Showing 105001 words to 108000 words out of 413917 words

Chapter 36 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4473

Wayan Chef din Yace"Amma in ba damuwa zamu iya sanin sunayenku? Don gaskiya bansan sunanku ba unaisah kadai nasani' Ya faWa Yana nuna ta da yatsa

"Ba damuwa ni zan faWa maku sunayen su," unaisah ce tayi maganar, kafin ta fara faWa masu sunayen

"wadannan biyun masu kama da twins sunayen su Jemimah sai Azeeza" ta faWa tana nuna su da yatsa sai faman sakin murmushi sukeyi.

?aga masu hannu chefs din sukai alamar suna miko gaisuwa

"Sajeed Naufal and Javed" ta nuna kowannansu da yatsa

"Wannan Kuma sunan sa Haris ga deejarsa a gefe, kamar anta da jini suke"

"Kina nufin masoya ne"? ?aga masu kai tay alamar eh"

"Wow masha Allah, shiyasa suke bala'en kama da junansu ashe soyayyace atsakani, Muna mi?o maku gaisuwa" chefs din suka fada suna Waga masu hannu, washe baki deeja tayi shima haris din murmushi ne kan fuskarsa

"Ita kuma wannan sunanta Hannah" ta nuna hannah dake tsaye gefen parven, ga kuma Parveen acici" dariya sukai don sunsan Halinta na cin abinci"

Juyawa tayi kan su Rubina"rubina, eve and yasmin sai hibba" da sauri eve tace"kin manta jiya na fada maki yaya salsabeel Ya canza min suna hawwa"

"Yeah Na tuna sunanta Hawwa, ga kuma sarah da mubeen" ta nuna su da hannu

"thank You unaisah, kunga yanzu munsan sunan kowan nan ku saura mu saba da juna koba haka ba"? Atare suka hada baki wurin amsa masu da Yeah

"Yanzu zamu fara shirya maku wurin zamanku tun da mun samu ?aruwa"

Ba tare da 6ata lokaci ba, mutun sha Biyu daga cikinsu suka zauna akan 12-seater dining table din da suka saba cin abinci akan shi, sauran suka samu gurbin akan 6-sitter dama ukune a dakin cin abincin.

Har sun fara cikin abincin, sautin cokulansu Ya cika dining room din kamar a restaurant yanayin yadda suka zauna, chefs din suna daga tsaye suna kallon.

Mi?ewa unaisah tayi tare da kallon chefs din tace"zanje na kira aunty ummi da batool" bata jira amsar su ba tay saurin kama hanya don tasan zasu iya tsayar da ita..

Har takusa isa ga stairs, sai ga su sunfito daga daki, Hannunsu ruke cikin juna yadda kasan uwa da Wiyarta, ummi na asanye da abaya maroon tayi rolling, batool tun kayan jiyane a jikin ta riga da wando na bacci

Suna ganinta a tare suka sakarwa juna murmushi da sauri batool ta saki hannun ummi ta nufi unaisah suka rungume juna kamar sun jima ba su a tare

"Barka da safiya My own sis, jiya ko ki neme ni, aunty ummi ta ?wace min ke" ta faWa tare da raba jikin su daga na juna.

"Ni da ke waye mai laifi? jiya kamar zanyi hauka wurin nemanki, ina kika je baki fada min ba"? rai aWan 6ace tayi maganar suna kallon juna

"I'm sorry, nima bada son raina na tafi nabarki ba, naga kuna firar yaushe rabo kuma bana son in katse ku shiyasa na tafi...."

"Ina kike je ne"? Ummi ce ta jefa mata tambayar

"Part din daddyna dake acikin gidan nan, " da mamaki ummi tace"oh dama anan yake zaune? Ko da yake naga gidan ba karamin girma ne da shi ba, ay ko zan haWu da shi maimakon ya gayyace mu muje baki Waya shine ya ware ki ko"? Ta fada da zolaya

yar dariya unaisah tayi"wlh ba haka bane, yace min next time kuma zai gayyace ku kuje part dinsa wurin auntyna danejo"

Murmushi ummi tayi"ai ko bai gayyace ni ba zanje da kaina, ko dan ingano danejo, inyi mata godiya saboda taimakon da tayi mana wurin ceto rayuwarki"

Fuskarta dauke da murmushi tace"naji dadin maganarki aunty ummi, Allah yabarmu atare" amsa mata sukai da ameen

