Showing 393001 words to 396000 words out of 413917 words

Chapter 132 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2703

ya tambaye sa wanene ke nemansa? Officer din yace Kanin makwabcin su ne Alhaji Musa, Shiru ya danyi jim aransa yana mai mamakin karfin Halin Alhaji musa da har ya iya takowa yazo gidansa neman shi, daga bisani yace ma Officer din ya shigo da shi.


sallamar Alhaji musa ce ta katse zancen zucin nashi, dakyar ya sakar mashi fuska suka gaisa har ya taya shi murnar kammala karatun su Aisha, bayan sun yi shiru na dan lokaci kowa da abunda yake sakawa aranshi, daga bisani Alhaji musa yai gyaran murya ya ce"dama nazo ne don in nemi alfarma agurinka" bai jira jin ta bakin sheikh imam ba ya cigaba da cewa"Ina son ka bani auren Aisha, saboda ta kwanta min araina"

wani kallo shiekh Imam ya watsa masa mai kama da harara.

Tashin farko Yace"sai yau na tabbatar da baka da Hankali Musa, kai baka ji kunyar tunkarata ido da ido ka fadamin wannan maganar ba? an gaya maka ni mahaukacine da zan dauki ?ata mai daraja in hada ta da fasi?in mutun, irin ka"?

Maganar imam Ta sosa zuciyar Alhaji musa amma dayake shike nema agurinsa sai ya shanye bacin ransa, yace"bai kamata ka gaya min maganganun nan ba, wanda yace yana son naka ai masoyinka ne, saboda nasan mutuncinta shiyasa na tako nazo da kaina don in nemi aurenta agurin ka..."

murmushin takaici Sheikh Imam yayi"Haba Musa, ko kayi zaton namanta wanene kai"? Ya fada tare da mi?ewa daga kan kujerar da yake ya juya ya nufi bookshelves din dakin mai Wauke da kundin dokoki dana tarihi, da sauransu.

A cikin kundaddakin Ya curo Criminal record Na Alhaji Musa, Ya wurga masa akan kirjinsa, Kafin Ya dafe table din gabansa da tafukansa Ya soma magana Yana kallon Cikin idanunsa..

"Mara Kunya fitsararre, Sau nawa Muna yanke maka hukunci a kotu akan mugayen laifukan ka, amma da zarar kaje prison sai dai muji labarin ka fita, saboda kasan me ka taka kana da manyan mutanen da suke daure maka gindi, sune suke sama maka mafaka a kasar waje, shiyasa kake sheke ayarka" ya faWa yana kallon Cikin idanun shi.

"Tayaya har kake tunanin Ni Imam malik zan iya baka auren yata aisha bayan nasan Halinka ciki da bai? Musa kaine Dealer mai fataucin miyagun kwayoyi a kasar nan, kai ne Cin zarafin mata masu rauni gurin tilasta masu don suyi karuwanci a kasashen waje, baka gajiya da keta haddin mata, last shari'ar da nayi akanka, yara masu talla kayi ma fyade sannan ka binne su da ransu don kada asirinka Ya tonu, cikin rashin sa'a aka samu wani bawan Allah dayaga lokacin da kake aikatan hakan harya kaika kara police station bayan sun gama bincike akanka suka mika ka kotu abun takaici bayan mun yanke maka hukuncin daya dace dakai mun tura ka prison sai dai muka ji labarin babu kai a kurkuku harma Ka gudu ka koma America da zama, saboda bakin zalincin ku, kai da ubayen gidan ka kuna amfani da haramtacciyar dukiyar da ku ka tara gurin toshe bakin shaidu da bawa jami'ae cin hanci...." Ya karashen maganar yana huci tamkar zai doke sa.


Alhaji Musa ya sunkuyar da kansa kasa, ya dunkule yatsunsa, ransa ya baci matuka da jin maganganun da Sheikh Imam ke gaya masa saboda kawai ya nemi auren yarsa.

"ka yi ha?uri ka nemi wata, amma sam ba ka cancanci ka mallaki aisha ba, nafi sha'awar ta auri mutun mai tsantsar ilmin addini musulunci, mai jin tsoron Allah, mai kuma kyawawan halaye da dabi'u wanda zai ruke min ita amana, Wallahi idan har na aura ma Aisha kai banyi mata adalci ba, Allah ma bazai barni ba saboda ita din amana ce agare ni"!

yanayin fuskar Alhaji musane Ya canza ganin wahalar shi na niyar ta tashi abanza.


