Showing 141001 words to 144000 words out of 413917 words

Chapter 48 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2712

magana ce mai mahimmanci, Ina fata zaka bani aron hankalin ka.."

Amsa mata yayi da toh, tsawon mintuna biyar ta shanya shi, kafin ta fara kora mashi jawabi dangane da zuwan su Zahra, da alfarmar da suka nema a wurin ta...." tun da ta fara maganar, Yake dubanta da alamun rudani akan fuskarshi.


"Ita zahran da ta kawo min maganar, tana Waya daga cikin interior designers din da suka yi mana aiki aranar dinner din hateem a hall dinne taga yarinyar, sunan yarinyar ta wurinsu Angel amma asalin sunan ta Unaisah, har hotonta sun nuna min, sunyi kama sosai da yarinyar wurin ka,"

Cike da son jin ?arin bayani yace"ko ta fada maki sunan Baban Yarinyar da sunan mahaifiyar ta"? Shiru tayi tana kokarin tariyo sunan su ....can tace"na tuna, sunan mahaifin yarinyar zaheer tajudeen, mommynta kuma sunanta benazir"

." Bari na kira Daddyn nata, naji idan Ya san su" da mamaki hajiya saratu tace"oh dama mahaifin yarinyar yana atare da ku"?
"Eh," ya bata amsa atakaice, har cikin ranta taji dadin jin hakan....
Phone dinsa Ya curo daga aljihu Ya danna ma Taj Kira, Tana fara ringing Ya saka wayar a handsfree don taji abunda zasu ce

"Yalla6ai barka da marece, Na shigo gidan na taras baka nan.."

"Ina agidan grandpa, zuwa anjima zan shigo"

"Allah ya dawo kai lafiya"

Am so nake na tambaye ka, Wa cece Aneelerh! Kamar na ta6a jin sunan abakin ka"

"Yalla6ai ka kamanta ne halan, matar aminina ce uzair, kamar mahaifiya take awurin Angel Wina..." murmushi hajiya saratu tasaki jin abun yazo mata cikin sauki

"Zamuyi magana idan na shigo gidan" amsa mashi yayi da toh, bayan yayi rejecting call din Ya Wago Ya kalli hajiya saratu dake kallon shi

"Yarinyarsa ce..."

"Alhamdulillah, Yanzu gobe da yaushe zasu zo ganin ta? ta tambaya tana kallon shi

"Duk lokacin da yayi miki, su zo kawai" murmushin gefen fuska tasaki, Taji dadin yadda yake bata girma
"Nagode my son, bari nasa akawo mana abun sha" da sauri yace"ina so zan shiga wurin baba"
"Okey, mu tafi tare" mikewa sukayi atare suka jera suna tafiya, abun ba karamin dadi yayi mashi ba, tsawon lokaci basa jituwa da juna, sai gashi silar neman unaisah da yan uwanta sukazo yi Allah Ya haWa kan su, Har fira ta fara jan shi da ita, a haka har suka karasa dakin baba obie...

Idan muka koma 6angarensu Hajiya Layla dake a asibiti, wuraren ?arfe 8 na dare, Hospital staff suka fara sallamar mutanan da ke zuwa dubiya, saboda a dokar asibitin karfe takwas na safe visitors suke zuwa da zarar takwas Na marece Yayi kowa zai tafi za'abar majinyaci karkashin kulawar nurses
Hajiya layla tace ita fa ba inda zataje, dole ta kwana don ta kula da yar ta, dr shureim ma ya goyi bayanta, tunawa da barazanar kashe benazir da ake Yi, Idan suka tafi ba lallai nurses su san lokacin da za'a farmake ta ba, duk da akwai cctv camera a kowani daki na marasa lafiya, bayan hakan asibitin Yana da tsaro sosai, kawai dai bai yarda subar benazir ta kwana ba tare da wani nata akusa ba
Hospital staff din basu Yi masu gardama ba, ganin sanannu ne a idon jama'a, kuma da ma ire irensu sunayi masu alfarma, kodan saboda matsayin dake gare su, musamman hajiya Saratu da takasance former firstlady ta kasar, tun da ta sanya baki a maganar suka amince hajiya layla ta kwana tare da ita.

