Showing 324001 words to 327000 words out of 413917 words

Chapter 109 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4484

amma In Allah Yasa hakan ya zamana gaskiya ne kinga kenan wannan wata hanyace da zaki yi amfani wurin kawo karshen su, Ki zamar masu mummunar ?addarar da zatayi silar tarwatsa su.


maganar salsabeel ta farfado da tunaninta na son kawo karshen kurkukun ?addara amma bataji zata iya tursasa danish don ya yi masu jagora.

Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"ya Salsabeel na fahimce ka, amma bana jin zan iya tursasa ma Danish, Ina matu?ar jin tsoron in jefa rayuwar shi cikin hadari, in har wani abu ya faru dashi bazan ta6a yafe ma kaina ba, idan ma zuwan ya zama dole sai da shi to ku haWa da ni.

kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya tokare makogwaronta nan hawaye suka dinga zarya kan kuncinta.

Zuciyarshi taso ta karaya da maganarta,

Shesshekar kukan tane Ya fargar da shi, Cikin sigar lallashi yace"in har kin yi imanin cewa Allah shi ke tsare bawansa bai kamata kina tunanin Zai rasa ransa a gurin Yaki ba, ay bashi kadai zaije ba Unaisah baga mu ba ko mu baki damu mu mutu ko muyi rai ba? Wlh Unaisah jininmu akan akaifa yake babu gudu ba ja da baya ko da zamu rasa ranmune sai mun yi ya?i da dukkan karfin mu, mun dogara da Allah kuma munyi imanin shine zai bamu nasara akan kyakkyawar niyar da muke da ita na ganin mun kawo karshen zaluncin kurkukun kaddara...."


Kwata kwata bata gane me yake cewa ba, ita fa damuwarta akan Danish ne cikin karyayyar murya tace"ni abun da nafi jimawa har yanzu shi ba musulmi bane, I don't want him to lose his life as an unbeliever! ya makomarsa zata kasance?..." ta faWa tana kallon fuskarshi da idanunta wadanda suka kaWa jawur da su

shi kanshi abun na damun shi, baida burin daya wuce Danish ya musulunta ko dan ya tsira da imaninsa, amma yasan bamai yiwuwa bane in ba wani iko na Allah ba, saboda wadannan evils din na jikin shi.

"Mu cigaba da taya shi addu'a in sha Allah zai musulunta, ni dai yanzu damuwana ki yi kokari kisa ya amince mana..." kifa kanta tayi jikin pillow, sam bata son maganar gani take kamar tursasa mata yakeyi don ta ingiza danish ga fadawa halaka..


Sarai ya fahimci daga ita har Danish din Giyar soyayyace ke dibarsu, shiyasa har suke neman su bijire..


Gwiwar shi ta sage, cike da rashin kwarin jiki Ya mi?e ba tare daya kauda idanun shi daga kallon ta ba Yace"banzo nan donna bata maki rai ba, kodan na tursasa maki nazo ne don mu hada hannu gurin cimma burin da muka dade muna jiran ranar da zamu aiwatar da shi, kada ki manta nayi ma mahaifiyata alkawarin zan kawo karshen zaluncin Elders bayan haka kema kin min alkawari watakil Yanzu kin manta nasani..." wani irin radadi take ji acikin zuciyarta tana maijin bakin cikin gaza amsa mashi bukatar shi

"Zan tafi Unaisah, ki zauna kiyi nazari da hankalin ki, Zan jira har zuwa lokacin da zaki aiwatar da abun da na sanyaki, bana so kiyi danasani mara amfani..." ya fada tare da juyawa ya nufi kofar fita daga dakin Harya ruke handle din Ya dan dakata tare da juyawa ya dube ta, still bata dago da kanta ba sai kuka take yi

"Kina tunanin zaman Danish agidan nan shi zaisa Ya tsira da ranshi? Abunda baki sani ba dokar elders ce duk wanda ya san sirrinsu dole su kashe shi, in har baije Ya farmakesu ba, to su zasu farkama ke shi ne akowani lokaci" ya na fadan hakan yasa kai ya fuce
Fitar shi keda wuya ta kuma fashewa da wani sabon kukan kamar ranta zai fita, maganar salsabeel ta fara tariyowa farkon haduwarsu agidan kurkukun ?addara

