Showing 213001 words to 216000 words out of 413917 words

Chapter 72 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2655

tafi kada mu 6ata masu lokaci" ta fada tare da ruko hannun zahra suka fara tafiya, har sun kusa fita daga falon muryar Ana ta katse masu hanzarin su

"Aunty Anila, Allah ya kiyaye hanya agaishe min da hajiya adama..." dakatawa sukayi da yin tafiyar, a wani irin yanayi Anila ta dubi fuskar Ana wadda ke acan tsaye kofar kitchen jikinta sanye da riga da mini skirt, ta Waure kanta da hula sai faman sakar mata murmushi takeyi .
Batasan ya akai ta tsinci kanta da jin faduwar gababa,
"Zahra kunyi kyau sosai, kun burgeni, sai naji dama hada ni zaku tafi" murmushi zahra ta sakar mata"mungode kada ki damu next time idan zamu ?ara zuwa hada ke zamuje, yanzu dai ki koma kitchen, pls kafin mu dawo ki gyara mana bedrooms dinmu sunyi datti..." amsawa tayi da toh, kafin ta sake kallon Anila wadda keta kallon ta ko kyaftawa bata yi murmushi Ana ta sake yi mata
"Aunty anila, adawo lafiya.."
Dakyar ta jinjina mata kai, cikin sanyin murya ta furta"Ana ba lallai mu dawo da wuri ba! Ki kula da gidan, sai anjima" awani slow ta kau da idonta daga na Ana, taja hannun Zahra suka fuce daga gidan...

Ana tana a kitchen tana goge gogen floor da wiper ta jiyo tashin motocin su,

*AGIDAN UNCLE ABDALLA"

Hajiya Adama Yau ba zama, tunda Anila ta sanar da ita zancen zuwan su, ta fara yan gyare gyaren gida, ganin tana ta wahala ita kadai ga girkin da zata yi masu ko farawa batayi ba, hakan yasa Uncle abdalla Ya dauko mata hayar house help wata bayerabiya kakkarfa, atare da ita suka fara girkin cikin kankanin lokaci suka kammala shi, hajiya adama har mamakin matar takeyi kamar inji bata gajiya da aiki, tana da kwazo da ?warewa ta bangaren aikace aikacen gida, kafin wani lokaci sun kammala tsaftace gidan..

da sauri hajiya adama ta shiga toilet, tayo wanka, ta fara shirya kanta,wani tsadadden leshi ta sanya a jikinta, ta kashe daurin dankwali, ta zauna kan mirror chair tana ?arasa yin make up Win ta...
Sallamar uncle abdalla ce ta katse ta,
"Har yanzu ba su iso ba"? ta cikin mirror ta kalle shi suit ne a jikin shi..
"Nima naji shiru, amma ina ji araina sun kusa karasowa,
"Kodai basu gane gidan bane"?
"Bana tunanin hakan, ay na tura mata address din gidan tun jiya, bari na kira Anila naji.." ta fada tare da mi?ewa ta nufi wayarta dake ajiye kan mattress, kafin ta Wauko kiran waya ya shigo da sauri ta duba sunan mai kiran nata, murmushi tayi tare da kallon uncle abdalla"Anila ce ke kira" picking call din tayi ta kara wayar a kunne
"Anila kun taho ne"?
On the other hand anila tace"Eh, dama na kirane in fada maki mun kusa shugowa unguwan naku" wani irin farin cikine ya lullu6eta"Allah ya kawo ku lafiya" bayan ta katse kiran ta kalli uncle abdallah"tace min sun kusa isowa, yakamata muje mu taro su"
Murmushi uncle abdalla yayi"naga kina ta zumudin zuwan su, idan ma don saboda junaid ne kwara ki fidda rai, yau ranar school ne, ba lallai su zo da shi ba" daure mashi fuska tayi"ko baka fada ba, na sani, farin cikin dakaga inayi badan komai ba sai don saboda za'a kawo min ziyara gidana, kasan ba wani ke gareni a garin nan ba..." tay maganar tare da daukar mayafi ta yafa akanta,
Tayi gaba yabi bayanta. daidai lokacin da suka fito daga entry hall, suka hango mai gadin gidan Ya buWe gate, a jere motocin suka kunno kai cikin gidan,
Bayan sunyi parking, hajiya adama ta nufi motocin da sauri kafin ta karaso anila ta rigata fitowa da sauri ta nufe ta suka rungume juna fuskar kowannansu dauke da annurin farin ciki.

