Showing 114001 words to 117000 words out of 413917 words

Chapter 39 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4474

yarinyar ba'a kusa take ba, suyi hakuri zuwa gobe sai a sanar da iyayenta amsa mata sukai da toh ..........

Bayan komai ya lafa, Aneelerh ta kira mami awaya don ta sanar da ita halin da ake ciki, a lokacin tana a falo zaune zuciyarta cike fal da tunanin kome Ya tsayar da su aneelerh har yanzu basu dawo ba? Ko dai sun samu shiga gidanne? Ita kadai take ta tufka da warwara, kiran na shigowa a hanzarce ta dau wayar dake akan sofa hand, ganin sunan aneelerh yasa tay saurin dagawa

"Aneelerh! Ina fata kuna lafiya? Naji shiru baku dawo ba, ba sai da nace maku in baku samu shiga gidan ba kada ku takura kanku?

On the other hand Aneelerh tace"mun samu shiga mami, amma bamu samu damar yarinyar ba...." a tsanake ta sanar da ita komai ta kara da cewa"tace zuwa gobe zata tuntu6e mu,..."

Mami tace"to kuyi hakuri ku dawo gida, wani jinkirin alkhairi ne..."

"Mami, Yanzu haka muna asibiti, benazir ba lafiya..." tunkafin ta kare maganar mami ta doka salati tana fadin wata benazir din? Meya same ta"? Gaba daya hankalin ta ya tashi
Shigowa ummi tayi falon tana kallon mami dake ta zagba salati tana sauraron Aneelerh dake bata labarin abun da Ya faru bayan komawarsu dr shurem gida,
"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'i abu baiyi dadi ba, kai jama'a baiwar Allahn nan tana jin jiki, ubangiji Allah Ya tashi kafadunta, Anerlerh gani nan zuwa asibitin, kice wa mahboob kada ya manta da junaid karfe shida Yaje ya daukosa" amsa mata aneelerh tayi da toh
Bayan ta katse kiran, fuska A yamutse ta kalli ummi dake tambayar ta lafiya meya faru taji ta ambaci sunan benzair
Girgiza kai tayi kafin ta kwashe komai ta sanar da ita, hankalin ummi ba karamun tashi yayi ba.

"Yanzu zanje asibitin, ki zauna ke inyaso gobe sai kije kada abar gidan ba kowa, duk da Ana tana nan ba lallai junaid Ya yarda da ita ba kinsan shi da rigima."

Amsa mata ummi tayi da toh, cike da Alhinin abun da Ya faru, da sassarfa mami ta dauko hijabi ta zubla ta fito daga daki, ummi tayi mata adawo lafiy sanna tace agaishe mata da mai jiki, kafin taje goben

Mami na fitowa daga gidan saiga motar abie ta shigo, hakan ba karamin dadi yayi mata ba, dama abun hawa zata tsayar akaita can, sai gashi Allah ya dawo da shi, Agabanta Yayi parking motar bata jira Ya fito ba, ta bude motar ta shige sai da ta zauna yake tambayarta ina zataje yaga kamar bata acikin nutsuwarta, nan ta sanar da shi abun da ya faru na rashin lafiyar benazir, har faWa sai da yayi akan fada matan da aneelerh tayi mami tace bafa laifin ta bane, itace ta matsa mata, kuskure daine an riga anyi sai dai ayi fatan Allah Ya tashi kafadunta....
Karya kwana yayi da gudu motarsu ta fuce daga gidan kai tsaye suka nufi asibitin.

_________________________________
'?

Slowly motar dr shureim ta kunna kai cikin gidan, bayan yai parking ya dago ya kalli zeenatu da ta kifa kai bisa gwiwa tana ta shesshekar kuka

"Bazan gaji da lallashinki ba, dan Allah ki hakuri ki jure ya shurem bayason ganin hawayen babynsa, na fada maki addu'armu take bukata, kuka ba abunda zaiyi mata...." tun da yafara maganar bata dago dakai ba
Fitowa yai daga motar ya zagaya dayan bangaren da take ya buWe mata"fito mu shiga" still bata tanka mashi ba, dama dakyar ya rabata da asibitin. Ba karamar badakala suka sha da ita ba. Kuka tadinga yi akan bazata koma gidan ba, dakyar suka lalla6ata.

