Showing 189001 words to 192000 words out of 413917 words

Chapter 64 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2698

bayan Anila kamar tana jin tsoron wani abu,

"Azeezaty, zo nan mana" Biy guy ne ya kira sunanta, fitowa tayi idanunta na kallon ?asa ta tsaya a tsakiyar su, gaba Waya ta tsargu da kallon da su ke yi mata, Hajiya Layla ta kasa rufe bakin ta saboda mamakin ganin yarinyar, sai taga kamar sunyi kama da Benazir Winta, sai lokacin Dr Jazz ya lura da ita sun Wan ruWe da kyawunta, musamman Dr. Adam har dai ya gaza jurewa ya ce "Tabarakallahu ahsanul khalikin..." bai ?are maganar ba, Dr jazz ya yi saurin yi mashi raWa a kunne"kallon ya isa haka! Future wife Win babban yayanmu ce, wlh ka shiga taitayinka" da sauri Dr Adam ya rufe bakin shi da tafin hannu.

"Azeezaty, ina fata anyi maki bayanin abunda ya kawo ki nan?" Waga mashi kai tayi alamar eh,
"Okey, abunda muke so kaitsaye ki shiga Wakin wurin patient Win, ki yi hugging Win ta sannan ki kirata da sunan Mommynki" amsa mashi tayi da toh, kafin slowly ta juya ta nufi Wakin zuciyarta na dakan uku uku wani irin faWuwar gaba take ji, gaba Waya sun nutsu suna kallon ta...
Duk taku Waya idan tayi sai gaban ta ya faWi rass, ta rasa gane dalilin shigarta yanayin da take a ciki.
Tunda ta zura ?afarta a Wakin idanunta suka sauka akan mara lafiyan dake a kwance tana bacci, walking slowly ta ?arasa ta tsaya daga bakin gadon tana kallon ta, tun daga kan fararen kafafuwanta har zuwa kan fuskarta, sumar kanta ta lullu6e gefen fuskarta daga gani ba ?aramin hauka tayi ba kafin a samu ta runtsa.
Wata irin kasala ce ta baibaye Unaisah gaba Waya ta kasa ta6uka komai sai kallonta takeyi kamar zata haWiyeta.....

"Ki rungumeta mana, ke muke jira" ?asa ?asa da murya Dr Adam ya furta maganar,
Numfashi ta ja kafin ta daidaita nutsuwarta, a hankali ta zauna daga gefen gadon kafin ta faWa kan ?irjinta tare da lumshe idanunta lokaci Waya ta fashe da matsanancin kuka me sautin gaske ita kanta batasan kukan Ya kubce mata ba, hankalinsu ba ?aramin tashi ya yi ba amma sai suka yi zaton tayi ne don abun ya tafi dai dai..
Sautin kukanta ne Ya daki kunnan Benazir, cikin magagin bacci ta fara sambatu tana faWin "Babyna, wayyo Allah mami! ina babyna naji sautin kukan ta, don Allah ku kawo mini ita..." yatsun hannunta na kerma ta Waura su kan bayan Unaisah, da dukan hannayenta biyu ta fara shafa bayanta taji mutun akan cikin ta, hakan yasa ta fara kokarin buWe idanunta, da?yar ta buWe su sun kaWa jawur saboda bacci,

Daga can waje Dr Adam ya ce "Nayi mamakin farkawarta, because bana tunanin allurar da nayi mata ta isa ta saketa..."
Su Anila duk sun ?agara Benazir ta karasa farkawa, gaba Waya jikinsu sai tsuma yake yi ga wani irin annurin farin ciki da ya wanke zukatansu,
Mayafin kan Unaisah tuni ya jima da zamewa, hakan yaba Benazir damar cusa hannayenta acikin sumar kanta ta cigaba da sambatu tana faWin "Babyna ne? Mami daddy kuna ina? Wanene Ya kawo min babyna? meyasa take kuka?" Sosai Unaisah ta ?an?ameta, ta ?ara cusa kanta a kirjin Benazir babu alamun zata saketa, Allah sarki jini Waya ba wasa ba, wannan unconditional love Win dake atsakanin uwa da Wanta shine yayi tasiri a zukatansu, a karo na farko da ta fara jin Wumin mahaifiyarta ba tare da sanin itace ba, aruWe Benazir ta zabura ta Wago da fuskarta ta ?ura mata ido tana kallonta, baiwar Allah Angel fuskarta tayi jawur da ita ruwan hawaye ya wanketa tass, da ?yar take buWe idanu tana kallon cikin idon Benazir, kallon kallo suka fara jefawa junansu duk hawayen Unaisah sun wanke fuskar Benazir, la66anta na kerma ?irjinta na bugawa ta furta "Mamana! Ni ce babyn ki, meyasa kika tafi kika barni? kin manta dani a rayuwarki? Nayi kukan rashin ki atare dani mamana!"

