lura da duk wani motsin yaran sunyi matu?ar yin al'ajabi da irin rayuwarsu, ba su san komai ba, kamar ranar aka haifo su duniya, daga sunci abinci sai bacci, ba zancen yin sallah, ranar da boss ya kunna masu kallo a tv sunga tashin hankali, kuka suka dinga yi ganin ba?on abu da ba su ta6a gani ba, a ?arshe deeja ce tayi silar mutuwar tv Win.

Chief ne ya Waukar ma su Jazz a matsayin likitan da zai dinga duba lafiyar su, kafin ya bashi aikin sai da ya gargaWe shi akan kada ya kuskura ya sanarma kowa ko da kuwa mommynsa ce, shiyasa dr jazz ya?i sanar ma kowa nashi wanda silar hakan yaja har sir mubarak ya fara zargin shi akan wayar da yake yawan kama shi yanayi ta maganar gidan kaji, matsalar da aka samu shi Sir Mubarak baisan da zancen Aikin da Jazz ya ke yi ma chief owais ba, sannan baisan a gidan da chief owais ya killa ce su ba, amma Yana bibiyar case din yaran don jin wani hali ake ciki game da binciken su.

Bayan wasu yan kwanaki, Su chief suka tuntu6i Salsabeel suka tsare shi da tambayoyi dangane da rayuwarsu, bai 6oye masu komai ba gaba Waya ya sanar da su, wa'iyazubillah kusan zaucewa sukayi saboda tsananin tashin da hankulansu suka yi, ba su ta6a jin labarin daya gigita su ba irin wanda Salsabeel ya ba su, abu kamar ashirin wasan kwaikwayo amman wai a zahiri yake faruwa zuciyoyin su sun karaya ainun.

to a cikin labarinsa ne suka ji ya ambaci sunan Angel, sunyi matu?ar girgiza da jin cewa tana a cikin su, kuma sun raba hanya da su, hankalin su ba ?aramin tashi yayi ba, musamman taj kamar zai zauce jin cewa Angel dinsa tana a cikin su, ba dan zuciyar imani ba da tuni ya haWiyi zuciya ya mutu, ganin yadda yake kuka kamar ?aramin yaro yasa Salsabeel tambayar shi meya faru, Chief ne ya bashi amsa da cewa yarsa ce Angel Win da ya ke magana akai, wani irin farin cikine ya lullu6e Salsabeel ganin Mahaifin unaisah, jiki na rawa ya ru?o hannun shi tamau ya fara jinjina mashi yana faWin ya gode ma Allah saboda yarinyarsa tana da kaifin basira Allah yayi mata baiwar da zaiyi wuya asamu mai irin ta, bayan haka yace da shi ya kwantar da hankalin shi, in sha Allah babu abun da zai faru da su saboda suna atare da garkuwa yayi imanin in har ba lokacin mutuwarsu ne yayi ba to kuwa zasu ku6uta batare da sun cutu ba, abun da ya dace shine su tayasu da addu'a kuma a bibiyi dajin evil forest inda rabon agansu toh, shi kanshi Salsabeel Win yayi mamakin daWewarsu a dajin, amma da yayi zurfin tunani sai ya tuna cewa Danish baisan inda zai kai su Unaisah ba, shi iya rayuwarshi daga gidan kurkukun ?addara sai cikin dajin evil forest, bai ma ta6a sanin akwai wasu mutane dake rayuwa a wajen dajin ba, kuma hada ?arin ba su da taswirar dajin da komai zaifi zuwa masu da sau?i, saboda dajin evil forest kurman dajine yana da wuyar sha'ani.

Jami'an isod sun yi matu?ar ?o?ari wurin ganin sun gano su a dajin, kusan kullum ne sai jiragensu sun kewaye shi suna shawagi Allah ne dai bai nufa za su haWu da su ba.

Babban abun da yaja ma su Angel daWewa a dajin, Lokacin da Danish ya ke yin amfani da sihirinsa wurin jigilar Waukarsu idan dare yayi lokacin sun yi bacci yana yin tafiya mai nisa da su duk don su nisanta da gidan kurkukun ?addara silar hakan yaja har suka 6ace hanya suka bar yankin da ya kamata su faWa, sukai can wani yankin daban.