Cikin kankai dakai yace"kada kayi min haka, wallahi inason Aisha itace mace ta farko da nayi burin in mallaka don mu raya sunnah, idan har don saboda halayena ne, nayi maka alkawarin zan shiryu in har zaka bani auren ta"

cike da takaici Sheikh imam Yace"Oh har saina baka aurenta zaka shiryu! Ba zaka shiru don Tsoron mahaliccinka ba"?

"Naji zan shiru saboda Allah, Kawai ni ka amince min in aure ta, komi ka ke so zan baka ina da tarin dukiya wanda zai ishemu muyi rayuwar mu" Da gadara yakeyi masa magana,

Dariya sheikh imam yayi"Musa kenan, Kai abun duniya ya dama, ni dukiya bata agaba na, ban damu da kyalekyalen duniyar nan ba, wanda wata rana zaka mutu kabarsu ne, daga kai sai halinka za'a binne ka, sannan ka duba kaga gidan da nake rayuwa cikin rufin asirin Allah, babu abunda na nema na rasa don haka kadaina yi min bagu da dukiyar daka tara ta hanyar Haram.."! hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, abunka ga mutumin da bai ta6a neman abu ya rasa ba, babban takaicin shi yadda ya aje girman kansa da komai yazo don ya nemi auren ta amma Sheikh imam Ya watsa mashi kasa a ido.

"Amma ai ka bari ita yar taka ta furta bata sona ko"? Ya fada tare da Wage masa gira...

Shiekh Imam Yace"Wallahi koda Aisha tana sonka ba zata aure ka ba! Balle ma nasan Jinina bazai ta6a kaunar fasiki irin ka ba, in sha Allah kaida Aisha sai dai hange daga nesa amma aure har abada, nayi fatan ma ace shureim ne yazo min da maganar auren ta, wallahi jiki na 6ari zan aura mata shi, saboda Ya cika duk wasu sharuddan da zan Iya mallaka masa Aisha..."

cikin rauni na murya Uncle musa yace"da me shureim yafi ni? wasu sharuddane ya cika wanda ni ban cika su ba"

Sheikh Imam Yace"ko ban fada maka ba, kai ka sani, shureim hafizi ne mai dumbin tarin ilmin addini, mutum mai tsoron Allah, mai koyi da sunnar manzon Allah SAW, ba kamar kai ba, daka sa duniya agaba...." wani irin zafin kishine Ya rufe idon Uncle musa, Yaji zafin maganar Shiekh Imam Ko sallama bai yi mashi ba Ya mike azafafe Ya fuce daga sitting room din.

Bayan Uncle musa Ya koma gidan yayansa damuwa ta hana shi sukuni, Yana ji aransa in har bai mallaki aishaba har ransa zai iya rasawa, bakomai yake hadama ba face surar jikin ta..

Dayaga bashi da wata manufa sai ya yanke shawarar tunkarar Aisha don ya nemi soyayyarta, yasan in har ta amince mashi Shiekh imam bai isa Ya raba su ba, Har court zai iya kai shi ?ara.

Da taimakon Aunty laura ta shirya mashi ranar da zaizo gidan donsu gana da aisha aranar shiekh Ya tafi gurin aikinsa. .

Agarden suka zauna, tana asanye cikin dogon hijab dinta cikin girmamawa ta gaishe da Alhaji musa ta kara yi mashi godiya bisa ga kokarin da yayi akan karatunsu, yaji dadin tarbar da tayi masa har yaji aransa ba zata ta6a ?in amsa bukatarsa ba.

Cikin nutsuwa Uncle musa ya fayyace mata irin kaunar da yakeyi mata, tashin farko Aisha tace"kayi hakuri da amsar da zan baka, wallahi bawai bana sonka bane, kawai ban ta6a yi maka so daya shafi aure ba, Ina jinka kamar Uncle dina saboda zumuncin dake atsakanina da Benazir, amma ni inada wanda nakeso..." bata kare maganar ba Yai saurin dakatar da ita ta hanyar Waga nata hannu har saida tadan sha jinin jikin ta.

