Showing 321001 words to 324000 words out of 413917 words

Chapter 108 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4572

na! Wai dagaske ne Yana faruwa?"

Commender James ne ya yi maganar tsabar ruWin tashin hankali yasa shi jin al'amarin kamar almara.

Jinjina mashi kai ya yi alamar eh ba tare da ya iya furta kalma ba.."

Gaba Waya saida ya kunna masu videos Win prisoners lokacin da aka zo kan nasu Jemimah kifa kai general Noah yayi kan table Win kamar zai fasa ihu saboda tsananin tausayin yaran, kukan zuci yake mai azabar radadi.

Babban abun takaicin da ya haddasa matsananciyar damuwa a zuciyarsu yadda matsafan suke lalata rayuwar ?ananun yaran saboda rashin imani a lokacin da suke tsaka da raWaWin ciwon cikin jinin al'ada.

Bayan haka sun karaya da jin irin kullan da suke yi masu tun suna jarirai babu shige babu fuce, abinci sau Waya a rana, kaya kala Waya, sun ?as?antar da rayuwarsu sun tauye masu hakkinsu na rayuwar duniya sun maida su kamar dabbobi.

"Wlh, na rantse da wanda raina yake a hannun shi, mutanan da suka ?ir?iri gidan kurkukun ?addara ba zasu ?ara sha?ar numfashi cikin kwanciyar hankali ba, Waya daga cikin su bazai sha ba, idan har suka kuskura suka zo hannu wlh sai sunyi danasanin haihuwarsu da uwayensu suka yi a duniyar nan, sai sun WanWani kuWarsu sai sun manta da duk wani jin daWi da suka ta6a ji a duniyar nan..." a harzu?e Noah ya faWa kamar ana tunzarashi da ?yar suka lalla6a shi ya koma ya zauna yana faman yin haki kamar wanda yasha gudu...

Shiru suka yi na Wan wani lokaci, batare da wani ya ?ara furta uffan ba, ?o?ari suke su kwantar da hankalunsu don su samu nutsuwar faWin ta cikin su, tashin hankali ya hana ko ruwan sanyi su kora ma ma?oshin su.

Muryar Big guy ce ta katse shirun nasu

"Abunda muka gano dangane da kungiyar matsafan, sadaukarwa da su ke yi, dole sai danginka, mutun ba zai iya sadaukar da wanda bai haWa ala?ar jini da shi ba".

Girgiza kai Dr. zahra ya yi, "Banma san me zance ba, mutanan nan sun san me suka taka, kuma daga ji manyan mutane ne a ?asar nan, shiyasa suka daWe suna aikata ta'addanci batare da asirin su ya tonu ba..." Maganar Dr. Zahra ta Waga hankalin Chief Owais da Big guy saboda sunsan su wanene ke ru?e da ?asar wato family Win su.

"Mutane ne masu hatsarin gaske, tunkarar su ba abune mai sau?i ba, ta ya za'ae ma mu san su wanene su balle har mu iya kawo ?arshen su? Babban abun da ya Waure mana kai yaran gaba Waya ba su ta6a ganin fuskokinsu ba, hatta shi babban cikin su Salsabeel da ya fi su daWewa a gidan kurkukun, kai hatta yaron da ke ru?e da mu?amin garkuwarsu, ya rayu tsawon shekaru baisan fuskokinsu ba amma yasan Nicknames Win su, saidai ya?i faWa mana komai dangane da su, yana da taurin kai, mutunne mai wuyar sha'ani, Wan uwansa Salsabeel ya faWa mana cewa yafi shi sanin su wanene elders..." Big guy ya ?are maganar yana dubansu.

Ci ya Waura da cewa, "Har yanzu suna sarrafa shi, mawuyacin abune ya bamu haWin kai, Wan uwansa yace in har muka tursasa mashi zai iya ja mana gagarumar matsalar da bazamu iya magance ta ba..."

Agent Jabeer Osman ya Waura da nashi bayanin, "Matsafan suna da kaifin basira da wayau, sun san cewa wata rana asirin su zai iya tonuwa shiyasa basu ta6a yin kuskuran da wani zai san fuskarsu a cikin yaran da suke raino ba, sun iya takun su..." ya faWa yana jinjina kan shi.