Shigowa Wakin Hajiya Layla tayi daga bakin gadon ta tsaya tana kallonsu, ?walla sun taru acikin idanunta,

"Mommy ki faWamin? Da gaske babyna ne nake gani ba mafarki nake ba? Angel Wina ne?" Kwata-kwata Angel bata fahimci sambatun Benazir ba saboda ita kanta ta Wan shiga ruWanin halin da ta tsinci kanta game da matar,

"Benazir, yarinyar ki ce Angel, ki rungume ta a jikin ki, " Hajiya layla ta faWa da murmushi akan fuskarta, fashewa da kuka Benazir tayi, da sauri ta kwantar da Unaisah kan kirjinta ta rungumeta sosai kamar zata mayar da ita cikin cikin ta.
Cikin shesshekar kuka take lallashin ta"kiyi shiru ki daina kuka, bana son ji, nasan nice na 6ata maki rai, kiyi hakuri ki yafe min bazan ?ara tafiya in barki ba, nayi maki alkawarin zan baki kulawa babyna, kinji my Angel"? Sambatu taci gaba da yi ta?i bari Unaisah ta Wago da kanta ta ?an?ame abun ta kamar wani yace zai kwace mata ita.....

Jikin Taj ba ?aramin sanyi yayi ba, da sauri ya du?ar da kan shi hawaye sun cika idanunshi, sai yaji inama ace zai iya zuwa ya haWa su duka a kirjinshi ya rungumesu,

Zahra sarkin tausayi tuni ta fara matse ?walla, ita kanta Aneleerh kukan ne ya kusa kubce mata, da hannu biyu ta toshe bakin ta don bata son ayi zargin ko yarta ce ta gaske,
Lumshe ido Chief ya yi a yayin da yake kallon su, ya jima baiga abun farin cikin da ya sanyaya zuciyarshi ba irin na yau! abun ya ta6a zuciyar shi....

Hatta Docs Win dake a tare da su saida suka ji tsananin tausayinsu, A hankali Dr shureim Ya zaro hanky daga aljihu Ya share kwallar da suka tarar masa, yana ji aransa da wuya yarinyar in ba jinin su bace!!

Dr Adam ne ya sauke yar ajiyar zuciya ya ce "in sha Allah zata samu sau?i, naga alamun nasara tun kan aje ko'ina, Yarinyar ba ?aramin wayau ne da ita ba, ta iya acting,..." kallon shi kawai Anila tayi su da suka san meke atsakanin su..
Dr jazz ma ya ce "Ubangiji Allah Ya bata lafiya, Allah yasa yarinyar nan ta zama silar warakarta" gaba Waya suka amsa mashi da ameen....

"Yalla6ai, muje office mu ?arasa magana" Dr. Jidenna ne Yayi maganar, atare da Chief suka nufi katafaren office dinsa.Tattaunawa suka yi dangane da Unaisah, Chief ya ce masa baya son kowa ya sake shiga Wakin mara lafiyan daga grandma Winta sai Unaisah, bayan haka Yana so a canza mata Waki su maida ta private room saboda Unaisah ta samu damar sakewa wurin yin jinyarta, ya Waura da faWin "Bana bu?atar wani likita ya shiga dakin ta in ba Dr Jazz ba, shi nake so ya cigaba da kula da mara lafiyan" Dr Jidenna ya ce "Consider it done sir, in sha Allah a cikin daren nan zamu aiwatar da komai" sun jima suna tattaunawa a office din kafin daga bisani suka fito a tare, har lokacin su Shureim suna a tsaye bakin kofar dakin suna kallon su Benazir,
Bayan sun dawo wurinsu chief Yaja hannun Dr Jazz suka ke6e wuri Waya dama shi mutuminsa ne, Yana jin dadin aiki da jazz yaron yana da hankali,
"Jazz, nayi magana da Md, kaine zaka cigaba da kula da mara lafiyan! Pls bana so asamu matsala!" murmushi jazz yayi "In sha Allah babban yaya zanyi kokari sosai gurin basu kulawa,"