"Karya kike kice bakisona, babu macen dana ta6a nuna inaso tayi rejecting dina, don haka kema akwai soyayyata acikin zuciyarki, idan ma kina jin kunyata ne to ki daina, ni ba Uncle dinki bane, ashirye nake da in aure ki, Aisha kiyi tunani akaina kafin ki yanke shawara, zan jira naji daga gare ki"

yana fadan hakan yayi tafiyarsa, gaba daya tashiga halin damuwa kuma ta kasa sanarma kowa, hatta Benazir da Aneelerh basu san da maganar ba, kusan sau biyar Alhaji musa yana tuntubarta a waya don yaji in ta canza????""""""" "
" " "
""""""""""""""""""" "!"""#"$"%"&"'"(")"*"+","-"."/"0"1"2"3"4"5"6"7"8"9":";"<"=">"?"@"A"B"C"D"E"F"G"H"I"J"K"L"M"N"O"P"Q"R"S"T"U"V"W"X"Y"Z"["\"]"^"_"`"a"b"c"d"e"f"g"h"i"j"k"l"m"n"o"p"q"r"s"t"u"v"w"x"y"z"{"|"}"~""?" ra'ayi amma ta nace akan ita bazata iya auren shi ba, tana da wanda takeso, daya matsa mata akan ta fada masa wanene takeso sai tace mashi yaya shureim ne, a lokacin ji yayi kamar ya binne ta da ranta saboda bakin kishine da shi, ya ji zafin furta sunan shureim da tayi, zuciyarshi ta raya mashi cewar ba ra'ayinta bane Shiekh imam ne ya cusa mata nasa ra'ayin dama ya nuna yafi sha'awar ta auri shureim daga nan ne ya kuduri aniyar saiya shiga tsakanin su.

Har gida yaje ya samu shureim Ya tambayesa meke a tsakaninsa da Aisha, dr shureim yace babu komai face mutunci, shi ya dauke ta kamar kanwarsa.

Uncle musa yace bai yarda ba, in har yana son ta ya fada mashi zaiyi mashi hanyar auren ta, daya matsa mashi da tambaya kawai sai yace mishi eh yana sonta amma bai ta6a sanar da ita ba.

Hankalin Uncle musa ba karamin tashi yayi ba, saboda ya fahimci dukan su suna son juna, kuma In har Shureim Ya furta yana son Aisha tofa babu makawa sai Sheikh imam Ya bashi ita.

hakan yasa shi yanke shawarar komawa gurin imam malik don ya kara rokonsa akan ya bashi ita, kusan sau biyar yana zuwa gurin imam amma ya rufe ido akan bazai ta6a aura masa aisha ba, ta ko'ina babu sauki, har aunty laura yaba cin hanci na makudan kudi donta karkato da hankalin sheikh imam akansa amma duk abanza, itama aishar ba irin magiyar da baiyi mata ba akan ta amince da soyayyar shi akarshe sai tayi blocking duk wata hanya da zata haWa ta da shi, hatta gidansu Benazir ta daina zuwa sai dai Benazir tazo gidansu ta same ta, ranshi ba karamin baci yayi ba, shi a ganin shi bata yi mashi halacci ba, kodan saboda dawainiyar da yayi dasu yaci ace ta saka mashi amma saita butulce dama shi baya abu dan Allah sai idan yasan zai samu riba.

bayan wasu kwanaki Uncle musa ya Wauke ?afa da zuwa Gidan yayansa kwata kwata suka daina jin duriyarshi, da Benazir ta sanar da Aisha baya kasar Ba karamin dadi taji ba, kuma ta saki jiki ta cigaba da zuwa gidan, wani lokaci atare suke zuwa gidansu Aneelerh wani sa'in kuma Anila ce ke zuwa gidajen su ta kawo masu ziyara, har takaiga iyayen su na ziyartar junan su.

Daga baya da soyayyar Aisha ta fara addabar Dr shureim har takaiga dakyar yake runtsawa saboda tunaninta, baya da burin daya wuce ya aureta, aranar daya shirya tunkararta don Ya fada mata irin kaunar da yake yi mata, A lokacin Aysha da Aneelerh sunzo Gidan su suna a dakin Benazir Suna fira, A bakin kofar dakin ya tsaya yana tunanin taya zai tunkareta da maganar? Zata kar6i tayin soyayyar shi ko kuwa? yana jin fargaban Aisha taki amincewa da shi shiyasama tuntuni yaki sanar da ita saboda fargaban amsar da zata ba shi.

Har ya zaro waya daga Aljihu da niyar Ya kirata don ta fito su ke6e, kwatsam kunnuwansu suka jiyo mashi firar da su ke yi..