"Garkuwar nasu Yaro ne mai kafiyar tsiya, bai yarda da bare ba, yan uwansa kaWai ya sani, amma abun Waure kai shine silar Waukar yarinyar da suka ru?a matsayin ?addararsu suka kaita gidan kurkukun wanda silar kasantuwarta a gidan ya ja har suka samu sha?uwa mai ?arfi tsakaninta da shi garkuwar nasu ta yadda su kan su suka gaza raba shi da ita, silar hakan yaja har ya ku6utar da su daga kurkukun.

Big guy ne ya kora jawabin, bayan ya kai karshe Commender James Ya ce"That means Unaisah is his weak point, she can be used to control him, right?"

Jinjina mashi kai chief yayi murmushin gefen fuska James ya saki, "Everything will be easy for us if we can use her to control him"

"Da bu?atar mu san ya ?arfin ikon su Yake? Menene rauninsu? da kuma Location Win da gidan kurkukun kaddarar Yake kafin mu fara shirye-shiryen kai masu farmaki" A cewar Captain lewis...

Chief Owais yace, "Karfin ikon su, suna iya 6acewa, bayan haka harsashin bindiga baya iya fasa fatarsu, makami ko wuta basa tasiri akan su, In har ba an ta6a lafiyar idanunsu ba, wanda kuma yin hakan ba abu ne mai sau?i ba, saboda kakin Gaints Win dake a jikin su garkuwa ne, makami irin namu bazai iya yi masu illa ba..." gaba Waya hankalinsu ya tashi da jin bayanin Chief! Tunaninsu ta ya za'ai su farmaki mutanan da basa jin bullet, ko wuta balle wani makamin irin nasu.


Big guy ya Waura da cewa, "Bayan haka, su basa faWa da makami sannan da bugu Waya suke kashe mutun." Waro idanu waje su commender suka yi gaba Waya sun kiWima da jin zancen nan,

"Sanin inda gidan kurkukun ?addara yake mutun Waya ne zai iya yi mana jagora kuma shi kaWaine zai iya taimaka mana gurin sanin ta yadda zamu iya kashe su cikin sau?i"


*Daga Al?alamin Boss Bature=?%?
'?*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 & 08103884440*
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: ________________________________
'?=?%?=???=???>???






..." bai kare maganar ba General Noah Ya katse shi da cewa"Dole saida shi zamu iya farmakarsu? Shi Wan uwan nashi salsabeel bazai iya yi ma sojojinmu jagora ba" girgiza kai big guy yai"saboda laifin daya aikata masu, sun Wauke garkuwar sihirin shi, Salsabeel bai da karfin ikon da zai iya jagorantarmu, dole sai dai shi Danish din"!

A kalla sun shafe tsawon awa da rabi suna tattaunawa a karshe dai ba su tsayar da ranar kai farmakin ba, har sai zuwa lokacin da Danish zai basu haWin kai....


A yammacin ranar Su uku ne zaune saman kujerun backyard din gidan, sunyi shiru babu mai magana acikin su, yanayin fuskokinsu kadai zai tabbatar maka da akwai wani abu dake damunsu, kowan nan su da abunda yake sakawa cikin ran shi..

Muryar chief ce ta katse shirun nasu"Ina salsabeel din? Ka kira shi? Naji shiru baizo ba"

Cikin nutsuwa big guy yace"yace min yanzu zai shigo, mu kara hakuri nasan yana akan hanya"

jinjina kai chief ya yi tare da kallon Taj, wanda gaba Waya hankalin shi baya akan su, Ya langwa6e kai jikin sofa, har yanzu damuwar Unaisah ta hanashi sukuni baida wata walwala.

"Taj"! A hankali Ya dubi Chief daya kira sunan shi Na'am..

"What's wrong with you? tun zaman mu anan banji kayi magana"!

murmushin karfin hali yayi in a cool voice yace"Sir bakomai, idan ma akwai abunda ke damuna bai wuci tunanin yadda zamu kawo karshen kurkukun kaddara ba"


murmushi chief yayi wanda bai wuci fatar la66ansa ba.


