Showing 405001 words to 408000 words out of 413917 words

Chapter 136 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4443

uku ina doka sallama baki amsa ba, nama yi zaton kin shiga toilet ne ko bacci kike yi, ashe idonki biyu kina a kwance kin takura kan ki, why pls dubi yadda kika rame? Fuskarki duk ta yamutse kamar wata tsohuwa" Ta fada tana ?are mata kallo..

A rude Anila ta girgiza kai muryarta da in-ina ta ce,"Lafiyana lou ba abun da ke damuna..."

Kaitsaye Benazir ta ce, "?arya ne wallahi, Dole akwai abunda ke damunki sai dai idan baki son fadamin ne."

Murmushi ta dan yi,"Bafa wani abu bane, kawai ina yawon yin mafarki akan Uzair...." tunkan ta kare maganar Benazir ta tari hanzarinta, "Mami ta faWa min hakan, amma ban yarda ba Anila, Look, nifa nasan wacece ke, mafarkin Uzair bazaisa ki shiga damuwa har haka ba, bayan kinsan mafarki ba gaskiya bane, in ma hakanne a yadda nasanki da tawakkali Addu'a zaki dage kina cigaba da yi masa bawai ki tsananta damuwa ba, kawai ni yanzu ki fadamin meke damunki kinsan tsakanina dake babu 6oye-6oye, Kinsan sirrina nasan naki, kuma dai abokin kuka shi ake fadawa mutuwa, pls In har kin yarda da ni...."

Shiru Anila ta yi jim tana tunanin kodai ta fadawa Benazir watakil ta taimaka mata su nemi mafita, ru?o hannayen Benazir ta yi acikin nata, suka ?urawa juna ido..

A hankali hawaye suka fara zarya kan kuncin Anila, hakan ba ?aramin Waga hankalin Benazir ya yi ba.

"Zan fada maki saboda na yarda dake, amma dan Allah ki rufa mini asiri Benazir, bana so kowa ya sani mu barshi a matsayin sirri tsakanina da ke.." A ?agare Benazir ta jinjina mata kai.

Nan take Anila ta fayyace mata komai, tun daga ranar da suka je gidansu Hajiya Adama da abunda ya faru bayan dawowarsu game da 6atan Ana, da inda suka ga Baby Junaid a sume cikin drawer shelve da yadda Junaid ya burkice masu suka rasa gane kanshi, komai saida ta sanar da ita, har wayar Ana ta curo daga cikin pillow case ta kunna mata videon ta mika mata don ta gani da idanunta.

tunkan ta ?arasa kallo yatsun hannunta keta kerma kamar wayar zata kife kasa, idanunta azazzare cike da tashin hankali ga wani irin faduwar gaba da take ji, labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairan minha..., bata ?are sallallamin ba Anila ta yi saurin toshe mata bakinta da tafin hannunta gudun kada wani ya ji yo su.

Tuni hawaye sun wanke fuskar Benazir, Sai faman girgiza kai ta ke yi.

Cikin muryar rada Anila ta ce,"Allah abun tsoro dan adam abun tsoro, muna nan sake da baki ashe muna a tare da mugun iri acikin mu! Benazir ki fada min taya hankalina zai kwanta? Wai Uncle dina shi ne yake aikata wannan fasikancin a cikin gidan nan? Babban tashin hankalina Ina Ana? Yau kusan wata uku babu ita Benazir, ina jin tsoron ace ya kashe ta...." Ta fada tana kuka ?asa kasa.

A hankali Benazir ta zame hannun Anila data toshe mata baki da shi.
Hawaye wasu na bin wasu akan kuncinta ta ce, "Anila dama Ana ta 6ace shine baki fadamin ba tun lokacin da abun ya faru?"

"Na yi zaton da son ranta ta gudu shiyasa ban fadamaki ba saboda na saka ran zata dawo."

Jinjina kai Benazir ta shiga yi.

"Mugu bashi da kama Anila, munafuki kamar na Allah, wlh bazamu kyale shi ba, dole mu ?watarwa Ana hakkinta sannan mu maka dan iska gurin hukuma...."

bata kare maganar ba Anila ta yi saurin katse ta, "Pls ki daina Waga murna bana so wani ya ji, yanzu me yakamata mu yi? Kin dai ji ta ce mutunne mai hadarin gaske in har muka yi kuskuren da maganar ta koma masa zai iya salwantar da rayuwarmu tunda ba imanine da shi ba, Allah kaWai ma yasan munanan ayyukan da yake aikawata bayan wannan da Ana ta fada."

