Showing 273001 words to 276000 words out of 413917 words

Chapter 92 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4485

da ke sintiri kan fuskarta tayi kukan tayi addu'ar amma har yanzu zuciyarta taki sarara mata daga radadin da take mata, gani take kamar ta rasa Danish.

aranta tana ji in har kurkukun ya koma tabbas zata bishi ne ko da hakan zaiyi silar rasa ranta don ji take bazata iya rayuwa batare da shi ba.

"Unaisah!" ummi ce ta kira sunan ta, tayi shiru tamkar bata ji ta ba

"Nasan kina ji na, ni bansan ya zanyi dake ba, duk irin kokarin da nayi gurin kwantar maki da hankali kinki daina kukan nan, ga abincin ki dana sa akawo maki shima kinki ci, to wai kukan da kike shi zaisa ya dawo ne? Tun da kinyi addu'ar sai kibar ma Allah komai In sha Allah zai dawo...." cikin sigar lallashi ta faWa tare da zukunnawa gaban prayer mat din

"Dan Allah ki tashi ki ci abincin ki..." da wata irin karyayyar murya ta furta"aunty Ummi, ba zaki gane ba, ni kadai nasan halin da nake a ciki, zuciyata bata min dadi ji nake kamar zan rasa raina ne, yaya Omar ya 6ata min rai, shine silar komai, wallahi Aunty ummi naji zafin kalaman daya gaya ma Danish, duk da baida ilmi ko jahili akayi ma gori sai yaji ba dadi"

jikin Ummi ba karamin sanyi yayi ba, ga wani irin tsantsar tausayin Unaisah daya kamata, tasan bai wuci hada soyayyarshi ke azabtar da ita ba.

"Kiyi hakuri Unaisah, In sha Allah Danish zai dawo, Allah shi zai tsare sa aduk inda yake, mu taya shi da addu'a ni inaji araina ko dan saboda kaunar da yake yi maki zai dawo"

dakyar ta buWe idanunta wadanda suka kada jajawur ta dubi ummi duk da halin da take a ciki tayi mamakin kalmar kaunar data furta.

fahimtar hakan yasa ummi tay saurin furta"naga kamar yafi kaunarki a cikin yan uwanki, kema haka shiyasa nace haka, kada ki Wauka ko ina sanya maku ido ne"

shiru tayi bata tanka mata ba.

"ni abun da nake tunani watakil ya ke6e kanshine awani guri don ya gusar da bacin ranshi in ba haka ba Danish ay ba za ace ya 6ace ba, mutumin da ba shi kadai bane tsaf zai iya kawo kan shi gidan nan..."

bata kare maganar ba ta dakata tana kallon Unaisah ganin yadda ta zabura ta mi?e tsaya kamar zata fadi saboda rashin kwarin jikin ta

"Ina zuwa"?

"Yanzu zan dawo aunty ummi, wani abu zan duba" tana fadan hakan tasa kai ta fuce daga dakin cike da sa ran hasashen ta zai zama gaskiya, maganar da ummi tayi ta tuna mata da wani abu daya ta6a faruwa.

________________=؋?Chief Owais=ت?

Kwance yake akan gadon shi, yar singlet da short ne ajikin shi, damuwa ta hana shi ta6uka komai, ya dade bai shiga tashin hankalin daya shiga a yau ba, wayarsa dake akan bedside drawers sai ringing ta ke yi daga kiran ya katse wani ke shigowa sautin ya cika kunnuwan shi, amma baya jin zai iya picking din su yasan bai wuci Na hannun damansa bane suke kira don suji ko an ga Danish.

Shaf ya manta da bakin da za su yi, saida tunanin Ya faWo mashi aran shi kafin ya mike ya janyo wayar shi tare da duba screen din My dad shine sunan daya gani saida ya fara daidaita nutsuwarsa kafin yai picking call din

"My Son, Ya kake Ya aiki, ka manta da daddyn ka ko"?