"In sha Allah komai ya kusa zuwa karshe, bi'iznillah mu ne da nasara"


da kwarin gwiwa ya furta maganar, suka hada baki gurin faWin"Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa"


kafin wani yakuma magana, sallamar Salsabeel ta katse su atare suka dago tare da kallon shi, cikin girmamawa Ya gaishe da su, da fara'a suka amsa amsa mashi


"Ay min afwa, Uziri ne Ya ruke ni, nabarku kuna ta zaman jira na" big guy yace"kada ka damu bismilla zauna mana" zama yayi kan kujerar dake a gefen Taj, ya maida duban shi ga chief ya nutsu yana jiran jin me zai ce.

Big guy ne ya zayyana ma shi komai da suka tattauna agurin meeting, ya ?ara da cewa"ko yau muka samu wanda zaiyi mana jagora zuwa gidan kurkukun, a shirye muke da mukai farmaki, yanzu haka da nake maka magana mun riga da mun tadani rundunar dakarun Sojoji, da kuma makaman ya?i, ku kadai muke jira Salsabeel! We don't need to waste time!.


Chief ya Waura da cewa"nayi alkawarin bazan ?ara takura ma Danish game da zancen kurkukun ?addara! Salsabeel kai kadai ne kasan ta wace hanya zamu iya samun haWin kanshi, saboda kafi mu sanin wanene shi, pls ka taimaka mana Salsabeel, muna so muje mu gane ma idon mu abunda suke aikawata mu kuma kawo karshen su...."

yanayin yadda chief ke yi mashi magana da raunin murya ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, ji yake inama ace zai iya yi masu jagora da kan shi basai sun bukaci Danish ba wlh da babu abunda zai hana koda hakan zai yi silar rasa rayuwarshi..yayin zurfi cikin tunanin shi muryar Taj ta dawo da shi hayyacin shi



"Kayi shiru baka ce komai ba, gaba dayanmu mun ?agara da muji daga gareka, Salsabeel mun yi imanin zaka sama mana mafita in sha Allah, pls kada ku sagar mana da kwarin gwiwar mu, hatta commender james shima ya shirya bada gudummuwarshi gurin kai farmaki, haka zalika Rundunar Sojojin Nigeria suma sun shirya tsaf lokaci kadai suke jira mu faWa masu"


ya faWa yana duban Salsabeel"saura kai Salsabeel ka bamu gudummuwarka mun san ka yi kokari amma muna bukatar ?ari"

Dukar da kanshi ?asa yayi lamarin na nema yafi karfin shi baisan ya zaiyi da Danish ba, shi kadai zai kawo masu cikas, baisan yadda zaiyi ya tankwara shi ba, amma tabbas yana da tabbacin mutun Wayane duk duniyar nan zai sa shi abu yayi, Cikin karyayyar murya.

yace"Yalla6ai, Ku bani mintuna shabiyar In ba damuwa, inaso zanyi magana da Danish din"


big guy yace"muna jiranka" mi?ewa yayi cikin takun sauri Ya nufi cikin gidan.

Yana shiga falon Ya hango Unaisah tare da Danish su biyu zaune kan rug, sun tasa notebooks agaba tana koya mashi karatu, tsakanin jiya izuwa yau, ta janye sharuddan data gindaya mashi duk da bata sakar mashi fuska.

Sam basu lura da shi ba, har saida yayi masu gyaran murya kafin suka dago tare da kallon shi, suna ganin shi suka mike tare da gaishe da shi ya amsa masu sam ba walwala ya dubi Danish.


"Inason yin magana dakai" ya faWa tare da juyawa ya nufi upstairs


sai da ya fara kallon Unaisah tace"yana jiranka, ka tafi, ni zan tsaya anan idan kun gama maganar sai mu ci gaba da karatun"


amsa mata yai da toh kafin Ya bi bayan Salsabeel, a dakinsa Ya same shi tsaye, cikin lalama Salsabeel Ya fara magana.