_inaso ki Waurawa kan ki nauyin yin hakan ko dan saboda rayukan dake rayuwa acikin kurkukun nan cikin mawuyacin hali! Akwai ire iren ku da yawa wadanda basu ji ba basu gani ba, An kulle su an hanasu sakat, Kullum ne sai an rasa rayuka agidan kurkukun nan, kashe mutane suke yi tamkar kyankyasai, Idan har bamu kawo ?arshen kurkukun nan ba to kuwa zasu cigaba da aikata 6arnar da babu ranar dainawa, Muna matu?ar jin tausayin yaran da ke rayuwa a kurkukun nan, Dan Allah Unaiserh ki taimaki rayuwar su! Ki daure ki jure wurin ganin kun tona asirin abun da ake aikata......" hannayenta Ya ru?o a cikin nashi ya dinga yi mata magiya sautin muryar shi kamar zai fashe da kuka_

_"NAYI MAKA AL?AWARI Idan Allah ya bani damar fita daga kurkukun nan zan tona asirin su harma mu bada gudunmawa wurin ganin an kawo ?arshen su, Bi'iznillahi_

Tuna wannan yasa ta ?ara sautin kukan nata.

A bangaren Salsabeel bayan ya koma backyard din kamar yadda yabarsu Chief haka ya taras da su zaune suna jiran shi.

Bawan Allah duk Ya rasa kuzarin shi, su Unaisah sun bata mashi rai ba kaWan ba..

Hankalin su baya akan shi har saida yai masu sallama kafin su ka dube shi, zama yai kan kujera ya sunkuyar da kan shi ?asa tun daga yanayin shi suka fahimci akwai damuwa..

"Salsabeel ka yi shiru baka ce mana komai ba! Ya kuka ?are da shi"? Cikin kulawa Taj yai maganar..

Cike da jin nauyin su ya girgiza kai,

"Danish ya bani kunya, ban ta6a zaton zai bijire min ba..." tun da suka ji hakan damuwa ta bayyana akan fuskokin su don sun riga sun hasaso karashen zancen na shi..

Rai a6ace Omar yace"meyasa zamu wahalar da kanmu akan shi? Yaron nan fa Wan rainin wayau ne, idan muka ce zamu bishi ta lalama bazai ta6a bamu haWin kai ba, kwara mu bi shi ta ?arfi da yaji mu ci ubanshi har sai ya mi?a wuya..."yana huci ya faWa kamar zai haWiyi zuciyarsa saboda bacin rai..


Chief ya Waga mashi hannu badan Ya ?arasa maganar ba yaja baki yayi shiru fuskar shi a murtuke..

"In har bashi yayi niya ba, ko da zamu rasa damar da muke da ita na zuwa gidan kurkukun bazan bari a tursasa masa ba, itama Unaisah ban amince ayi amfani da ita gurin shawo kan shi ba, cos zai ga kamar ni na sanya ta ne" Salsabeel ya Wan kalle sa cos shi harya riga daya tuntu6i Unaisah.

Cike da takaici Big guy ke kallon chief da yai maganar


"Haba Owais, Saboda shi kawai zamu fasa niyar mu"?

"Omar, ba ina nufin zan fasa aikin mu bane, sai dai mu nemi wata hanyar..." bai ?are maganar ba, Big guy ya mike yana huci ya kama hanya zai bar backyard din..

Damuwa ta hana Taj furta kalma baima san me suke cewa ba.
Mi?ewa chief yayi da sauri yabi bayan Omar, don bazai bari su sabamu sabani tsakaninsu ba dama kwanakin nan yana jin haushin fifita Danish da yake yi.

Bayan tafiyar su, ya rage saura Taj da Salsabeel sunyi shiru babu mai magana acikin su.

Ganin yadda Taj???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ya zabga uban tagumi ne yasa Salsabeel furta"Sir are you Okay"?

Yamutsa fuska yai"kada ka damu, i'm okay, just banji dadin yadda Wan uwanka ya?i bamu haWin kai ba" ya fada yana kallon Salsabeel

"Amma Salsabeel babu dabara da zamu iya yi don mu shawo kan shi"?

Shiru Salsabeel yayi yana nazarin maganar shi, wata dabara ce ta faWo mashi arai da sauri Ya dubi Taj

"Akwai hanya Waya" akagare Taj yace"Ina sauraronka"

"?arka Unaisah, Ita kaWai ce zata Iya sa shi dole yayi..." lokaci Waya Taj ya haWe rai, annurin fuskar shi ya Wauke, saboda zafin maganar Salsabeel daya ji.