Ganin zata bata lokaci Yasa shi kai hannayensa ya tuttu6eta kamar yar tsana Yai mata irin daukar da ake ma jariri Ya nufi cikin gidan da ita.

Tana kuka tana fadin yaya shureim bazanje ba ni ka sauke ni, wurin aunty benazir zan koma...bai saurareta ba har ya karasa katafaren falon, Alhaji musa na azaune kan sofa ya daura kafa Waya bisa Waya, idanunsa na akan laptop dinsa, hada mug din coffee a gefe yana sha babu alamun damuwa akan fuskarsa hankalinsa kwance

Shigowarsu ne Yasa shi dago da ido Ya kallesu Fuskar shureim a daure Ya dira zeenatu, ransa Ya baci da ganin uncle din nasa kamar baisan halin da suke aciki ba.

"Shureim..." har ya kusa Fita ya dakatar da shi waiwayowa yayi babu walwala Ya ke kallonsa, shi kanshi alhaji musan Ya fahimci fushi Yake da shi
"Ya jikin benazir din? Kamar bazai tanka masa ba ya furta"da sauki"
"Menene sakamakon abunda ke damunta"?
Sai da ya Wanyi jim kafin yace"It's depression and panic attack...." bai kare maganar ba yai hanzarin fucewa daga falon don baya jin zai iya jurar kallon uncle musa tsaf zai Iya gaya masa magana
Har ya kusa fita daga entry hall din kwatsam sautin muryar zeenatu Ya dakatar da shi Ya kasa kunne Yana sauraronta
Cikin muryar kuka take fadin"Wallahi daddy baka da tausayi, kowa ya damu da halin da aunty benazir take aciki ban da kai! Jiya kana gani haka ta kwana akulle kaki taimakawa ka buWe mata kofa, har sai da ta kwana, why daddy? Baka sonta ne? Ko tayi maka wani laifi ne da yaja har kake nuna halin ko'in kula akan ta, ni wlh ka 6ata min rai daddy tun da har baka damu da rashin lafiyar aunty benazir ba, hankalinka kwance kana agida sai kace ba Wiyar yayanka ba,....." kamar daga sama dr shureim yaji saukar mari ji kake tasss
A matu?ar furgice ya ware dara daran idanunsa, jikinsa na 6ari a sukwane Ya juya cikin takun sauri Ya nufi falon Har zai shiga wata zuciyar ta gargadesa akan kada Yaje Tsayawa yayi yana sauraron su daga inda yake yana iya hangen zeenatu wadda tunda daddynta ya kwasa mata mari gaba daya ta jirkice ta kife kan hannun sofa, jikinta yadinga bari kusan wannan ne karo na farko daya fara ta6a lafiyar jikin ta....baiwar Allah gaba Waya ta furgice ta kasa dagowa ta dinga tsala kuka tana fadin na tsane ka daddy, da kanka ka sa hannu ka buge ni? Daddy ka makance ne? Wlh sai dai ka kashe ni daddy..." masifa ta dinga zazzaga mashi
Zeenatu bata ta6a bashi mamaki ba irin na yau, duk irin shakkarshi da take ji hakan bai hanata fadan ta cikin ta ba, hakan ya tabbatar masa da taji haushin abunda yayi
Yatsun Hannunsa Ya zubawa idanu cike da jin haushin marin ta da yayi,

Duk da ita taja ma kanta, shi fa ba'ay masa fada ana Waga masa murya balle ita da take yar cikinsa...
Walking slowly Ya nufi sofa din da take Ya zube kan gwiwowinsa agabanta.
dr shureim dake la6e Yana kallon shi har saida Ya Wan ware idanunsa cike da mamakin Yadda Alhaji musa Yai kneel down agaban zeentu mutumin da ko uwarsa baya tunanin Ya ta6a zukunna mata, wannan wani irin sone ya ke yi mata?
Kamar zai mata sujjada haka Ya fara magana"i'm really sorry my daughter, kurkurene ba da son raina ba, kece kika fusata ni zeenatu, banso na mareki ba..." yadda yake yi mata magiya ba karamin Waure kan dr shureim yayi ba, har tafin hannu yasa ya shafa fuskarsa don Ya tabbatar in ba mafarki Yake Yi ba