"Danish ka bani mamaki! Ina hankalinka da tunaninka suke? Kamar baka da zuciya a kirjinka ka rasa su wa zaka rufa ma asirin sai waWanda suka cutar da rayuwarka? Danish baka da burin daukar fansa akansu? Ko dan saboda mu kawo karshen zaluncin su mu kuma ceto rayuwar sauran yaran dake a hannunsu yakamata ka basu hadinkai, mutanan nan sun shirya tsaf don sukai farmaki a mutu ko ay rai kai kadai suke jira pls Danish kada ka bani kunya mana, a yadda nasanka kai mutunne mai tausayi da son taimako kuma da kake cewa sune iyayenka masu sonka karyane elders baxasu taba zama masoyanka ba iyayenka daka kullata a ranka zai iya yiyuwa basu suka sadaukar da kai ba suma suna cen suna kewarka ka wani ne a danginka kayi tunani mana. .." tunda ya fara maganar facial expression din Danish bai nuna ya karaya da kalaman Salsabeel ba.



Bai ma bari Ya karasa maganar ba, Ya katse shi da cewa'I can't, please don't pressure me i don't want anything to disturb my peace of mind, Salsabeel you know who the elders are! basai nayi maka bayani ba, ka kuma san su wanene Evil giants, sannan ka san kurkukun kaddara gaba da baya, tayaya kake tunanin zasu iya kai masu farmaki su yi nasara akansu? Inajiye masu tsoron su rasa rayukansu saboda basu da karfin da zasu Iya cin galaba akan su"


bai kare maganar ba Salsabeel Ya katse shi cikin marairaice fuska yace"Danish! Wannan ba hujja bace! Allahn daya halicci elders din shi ne zai basu nasara, saboda sun dogara da shi kuma sunyi imanin zasu iya cin galaba akansu, kawai ka yi abun da suke so"


"Bazan ta6a fahimtar abunda kake fadi ba, ka daina wahalar da kanka salsabeel, banaso mu samu sabani atsakaninmu pls na roke ka ka kyaleni, kaima kuma ka fita sabgarsu in har ba so kake rayuwarka ta salwanta ba..."



duk yadda Salsabeel yaso ya shawon kanshi Yaki fahimtarshi ya kangare ya sanya taurin kai da kafiya, tun yana lallaba shi ta lallama har takaiga Ya cakumi Gaban rigarshi da hannayenshi cikin jin kunar rai ya dinga zazzaga mashi masifa kamar zai rufe shi da bugu ta inda yake shiga batanan yake fita ba, a karashe yace tunda na bika ta lallama ka ki bani hadinkai, zan bi dakai ta tsiya ne, hanyar da baka isa ka guje mata ba, dole kaje ko kana so koba so.."


bayan ya fita daga dakin akan stairs ya tsaya yana faman fitar da hucin bacin rai, yaji haushi da takaicin hali irin na Danish, duk da yanayi mashi Uziri saboda sanin cewa bashi kadai bane har yanzu elders suna iya sarrafa shi amma A halin Yanzu daga zuciyarshi ne bawai Evils din jikinshi bane.


Abunda ya fahimta dangane da Danish baya son rabuwa da Unaisah shiyasa yaki basu hadin kai, gani yake kamar in yabisu suka je kai farmakin rayuwarshi zata Iya salwanta batare daya cika burin shi akan Unaisah ba gyaWa kai yai da alama ya kamo bakin zaren saukowa down yayi bai ganta a falon ba, kaitsaye ya wuce bedroom din su, yayi knocking almost 3 times kafin ta buWe mashi kofar yaci sa'a ita kadai ce a ciki.


"Ya salsabeel yau kai ne adakin mu" dakyar ya kakaro murmushi kan fuskarshi yace"ni ne Unaisah, tun da kika ganni kinsan abune mai mahimmanci ya kawo ni gurin ki"

cike da mamaki tace mashi toh, daga gefen gadon suka zauna suna fuskantar juna, ta tsare shi da idanunta cike da ?agarar son jin wata magana zai mata


"Unaisah Kin san meya faru lokacin da chief ya shiga da Danish Questioning room a headquarter wanda yayi silar fusata Omar har suka samu sabani..." aWan ruWe ta girgiza mashi kai"ba komai na sani ba, kaWan na fahimta daga furucin ya omar"

Nan take Salsabeel Ya labarta mata abun da Ya faru tsakanin Danish da Chief,shi ma abakin big guy yaji komai.

ranta ya sosu da jin abunda Danish yayi ma chief, babban abunda ya fi bata takaici daya ce ma chief ba gaskiya ya ke faWi ba, they've never hurt him Suna sona shi kuma sune iyayen shi, bayan su bashi da wasu iyaye a duniyar ranta yayi mugun 6aci ba kaWan ba, sam ta kasa magana sai jinjina kai take.