"Meyasa kace haka"?

Murmushi Salsabeel ya Wanyi kafin ya fara zayyana masa dalilinsa nacewa haka!

"in har ta umarce daya je zai je, saboda ya mutu akan Sonta, ba irin magiyar da banyi mata ba akan taje ta rokar mana shi amma ta?iya saboda gudun kada ta yi silar da zai rasa ranshi, amma ina da tabbacin in har ka yi mata magana zamu iya cin galaba akan ta saboda kai mahafinta ne, bazata ki bin umarninka ba"...


Tun da ya fara magana Taj ya tsare shi da ido batare da kyaftawa ba, bakomai yake tunawa ba face abunda idanun shi suka gane mashi, Wari bisa Wari ya yadda da maganar Salsabeel saboda shi shaidane akan mahaukacin son da suke ma junan su, duk da ya Wauke ?afa akanta amma yana jin zai iya zuwa gurinta don ya jarabata"

Har salsabeel ya ?are maganar Taj bai sani ba, gyaran muryar da yayi mashi ne ya fargar da shi

"Pls, ka taimaka koda sau Waya ne ka jaraba yi mata magana.." fuskar shi amarairaice ya fada..

Wayar Taj ce tay ringing, kallon Salsabeel yayi"it is Okay, zan jaraba" ya faWa tare da mi?ewa Yai picking call din

"Sir, ina fata lafiya, naji shiru baku dawo ba"

"Boss, Ka sallami Salsabeel ya tafi, kaima zaka iya tafiya..." amsa mashi yai da toh..

"Chief yace ka tafi, zai neme ka" mikewa yayi"pls sir, sai naji daga gare ka" jinjina mashi kai yai batare daya fur ta kalma ba.

_________________________________
'?


Su Batool na zaune a falo suna fira kusan su dukkansu in ka cire Unaisah da Danish sai ummi su kadai ke babu a cikin su...


Sam basu lura da shugowarshi ba fira taja hankalin su, ganin babu Unaisah yasa shi juyawa ya nufi bedroom din...

Adai dai lokacin ta fito daga bathroom, sanye da yar rigar wanka, zuciyarta cike fal da tunanin abunda suka tattauna da Salsabeel

Wayar ce ta fara ringing, har zata dauka taji anyi knocking din kofar

"Wanene"?

"Ki buWe kofar ki gani" ras ta Wan ji gabanta ya fadi jin muryar daddynta, tana jin shakkar shi yanzu ba kadan ba saboda canzawar da yayi mata.

"Unaisah ba zaki buWe min ?ofar bane"! Jikinta na 6ari ta je ta buWe ?ofar, shigowa ciki yai tare da aza idanun shi kan fuskarta wani irin tausayinta ne ya kama shi.

Cikin rawar murya tace"daddy Ina wuni" ta fada tana kallon shi

Shiru yayi bai tanka mata ba hakan ba karamin karya mata zuciya yayi ba.. Kasa jurewa tayi batasan sa'adda ta faWa kan kirjin shi ta kankame shi tana tana kuka tace laifin me na maka daddy? Meyasa ka canza min? Ka daina sakar min fuska, idan na gaishe ka dakyar kake amsa min idan na kira wayarka baka Wagawa, daddy don soyayyarka da manzon Allah ka fadamin laifin me nayi maka sai in nemi yafiyarka, wlh bana so kana fushi dani Daddy, kaifa mahaifina ne kasan hukuncin wanda iyayensa ke fushi da shi ...."sambatu taci gaba dayi batare data raba jikinta daga nashi ba..


Zuciyarshi ta karaya da jin furucinta, ta bashi tausayi ba kadan ba, ga kaunarta dake kara ninkuwa cikin zuciyarshi, jiya dakyar ya runtsa hatta Danejo saida ta lura da yanayin shi ba irin magiyar da batai mashi ba akan ya fada mata gaskiyar abunda ke damunshi amma yakiyi saboda bazai iya tona ma yarsa asiri ba, kamar tona ma kansa ne..