"Good, sannan inaso ka duba jikin yarinyar, ta faWamun bata jin dadi, pls inaso ka bata kulawa ta musamman, bana so ta nemi wani abu ta rasa! Kayi kokarin kwantar mata da hankalinta kamar akwai abunda ke damunta"

Jinjina kai jazz ya yi "In sha Allah My Boss, kasan bana wasa da duk wani abu da ya shafe ka" harara Chief ya Wan watsa mashi, ya sunnar dakai ?asa yana murmushi...
Ru?o hannunsa chief yayi suka koma wurinsu Taj,
Duba agogo big guy ya yi "Yakamata mu tafi dare yayi, almost 12,"
Da sauri Anila ta ce "pls muna son muyi mata bankwana kafin mu tafi"
Dr Adam ya furta "Okey, bari na kira maku ita" shiga dakin yayi,

"Azeezaty yan uwanki suna son ganinki zasu tafi, ki fito kuyi sallama" shiru yaji bata amsa mashi ba, le?a fuskokinsu yayi abun mamaki bacci ne ya Waukesu rungume da juna bayan sun gama shan kukan, gaba daya Unaisah tana kwance kan jikin Benazir shiyasa gadon ya dauke su....

Fitowa Dr Adam ya yi fuskarsa Wauke da murmushi ya ce "sai dai kuyi hakuri bacci suke yi, ba zamu iya tada su ba"

"Dr ga backpack Win kayanta, ka shigar mata da ita ciki" sauke jakar Taj ya yi tare da mi?a ma Dr Adam ya shiga da ita ciki ya Waurata kan kujerar gaban gadon.
Kamar kar su tafi haka suka dinga kallon su ta cikin door glass Win, kafin daga bisani suka kama hanyar barin asibitin, har bakin parking space Hajiya Layla ta rakasu tana ta faman yi masu godiya kamar zata du?a ?asa, shima Dr. Shureim godiya sosai ya yi masu tare da fatan alkhairi, sallama sukayi wa junansu Zahra da Anila suka shiga motarsu, Taj da Big guy suka shiga tasu motar, kafin Chief ya shiga motarshi, saida Hajiya Layla ta ?ara yi masu Anila godiya saboda halaccin da su ka yi masu kafin motocin suka fuce a jere da matsakaicin gudu, ya rage saura Hajiya layla da Dr Shureim, su jazz tuni sun koma cikin asibitin..

"Shureim ka ga wani ikon Allah? Yarinyar nan tana kama da Benazir, bansani ba ko idanuna ne suke nuna min hakan"
Murmushi shureim ya yi "ba idanunki bane, nima naga kamanceceniyarsu, wlh Mommy naji dadin ganin yadda Benazir ta rungumi yarinyar ajikinta, sai naji inama ace yarta ce, saboda ta kwanta mun araina..."
Hajiya layla ta ce "ba kai kadai ba shureim, nima yarinyar ta burgeni, ga wayau daga gani tana da kaifin basira, iyayenta sunyi mana hallaci kuma basu nemi komai daga gurin mu ba, ko da yake naga yarinyar ma ?ar masu arziki ce...."
Dr shureim ya ce "Mommy zan wuce gida dare yana ?ara yi, pls ki kula da yarinyar nan, kinga dai yadda yan'uwanta suka dam?a mana amanarta, bana so asamu matsala..."
"In sha Allah Shureim, ay bazan yi sakaci da rayuwarta ba, dole inyi takatsantsan tun da naga Wiyar manya ce, hada fa jami'ai cikin waWanda suka kawo ta"
?ara tattaunawa suka yi kafin ya yi mata sallama ya buWe motar shi ya shiga ciki, akan idon ta motar ta fuce daga asibitin, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juya ta nufi ciki cike da zumudin son ganin yarinyar..