Gaba dayansu sun hallara a harabar ajiye motocin asibitin, Sun fito domin tafiya gidajen su,
Mami da abie suna atsaye, Ga Aneelerh da Zahra da mahboob, Aneeleeh taso abarta tayi jinyar benazir,
"Mu zamu wuce, Ubangiji Allah Ya bata lafiya, Allah Ya tashi kafadunta, in sha Allah zamu cigaba da tayata addu"a" abie ne yai maganar tare da mi?a ma Alhaji ubaid hannu suka yi musabaha
"Mungode sosai, Allah yakaiku gida lafiya,"
Mami tace"dan Allah duk halin da ake ciki game da rashin lafiyarta ayi kokarin sanar damu"
Hajiya sarah tace"in sha Allah zamuyi kokarin hakan"
bayan abie da mami sun shiga mota, Hajiya layla ta ruko Hannun Aneelerh acikin nata fuskarta dauke da matsananciyar damu tace
"Dan Allah kiyi kokari Aneelerh, Zuwa gobe, Ku tuntu6i iyayen yarinyar da kikace tana kama da yarta, ku rokar mana alfarma awurinsu, su ara mana ita, idan ma suna bukatar mu biyasu kudi su faWi nawa suke so, ko nawa ne zamu biya, wallahi bana so na rasa benazir, ina matu?ar jin tausayinta...." la66anta na kerma ta ?are maganar, tuni taji hawaye sun wanke fuskarta
Wani irin tausayinta ne Ya kama Aneelerh, bata san sa'adda itama ta fara share kwallar ba, Yau dai sun sha kuka bayin Allah
"Mommy in sha Allah zanyi kokarin ganin sun bamu yarinyar, Indai akan benazir ne wallahi sai inda karfi na ya ?are...."
"Pls kukan Ya isa haka, Ku yi hakuri, mu cigaba dayi mata addu'a Allah Ya bata lafiya..." acewar hajiya sarah
Dakyar sukayi sallah da juna, bayan sun aneelerh sun shiga motarsu, A jere motocin suka fuce daga asibitin,

"Zan tafi ba dan naso ba, amma In sha Allah, gobe da wuri zan shigo asibitin"
Fuskar hajiya layla a yamutse tace"Sai Allah Ya kaimu.."
"Duk halin da ake ciki, pls ki sanar dani" ta amsa mata da toh,
"Allah Ya bata lafiya" ta amsa mata da ameen, dr shureim ne ya buWe mata murfin motar, Ta shiga daga ciki, kafin Ya datse mata, akan idonsu motar hajiya sarah ta fuce daga asibitin
Ya rage saura su uku dake atsaye suna kallon juna,

"Shurem muje ko"? Alhaji ubaid ne yayi mashi maganar, Sam baya son tafiya, Gani Yake kamar in ya tafi wani abu zai faru da benazir,
"Toh daddy" Yayi maganar, Tare da ruko hannun hajiya layla
"Mommy, nasan ko ban fada maki ba, zaki kula da ita, amma inaso ki sanya ido sosai, dole sai kin hana idonki bacci in ba haka ba..." bai kare maganar Ba Alhaji ubaid Yace"meyasa kace haka"?
"Daddy akwai wani abu da nake zargi akan benazir, zan sanar daku amma ba yanzu ba, saboda bana son Waga maku hankali, kawai abinda nakeso mommy kada kiyi gangancin kula da ita, in ba haka ba za'a iya samun matsala, duk da munsan Allah ke tsare bawansa amma da bukatar muma mu kula"
Hankali atashe Hajiya Layla ke kallon shi, Muryarta na rawa tace"Shureim dan Allah ka fada min meke shirin faruwa da Benazir dina, ni dama najima ina zargin akwai wanda ke bibiyar rayuwarta, so ake akashe min ita, ko faduwar da tayi a toilet sai da raina ya bani wani mugun abunne Ya faru da ita, in ba haka ba taya za'ace ta fita hayyacin ta? Bata gane kowa dake akanta?..." maganganunsu sunso rikita Alhaji ubaid Ya rasa gane inda zancen su Ya dosa
"Dan Allah kuyi min bayani meke faru ne"?
Da ido Hajiya layla tayi ma dr shureim Alamar yayi shiru saboda tana zargin ba hakanan Aka kyale Alhaji ubaid ba, kada su saki baki su sanar da shi zargin da suke Yi Yana iya zuwa ya sanar ma Alhaji musa, tunda Ya zama kamar ubansa komai zaiyi sai ya nemi shawarar shi
Jinjina kai dr shureim yayi alamar Ya fahimce ta,
"Daddy, Muje gida zan sanar da kai komai" Ya faWa tare da ruko hannun shi, Hajiya layla tayi masu Allah Ya kiyaye hanya, tana atsaye tana kallon motarsu har suka fuce daga hospital din,
Da sauri ta koma Wakin benazir, tana shiga, ta iske Nurse agaban gadon ga benazir zaune jikin ta sai kerma Yake tana ta sambatu
"Daddy, mommy, ku kira min taj, Ya kawo min babayna dana bar mashi, dan Allah ku bani ?ata, kada na mutu ban ganta ba...." lallashinta hajiya layla ta cigaba da yi sam bata fahimtar komai, sunan ?arta da mijinta kadai take ambato,
Har abinci nurse ta kawo mata, kwata kwata ta kasa cin shi, duk yadda mami takaiga lallashinta abun Ya faskara, Addu'oi ta koma tana tofa mata, har dare Ya tsala mami tana zaune kan kujera tana kallon ta, Har dr ya shigo ya kara duba jikinta, Ya bata magungunanta dakyar suka samu ta sha, daga bisani bacci Yayi awon gaba da ita, lokacin da aka fara kiraye kirayen sallar ishai'a, mami ta shiga toilet cike da zullumin kada wani ya shigo dakin Ya cutar da benazir, saboda ta razana da jin kalaman dr shureim, jin motsin mutun adakin yasa tayi wuff ta bangaje kofar toilet din ta fito tana haki, Ko alwalar bata karasa ba..