Abie da Uncle dan iya suka nufi uncle abdalla dake tunkaro su, suka fara yin gaisuwarsu ta manya Sassannun ku, da zuwa, ku ?araso ciki , Mamie da hajiya adama suka rungume juna fuskar kowan nan su Wauke da murmushi, bayan sun raba jikinsu, Ummi ta mi?a mata hannu suka gaisa a mutunce,kafin ta janyo zahra tayi hugginta dinta, daga bisani suka haWu gaba daya suka shiga falon gidan, yau ne karo na farko da su anila suka fara zuwa, zahra sai yan kalle kalle takeyi gidan ya burgeta ginine babba, ita kanta anila tayi mamakin haduwar gidan surukan nata, an wadata gidan da duk wani abu na biyan bukata.

Bayan kowan nan su Ya zauna kan sofa, Uncle dan Iya yace"masha Allah, kunsan ni bani gani inyi shiru, abdalla kayi kokari wannan dankareran gida haka kamar dubai"? ya fada Yana bin falon da kallo, hakan ba karamin dariya ya basu ba,
Mami tace"naso ace tuntuni mukazo ganin gida Allah bai nufa ba sai yau, gaskiya bamu kyauta ba.." hajiya adama tace"ay kun goge laifinku, tun da kuka zo yau gaba dayanku don ma babu jikalle na..."
Mami tace"Allah sarki, Ya tafi school, abunda yasa ma bamu tsaya jiran shi ba, sai marece suke dawowa.."

Fira ce ta barke tsakaninsu yadda kasan dangi Waya, daga bisani bayerabiyar dake a gidan ta shirya masu abinci akan dining, suka hallara gaba daya suka zauna suna ci, uncle dan iya sai santin abincin yakaye yi, ita dai anila hankalinta kamar ba akwance yake ba, ta kasa cin abincin, saboda wani irin faduwar gaba da take ji..
"Anila meke damunki ne? Naga kamar bakison cin abincin" cikin kulawa hajiya adama tay maganar, cikin sanyin jiki Anila tayi murmushi tace"babu komai mommy, abincin ne yayi min dadi shiyasa nake santin shi" dariya hajiya adama tay"karki damu idan ma baki koshi ba zansa akara maki ne nafi so ku ci ku koshi dama saboda ku akai girkin dayawa" murmushi kowan nan su yayi, zahra ba baka sai kunne Hankalin ta na akan plate din fatan doyan da take ci......