Baiwar Allah muryarta harta disashe, Unxpectedly taji ya Waura tafukan hannyenshi akan sumar kanta ya Wan shafa bayanta cikin sigar lallashi


Kafin ya fara magana
"Unaisah, kin bani mamamki, kinyi min abunda ban ta6a zato ba..." a firguce ta dago tana kallon fuskar shi

"Ina yi maki kallon mai hankali, kuma mai jin tsoron sabawa Allah ashe nayi kuskure Unaisah, na yaudari kaina.." cike da tashin hankali ta furta"daddy ni din? Me nayi maka"? girgiza kai ya danyi cike da takaici ya zayyana mata abunda Ya taras sunayi adakin Danish...

Dafe kai ta yi da tafin hannunta, wani irin faduwar gaba da tashin hankali taji

"Idan shi jahili ne baida addini, ke ay ba irinsa bace, Kinsan babu kyau unaisah, ina tarbiyar dana baki? Baki ji komai ba kika biye mashi kuka rungume juna, haba Unaisah baki kyauta ma kanki ba, nima kuma baki kyauta min ba, wlh kin karya min zuciyata, kin samin fargaba saboda zullumin kada ya lallata min rayuwar yata...."


kusan suman tsaye tayi, jikinta ya fara kakarwa kamar mazari ga kunyar shi data lullu6e ta, tasan bata da gaskiya shiyasa ta sunnar da kanta ?asa cikin sanyin murya ta furta"daddy, na kar6i laifina, amma dan Allah kada ka zarge mu, wlh bamu ta6a aikata wani abu daya sabama Allah ba, duk da Danish baida addini ba Wan iska bane daddy, bazaiyi abunda zai cutar dani ba, idan yayi ba daidai ba ina faWa masa babu kyau a addinina kuma baya musa min, abun da ya faru ranar bana a cikin hayyacina daddy, hankalina ya tashine naji matu?ar tausayin shi kuma naji tsoron kada na rasa shi shiyasa na rungume shi, amma wlh ba shine ya fara rungumata ba, ni ce daddy...."


yanayin yadda take yi mashi magana jikinta na kerma ba karamin rauni ta sanya mashi ba, yayi niyar yayi mata fada sosai amma sai yaji bazai iya ba, ya yarda da maganarta yasan Unaisah bazatai mashi karya ba.

"Meke atsakaninki da shi"? Ya tambaya yana kallon ta

Kamar mai in ina ta fara yan kame kame tana fadin"amm..umm..dama.."ta Wan kau da idonta gefe kamar bazata karasa maganar ba tace"bazan boye maka ba, dama najima inason in faWa maka, nasan zaka goya min baya akan abunda nakeso...." tashin hankali idanun shi aware yake kallon ta.

"Daddy Allah ya jarabce mu da son juna ni da danish, soyayyar dake tsakaninmu bazata misaltu ba, har rayukan mu zamu iya sadaukarwa akan junanmu, daddy wlh ina son danish, shi kadai ne namijin da nake da burin in aura..." bata ?are maganar ba, sakamakon tsawar da Taj Ya daka mata wadda tay silar rikicewarta arazane Ta zazzare grey eyes dinta akan fuskar shi Yana faman fitar da huci yace"Impossible Unaisah! Wlh bazan lamunta ba, ba zaki sa nayi karamar magana ba, baki isa ki kunyata ni ba, kina hauka ne unaisah? Meye abunso atare da shi? Yaron da baida adinini arne ne, ga jahilci cike da kai, sannan bashi da wani galihu, bayan haka ina yake da halin da zai iya ruke min ke!?

wani irin jiri jirin tashin hankali ta gani acikin idanunta kalaman daddynta sunyi matu?ar Waga hankalin ta, tayi mamakin furucin da yayi akan danish kamar dai ya manta cewa komai ya faru arayuwar shi bayin kan shi ba ne...

"Unaisah Ina burin da kike shi na son auran attajirin me kuWi? Mai ilmin addini dana zamani mai cikakken asali wanda zai gatantaki Ya tarairayeki ya baki kyakkyawar kulawa?