*Daga alkalamin Boss Bature mu haWu next page
'?*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: _________________________________
'?


Bayan komawar Unaisah cikin parlour, a dining room ta hango ?an uwan ta, har sun fara yin breakfast sunyi neman ta har sun gaji ba su ganta ba, suna jin takun tafiyarta gaba Waya suka dago suna kallon ta.....

"Sister! Ina kika shiga muna ta neman ki"? Batool ce tayi mata maganar, bata tanka masu ba, sai faman sakin murmushi takeyi kamar wadda akayiwa albishir da gidan Allah, yau ranta fari fess, cike da zumudi taja kujera ta zauna tana kallon su Waya bayan Waya, tasan in har ta sanar da su Azeeza game da zuwan auntyn ta aneelerh ba karamin dadi zasu ji ba saboda tasha basu labarinta agidan kurkukun ?addara,

abunda bata sani ba tun da ta zauna suke ta kallon ta


"Aunty ummi Ina kwana.. " wani kallo ummi tabi ta da shi, har saida tasha jinin jikin ta

Kafin ummi ta furta kalma Sajeed Ya riga ta cewa"Sister baki da lafiya ne? ko kinyi kuka ne"? lokaci Waya yanayin fuskarta ya canza! Kwata kwata ta manta da abun da ya faru daren jiya, saboda murnar zuwan Aunty Anila, maganar sajeed ce ta tuna mata, tuni murnar da take yi ta koma ciki.

"Sister kinyi shiru baki ce komai ba? Meke damunki"? Cike da tashin hankali batool tayi maganar, su Parveen duk sun kura mata ido suna kallonta, jemimah tace"le6enki ma ya kumbura kamar yankan tumatur"

"Unaisah! Lafiyarki kuwa"? Acewar ummi ta faWa tana kare mata kallon ?urulla

Adabarbace ta furta"am.. Umm.." sam ta kasa ?arasa maganar, idanunta azazzare take kallon su.

gani take kamar sun san komai daya faru da ita adaren jiya, da sauri ta mi?e jikinta na kerma tace" aunty ummi babu komai, ba abunda ke damuna, lafiyana lou..." bata ?are maganar ba, kamar mara gaskiya ta nufi hanyar fita daga dining room din zuciyarta cike fal da tashin hankali
Gaba daya sun lura da tashin hankalin dake akan fuskarta
Deeja na dariya tace"wallahi Allah kumatunta sun kumbura suntum kamar alkubus, wama ya sani ko bugun tsiya akai mata..." bata kare maganar ba, Haris ya toshe bakin ta..
Mi?ewa ummi tayi sam hankalin ta bai kwanta da yanayin unaisah ba, mi?ewa batool tayi da niyar tabi bayansu, da sauri ummi ta dakatar da ita"ki zauna ku karasa cin abincin, zanji da ita" jiki asanyaye ta amsa mata da toh..
Da sauri ummi ta nufi dakin su Unaisah, tana shiga tajiyo sautin kakarin amanta a toilet kamar zata fasa makoshin ta.