Jinjina kai Benazir ta yi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata abubuwan dake faruwa da ita a gidan Uncle Musa, yun?urin kashetan da ake yi ga kuma kurciya da aka yi mata, tun rana ta farko da aka fara yi mata take zargin akwai wanda ke bibiyar rayuwarta.

Anila da ta zuba mata ido ganin ta yi shiru bata da niyar yin magana yasa ta dafa kafadarta, "Benazir kin yi shiru ba ki ce komai ba?" Numfasawa Benazir ta yi kafin ta ce, "Aneelerh, akwai damuwa, nima fa akwai wanda ke bibiyar rayuwata a gidan Uncle Musa, kusan sau hudu ana yunkurin kashe ni....."

Waro idanu waje Anila ta yi, cike da ruWani take kallon Benazir ya yin da gabanta ke faduwa rass rass!!!

Nan Benazir ta labarta mata komai da ya faru da ita tun farkon zuwanta gidan..

"Aneelerh wallahi ba don Allah yana kawo min Wauki ba, da tuni an jima da kashe ni, don ma yanzu babu tabon yatsun hannun mutumin a wuyana ya goge dana nuna maki kin gani"

Hankalin Anila fa ya tashi sosai, duk tabi ta rude, "Benazir! anya ba iska bane? In ba haka ba wanane zai yi maki hakan agidan Uncle Musa? Gidan dake a tsare da Security Officers taya wani bare zai ????####### #
# # #
################### #!#"###$#%#&#'#(#)#*#+#,#-#.#/#0#1#2#3#4#5#6#7#8#9#:#;#<#=#>#?#@#A#B#C#D#E#F#G#H#I#J#K#L#M#N#O#P#Q#R#S#T#U#V#W#X#Y#Z#[#\#]#^#_#`#a#b#c#d#e#f#g#h#i#j#k#l#m#n#o#p#q#r#s#t#u#v#w#x#y#z#{#|#}#~##?#iya shigowa har dakin ki ya yi yun?urin kashe ki??" ta fada tana zare idanunta...

Girgiza kai Benazir tayi, "Wlh Anila ba iska bane, mutunne! Abunda yasa na kara karfafa zargina saboda abu biyu, na farko kurciyar da aka yi mini! Aka rabani da dangina, Na biyu labarin da Ana ta bada, Shine ma ya farfaWo da tunanina, koma wanene mutunne kuma yana amfani da sihiri kamar yadda Ana tace Uncle Wan-iya yana amfani da sihiri gurin sarrafa ta"

Da ?warin gwiwa ta yi maganar tana duban Anila wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa yake yi kamar mazari.

"Ina zargin mutumin da yayi min kurciya shine yake son kashe ni.."

Cikin shesshekar kuka Anila tace, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'iun! Banazir mun shiga Uku! Wanene wannan? Laifin me ki ka yi masa da ya ja har ya ke son raba ki da rayuwarki? Wai dan Allah meyasa hakan ke faruwa da rayuwarmu? Daga wannan sai wannan?"

Maganar Anila ta sake tuna mata abunda ta faWa mata game da Taj, cikin saurin ta ce, "Anila! Kinsan tunanin da nake kuwa??" Girgiza kai tayi da sauri, "A'a."

Gyara zama Benazir ta yi,

A labarin da kika bani na abunda ya faru da su Uzair, kin tuna Alhazawan da suka yi ma le?en asiri? Har suka rikiWa suka handame uba da ?a'yansa saboda yayi masu le?en asiri...?" Cikin sauri Anila ta jinjina kai,"Kwarai kuwa haka ne!"

"To baki tunanin ko halin da nike ciki nada ala?a da hakan, sai nike ganin kamar idan muka fada ma Taj komai zai taimaka masu gurin yin binciken da su ke yi akan Alhazawan nan da kuma 6atan Uzair? Kuma kinga Taj yanzu jami'e ne shi, sannan yana a gidan Director General In har muka je masu da maganar wallahi ina mai tabbatar maki zasu dauki mataki akan Uncle dan-iyan, tunda su jami'ai ne sun fi mu sanin ta yadda zasu bullowa lamarin, ko ya kika gani?" wata irin nannauyar ajiyar zuciya Anila ta sauke, Wlh sham ta shafa'a ta manta da cewa Taj jami'in bincike ne ai da tuni ta sanar da shi komai.