"angama shirya mana breakfast a dining, naga baku futo ba shi ne nazo don in kira ku"

"Yanzu haka da kika ganmu yunwar ce ta koro mu nida baby girl dina" ta faWa tare da ruko hannun batool har zata ruko na unaisah donsu tafi a tare tayi saurin cewa" zanje na kira danish ne" amsa mata tai da okey, bayan sun tafi ta nufi bedroom dinsa tana gab da zata shiga taji motsin fitowarsa kusan atare idanunsu suka shiga cikin na juna kwata kwata fuskarsa babu annuri ganinta da yayi ne yasa shi Wan sakin fuskarsa tun daga kan yatsan kafarta ya fara kallonta ba karamin kyau tayi mashi ba, rigar ta ?ara fito mata shape dinta.

"My man, ina fata ka tashi lafiya," lumshe mata ido yai alamar eh

"Oh ba zaka min magana ba, kasan kuwa yadda na ?agu da inzo ganinka" ta faWa tana jifar shi da kallo mai kama da harara irin kallon da ke jan hankalin shi gareta

"Saboda kaga na damu kai ko" ta fada tana ru?e qugunta

Da?yar Ya iya haWiyar yawu Ya furta"kin tashi lafiya"

?aga mashi gira tayi"ina lafiya, pls ka shiga ka canza kayan baccin nan, sauran yan uwanmu suna jiranmu a dining muyi breakfast"

"Mu shiga atare" ma?e masa kafada tai"a'a zanjiraka anan, ka shiga ka fito" batai aune ba taji yaja hannunta cikin dakin, ba yadda ta iya dole tabi shi ciki.
Juya mashi baya tayi bayan ta cire hannunta daga nashi tace pls ka sanya kayan suna jiran..." kafin ta ?are maganar ba zato ba tsammani taji Yai huggin din bayanta gaba daya ya kwanto da kanshi kan shoulder dinta tare da zagayo hannayensa kan waist dinta, a matu?ar ruWe ta furta"meye ha????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ka"? Ta fada tana kokarin raba jikinta daga nashi, kamar ya Waureta da igiyoyi sam ta kasa ?watar kanta ?ara tighting nata yai tuni taji wani irin yanayi da bata ta6a fuskantar shi ba, rai a6ace ta fara zazzaga mashi masifa kamar baisan tanayi ba

Muryarshi tamkar tame jin bacci Ya furta"ki taimaka min na sanya kayan" gaba Waya nema yake ya burkita mata lissafin kwalwa, muryarta na rawa ta furta"wai meke damunka ne? akan wani dalili zan taimaka maka ka sanya kaya"? A hasale Ta faWa tare da kamo hannunsa dake akan cikinta tasoma kiciniyar banbare shi bakomai take jima fargaba ba face Wan mayafin data Waure kirjinta da shi muddin ya warware danish zaiga abun da yajima yana jira kuma tasan sauran in har ya gani sai wani abu ya faru.

Kamar zata fashe da kuka tace"danish ka sakeni banaso, Babu kyau! Ka matse min cikina! tsabar masifa idanunta arufe ta furta maganar
Babu akamun zai saketa sai faman goga tsinin hancinsa Yakeyi akan fatar wuyanta wani irin Yanayi da bai ta6a jin makamancinsa ba.

A lokacin da baiyi tsammani ba, Yaji ta gartsa masa cizo A hannunsa, ba don Yaji zafi ba Ya saketa, da wani irin kallo Yabita har ta fuce daga dakin da gudu.....

Fitarta keda wuya Yaji kamar ancanza mashi tunaninshi, lokacin Waya yafara tunanin me yasa yayi mata hakanS'

Tun akan stairs jikinta ke kakarwa kamar wadda sanyi ya kama, Gaba Waya Ya jefata cikin Yanayi kamar bata a hayyacin ta

Sam bataji takun tafiyar sa ba, har sai da muryarsa ta katse mata zancen zucin ta"Good morning daugher"! Wani irin firgita tayi don sai taji kamar muryar danish ne ganin daddyntane Yasa tayi saurin daidaita nutsuwarta gudun kada Ya fahimci wani abu Ya faru.