"Daddy, na jima da soke wannan burin, ba dole sai na auri miji mai kudi zan samu farin ciki ba, sau dayawa wasu masu ilmin basu aiki da shi daddy, ni kawai miji na gari nake nema kuma na samu daddy, duk abunda ka lissafa Danish zai iya bani fin su, saboda yanayi min soyayyar da bazai iya cutar dani ba, yana yi min son da zai iya hana kanshi farin ciki saboda farin ciki"

Ta Wan numfasa kafin taci gaba da cewa" ka kira shi jahili daddy banji dadi ba, bayan kasan ba shi yaja ma kanshi hakan ba, idan ka amince min, zanyi amfani da son da yakeyi min in musuluntar da shi..."

bata ?are maganar ba, Ya dakatar da ita ta hanyar Waga mata hannu! wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makogwaronsa, Ya ma rasa me zaiyi ya huce haushin sa, Yayi mamaki wai har Unaisah ta iya gaya mashi da bakinta bata ji kunyar shi ba lallai ba karamin so take ma shi ba, zata iya komai akan shi..

Kafadunta Ya dafa da tafukansa Ya jijjigata har saida Sumar kanta ta yarfo ta gaban fuskarta fashewa tayi da kuka don ta gane bai fahimce ta ba..

Da kakkausar murya ya furta"Bazan ta6a amince ma soyayyarku ba, ba son shi kike ba, tausayin shi kike ji, tun wuri ki cire zancen zaki aure shi, saboda na riga da nayi maki miji sadakinki ne kadai bai biya ba, kuma yana sonki, shine za6ina unaisah in har ba bijiremin zakiyi ba, bana so ki bani kunya kada kisa na karya alkawarin da nayi masa, ki cika min burina Unaisah, danish ba dole saida ke zai iya rayuwa ba, ga sauran yan uwanki nan sai ya zabi daya acikin su, Unaisah burin kowace uwa ta sama ma ya'yanta uba nagari ba jihili ba.


abun da Taj bai sani ba tuni tajima da sumewa, idanunta daya gani a kakkafe shi yasa shi gane hakan..cikin jin faduwar gaba ya hadiye sauran maganarshi da bai amayar ba, saboda tashin hankali, Ashe nashi wasane bai ta6a ganin true love ba sai yau, ay yayi zaton daga layla da majnoon andaina samun irin soyayyar nan, sungumarta yayi kan fadar shi ya kwantar da ita kan gadon su, Ya fito daga dakin jiki na kerma Ya tafi dauko ruwa kafin dawowar shi, Batool ta shigo dakin fuskarta dauke da murmushi ta zauna gefen gadon tana kallon wani sabon salon kwanciya agurin Unaisah, tayi zaton dadin baccine yasa ta dauki tsawon lokaci bata leko waje ba.


"Sister Ya kamata ki tashi, Aunty Ummi ta hanamu baccin marece.."

ta fada tare dakai hannu ta Wan bubbuga ?afar Unaish shiru bata farka ba,

"Unaisah wani irin bacci ne wannan kamar mai fama da cutar bacci" ta fada tana kara bubbuga legs din ta.

Adaidai lokacin Taj ya fado dakin hannun shi ruke da robar ruwa me sanyi, Yana ganin Batool yaci burki gaban shi na faduwa yasan muddin tasan Unaisah suma tayi sai ta yi kukan da zai jawo hankalin sauran yan uwanta.


Jin motsin adakin yasa Batool ta juyo ganin daddyn Unaisah yasa ta mi?e da fara'a tace"ina wuni daddy, i'm sorry watakil ka yi sallama banji shigowarka ba..." yawu ya haWiya dakyar ya tattara nutsuwarsa yana kokarin danne damuwar shi yace"lafiya lou daughter.." da alamun rudu kan fuskarta tace"daddy naga water bottle a hannunka.." washe baki yayi"eh ni zan sha ne, kishi nake ji" murmushi tayi"ko kazo ganin Unaisah ne" a kagare ya daga mata gira"bacci take, yanzu nake kokarin tadata" da sauri yace"kinga bari ni in tashe ta, kije gurin ummi naji kamar tana nemanki..." kamar taso ta Wago shi, ta lura kamar wani abu badaidai ba, amma sai batayi mashi gaddama ba, ta fuce daga dakin, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya datse ?ofar dakin, ya zauna gefen gadon da sauri ya cire murfin robar ya yayyayafa mata ruwan kan fuskarta.

dogon numfashi taja tare da sauke ajiyar zuciya..


"Unaisah, Pls ki yi hakuri ki tashi, kinji! I won't hurt you anymore..."

dakyar ta iya buWe idanunta wadanda suka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0