_______________________________
'?

A hankali motar dr shureim ta kunno kai cikin entrance gate din asibitin, bayan yayi parking din motar, Ya dan juya ya kalli zeenatu data langwa6e kanta kan shoulder dinshi, kwata kwata batasan inda suka zo ba, ta nutsu tana shakar kamshi turaren shi ta wani lumshe idanunta...
Cikin sanyin murya ya furta"zeenatu mun ?araso" buWe idanunta tayi tare da gyara zamanta, kwata kwata bata lura da inda suka zo ba, kusan atare suka fito daga motar, kamar ance ta kalli saman ginin karaf idanunta suka sauka akan sunan asibitin da aka rubuta da manyan haruffa masu daukar ido, wani irin bugu kirjinta yayi da sauri ta dafe saitin zuciyarta,
"Yaya shureim! Ina ne nan? Kamar asibiti nake gani? Dama nan zaka kawo ni"? Cikin rawar murya tay maganar tana ja da baya
"Zeenat ki kwantar da hankalin ki, kamar yadda kika gani asibiti ne, wurin auntynki benazir na kawo ki, kullum saita tamabayi kina ina meyasa baki zuwa dubata...." bai ?are maganarba, zeenatu ta juya a firgice ta dam?i murfin motarsu ta kutsa kai zata koma ciki da sauri Ya cafki hannunta ya fiddo da ita yana fadin meya haka zeenatu? Meke damunki ne? Benazir din ke bakison gani" wani irin kakarwa jikinta ya farayi ta Waura hannu biyu akai ta fasa wata iri gigitacciyar ?ara wadda tajanyo hankulan visitors din dake zarya a harabar asibitin, gaba daya hankalin mutane ya dawo kansu wasu har sun fara tambayar meya faru? wasu kuwa sunyi tunanin wani mugun abun akai mata...."
Cikin shesshekan kuka da murya mai ?araji take fadi "bazan shiga ba Yaya shureim ka maidani gida, wayyo Allahna na shiga uku, na bani ya shureim...." tsantsar tashin hankali ne akan fuskarshi gaba daya tabi ta rikitashi, ga jama'a da suka tasa shi gaba suna tambayar me akai mata...bai san sa'adda ya janyota kan kirjinshi ya rungumeta sosai kamar zai maida ita cikinshi, idanunshi sun kaWa jawur yai saurin kai la66anshi saitin kunnanta, A hankali ya fara zuba mata kira'ar alqur'ni wohoho zokaga idanu mutane sun nutsu suna ba idonsu abinci, wasu sai santin karatun shi sukeyi, yayin da wasu kuma suka kokwanton watakil aljanu gare ta, wani irin sanyine ya ratsa zuciyar zeenatu, gaba Waya ta narke mashi tana faman sauke ajiyar zuciya, tuni ta nemi kukan da takeyi ta rasa shi, tayi shiru sai ?ara nutsa kanta cikin kirjinshi takeyi, mutanan dake kallonsu sunyi masu ?awanya hada masu daukarsu hotuna da video hakan yasa shi kare fuskarshi ya ?ara ?an?ame zeenatun shi, ahaka yajata suka nufi cikin asibitin don bayajin zai iya juyawa da ita gida.=???

Duk ta kankame shi, mutane sai kallonsu sukeyi, nurses har tambayar shi suke yi patient ce? Yace masu a'a lafiyarta lou,
hajiya layla dake tsaye tana waya bakin kofar privet room juyowar da zatayi keda wuya ta hango su, arude take binsu da kallon har suka karaso inda take
"Shureim wacece wannan ka rungumo haka"? Ta fada tana kallonta sam bata gane wacece ba saboda ya rufe fuskarta.
"Mami zeenatu ce, tazo duba jikin benazir ne"
A ruWe tace"meke damuntane? Ke zeenatu ya akai? Ko bakison zuwane aka matsa maki? Muryarta kasa kasa ta furta"bana jin dadin jikina..."
"Haba shureim kasan bata da lafiya ka taso ta? Ko likita kukazo gani ne"?
"A'a mami, lafiyarta qalou, zanyi maki bayanin abunda ke damun ta, mu shiga daga ciki....."