Cikin shesshekar kuka take fadin"Dad ..dy dama ka daina bani hakuri, don bayi zanyi ba, ni bana son ganin ka, tun da bakason Aunty benazir dina..." bata kare maganar ba, Yai hanzarin furta"waya fada maki bana sonta? benazir kamar ?a take awurina..."
To amma meyasa jiya kaki bude mata kofa
"Saboda bani na kulleta ba, itace ta kulle kanta .."
"Daddy ni ban yarda kana sonta ba, tun da kaki zuwa asibiti dubata..."
Hannu yakai tare da janyo zeenatu ya kwantar da kanta saman broad chest dinsa Ya daura tafin hannunsa abayanta yana lallashinta..."ki daina kuka bana so, indai akan benazir ne zanje na dubata hope hakan yayi maki"
Tana faman matse kwalla tace"daddy dr yace in har ba'a bemo mata yarta ba, zuciyarta zata buga ta mutu, dan Allah kasa a nemo mata yar babynta, daddy nasan zaka iya..." yamutsa fuskarsa yai kafin yace"naji zanyi kokarin sanyawa a nemo mata ita, Yanzu ki kwantar da hankalinki, Muje daki ki kwanta ki huta, zan sa tani ta kawo maki abinci nasan kina jin yunwa..." yai maganar tare da mikewa ya ru?o hannun zeenatu acikin nashi, suka nufi bedroom dinsa
gauran numfashi dr shureim Ya sauke aranshi yana mai al'ajabin irin son da Alhaji musa yake ma zeenatu
Sai dai baiji dadin marin da yayi mata ba, yaji zafi aranshi, saboda yaga shatun yatsunsa sun fito ruWu ruWu kan kuncinta yasan dakyar in zazza6i bai kamata ba, saboda zafin hannu gare shi, ya ta6a marin zainab mai aikin gidansu lokacin dayaje joss kawai saboda ta haWa hanya da shi har ta bangaje shi cikin rashin sani, tun da ya kwasa mata mari sai da tay 1 week tana jinyar fuskarta....
sai dai yasan ba lallai ya bari zeenatu taji jiki ba, tunda yana sonta zai mata maganin abunne
Da wannan tunanin Ya fuce daga gidan Ya shiga mota Yaja Ya nufi asibiti.

______________________EX-PRISONERS

A tsaye suke su biyu suna fuskantar junansu, tunda batool ta sanar da ita game da wayar da tajiyo aunty ummin su, tana yi a tsakar dare cikin toilet, taji hankalinta Ya tashi zuciyarta harta fara raya mata ko dai aunty umminsu da wata muguwar manufar take atare da su?