______________________________
'?

Bayan su taj sun rako chief part dinsa, saida suka ga shigarshi cikin bedroom dinsa kafin suka sauko falo, har sun kusa fita suka tsinkayi muryar ummi daga bayan su

"Boss sannun ku da zuwa"! Atare suka juyo tare da kallonta, sleeping gown ce a jikinta, ta yafa mayafi akanta, da alama ta fara bacci ta farka

"Yawwa Ummi, me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba"?

Fuskarta ayamutsa tace"na kasa bacci saboda damuwar rashin unaisah, tun wuraren karfe takwas da rabi muke ta nemanta saboda muyi dinner shiru babu ita, ko'ina mun duba, ?an uwanta ma dakyar na kwantar masu da hankali har su ka yi bacci, nayi zaton ko taje part din ka ne" Tay maganr tare da nuna taj

Big guy dake kallon ta from head toe gaba daya ta jefa shi ayanayi, saboda kayan baccin jikinta sun bayyana surarta,

"Ummi, unaisah ba agida zata kwana ba, taje asibiti" bai ?are maganr ba, ummi ta zaro ido tare da dafe kirjin cike da tashin hankali tace"inna lillahi meke damunta? Bata da lafiya ne"? abun da yasa ta ruWe saboda halin data ganta dazu a daki, abun ya tsaya mata arai, har jiran zuwanta tayi kamar yadda tace mata zata zo amma shiru bata neme ta ba...
Kwantar mata da hankali taj yai"lafiyarta ?alou ba ita ce ke bata da lafiya ba, yar uwar chief ce...." bayani yayi mata dalla dalla, lokaci daya ta sauke ajiyar zuciya,
"Hankalina har ya kwanta, amma banji dadin tafiya da tayi batare data yi mana sallama ba, yanzu sai yaushe zata dawo gida"?
"Bani da masaniya, amma bana tunanin zata dauki lokaci, pls ki kwantar ma yan uwanta da hankalli banaso su sanya damuwa aransu"
"In sha Allah, mu kwana lafiya boss, agaida min da madam" ya amsa mata da toh, satar kallon big guy tay ya wani tsareta da ido, harara ta dan watsa mashi haWi da yin murmushi ta juya ta nufi ciki, harta bace ma ganinsa bai kauda idonsa ba, sai da taj ya bugi kafadarsa kafin ya juya suka fuce kowa ya nufi part dinsa..

______________________________
'?

*Prisoners Shield=???*

Bawan Allah, kwata kwata baya acikin hayyacinshi, Yasha bakar wahalar radadin da zuciyarshi keyi mashi, tun safe har kawo iyanzu da dare ya ratsa ko ruwa bai gifta makoshin shi ba, saboda tashin hankalin da yake a ciki, yayi haukan yayi kukan amma babu abunda Ya canza nadaga kuncin da yake ji, babu wanda yayi tunanin ya leko dakinsa yaga awani hali yake ciki, saboda su kansu yan uwan nashi yanzu mantawa su ke yi da shi tun da suka fahimci bayason shiga cikin su kuma baya son kowa ya ra6e shi, a fahimtarsu, unaisah ita kadaice ta damu da shi, bata iya wuni batare da ta leko dakinsa ba, ta damu da shi fiye da yadda ta damu da kanta, itace farin cikinsa kuma gatansa, baya jin zai iya rayuwa batare da ita ba, Unaisah kaddararsa ce! Bugun zuciyarsa ce.



Cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya Wauke shi, hakan ba karamin relief ya sama mashi ba, yayi bacci sosai har na tsawon awanni, gab da za'a fara kiran sallar asuba, ya fara mutsu mutsu, yatsun hannayensa dana kafarsa suka fara kerma....."
Farat Waya ya buWe idanunsa waWanda suka kaWa jawur tamkar garwashin wuta, Gaba Waya rasa ?warin gwiwarshi, kamar matacce Sam ya kasa motsawa daga kan floor, ko yatsansa Ya gaza Wagawa, wani irin gumi ne Ya wanke jikinshi kamar wanda aka tsamo daga cikin teku, ta ko'ina zufa ke tsatsafo mashi, ga wani azababben zafi da jikin shi ya Wauka.

shatun jijiyoyin goshinsa sun fito rudu rudu kan fatarsa,a kalla ya shafe mintuna yana kokarin sarrafa zuciyarsa gudun kada evil heart dinsa ta motsa, bakomai idanunse ka hango mashi ba face fuskar Unaisah.

Dakyar ya samu kwarin gwiwar motsa gabban jikinsa, Ya lalla6a Ya mi?e tsaye kan ?afafunsa, jansu ya dinga yi saboda wani nauyi da sukai mashi dakyar yakai kan shi toilet ya faWa ciki yana jan numfashi, agaban sink ya tsaya yana faman sauke ajiyar zuciya.

Sannu a hankali brain dinsa ta fara tariyo mashi abunda Ya faru daren jiya atsakaninsu, yaga komai a mafarkinsa.

Wago da hannayensa yayi tare da saita su saitin fuskarshi Ya ?ura ma tafukansa ido Yana kallon su ....da sauri ya girgiza la66ansa na kerma ya furta"bani bane! Bada son raina ba, bansan na akaita ba, bana a cikin hayyacina!...." dafe kansa yai da hannu Waya ya cusa yatsunsa acikin sumar kanshi, ya cigaba da cakuWata gaba daya ya haukata gashin kanshi, duk ya rikice saboda ya gane shine da kafafuwansa Yaje dakinta adaren jiya har yayi mata aika aikar nan sai dai yayi imanin bayin kanshi baneW' cije la66ansa yayi har saida suka fashe jini ya fara WiWWigowa, wani irin tsanar kanshi ne Ya kama shi, kamar ya kashe kanshi haka Yake ji, da karfi ya buga forehead dinsa jikin sink nan take fatar wurin tayi jawur kamar zata fashe, buga kanshi yacigaba dayi yana sambatu yana fadin Ni ne da kaina na cutar da Angel dina? tana kuka tana rokona dan in taimaka mata amma nagaza share mata hawayenta, bani da tausayi, ni mugune, na tsani kaina..." jinine ya fara gangarowa ta kofofin hancin shi, wani irin jiri ya fara kokarin kwasarshi, ya fara tangal tangal zai kife kasa kwatsam ba zato ba tsammani Yaji hannu mutun akan damtsensa, gaba daya ya janyo shi tare da rungume shi akan broad chest dinsa, ya zagayo da hannayensa akan bayan shi, bawan Allah baya gane komai, idanunsa sun makance, ji yake tamkar angel dinsa ce ta rungume shi, hakan ya shi ?ara ?an?ame mutumin da ya rungumeshi duk ya 6ata mashi gaban Rigarshi da jininsa, hakan baidame shi ba, babban tashin hankalin shi halin da yaron yake aciki! Ya tsorata da ganin yadda yake kokarin kashe kan shi W'lamarin yayi matukar gigita shi..
"Ki yafe min Angel, ba yin kaina bane, bazan iya cutar dake ba, sharri akaimin, ba halina bane, ki tausayama rayuwata, ke kadai ce farin cikin da nake da shi a duniyar nan, bani da gata daya wuce ke...." gaba Waya sambatunsa acikin kunnan sa, Ya nutsu Yana sauraron shi, har lokacin bai Wago da kan shi ba, balle har yasan wanene Ya rungume shi.

___________________________________
'?

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu duniya
*Zuzeam empire* takawo muku babbar gara basa
Duka akan 5500 ki daure ki mallaki naki kar ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????dama ta wuceki Garabasa gara basa =????=????=????=?? ?

Wa.me/+2348144015291 For more information say hi =?K? Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam empire tashirya tsaff dominku=???=???=??? muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu

*DAHUWAR KAZA*

Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato *Ni ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya*
Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt *Akwai kyauta
*INA MASU JEGO DA AMARE*
Karku bari wannan dama ta wuceku
*08144015291*
Zuzeam empire

ASSALAMU ALAIKUM Mata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login