"Ban ta6a sanin ni shashasha bace sai yau da kika ankarar dani, Mu da muke da jami'i a hannu, Wlh gaba Waya kaina ya kwance tsawon kwanakin nan inata neman mafita, kwata kwata tunanina bai bani in tuntubi taj ba, nama manta da cewa shi jami'i ne sai yanzu da kika tuna min."

Murmushi suka sakar ma Juna.

"Yanzu ya za a yi? Babu bu?atar 6ata lokaci, da zafi zafi ake bugun ?arfe, ?wara muyi amfani da damar da muke da ita tunkafin lokaci ya kure mana" A cewar Anila.


Benazir ta ce, "Ay daga nan sai gidan DG, Nifa dama da shirina nazo wlh, na ma manta ban fada maki abunda ya kawoni ba saboda halin dana riskeki..."

"Anila kusan One month bana samun Unaisah a waya! Shima Taj kona kira baya picking? Baki ga na rame ba nima? Damuwa ce wllh, Gashi kwanakin nan sai munanan mafarke-mafarke na ke yi akanta da ni kaina, Ina ji araina kamar wani abu na faruwa da su..."

Fuskarta a marairaice ta faWa, Anila ta ce, "Ai bake kadai ba, Ni kaina Idan na kira bana samun su a waya, wlh hankalina ba a kwance yake ba, don ma tashin hankalin videon nan da na gani ya dauke mun hankalina almost 2 weeks ban neme su ba."

"Ba surutu yakamata mu tsaya muna yi ba, na baro Dr Shureim a waje yana jirana, ki tashi ki shirya mu tafi."

_________________________________
'?

"Shiru Har yanzu basu fito ba," A cewar Ummi, Mami ta ce, "Kinsan ?awaye In aka haWu ba'a gajiya da fira,"


Ummi ta kuma cewa,"Kuma na ji ta ce ita da yayanta ne, shi ba zai shigo bane? An bar shi a waje yanata jira."

"Nima abunda na gani kenan, bari na je na yi masu magana su je suce ya shigo." tana kokarin mikewa sai ga Benazir da Anila sun nufo falon hannunsu ru?e cikin na juna.

Ba zaka ta6a gane sun yi kuka ba, kowaccensu ta gyara fuskarta ko alamun hawaye babu, dubai abaya Anila ta saka ta yi rolling veil akanta ko makeup bata tsaya yi ba.

"To fa Ina zuwa kuma? Ai da yanzu nake niyyar shigowa inji me ake kitsawa ne, Kun yi zamanku shiru a Waki."

Murmushi suka saki, Mami ta kuma cewa, "Yakamata kuyi wa Shureim magana ya shigo ciki mana."

Sai lokacin Anila ta ce, "Dama zamu fita unguwa ne."

"Ina zaku je ne?" Kallon juna suka dan yi kafin Benazir tayi saurin cewa, "Gidan Hajiya Adama, tuntuni ni ke ta so inje Allah bai nufa ba, sai yau na yanke shawarar zan zo Anila ta rakani, dama itace ta fadamin sun dawo nan da zama...." Fara'a Mami tasaki, "Kai Amma kinyi tunani mai kyau, nima nayi kauron baki ne amma wlh abun na araina, tuntuni nike ta so in shawarci Anila ta raka ki ku je su gan ki, ni nasan zasu yi murnar dawowarki."

Ummi ta ce, "Nifa wlh na yi zaton ma sun san da dawowarta, ashe ba'a fada masu ba, gaskiya ba'a kyauta masu ba"

"Ai yau zamu wanke laifinmu, zan basu mamaki, har gida zan kai masu Benazir" A cewar Anila, dariya su ka yi, Mami ta ce, "Ku tafi yana ta jiranku gashi ko ruwa ba a kai mashi bama, in kun isa ku gaishe mana da su, sannan kada ku daWe dan Allah, zan ma kira Abie dinku in faWa masa"

"Zasu ji, in sha Allah bazamu dade ba."

A bangaren Dr Shureim, har ya gaji da jiran Benazir jin shiru bata fito ba, buWe motar ya yi tare da fitowa da niyyar ya bisu, ?arar horn din motar da ya ji ne yasa shi Wan dakatawa ya juya yana kallon motar dake kunno kai cikin gidan.