Jiki asanyaye ta nufe shi ta fada kan kirjinsa tana faman sauke ajiyar zuciya ta furta"daddy Ina kwana, Ina auntyna danejo, Ina fata kun tashi lafiya"
Dago da fuskarta yai suka hada ido cikin na juna, farat Waya yaWan fahimci wani abu na damunta
"Kamar wani abu na damunki? Ko baki da lafiyane" adan rude ta girgiza masa kai"bakomai daddy lafiyana lau"
Ajiyar zuciya ya sauke
"Auntynki tana gaisheki, Kamar zata sanyamin kuka tun jiya bayan mun yi maku rakiya mun koma gida ta dinga yi min surutu akanki, yau da safe har ce min tai zakizo nace mata aa sai tace min tana son tazo taganki dakyar fa na lallasheta ta hakura' Murmushi unaisah tayi"Allah sarki auntyna. Kada ta damu har sai ta gaji da ganina'

Ru?o hannunsa tai acikin nata"daddy muje muyi breakfast"

"Am sorry daughter bana Jin yunwa, aunynki ta cika min cikina, but da anjima idan na shigo zamu ci dinner a tare yanzu zan tafi dama na shigo ne don inga sanyin idaniyata" farfari tayi masa da ido yakai hannu ya Wan ja kumatunta

huggin dinta Ya sake yi kamar karsu rabu

"Ki kula min da kanki, Allah Yayi maki albarka," amsa mashi tayi da ameen daddyna kaima ka kula min da kanka

Bayan sun raba jikinsu daga na juna. har ya juya zai fita sai kuma Ya Wan dakata tare da waigowa Ya kalleta tana atsaye bata motsa ba itama shi din take kallo

"Kin shiga wurin chief "? Girgiza masa kai tay alamar a'a,"pls ki dinga zuwa kina gaishe da shi, inaso kina kyautata masa dan Allah"

"In sha Allah daddy, zanyi kamar yadda kace"

"Ina wayarki ne"

"Nabarta adaki"

"Okey, zan tura maki sakon contact dinsa, ko da baki samu zuwa wurinsa ba, ki dunga tura masa sakon gaisuwa ko ki dinga kiransa awaya kuna gaisawa" cike da ladabi ta amsa mashi da toh, murmushi suka sakar ma juna kafin taj Ya fuce daga dakin

Gaba daya abunda suka tattauna akan kun nan danish dake tsaye kan stairs Ya Waura gwiwar hannunsa na dama akan handrail, fuskarsa kamar jan gauta tsabar 6acin rai, ashe Yaji maganar Taj na cewa tadinga zuwa part din chief lallai kam akwai ?ura mai haya?i

Saboda abunda danish Yai mata gaba daya taji breakfast din Ya fita aranta, kamar an dauke mata yunwar cikinta, wani irin fitsari Taji Ya Waure mata mara, ba arziki ta nufi dakinsu duk Yana kallonta, tana shiga ta faWa toilet taja ?ofa.

Tunda tafara sakin shi take ganin wani bakon abu da bata ta6a gani ba, hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, bayan ta yi tsarki, gaban madubi ta tsaya zuciyarta na harbawa da wani irin sauri, In har fa bata gano menene ba hankalin ta bazai ta6a kwanciya ba...

A 6angarensu ummi bayan sun zauna a dining chairs din, cikin girmamawa su rubina suka gaishe da ita, da fara'a ta amsa masu yayin da take kallonsu masha Allah, Gida Yayi albarka, dagowa tayi suka hada ido da chiefs din dake kallonta daga masu hannu tayi"hi sannunku da kokari" amsa mata sukai Da yawwa madam ba tare da sun daina kallon ta ba, ba tun yau ba indai zasu ganta sai sun bita da kallon mayuntaka wato sunga sura..

Gwanin ban sha'awa suke cin abinci, sam babu wanda Yayi tunanin Ina danish da Unaisah saboda firar da suke Wan tabawa da su rubina taja hankulan su ...

___________________________Hajjaty
'?

Wuraren karfe 11 na safe ta fito daga kitchen hannunta ruke da madaidaicin faranti mai dauke da mug na green tea da kayan marmari

Tuntana tafiya take jin motsin mutun abayanta alamar akwai wanda ke bibiyarta, da zarar ta juya sai taga wayam babu kowa, hakanan ta dinga jin tsoro da fargaba, gashi babu kowa main falo din gidan duk suna a part din su.