"Yanzu tun da mun kammala karatu me ya rage mana"? Benazir ce tayi tambayar.

Aneelerh tace"Aiki da kuma Aure, amma Abie yace bazai bari in fara aiki a private hospital din daya buWe min ba har sai na tsayar da miji"

Benazir tace"Why not Ki ba Uzair damar ya turo da magabatansa? Tun da naga Jininku Ya haWu da shi"

Murmushi Anila tayi"Wai da Ke nake Jira, Idan Kinba Taj damar Ya tura da nasa magatan Gidan ku nima sai in ba Uzair Damar Ya tura gidan mu..." wani kallo mai kama da harara Benazir tayi mata..

"Pls mana ki amince masa nasan fa Kin mutu akan kaunarsa amma sai ki ta wani Ja mashi Aji"

"hmmm nifa ba aji nake ja masa ba, Ina tunanin ta yadda zan tunkari mommy da wannan maganar, daddy baida matsala nasan zai amince min, amma mommy bansan ya zata dauki abunba kinsan Mommy bata son dan jarida sannan shi ba dan wani Hamshakin mai kudi bane..."


Tun da suka fara magana Aisha bata tsoma baki ba, tayi shiru kamar hankalin ta baya akansu, har saida Benazir ta Wan dafa kafadarta tukunna ta mai da hankali akansu.

"Meke damunkine? Tun dazu kin yi shiru ba ki ce komai ba, ko baki ji abunda muke magana akai bane"

Murmushi tayi"Naji mana, mamakine ya kamani, Naji kuna maganar Taj da Uzair su wanene su din? Yanzu duk kawancen mu daku ashe har akwai wani sirri naku da bansani ba"?

Dariya su ka yi, Anila tace"Ay mana afwa Ustatha, ba haka bane, wlh mu ma bamu dade da sanin su ba, kin tuna ranar da muka fada maki zamuje shopping mall? One week da dawowarmu"?

"Hakane na tuna, Ay ranar na fadamaku Uzirin daya hana ni fita"

Benazir tace"toh A ranar muka hadu da su, kyawawan Samari kuma sun kwanta mana arai"

Taya su murna tayi Allah ya sa su zama Alkhairi agare ku

Suka amsa mata da ameen.

Anila tace"pls muna so muji ra'ayinki, Donni bana so mu riga ki yin aure, nafi so yadda muke aminnan juna, Muyi aure atare ya'yan mu su taso a tare"

Benazir tace"Aisha fa bata da matsala, Kinsan Allah yayi ta da farin jinin samari iri iri, attajiran masu kudi, Manyan Malamai sai ta zaba ta darje, Ko yau ta fidda miji baba Imam aurar da ita zaiyi Allah"

ta fada tana dariya, Murmushin takaici malama Aisha tayi Cikin raunanniyar murya tace"Bazan boye maku ba, dani daku mun riga da mun zama daya, Munsan sirrin Juna, Wallahi bana alfahari da farin jinin da nake da shi, saboda mafi akasarin mazan da suke sona ba dan Allah bane sai don Surar Jikina, Wlh Benazir da wuya namiji yazo gurina da sunan soyayya batare daya neme ni ba, Ina jin bakin ciki da taikacin hakan, ni nasan zaiyi wuya asamu wanda zai soni dan Allah..." dakyar ta kare maganar saboda kukan daya ciyota, Kalamanta sun karya masu zuciya.

Cikin shesshekar kuka tace"Inason Aure fiye da tunaninku, inaso in raya sunnar manzon Allah SAW amma taya zan samu wanda zai soni dan Allah"? Gaba daya tausayinta ne ya kamasu.

Lallashinta suka somayi tare da kwantar mata da Hankali, su ka ce In sha Allah zasu tayata da addu'a Allah ya bata miji nagari wanda zaiso ta tsakani da Allah.

Dr shureim dake a labe yana sauraronsu tun dayaji maganganun Aisha sai jikinsa yayi sanyi zuciyar shi ta karaya, Har Yaji shakkar furta Yana sonta saboda gudun kada tayi tunanin shima surar jikinta ya ke so.