Knocking ?ofar toilet din tay"unaisah ina son magana dake"

Fitowa tayi fuskarta sharkaf da hawaye, hannun ta ruke da Wan pant din ta.

"Meke damunki ne"? tana faman jan numfashi tace"bakomai aunty ummi..." katse ta ummi tayi"kada kiyi min karya, yanayinki ya riga ya nuna baki da koshin lafiya, kawai ki fadamin meke damunki! Idan ba haka ba hankalina ba zai kwanta ba..." cikin nuna damuwa tayi maganar, shiru tayi jim tana tunanin ko dai ta fada mata watakil ta taimaka mata....

Mi?a mata pant din hannunta tayi, waro ido ummi tayi"me zanyi da shi" matse shi tayi, tana faman no?e kai tace"jiya da tsakar dare na tashi da matsanancin ciwon mara, kamar bazan rayu ba, bayan na shigo toilet na duba sai naga jini ne ya dawo min"

cike da jin tausayinta ummi ta ruko hannunta suka zauna gefen gadon.

"Sannu unaisah, wallahi daga gani kin ji jiki ba kaWan ba, meyasa a daren baki neme ni ba? Ay da na taimaka maki, halan ko magani baki sha ba"?

"Ban shaba ba aunty ummi, saboda naji saukin ciwon, kuma lokacin dana farka da safe banga jinin ba ya dauke! Aunty ummi dama Yana haka"? Waga mata kai ummi tay alamar eh"kada hakan ya dameki, nima sometimes yana yi min haka yaje ya dawo, in har bai wuce kwanaki goma shabiyar ba, to still jinin ne, amma da zarar kinji ya dauke duf babu shi sai kiyi wankan tsarki ki cigaba da sallah" ajiyar zuciya unaisah ta sauke, sam tagaza fada mata abun da ya faru jiya.

"Me kike son nuna min a jikin pant din . " cike da jin kunyarta tace"wani abune da nake gani kamar kunu gayanan kyankyamin shi nake ji .."

kiris Ya rage ummi ta fashe da dariya ganin yadda ta kwa6e fuska tana gwale la66anta.

"Nuna min in gani .." buWe mata pant din tayi.

Shiru ummi tayi jim alamar tana nazartar abunda ta gani, tabbas sperm ne amma meya kawo shi? Cos Bata tunanin unaisah ta fara feelings...rayawa tayi aranta watakil ba abun da take tunani ba ne

"Unaisah, dole fa sai kinyi takatsantsan, kamar yadda nayi maki bayani zan ?ara jan kunnanki, daga yanzu kada ki kuskura ki ?ara ba wani namiji damar da zai ta6a jikin ki, ko da ru?e hannunki ne! In ba haka ba ke zakija ma kanki zunubi, saboda duk wasu hukunce hukunce na musulunci sun hauki, Idan kika aikata mai kyau za'a rubutaki, haka zalika idan kika aikata zunubi za'a rubuta maki. .."nan dai tayi mata takaitaccen bayanin dalilin dake kawo hakan dallah dallah yadda tasan zata fahimta, hankalin unaisah ba karamin tashi yayi ba.

"Kuma idan kika bari Namiji yana wasa dake yana tattabaki, you can get pregnant, a yadda kike ?aramar nan har ranki zaki iya rasa wa...." ummi bata kare maganar ba Unaisah ta daura hannayenta biyu akai la66anta na kerma ta furta inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un...." da biyu ummi ta fadi hakan saboda taja mata kunne.
Tayi mamakin ganin Yadda jikinta ke kerma, da gudu ta fada toilet taja kofa ta datse.. " lamarin ya daurewa ummi kai, arude ta mike tana kwala mata kira"unaisah! Unaisah? Lafiyarki kuwa? Meya faru? ko dai maganar dana fada ce? To meye na damuwa"? Shiru bata amsa ba, bugun kofar ummi ta dinga yi kamar zata balle ta"ki bude min kofa, keda baki jira kin karasa jin me zance ba, meye na tada hankali kamar baki da gaskiya"? Ta faWa tana kumshe dariya a bakinta saboda ta bata dariya.