"Taya za'ay insan dawa take magana"? Ta jefa wa kanta tambayar

"Wai hada cewa ay bani da wayon da zan iya sanya mata ido..." acewar batool
"Anya batool ba zaki daina kwana dakin ta ba?
"Saboda me"?
"Indai zaki cigaba dayi mata la6e duk ranar da ta gano ki, wlh zata Iya hukunta ki, tun da bamusan me take ?ullawa ba!
Girgiza kai batool tayi"ni dai bana Yi mata mummunan zato, kuma bana so na daina kwana dakinta..." fuskarta ayamutse tayi maganar
"Nima ina kyautata mata zato, amma meyasa take abu kamar mara gaskiya? Waya a toilet kuma a tsakar dare? Sannan har tana fadin baki da wayon da zaki iya sanya mata ido?
Ruko hannun batool tayi"bazan hanaki kwana dakinta ba, amma kiyi takatsantsan, kada ki ?ara yi mata la6e kibarta kawai, In sha Allah ba abun da zai faru watakil ma bata son ki farka daga bacci ne shiyasa ta shiga toilet tanayin wayar don kada ta takura maki' jinjina kai batool tayi alamar gamsuwa da maganar unaisah
Kafin wani ya ?ara yin magana a cikin su, suka ji an turo door room din, kusan atare suka dago suna kallon mai shigowa har saida gabansu Ya Wan fadi ganin matar da suke gulmarta
Tayi gayu abunda cikin riga da wando sun kama jikinta, head din data daura ba karamin kyau yayi mata ba, tuni kamshin turarenta Ya buWe hancinansu
Ganin yadda suka tsareta da ido ne Yasa tace"lafiya naganku atsaye? Ko dai gulma ta kukeyi ne"?
Har suna hada baki wurin fadin"A'a" kashe masu ido tay tare da sakin murmushi tace"ku fadamin gaskiya ba abunda zanyi maku, meyasa da kuka ga nashigo kukayi shiru? Bayan kafin na shigo naji kuna magana cikin raWa
"Wlh ba gulmarki mukeyi ba..." ta6e baki tayi"shikenan tun da kunki fadamin gaskiya, Ku zo mu tafi dining, it's lunchtime. Yan uwanku suna jira..."
Amsa mata sukayi da toh, a tare da ita suka fito daga dakin...tunkafin su Isa suka hango su Haris zazzaune kan dining chairs an cika masu table da lafiyyayan abinci
Wuri suka samu kowa Ya zauna har sun fara cin abinci unaisah ta tuna da danish, har ta fara gajiya da halin shi, sam bayason zuwa dining cin abinci sai in taje tay masa magana tukunna Yake fitowa,
Haka da safe lokacin da zasuyi breakfast sai dai Sajeed ne Ya kai masa adakinsa
"Ina Wan uwanku ne? Na lura baya son zama acikinmu Yaci abinci.." Ummi ce tayi maganar
Naufal Yace"Bari naje na kira shi" yai maganar tare da mikewa, ajiyar zuciya unaisah ta sauke dama neman wanda zaije Ya kirasa Takeyi don batajin zata ?ara zuwa dakinsa gudun kada ya kara yi mata abunda yayi jiya
Dawowa Naufal Yai"yace ki kai masa adakinsa" Ya fada idonsa akan unaisah, Yamitsa fuska tayi"batool ki kai masa pls"
Ummi na murmushi tace"bake Yace kikai masa ba? Ki tashi mana ke Yake son gani"
Ma?e kafaWa tay alamar bazata je ba,
Mikewa batool tayi"Bari naje na kai masa.." da sauri ummi tace"koma ki zauna ita zataje, tunda ita Yake son ta kai mashi, Ki kasan ko akwai abunda zai faWa maki...." turbune fuska tayi ranta ajagule kamar an mata dole ta dauki plate da saving spoon ta zuba mashi fried rice ta haWa mashi da juice, tasan bai cika son cin abinci dayawa ba...

A bakin kofar dakin ta tsaya tare da kai hannu tay knocking, shiru ba'a buWe ba, daga murya tayi"My man ni ce...." ta fada tana faman haWe rai

BuWe kofar yayi, lokacin da ta daura idonta kanshi har saida gabanta Ya faWi ganin babu riga a jikin shi, zanene kirjinsa Ya Wan sanya ta jin fargaba
Mi?a masa plate din tay"ga abincin..."
Lumshe idon yai"ki shigo min da shi ciki" make kafaWa tay"pls ka kar6a kawai ba saina shiga ciki ba,..."
Ya fahimci rigime take ji"wani abu zan nuna maki..."
Harara ta galla masa"salon in shiga ka kara yi min irin abun jiya ko. " sai da tay maganar Ya fahimci abun da take ma fargaba
"Nayi maki al?awarin bazan ta6a ki ba, tunda bakiso, pls ki shigo ki gani...." yanayin yadda yayi maganr ba karamin sanyaya mata zuciya yayi ba, cikin lallami Ya samu ta shigo Ya mai da kofa...
Akan table ta daura masa plate din tare da juice
Ganin Ya nufi gefen gadonsa yasa takai ido wurin har sai da taWan ji gaban ta ya faWi ganin acessories din dake zube kan mattaress dinsa masu kyau da tsada
Da mamaki ta furta"My shield Waya baka wannan"? ta fada tana tunkarar kayan kamar mai jin tsoron su
"Wannan mutumin ne Ya kawo min namanta sunanta, Yace min uncle dinsa hateem ne Yace abani su..."
Waro idanu waje tayi tana Yarfa hannu Ta furta"wayyo Allah daWi, my man yanzu duka wannan naka ne?amma natayaka murna.... Agaban gadon ta zauna yatsun hannunta har kerma suke Yi ta dauki Apple laptop din ta buWe ta tana kallon ta.