_Alhamdulillah, Kunji yadda akai Su salsabeel suka ku6uta daga gidan kurkukun ?addara, da kuma yadda akai suka haWu da Chief Owais, kuma cikin ikon Allah daga baya sai gashi suma su unaisah an ceto rayuwarsu, a ranar da sojin america suka tuntu6i chief da case din samun yara yan Nigeria a daji, wani irin farin cikine ya lullu6e su, anci sa'a a lokacin yaje babban burnin america kuma sai ga labarin tsintar su unaisah, tunkafin suga su wanene ransu ya basu cewar sauran yaran ne kuma zaiyi wuya in babu ita acikin su, cikin ikon Allah sai ga hotunansu sun gani wayyo Allah tsabar murna lokacin da chief ya turama taj hotunansu da yake shi yana a Nigeria, ko runtsawa baiyi ba adaren ranar da suka shaida baiyanarta_

_A tsanake salsabeel ya ?arasa ba su labarin yana duban fuskokin su_



*Mu haWu Jibi Idan Allah yakaimu da rai da lafiya, don jin yadda zata kaya*


Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*


*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: _*~
'=؋?BOSSLADIESWRITERS=؋?*~_



3,F 'DB/=؋?=?%?=؞?


~Takun ?arshe=?%?~



Dedicated to Aunty Kubra=؋?=؞?



B5) -( 1HE'F3J) :J1 9'/J) (JF 'D3,F'! E9 *7H1'* E9B/)=؋?=ؘ?=??


An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists d'=؋?=ؘ?




Daga al?alamin Boss Bature=؋?
'




_________________________________E22
'?



Ta jima tana kallon hotunan kafin Ta mi?e Wauke da su a hannunta, da sauri ta juya ta nufi mirror drawer ta buWe gida na uku ta saka su a ciki.

Tana ?o?arin mikewa sallamar Taj Ta katse mata hanzarin ta daga wajen dakin ta jiyo muryarsa.

"Daddy gani nan zuwa na gama shiryawa, waya ta nake nema banganta ba"

"Ina kika ajiyeta ne"?

Watsa hannu tai kamar tana agabansa na manta daddy

"Jiya naso na ganta a hannun Wan uwan ku sajeed, bari na tambaye shi" amsa mashi tayi da toh aranta tana mai mamakin yadda sajeed yake da nacin son waya, sam baya gajiya da ita."

Badajimawa ba, taj Ya turo kofar dakin Ya shigo hannunshi ruke da wayar.

Face dinsa da murmushi Ya mika mata"Na lura baki son wayar nan taki, saboda ba ki damu da ita ba, me zai hana ki bar ma sajeed din tun da yafi ki sonta"


Muryarta da yar shagwaba tace"wallahi inason abuna, sai dai asiya masa wata tunda Yana so, dr laura fa ta bani ita taya ma zan bada ita" ta yi maganar tare da kar6ar wayar daga hannun sa

"Kin ta6a kiranta ne kunyi magana"?

"Mantawa nakeyi wlh, amma in sha Allah zan kirata in na samu nutsuwa"

"Baki kyautaba yakamata kiyi kokari ki kirata" amsa mashi tayi da toh

"Daddy dani kadai zamu tafi"?

"Eh, next time suma zan kai su gidan"

Ru?o hannunta yai acikin nashi, suka fito daga dakin, babu wanda Ya lura da su fira taja hankulan su, tana kallon su Deeja dake ta faman sakin murmushi wani irin sanyi taji aranta, yanzu damuwarta akan sauran prisoners ne wadanda ke AGIDAN KURKUKUN ?ADDARA!

Har sun kusa fita daga falon, Kamar ance ta wurga eye balls dinta kan second floor, kwatsam Ta hango Danish dake kallon ta, cikin shiga ta pajama launin blue sky, tayi tunanin ba ita Yake kallo ba, sai tai saurin kau da idon ta, gudun kada ya ga za su fita, tasan halin mutumin nata.

Suna fita daga falon ta sauke ajiyar zuciya, kasancewar baida nisa part din nashi, A ?afa suke tafiya suna fira hanyar da suka biyo ko'ina hasken electric bulbs ne tamkar ba dare ba ga wata iska mai ni'ima dake kaWawa

"Daugher, kina jin sautin da nake Jiyowa kuwa"? da mamaki Tace A'a daddy menene"?
"Akwai mutun abayan mu, baki ji sautin tafiya ba" aWan ruWe ta furta mutum kuma? Wanene? bata jira ya bata amsa ba tayi saurin juyawa don ganin waye.

Har saida gaban ta ya faWi idanunta adan zare take kallon shi, Hannayensa harWe akan kirjinsa, fuskarsa babu fara'a, kayan baccin da ta gan shi da su sune a jikinsa fararen ?afafuwansa ko takalma babu.


Juyowa taj yai tare da kallon shi, ashe tunda suka fito Yake biye da su, shi taj yasan da zaman shi itace bata lura ba.

Muryarta kamar zata fashe da kuka tace"daddy, mu tafi da shi kawai"

?ar dariya taj yai tare da cewa"ya zama dole ay, wa ya isa ya hana shi zuwa"?