Bayan wani Lokaci, Alhaji Ubaid Ya tsunduma a harkar siyasa kuma cikin sa'a ya shiga da kafar Dama, Arzi?in shi ya habbaka sosai, Rawar kai a wurin Hajiya layla har ba'a fada, dama ta jima tana cusa mashi ra'ayin ta akan ya shiga siyasa saboda taga yadda Alhaji musa ke fantama da dukiya abunda take ma kwadayi kenan, dama arayuwarta ta tsani taga Alhaji musa yafi Alhaji Ubaid Arzi?i tana jin haushin hakan sosai.

Dr shureim ya so ya kalubalanci siyasar da mahaifinsa ya shiga, Amma Hajiya layla ta take mashi burki ta hana shi magana adole yaja baki yayi shiru.

Alhaji musane yayi mashi hanyar da ya shiga Jam'iyarsu, a Karon farkon da Jam'iyar JDP ta tsayar da shi a matsayin Dan takararsu Na Gomna sunyi murnar da bazata Misaltu ba.


Saboda Farin Cikin hakan yasa Hajiya Layla ta shirya masu gagarumin Party don taya Alhaji Ubaid murnar takarar da aka tsayar da shi da kumayi mashi fatan Alkhairi.


Kafin Shigarshi siyasa saida ya fara tuntubar Shiekh Imam don ya bashi shawara, Sheikh yace shi bazai hana shi yin siyasa ba amma da zai bashi shawara yacigaba da kasuwancinshi sai yafi zama alkhairi a gare shi, saboda yawancin yan siyasa sai sun kauce hanya suke samun mulki, Nasiha sosai yayi mashi har yace ya dauki shawarar shi amma daga baya sheikh imam sai dai yaji labari agurin mutane cewa Alhaji Ubaid Ya tsunduma a harkar siyasa yayi mamaki sosai saboda bai ta6a bashi shawara bai dauka ba sai a wannan karan, abun daya kara Waure mashi kai, Wauke kafa da Alhaji Ubaid yai kwata kwata ya daina shigowa donsu gaisa sai in sun hadu a masallaci, daya fahimci kaukaucewar da yakeyi masa sai ya kyale shi don ya gano baya son ya hana shi yin siyasa shiyasa ya janye jiki da shi.

Lokacin da Celebration din Ya matso, Hajiya Layla ta gayyaci yan uwa da abokan arziki don su tayasu Murna, daga cikin wadanda ta gayyata hada Aunty Laura, Benazir kuma ta gayyaci Anila da malama Aisha, koda Aisha ta nemi izni agurin baba Imam yace bai amince taje party ba saboda yahudancine babu shi a addinance, bata ta6a musa masa ba sai akan maganar Party din nan, ta dinga rokonshi akan yabarta taje saboda ta yi ma Benazir alkawarin za ta je, In har ba ta je ba Benazir ba za ta ji dadi ba, Shiekh imam Yace tayi hakuri kawai, don bazai ta6a bari taje ba, wunin ranar kwata kwata babu walwala akan fuskarta, Har Aunty laura ta roka akan ta nema mata alfarma agurinsa aunty laura tace ita bazata sanya masu baki ba, saboda an nuna mata iyakarta don haka suje can su karata ita da uban nata, abunda yasa tace haka saboda taji haushin bukulun da shiekh imam yayi mata akan kudin da Alhaji musa yayi mata alkawarin zai bata intaja hankalin imam da Aisha suka amince da auranshi amma gaba daya suka watsa mata ?asa a ido abun ya kona ranta.

Ana i gobe za'ayi partyn, Tafiya ta kama sheikh Imam malik, manyan abokansa wadanda suka kasance shahararrun malaman addinin Islam yan kasar sudan dayake acan yayi karatu lokacin daya zauna gurin Kawunsa, abokanne suka gayyace shi wani taron karrama malamai da za'a gabatar a kasar sudan, kafin tafiyarshi saida ya kira Aisha ya kara gargadinta akan bai lamunta taje partyn nan ba, tace mashi toh in sha Allah bazata je ba, bayan tafiyarsa Aunty laura tace ma Aisha ay yanzu tunda mai gadin nata bayanan, sai ta shirya ta tafi tace ta fasa zuwa saboda batason ta sa6ama mahaifinta, bata matsa mata ba amma da Alhaji musa Ya kira ta waya yace mata yana son Aisha ta halarci Partyn in har tasa tazo zai bata Dala dubu goma sha biyar, Jiki na 6ari Aunty laura taje har dakin Aisha ta tunzurata akan ta shirya su tafi, baiwar Allah

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login