Tana tafiya tana ?an waige waige kamar zatayi tuntu6e, cikin takun sauri ta ?araso dakin baba obie, sallama ta fara yi masa daga ciki tajiyo muryarsa ya amsa mata sallamar tare da bata iznin ta shigo

a kishingiWe ta same shi kan gadon shi, Ya tada kansa a pillow, hannusa Waya ruke da cazbaha yayin da idanunsa ke a lumshe, tuni kamshin turarenta Ya karaWe ilahirin dakin har saida Ya Wan buWe idanunsa..

A hankali Ta Waura masa tray din kan table

"Barka da safiya baba, Ina kwana, kun tashi lafiya"? Murmushi ya sakar mata kafin yace"lafiylou Alhamdulillah, Ina fata kema haka" ta amsa masa da eh

Mug din ta dauka ta mika masa yasa hannu ya kar6a tare da yi mata godiya'

"Ko akwai wani abu da kake bu?ata" ta faWa cikin kulawa, bakomai ya fado masa aransa ba face maganarsu ta jiya shi da owais lokacin da yace masa ko yana son ta, shi kanshi yana yaba kulawarta da kyautatawarta agaresa matar tayi ta ko'ina, ga iya daukar wanka....jin yayi shiru bai amsa mata tambayarta ba yasa ta Wan Wago ta kallesa ganin kamar ya koma bacci yasa tace"baba ko ka koma bacci ne"? Girgiza kai yai alamar eh,

"Idona biyu ke nake kallo" waro idanu tayi waje jin abun da yace da sauri ta sunnar da kanta ?asa

?ar dariya yayi ganin yadda ta ruWe"kwantar da hankalin ki, ay ba laifi bane don na kalle ki, kinyi min kyau ne" gaba daya ta ?ara kame kanta, dakyar ta kakaro murmushi kan la66anta

"Tashi ki tafi, nagode da kulawarki agare ni"nike da godiya" ta fada tare da mikewa ta nufi kofar fita kwatsam tajiyo sautin takun mutun, lokacin da ta fito bata ga kowa ba, tunani tayi anya ba wani ke bibiyarta ba? ga dukkan alamu anyi masu la6e, tuni tasha jinin jikin ta, da sauri ta mi?i hanya ta koma dakin ta, kamar yadda tabar pravin haka ta same shi kwance ya lullu6e rabin jikinsa da barko.

Zama tayi gefen gadon tana faman sauke ajiyar zuciya.

Jin motsu motsin pravin yasa ta kalli bargonsa, murmushi tasaki ganin Ya fara buWe idanunsa alamar zai farka, da sauri ta faWa kan jikinsa muryarta da yar shagwa6a take fadin"babyn baby, tun Wazu nake jira ka farka, ina fata ka tashi lafiya....." da wata irin kasala Ya ware manyan idanunsa da suka kada jawur saboda bacci ya sauke su kan fuskar hajjaty, manna masa sumbata tayi kan lips dinta kafin ta sumbaci karan hancin sa
"Honey, ina alkawarin da kayi min jiya? ko har yanzu ba agyara wayar bane? ta fada kamar zata sanya masa kuka tsabar shagwa6a

Har ya motsa la66ansa zai furta magana, unexpected sautin motsin ?ofarsu Ya daki kunnuwansu, lokaci Waya suka dakata tare da kallon ?ofar dake lilo alamar an ta6a ta...


Hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, aruWe hajjaty ta furta"wanene ke ta6a min kofa" muryar marwa ce ta karade kun nan su"Ni ce marwa" kallon juna sukai ita da pravin cike da mamaki, saboda babu wanda ke shigowa dakinta, tsakaninta da sauran ma'aikatan gidan daga kitchen sai in sun haWu a main falo ko wani part na gidan, kwata kwata bata sakar masu fuskar da zasu zo dakin ta, balle har suga sirrinta..

Muryar pravin kamar tame yin raWa ya furta"wannan wani irin ganganci ne"?