Ta gaban shi motar ta wuce ta yi parking a gaban entry hall, bayan ta kashe motar ta fito tare da zagayawa other side din motar ta buWe backseat, ta Wauko baby Junaid dake ta sharar bacci jikin shi sanye da uniform dinshi, dayan hannunta ruke da food basket dinsa, Two weeks kenan da komawarsa School.

"Yaya Shureim ina wuni?" Ta faWa da fara'a akan fuskarta,

Fuskarshi dauke da murmushi yace, "lafiya lou Zahra, ya kike? Ya gajiyar aiki?"

"Alhamdulillah, Kai kadai ka zo ne"?

"Benazir na kawo tana ciki." ya fada tare da kallon Junaid, "Junaid bacci ake yi, ankwaso gajiyar school."

Murmushi Zahra ta yi tare da cewa, "Mu shiga daga ciki" Ta faWa tare da yin gaba yabi bayanta, har sun kusa shiga falon sai ga Benazir da Anila sun fito suka yi kacibus da juna.


Da fara'a Zahra ta gaishe da Benazir ta amsa mata da fara'a itama akan fuskarta.


"Aunty Benazir why zaki bar ya Shureim a waje fisabilillah?"

Yar dariya Benazir tayi, "Bafa ni na hana shi shigowa ba, shine ya ce in fara shiga zai biyoni daga baya."

Bayan Anila ta gaisa da Dr Shureim ta ce ma Zahra unguwa zasu fita, ta kula da Junaid, sai zuwa anjima zasu dawo."

Bata nemi sanin inda zasu je ba ta ce, "Allah ya dawo daku lafiya."

Suka amsa da ameen, bayan Zahra ta shige ciki Dr Shureim ya dubesu da dan mamaki yace"Bangane ba! ina zaku je ne?"

"Yaya Shureim mu je zamu faWa maka."

Bai yi musu ba suka nufi motar, bayan duk sun shiga ya tasheta suka tafi.


_____________________Obie Estate=?%?


Koda suka ?araso main gate na estate din basu sha wahalar shiga ba, Security Officers basu dakatar da su ba, Saboda sun gane fuskar Anila kuma tayi masu bayanin cewa gurin Hajiya Saratu suka zo, suna jin hakan suka basu permission din shiga.

Bayan Motar su ta shiga cikin estate din kaitsaye suka nufi villa Win Owais, Tunkan su ?arasa Security Officers din dake tsaron gate din suka nufo motar hakan yasa Dr Shureim yin packing din ta.

Officers shidda ne suka yiwa motar tasu ?awanya,

Knocking window glass din aka yi, "Get out of the car!" Waya daga cikin su ne ya umarta.

Bayan sun fito suka fuskance su.

"Su wanene ku? Daga Ina kuke? Wa kuka zo nema?"

Da hannu Dr Shureim ya nuna Benazir da Anila, "Ai sai ku yi masu bayani, Ni dama ban so zuwa ba, don nasan ba lallai mu samu shiga ba, amma kuka matsamin, yanzu ba ga irinta nan ba." ya faWa fuskarsa a haWe don shi baya son abunda zai haWa shi da masu kaki...

"Ki kira Taj din a waya, Ni nasan kona kira ba lallai ya Waga ba."

Benazir ce ta faWa idanunta akan Officers din da suka zuba mata ido har saida Dr Shureim ya ankara da mayataccen kallon da suke binta da shi, ransa ya 6aci cikin harshen larabci yace ta lullu6e jikinta da mayafinta.

Da sauri ta gyara mayafin ta lullu6e kirjinta da kanta sa6anin da da yake akan kafadarta, duk da haka basu daina kallonta ba, ta ji haushi ita da ta yi kwalliya don Taj ya gani sai gashi wasu na nema su riga shi gani.

Almost 3 times Anila tana doka masa kira baya picking, hankalin su ba ?aramin tashi ya yi ba..

"Ya zamu yi Benazir! Ya ?i Wagawa wlh"

"Keep trying, idan ba haka ba wadannan masu fuskar shanun ba bari zasu yi mu shiga ba."

Cikin harshen larabci ta yi maganar..

Murmushi Dr Shureim ya yi tare da Wan girgiza kanshi jin abunda yar'uwarsa ta fada, jami'an kuwa sun baza kunne da yake ba arabi da ace da hausa ko da turanci ta fada da taci na jaki.