Duk da halin da yake aciki sai da yaji nutsuwa ta shige shi jin muryar daddynsa

lumshe idanun shi yayi cikin sanyin murya ya furta"lafiyalou daddyna, ni na isa in manta da bugun zuciyata? Mutumin da nake kwana in wuni da tunanin shi araina saboda kaunar da nake masa"

Sautin dariyar mai girma sharafuddeen ce ta ratsa kunnan shi cike da nishadi yace"My Son kasan duk wata hanya da zaka kare kanka agurina, ka faranta raina, but meke damunka ne? Naji muryarka kamar baka jin dadi..."

Shiru yayi jim dama yasan zai yi wuya in daddyn nasa bai gane wani abu ba, dayawan lokutta ta muryar shi kadai yake gane halin da yake a ciki.

"Babu komai, yanzu na tashi daga bacci ne, shiyasa kaji voice dina wani iri"

"Hmm owais kenan, har ni zaka boye ma damuwarka"?

"Daddy, ka yi hakuri zan iya kiranka anjima mu yi magana"?

"Okay, in ba baka kira ba, Ni zan kiraka, ko inzo gidan naka da kaina kasan bana wasa da lafiyarka" yar dariya chief yayi saboda yaji dadin maganar shi ba wani jimawa sukayi ba sukai sallama

layin Omar ya danna ma kira kusan sau uku tana ringin bai Waga ba sai a kira na hudu yayi picking.

Kara wayar yayi a kunnan shi"Omar, kana Ina"?

On the other hand big guy yace"na tafi neman bugun zuciyarka saboda bana so in rasa ka" shiru yayi jimm yana maimaita maganar big guy harya fahimci ranshi ya 6aci saboda yayi mashi karya, location dinshi ya nuna yana agidan kamar ko ya sani yana akwance kan gadon bai jima da tashi daga bacci ba.

"Omar zamuyi magana, nasan meke damunka, pls don't forget to get the soldiers ready and go to the airport, jirgin su commender yakusa yin landing nan da minti talatin "

"Consider it done, sir, amma ya yakamata kaima ka shirya mu tafi airport din atare, zasu fi jin dadin tarbar da zamuyi ma su"


"Just do what I say" ya umarta, bai bari big guy ya kara magana ba yayi rejecting call din don baya jin zai iya fita daga gidan a halin da yake a ciki.

*Unaisah Angel*

Bayan fitowarta daga dakinsu bata nufi ko'ina ba sai upstairs tana tafiya jiki duk ba kwari ta tura kofar Wakin ta shiga daga ciki bata ga kowa ba.


Gadon shi tabi da kallo sai ta dinga ganin kamar zata gan shi kwance yana bacci, kau da idanunta tayi ta juya ta nufi toilet dinsa.

A hankali ta daura tafukan hannayen ta, ta tura ?ofar ta buWe ta, dira ?afarta ke da wuya taci karo da abunda yayi silar razanar da ita ta daddage ta fasa kara tana ambaton sunan Allah ta dafe kanta da tafukan hannayenta, hadi da runtse idanunta jikinta ya fara kakarwa, wani irin faduwar gaba taji tamkar ana dakan sakwara a kirjin ta.

dukkan ilahirin jikinta rawa yake kamar mazari tayi matu?ar firgita da abunda idanunta suka gane mata, tayi matukar razana, yatsun hannunta na kerma ta bude kofar Wakin garin saurin ta fita cikin rashin sa'a tayi tuntu6e da ?asan hijab dinta dake ja da kasa gaba Waya ta wuntsila ta yi kundunbale ta kife ?asa hankalinta yayi mugin tashi jikinta yadau zafi rau wata irin zufar tashin hankali ce ta fara tsastsafo mata.

Tana ta kokarin mikewa donta gudu taji motsin buWe ?ofar tuni tasha jinin jikin ta, ta ?ame a durkushe ta kasa Wagowa yayin da ?wa?walwarta ke tariyo mata Halittar da tagani a cikin toilet dinsa kamar Wolf (kerkeci) jibgegen gaske.