___________________________________
'?

A lokacin Unaisah tana zaune kan chair din gaban gadon Benazir, hannun ta ruke da glass na ruwa, magani take bata in ta sanya abaki saita bata ruwan ta sha, ta maida kanta kamar ?aramar yarinya agaban unaisah, har yanzu bata daina binta da kallon kurullan ba...
"Mommy ki maida hankali kan ruwan da kike sha, kada ki shake" murmushi taskar mata"bana gajiya da kallon ki ne, Kin sace min zuciyata" da mamaki unaisah take kallonta, kalaman matar suna sanyata kokwanton kamar ta dawo hayyacin ta
Shigowarsu dr shureim dakinne Yaja hankulansu ga kallon kofar,
"Benazir yau Allah yayi, zeenatu tazo dubaki, sai dai kamar bata jin dadin jikin ta,..." da wani irin yanayi benazir ke kallon zeenatu wadda ta 6oye fuskarta jikin shureim...cikin?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? sanyin murya ta furta"Zeenatu...."! shiru bata amsa mata ba, Unaisah dai ta zuba ido tana kallon matashiyar dake kankame da shurem, jikinta sai kerma yakeyi kuma ta?i dago da fuskarta...
"Zeenatu bakiga auntyn naki ba"? In a low voice ta furta"bana son ganinta" waro ido waje benazir tayi sam ta manta da pretending din da takeyi saboda ruWewar da tayi, lamarin ya daure masu kai, arude hajiya layla ta kalli shureim suka hada ido, unaisah dake kallon su abun ya bata mamaki aranta ta ayyana kowacece wannan take ta wani boye fuskarta? Yanzu haka bawani kyan kirki gareta ba, in banda wulakanci hada wani cewa bata son ganin mamanta, yanzu haka yar kishiya ce... Acikin zuciyarta take wannan sambatu
Banezir kuwa jikinta yayi sanyi lakwas zuciyarta ta karaya da jin kalmar da zeenatu ta furta abun Ya girgizata sam takasa magana sai motsa la66anta take
"Pls kada hakan Ya dame ku, bayin kanta bane, Ina tunanin iska ne suka shiga jikin ta..." calmly ya zayyana masu komai dangane da abun da ya faru ranar farko da ya koma gida har yayi mata maganar benazir ta share shi, har zuwa ga abunda ya faru yau, mami ta tafa hannu tana ambaton "inna lillahi wa'inna ilaihirraji'in zeenatu Allah ya baki lafiya, Allah ya yaye maki abunda ke damunki, baiwar Allah ashe shiyasa tadaina zuwa asibitin, sannu zeenatu ta faWa tana le?en fuskarta, banza tayi da ita, benazir dai takasa magana kallon su kawai takeyi, ita dai unaisah ta baza kunne tana sauraron su bakomai ya bata haushi ba face Yarinyar da take ta boye fuska.

"Yaya shureim ka maidani gida! Kada daddy ya dawo ya iske bana nan!..."
Cikin kwantar da murya yace"ko ya dawo ba abunda zaiyi maki, ai ni na fito dake, da anjima zan maidaki, mu karasa ciki ki zauna..." yai maganar yana kokarin janyota cikin dakin, aikuwa ta turje tana yan fizge fuzge Hankali atashe mami tace"shureim abun da ban tsorofa kamar ba zeenatu ba, pls ka maida ita gida, tunda ta nuna bata son zama nan din..
Shi dai baison Ya maida ta gida saboda bai shirya komawa ba
"Mami babu kowa gidan, ita da kanta ta nuna batason zama ita kadai shiyasa na taho da ita..." ya fada fuskarshi ayamutse...
Saukowa Benazir tayi daga kan gadon ta tsaya agabansu cikin karyayyar murya ta furta"zeenatu! dagaske bakison gani na"? da wata irin tsiwa ta furta"Bana son ganin ki, ki daina yi min magana...." kafin ta ?are maganar, Benazir takai hannu ta dam?i shoulder dinta dakyar ta rabata daga jikin dr shureim ta jijjigata da karfi har mayafin daya rufe fuskarta ya zame kan kafaWarta....

Kamar daga sama sukaji Sautin fashewar glass kusan atare suka kai dubansu ga Unaisah wadda ta mi?e a sukwane tana faman zazzare idanun ta, tsantsar tashin hankali da rudani ne akan fuskarta
"Azeezaty meya faru...." hada baki sukayi wurin tambayar ta, la66anta sai kerma sukeyi gaba Waya ta rikice ta kasa magana, gabanta na faduwa ta nufi zeenatu wadda ke ta kerma tana zare blue eyes dinta akan fuskar Unaisah

Wani irin gumi ne ya wanke fuskar Angel duk da sanyin A.c din dake a dakin, ta sanya tafukanta ta murza idanunta saboda tana kokwanton ko dai gizau takeyi mata ne? In ba haka ba tayaya mutumin daya mutu zai dawo araye? Ta kasa yarda da abunda idanunta ke nuna mata, kusan sau uku tana murza su don su dawo dai dai, Hankulan su dr shureim na akanta, sun rasa gane meke damun ta! Ko dai tasan zeenatu ne? Meyasa ta razana da ganin zeenatu harta fasa water glass din hannun ta! Dukansu kansu ya daure