Taj na ?o?arin fitowa daga toilet yana ta gungura wheelchair dinsa ya jiyo muryar Batool tana kwaWa masa kira,"Daddy, wayarka tana ringing, wani ne ke kiranka"

Har ya nufi ?ofar dakin sai gata ta faWo ko sallama babu, tana ta haki ta mi?a masa wayar tana fadin, "A falo ka barta saman hannun kujera."

Bai kar6i wayar ba sai cewa ya yi ta karanta mashi sunan me kiran, Wan zare ido ta yi kafin ta dubi sunan da ya bayyana akan screen din wayar.

"An..An..Antin Yu.. nai..sah.." da?yar ta ?are karatun a lokacin har kiran ya katse, Murmushi Taj ya sakar mata, "Auntyn Unaisah ne, kin yi kokari daughter, Allah ya yi maki albarka."

Ya faWa tare da kar6ar wayar, sai faman sakin murmushi ta ke yi, tana son taji an yabeta in ta yi abu.

"Ina ?ar uwar taki ne?"

"A Waki na barota kudundune cikin bargo."

"Bacci ta ke yi ne?"

Girgiza kai ta yi, "Waya ta ke yi da Chief, Daddy baka ji yadda take kashe mishi murya ba hada shagwa6a fa," fashewa yayi da dariya har fararen hakoransa suka bayyana.

"Sha?a mini in ji me take ce masa?"

Da biyu ya yi maganar saboda yana son yadda Batool take kwaikwayon maganar Angel dinsa, aiko da yar shagwa6a ta ce, "Shine ka tafi baka jira na tashi daga bacci ba, pls kada ka daWe ka dawo gida bazan jure zama batare dana sanyaka a idanuna ba"

Tuntsirewa Taj ya yi da dariya, Itama dariyar ta kama yi yadda kasan uba da ?arsa.

"Daddy, ka ji daWi?" ?aga mata kai ya yi, "Sosaima, kema da kika bani labarin ga wannan" Ya fada tare nuna mata robar peanut din da ya aje kan drawer bai kaiga fara ci ba, da sauri taje ta dauka tare da yi ma shi godiya.

Fitowa ta yi daga Wakin jikinta a sanyaye, kwata kwata babu walwala, a saman stairs ta zauna hawaye cike tab da idanunta take kallon Peanut din da daddy Taj ya bata, A hankali ta soma Webowa tana afkawa a baki tana ci, hawaye na sintiri kan kuncin ta, Allah kaWai yasan me ke damun ta.

Fitar Batool ke da wuya, wani kiran na Anila ya sake shigowa wayar tasa, picking ya yi tare da kara wayar a kunne.

Bayan sun gaisa ne Anila ta fada masa gasu a bakin gate na gidan security sun hana su shiga ya taimaka ya yi masu hanya su shigo.

Shiru ya yi yana tunanin hanyar da zai dakile shigowarsu saboda baya son suga halin da yake a ciki, ga Chief ma baya nan, bayan haka ba'a son ma kowa yasan wani abu dangane da farmakin da suka kai, in har su Anila suka gan shi zaune kan wheelchair dole hankalinsu zai tashi harma su nemi jin me ya faru da shi..

"Taj na ji ka yi shiru baka ce komai ba?" Muryar Anila ce ta katse tunanin da ya ke.....
Muryarsa a dabarbarce ya furta, "Anila meyasa baki kira kin fadamin zaku zo ba?"

"Banyi tunanin yin hakan ba, saboda na ga Almost weeks kona kira bana samunka."

"Anila, sai dai ku yi hakuri ku koma gida, yanzu bama nan mun je yin meeting a headquarter Win mu."

On the Other Hand Anila ta zabga salati tana fadin, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, dan Allah Taj ka taimaka ka bada iznin a barmu mu shiga ciki, wlh zamu jira har zuwa lokacin da zaku dawo gidan, Don Allah Taj, wlh wani abune mai mahimmanci ya kawo mu, It's urgent, please help."

Ta fada tana kallon Benazir data yamutsa fuska kamar zata sanya kuka.

Shiru Taj ya yi yana nazarin maganarta, tun daga kan yanayin muryarta ya fahimci da akwai wani abu da ya kawota gidan,

"Okay,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0