"mu tafi My man, nayi zaton kayi bacci, shiyasa ban neme ka ba, dama zamu je part din daddyna ne don in gaisa da Auntyna"

kamar jira yake ta bashi damar yabi su, da sauri ya nufe su, a maimakon ya tsaya gefen ta sai ya shiga tsakaninta da taj, yasa hannu ya raba hannayensu dake ruke cikin na juna lamarin ya daurewa taj kai aranshi ya ayyana wannan wani irin namijin kishine? Uban nata ma bai ?yale ba inaga idan wani ne daban ba? Tun yanzu ya fara jin fargaban yadda zata kaya tsakanin chief da danish tabbas akwai ?ura.

A haka suka jera har suka ?araso ?ofar shiga Part din, Komai nasa shigen kalar na sashen da suke ne banbancin kaWan ne amma fa Ya haWu, Ita kanta Angel tayi mamakin katafaren Ginin gidan Chief gari guda An ?awatashi kamar A dubai.

Dafe kofar taj yai da hannunsa a hankali ta zuge masu, katafaren falo ne an kawatasa da furniture, ga wani sanyin A.c na mai sanyaya zukata

Sai ?ara kallon ko'ina take tana Wan jinjina kanta, har cikin ranta ta ?ara jin ?aunar chief saboda kyautatawarsa ga daddyn ta.

"Bismillah, Ku zauna bari naje nayi mata magana" ya fada tare da wuce ya nufi upstairs.

A hankali suka zauna kan sofa, kallon sa tai suka hada ido cikin na juna.

"Baki kewata ba? kin manta da dani jiya ko ki neme ni" yana magana tamkar baisan motsa lips dinsa

"Ni da kai waye mai laifi? Jiya ko kallo ban ishe ka ba, ka kama hanya ka bi uncle din chief inata kallon ka ko waiwaye na bakai ba" ta faWa tana kwa6e masa fuska

Lumshe idanunsa yai batare daya furta mata komai ba

"Har ciwon ciki nayi jiya kamar zan mutu, ni kadai a restroom na kasa bude kofa har na fadi kasa na suma duk kana ina"?

"Ina atare dashi," atakaice Ya bata amsa

Ru?o hannunsa tai tana kalllon dogon yatsan hannunsa dake asanye da silver ring, yayi matukar yi mata kyau

"Shi ne Ya baka wannan"? ?aga mata kai yai alamar eh,

Da fara'a akan fuskarta tace"Bani labarin abun da ya faru tsakanin ku jiya"?

Sai da ya fara kai soft lips dinsa saitin kunnanta kafin ya fara bata labari saboda bai iya Waga muryar shi.

Sai faman sakin murmushi takeyi hakika taji dadin kyautatawar da prime minister yayi masa, kuma ta fahimce shima yaji dadi tun da gashi nan da bakinsa yake bata labari mutumin da be cika surutu irin haka ba.

"My man, Ni dai fatana Allah yasa mutumin nan ya zama alkhairi agare ka, wlh tunda nagansa naji ya kwanta min araina saboda kamannin dake a tsakaninku..."

kafin ta ?are maganar Sautin takalman daddynta ne Yaja hankalin su ga dubansa, saukowa yai down a hanzarce Ya nufe su Yana fadin"daugher, bacci takeyi auntyn naki, ko zaki je ki same ta adaki, Inaso ki bata mamaki" murmushi tayi tare da mikewa da sauri Danish Ya mi?e zai bita, kallon shi tayi cikin sanyin murya tace"ka zauna ka jira ni, Yanzu zan fito ba daWewa zanyi ba"

Taj dake kallon su murmushi yai tare da ?arasawa gefen Danish yace"Idan saboda ni ne, To mu zauna gani ka gaka ita sai ta shiga watakli hankalinka zaifi kwanciya,'

Kamar kuwa yasan sbd shi Ya mi?e zai bita, komawa yayi ya zauna hankalinsa akan Angel dinsa Harta haura kan stairs.

A hankali Ta zura kafarta cikin dakin, tana shiga ta soma bin ko'ina da kallo masha Allah, a hankali ta sauke idanunta kan Danejo dake a nannaWe cikin bargo sai sharar baccin ta take yi.

watsa wa tayi da gudu ta daddage ta haye kan gadon gaba Waya ta ?an?ameta tana dariya, wata irin firgita danejo tayi cikin magagin bacci take fadin"daddyn Angel, wayyo Allahna kana ina wai wanene ke takura min! Nashiga ukuna"

Yaye mata bargon Angel tayi, tana faman haki ta buWe idanunta waWanda suka kada jawur saboda bacci, A hankali ta sauke su

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0