Hankalinta atashe tace"wlh ba laifi na bane, bansan meya kawota dakin nan ba, kaima ka sani bazan ta6a gangancin yin hakan ba"

"Je kiji me zata ce maki, kada ki bari ta shigo" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta sauko ta nufi ?ofar ta buWe ta le?a karaf suka haWa ido da marwa dake ta faman washe mata baki, da sauri ta ?ara babbake bakin ?ofar don kada ta samu damar ganin meke a dakin

"Marwa! Ta fada da mamaki da sauri marwa tace"am...um..barka da safiya.." bata amsa mata gaisuwar ba, sai cewa tay"ina fata lafiya? Don banta6a ganinki a Wakina ba..." washe baki marwa tayi muryarta da alamun rashin gaskiya ta furta"dama..um inaso zan fara aikin dinner ne da wuri to na shiga kitchen din sai naga store a kulle kuma babu makulli a bakin kofar, na tambayi abla ko ta dauka shine tace min yana a wurinki" wani kallon tuhuma hajjaty take jefa mata, abun yaso bata mamaki,
Murmushin gefen fuska tayi"hmm marwa kenan, kina abu kamar wadda ta samu cutar mantau, in ba ni ba waye dama yake ruke makullin store? da har zaki tambayi abla ina Yake bayan haka wani girkine zaki fara a yanzu? Bayan breakfast da kuka kammala ko dai baki kalli agogo bane?
Sosa ?eya tayi"wai da afara dinner din da wuri"
Kaitsaye tace mata"a'a babu bukata, kamar yadda kuka saba haka zakuyi dole sai lokaci Ya cika, sannan pls idan kinason Yin magana dani basai kinzo dakina ba! Ki kirani da landline din kitchen kamar yadda kuka saba kirana ku sanar da ni abu"! Ko amsar marwa bata jiraba, taja kofa Ta datse

Rai a6ace marwa take kallon kofar, dakin wai har ita hajjaty zata ja ma kunne kan karta kara zuwa mata daki? Lallai buri ya yi kama da mutun da alama maganar hajiya saratu zata tabbata matarnan bata da gaskiya Allah kadai Yasan makircin da take kullawa da har batason wani Yazo dakinta, dani kike magana hajjaty saina zame maki karfen ?afa agidan nan..." acikin ranta tafada Harta fara tafiya zata koma kitchen sai kuma ta dakata tana tariyo abunda Tajiyo adakin farkon dataje tafara yin la6e a kofar, tabbas taso tajiyo muryar hajjaty kamar tana magana da wani sai dai bata kaiga shaida hakan ba

Murmushin mugunta marwa tasaki a fili ta furta"ni da ke ne" tayi maganar tare da kama hanya tabar wurin.

Bayan komawar Hajjaty dakin, a zaune ta iske pravin yana jiran ta fuskarsa a yamutse saboda Ya tsani duk wani abu da zaija asirin shi Ya tonu

"Ta fada maki abun da ya kawo ta"? Ya jefa mata tambayar, zama tayi gefen shi kafin ta sanar da shi maganar da sukai da marwa

"Ni sai nake ga kamar le?en asiri ta zo yi min saboda babu kwanciyar hanlali atare da ita" ta faWa tana kallon fuskarsa

Pravin yace bana tunanin haka, just ki bar komai a hannuna idan ta ?ara yi maki wani abu da hankalinki bai kwanta da shi ba ki sanar dani" ta amsa mashi da toh


___________________________ANEELERH
'?

Yau saboda da zumudin zuwan benazir ko breakfast batay ba saboda tafi son idan benazir tazo su ci abincin a tare,

Su uku ne a kitchen suke aikin girka ma bakinsu abinci, gaba Waya kamshin abincin Ya cika ko'ina

"Pls ku yi sauri mu kammala ta faWa min da wuri zasu zo, dakyar ma in basu tafo ba"

"Aunty Aneelerh wacece bakuwar tamu ne"? Ana ce ta faWa tana kallon ta yayin da take tsaye gaban gass cooker tana aikin soye soye

"Ki bari idan tazo zaki ga wacece, nafi so na baki mamaki" cikin raha ta faWa

"Allah ya kawo su lafiya, har nakosa na ganta"

"Ameen,"

Kallon zahra tay, gaba Waya hankalin ta ba akan su yake ba, tana a tsaye gaban counter, inda ta Waura juicer ga kayan marmari sha?e da bowl da alama ta tafi duniyar tunani, tafi karfi mintuna biyar bata ta6uka komai ba, gaba Waya tunaninta na akan zayn, zuciyarta sai azalzalarta ta ke yi akan son ganinsa tayi missing dinsa.

"Zahra! Zahra!!" muryar aneelerh ce ta fargar da ita lokaci Waya ta sauke ajiyar zuciya tare da kallon ta

"Me kike tunanine? Naga kamar wani abu na damunki"? Murmushin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0