Agaban zeenatu ta tsaya suka fuskanci juna, ido cikin ido, dafe kai unaisah tayi da hannayenta biyu saboda wani irin sara mata da yayi, zuciyarta ta fara dakan uku uku, Muryarta adabarbace ta furta*"UNAIZAW'S'*


*Daga Alkamin Boss Bature=?%?
'?*


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya=?%?=?%?=?%?
*Zuzeam empire* takawo muku babbar gara basa
Duka akan 5500 ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa =????=????=????=?? ?

Wa.me/+2348144015291 For more information say hi =?K? Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam empire tashirya tsaff dominku=???=???=??? muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu

*DAHUWAR KAZA*

Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato *Ni ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya*
Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt *Akwai kyauta
*INA MASU JEGO DA AMARE*
Karku bari wannan dama ta wuceku
*08144015291*
Zuzeam empire

ASSALAMU ALAIKUM Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 08144015291. 1000 kacal =?L?
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd

Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar g1da set
Mai jego set

Dadai sauransu





__________________________________
'?




"Junaid Dan Allah ka daina kuka! Me ya faru dakai? Meyasa ka 6oye a cikin wardrobe? ina Anah? Kwata kwata baya fahimtar me take cewa, kuka yakeyi na fitar hayyaci hada kai hannu ya dunga bugun bayan ta, fashewa sukayi da kuka daga ita har zahra wani irin tausayin shine ya kama su, gashi sun rasa gane kan shi.

banko kofar dakin ummi da mami su ka yi daga waje suka jiyo sautin kukan junaid hakan yasa suka watso aguje suka fado dakin, lokaci Waya suka ci burki suna kallon Anila dake a rungume da junaid, waro idanu sukayi hadi da buWe baki tsabar mamaki da al'ajabi ne ya kama su! Sam sun kasa furta magana na dan wani lokaci kafin mami ta matsa kusa da su, muryarta da rudu ta furta"ikon Allah kamar junaid nake gani! a ina kuka gan shi ne"? Shuru ba wanda ya bata amsa har saida ta Wan daka masu tsawa saboda akagareta"bakuji ina magana bane? A ina kuka gan shi"? Dakyar Zahra ta tsagaita da yin kukan tana faman jan numfashi ta labarta masu komai.

Mami ta zagba salati tana tafa hannayenta, gaba daya sun shiga rudani, lamarin yayi matukar rikirkita tunaninsu sun rasa tunanin me zasuyi, kowa da abunda yake sakawa aranshi..."
Mikewa Aneela tayi Wauke da shi, ta nufi mami tana kuka Yana kuka an rasa me lallashin wani"mami ku taimaka ku lallashe shi ya?i yin shiru na rasa gane meke damun shi, junaid baya a cikin hayyacin shi, idanunshi sun kaWa jawur sai sambatu yakeyi mana"
mi?a hannu mami tayi zata dauke shi aikuwa ya ma?e kafaWa ya ?ara shigewa jikin mamanshi, sautin kukan shi ya cika kunnuwansu, sun rasa ya zasuyi da shi, gaba Waya suka yi mashi ?awanya suna kokarin shawo kanshi ta hanyar lallashin shi kwata kwata baya sauraron su, adai dai lokaci su abie sun dawo daga masallaci kwatsam sukajiyo kukan junaid mai ?araji, wani irin faWuwar gaba ne ya darsu a zukatan su, mahboob har yana tuntu6e garin saurin ya shiga ciki, gudu gudu sauri sauri uncle ?an iya da Abie Sukeyi suka nufi dakin Anila, suna shiga suka iske su mami tsaitsaye cirko cirko fuskokin su sharkaf da hawaye, kusan atare su abie suka kai dubansu ga junaid, arude mahboob Yace"Junaid! Aunty Anila a ina kuka gan shi? Ko Ana ce ta dawo da shi"? Abie ne yayi hamdala Yana fadin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login