"Unaisah, ki fito muyi magana, watakil baki fahimci me nake nufi ba, zan yi maki bayani..." cikin disasshiyar murya ta furta"aunty ummi ki tafi dan Allah, cikina ne Ya katsa, idan na gama zan same ki a daki muyi magana" ajiyar zuciya ta sauke"shikenan zan jiraki"

Sai da taji alamun ummi ta fita daga dakin, kafin ta fito fuskarta sharkaf da hawaye baiwar Allah, hankalinta yayi matu?ar tashi, ta raza da jin kalaman ummi, fargabanta kada ta samu ciki!

Wani irin ciwon kaine Ya farmata, ga wani bacci da ta fara ji mai hade da kasala, Pant din da ta bari kan floor ta Wauko ta koma toilet din,

Wankan tsarki tayi tare da alwala, daga bisani ta fito sanye da towel, da wata irin kasala ta dauko wasu kayan tasa tare da hijab ta zura a jikin ta.


Bayan ta kammala sallah ta zauna kan darduma ta Waga hannayenta tana addu'a hawaye na sintiri kan kuncinta, ko da ta gama bata motsa daga kan dardumar ba.

Bakomai ne Ya faWo mata aranta ba face Danish, ko ya ci abin ci? taga bata ganshi a dining ba, har cikin ranta ta damu da shi, bata son yana ke6e kan shi a Waki, batasan meke damunshi ba...

"Sister dina!" muryar batool ce ta katse zancen zucinta, da sauri ta mike tare da juyawa ta kalle ta.., sam babu walwala atare da ita, duk ta damu da yar uwartata

"Dan Allah ki fadamin meke damunki" ?a?aro murmushi tayi akan fuskarta

"Calm down your mind! Ni Ba abunda ke damuna, lafiyana lou, ciwon ciki nayi jira da daddare naci wahala sister, amma yanzu da sauki jikin nawa..." huggin dinta Batool tayi sai taji wani sanyi ya ratsa zuciyarta.

"Ni kadai na kwana jiya adaki"

tausayinta ne Ya kara kama Batool

"Da na sani jiya na tayaki kwana, amma kodan saboda ke zan dawo kwana dakin nan"


Murmushi unaisah tayi"kada ki damu, ay naji sauki ma"
Kallon dakin Batool tayi"duk yayi datti bari na taimaka maki"
"Nagode sister," ta fada tare da zama kan mirror chair tana jiran batool ta kammala gyaran.

"Sister an kaiwa danish abinci a dakin sa"?

"Eh, Haris Ya kai ma shi, ni bansan meke damun shi ba, kema kin lura da yanayin shi na?in shiga cikin mu"? Ta faWa a yayin da takai hannu tajanyo zanin gadon da yayi uban squeezing kamar an ?watoshi daga bakin kura.

"Batool na lura, abun yana damu na, nayi masa faWa ya?i dainawa to ya zanyi da shi? ta faWa da damuwa akan fuskarta"ko da yake halinsa ne ko a prison bai fiye shiga cikin mu ba, yafi son yaganshi kwance kan gado" daurewa kawai takeyi sam bata son batool ta fahimci halin da take a ciki.

Adai dai lokacin Batool ta fara kakka6e zanin gadon, Kwatsam ba zato ba tsammani unaisah ta hango zoben da ya faWo ta cikin bedsheet din..saukowa tayi daga kan kujerar, ta nufi inda Yake ta zu?unna tana kallon shi, zoben azurfa ne sai kyalli yake a hankali tasa yatsanta daya ta Wago da zoben, hankalin batool kwata kwata baya akanta, sai surutu takeyi mata....
?ura ido tayi sosai akan zoben, was wasi ta fara yi kamar wanda prime minister ya ba danishW'
Anya kuwa shi ne?S' kokwanto ta shiga yi, tayaya akai zoben ya shigo dakin su idan na shi ne ...? yunkurawa tayi a sukwane ta mike, batare da sanin batool ba, ta fuce daga dakin.

"Sister jiya kafin mu kwanta aunty ummi ta kunna min kallo a laptop din ta...." dakatawa tayi da yin maganar ganin babu kowa adakin.

"Unaisah! Unaisah! "ranta ne Ya bata kodai ta shiga toilet, hakan yasa taci gaba da gyara mata dakin......."

________________________________
'?

Prisoners shield=???

Fitowa yai daga toilet, jikinshi a sanye da bathrobe, baijima da tashi daga bacci ba Ya shiga wanka, yayi wani fresh dashi, sumar kanshi ta lullu6e bayan shi.

Walking slowly

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login