"Unaisah babu irin magiyar da banyi ma Danish ba, akan ya amince ya basu hadin kai yakiya, nayi lallashin nayi ro?on duk abanza wlh da raina ya baci kamar in rufe shi da bugu saboda ya bata min rai..." ya faWa rai a6ace ya Wan dakata Yana kallon unaisah dake kallon fuskarshi

"Wallahi da ace zan iya jagorantarsu zuwa gidan kurkukun kaddarar da tuni nayi hakan Unaisah, sai dai ni yanzu bani da wani karfin ikon da zan iya yin hakan, bayin Allahn nan sun shirya tsaf sun tanadi rundunar sojoji da makaman ya?in da zasu farmake su abu Waya ne zaiyi masu cikas wanda zai yi masu rakiya zuwa gidan kurkukun kaddarar, Unaisah basu san hanyar da zasu bi ba, ba su san a daidai ina ginin yake ba! Shin akan ?asa Yake ko karkashin kasa Yake? Bayan haka ke kinsan yadda ginin yake wani irin kurman ginine mai rikitarwa da tsoratarwa in har mutun baida ilmi akan shi wlh tuni zai zauce, Danish shine makamin da zamu iya tunkararsu da shi ..." da yai wanann maganar bakomai ta tuna ba face lokacin data saci hanya ta fita matakalar bene ta dinga mayar da ita baya, ga wannan rudin mai rikita kwakwalwar mutun ya dinga ganin abun da babu azahiri.


"Kinyi shiru baki ce komai ba, yakamata Mu ne mi mafita Unaisah, In ba haka ba elders zasu cigaba da aikata zalunci, kwara muyi amfani da wannan damar kada muyi gangancin da zata kubce mata..'

tsantsar damuwace akan fuskarta cikin sanyin murya tace"Yaya Salsabeel menene mafita? Kafi kowa sanin halin Danish, Yana da taurin kai da kafiya, Idan ya fadi abu babu wanda Ya isa Ya canza ra'ayin shi...." bata ?are maganar ba, Salsabeel yai saurin furta"akwai mafita Unaisah" a kagare tace"menene mafita" shiru yayi jim yana jin shakkar yadda zata dauki abun amma daya tuna irin burin da take dashi na son ruguza kurkukun kaddara sai ya samu kwarin gwiwar ce mata"Unaisah, duk duniyar nan mutun Waya ne kacal zai iya tursasa mashi Ya bashi umarni kuma Ya bi shi sau da ?afa..." da ruWu akan fuskarta tace"wa kenan"?
Nuna ta yai da index finger din shi waro idanu waje tayi kamar wadda taji wani mugun abu

"Ke Unaisah! Basai nayi maki dogon bayani ba, kin riga da kinsan irin tsantsar kaunar da Danish ya ke yi maki, wanda ko sauran yan uwanshi da suka taso atare bai ta6a yima kwatankwacin shi ba, wlh nayi imanin in har kika bashi umarni yaje zai je..."

da matukar tashin hankali ta girgiza mashi kai labbanta na rawa tace"I can't... I can't change his mind Danish won't listen to me ya Salsabeel kai fa ka fadamin wasu lokuttan ba shi bane zai iya wuni baya a hayyacinsa taya kake tunanin zan iya bashi umarni ya bi"?


Ta fada idanunta azare take kallon shi, ita babban tashin hankalinta a haWa ta dashi don ta shawo kanshi bataso su sake samun sabani bayan haka tana jin tsoron tayi silar jefa rayuwar masoyinta cikin haWari, da alama soyayyarshi na nema ta rufe mata idanunta..


"Unaisah Zaki Iya, Ko ba don saboda son da yake yi maki ba, idan ba zaki manta ba na ta6a fada maki dalilin dayasa suke kiranki da kaddarar kurkuku" kura mashi ido tayi batare da kyaftawa ba.


"Ma'anar hakan shine ke kaWaice zaki iya tarwatsa tarihin kurkukun ?addara! Kamar yadda yazo a allon tsafin su, duk da bamu da tabbaci Allah kadai yasan gaibu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0