Ta aje laptop din gefe Waya takai hannu ta Wauki iphone din sak kalar wayarta banbanci su colour ne..
bayan ta ajiyeta ta dauki apple ipad din tana jujuyata faskekiyar gaske...
"Amma dai mutumin nan Yana ji da kai, Allah Ya saka masa da mafificin alkhairi, kamar yadda yake kaunarka nima ina kaunarsa...." abun da bata sani na tun da tafara magana danish Ya nutsu yana kallon duk wani motsin ta, gaba daya ta tafi da imaninsa Yanayin yadda take yaba kayan tana murmushi tare da Wan zare gray eyes din ta ba karamin kashe mashi jiki tayi ba.....idan ta motsa pink lips dinta kuwa har wani haWiyar yawu Yake Yi

Duk bata lura ba, Headset ta dauka tana dariya tace"amma dai atare zamu dinga amfani da su ko? Kaga ni bani da wannan.." tay maganar tare da kallon shi ta kashe mashi ido Waya tare da daura mashi headset din a kansa ta saita mashi a kunnansa.

"Wow!...." wani Irin kyau yayi mata har bata san sa'adda ta manna masa kiss a cheeks din sa ba, mutumin fa gaba Waya ya fara zaucewa wani irin yanayi yake jin kanshi
Cire mashi headset din tayi, ta aje kan mattress din ta janyo eye glss box din tana danna akwatin nan take ya bude jerin hadaddun glass ne na maza ta dauko wani mai walwali launin blue sky ta zura mashi a idanun shi
Tabarakallahu ahsanul khaliqin shine abun da ta furta
Da tafukan hannyenta biyu ta tallabo fuskarsa ta zuba mashi ido tana kallon
Kamar yadda shima yake kallonta ta cikin glass din numfashin su har yana kokarin hadewa dana juna
"Sai naga ka ?ara min kyau my man, bari na canza maka wani" da sauri ta cire na fuskarsa ta dauko wani glass din black colour ta sanya mashi
"Wow kana kashe ni da kyanka...' ta fada tare da cire mashi glass din ta maida shi cikin Wan akwatin
Ta janyo watchbox ta buWe shi jerin tsadaddun agogunane ?an ubansu

ta dauko Waya ta kamo hannun shi ta soma kiciniyar sanya mashi a wrist dinshi
"Ka wani kura min ido kana kallona kamar yau ka fara gani na" tayi maganar da zolaya...
Lumshe idonshi yayi ba tare daya furta mata komai ba....
"Wohoho Ina gwanin wani ga nawa..My man wlh kai na musamman ne, komai naka na kece raini ne...Kalli hannunka irin na ?an gayu wadanda sukaji hutu..." sai faman santin hannunsa take agogon tayi bala'en yi mashi kyau .....
Sam ta manta da abun da ya faru jiya atsakaninsu ta za?e sai zuba take yi masa kamar aku
"Kin fara period neS'Kamar daga sama Taji Ya furta wani bugu zuciyarta tayi mata, a ruWe ta dago tana kallon shi ido cikin ido suke kallon junaW'S'



*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*


*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: Rass Taji gabanta Ya faWi La66anta na kerma tace"Zahra itama ainihin sunanta Unaisah, Angel da muke kiranta nickname ne da daddynta Ya sanya mata, Wiyar wacece ne a family din su"?

Hankalin zahra ba karamin tashi yayi ba, ganin yadda aneelerh ta ruWe ita kanta aruWen take


"Na manta ban faWa maki labarin Yaran ba, Kamar Yadda naji daga bakin chief owais, kamar ba su da alaka da su, hasalima a daji suka tsinto su..." tiryan tiryan Zahra ta kwashe duk abunda Ya faru a wurin dinner din dangane da su Unaisah ta sanar da aneelerh

Kusan zaucewa tayi hannunta dafe da kai, ganin tana tangyal tangyal kamar zata faWi Yasa Zahra Yin saurin ru?o Aneeelerh ta taimaka mata ta zauna gefen gado

"Wallahi itace, Angel ce, Har abada bazan ta6a mantawa da fuskarta ba, ko shakku banayi wannan Yarinyar ANGEL ce tun da har kika ce tsintar su akai....

Gaba Waya rudanine akan fuskokin su,
"Hakan na nufin Junaid Shi Ya fara gane itace?
"Bangane me kike nufi ba yaga hoton ne"!
Jinjina

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0