?amshin turaren Chief ne Ya ziyar ci kofofin hancin ta, Kafin DaddaWar muryarsa ta katse zancen zucin ta

"Unaisah? Are you Okay"? Ay tana jin muryarshi ta yi wani irin yunkuri da iya karfinta na karshe ta zabura ta mi?e, gaba Waya ta faWa kan broad chest dinsa ta ?an?ame shi, cikin shesshekar murya take faWa mashi abunda ta gani a cikin toilet din tare da yi mashi nuni da yatsan ta.

Sam ya kasa fahimtar me take nufi, sai kallonta yake yadda ta kankame jikinshi ta hanashi motsawa daga gani ta tsorata ba kadan ba.

"Unaisah, what's wrong? Who's in the toilet?"

Batare data Wago ba ta furta"dodo ne a toilet din sa,"

"Okay, zanje na duba, ki jira anan" ya fada tare da ruko hannayenta a hankali ya banbare su daga kan waist dinsa.

yayi mamakin uwar zufar daya gani akan fuskarta kamar an yayyafa mata ruwa ga zafin da jikinta ya Wauka yaji shi har jikin shi da ta rungume shi sai faman jan numfashi take tafin hannunta Waya dafe da saitin zuciyarta.


"Ki kwantar da hankalin ki, Ina atare dake, ba abun zai faru..."

yawu ta haWiya tana faman zare idanunta acikin nashi ta amsa mashi da toh.

har ya Waga ?afa zai nufi toilet din Yaji ta dam?o upper arm dinsa, slowly yakai duban shi gare ta.

Girgiza mashi kai tay a tsorace tace"Don't go alone, I don't want anything to harm you"

murmushin gefen fuska ya sakar mata har cikin ranshi yaji dadin nuna damuwa da ta yi akan shi hakan ba karamin faranta ranshi yayi ba.

"Kada ki damu, ba abun da zai faru dani in sha Allah" ya fada yana kallon Heart shaped lips dinta da suka ji?u da ruwan hawayen ta.

Ta?i sakin rigar shi saboda ta tsorata da abunda tagani tana jin fargaban wani abu ya same shi, shi da bai saba da wahala ba.

Ma?e mashi kafada tay kamar ?aramar yarinya cikin sanyi murya tace"hankalina bai kwanta daka shiga ba, pls kada kaje, ka kira salsabeel awaya yazo ya gani ko ka kira sheikh imam malik"

A hankali ya cire hannun ta daga kan arm dinsa

Kamar ta sanya mashi kuka, bai jira ya kara jin me zatace ba, Ya nufi toilet din sai da ya fara karanta addu'ar shiga kafin ya sa tafin hannunsa ya ture ?ofar A hankali ta buWe.


Without feeling nervous ya fada cikin toilet din, Yana shiga idanunshi sukayi mashi kyakkyawan gani yayi matu?ar mamakin ganin shi kwance cikin kwamin wanka Ya cika shi da ruwa, ko kayan jikin sa bai cire ba ahaka ya kwanta a ruwan Kamar ma bacci yake yi.


_Tsantsar mamaki da al'ajabi ne suka bayyana karara akan fuskar shi, Ikon Allah mutumin da suke ta wahalar nema kamar zasu tada garin abuja, ba irin neman da jami'an su basuyi mashi ba sako da lungu na garin saida suka bincika basu gan shi ba ashe yana acikin toilet dinsa kamar al'jani, ko taya akai ya shigo gidan? Bayan har gate officers Win gidan sai da ya tambaye su koya dawo gidan suka ce mashi bai dawo ba, gani yake kamar amafarki yake kallon shi saboda zuciyarsa taki aminta da abun da idanunsa ke nuna mashi_

Da tsantsar ruWani ya furta"Danish! Is that you?"


*DAGA ALKALAMIN BOSS BATURE
'?*
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: __________________________________=؋?
'?=؋????=ؘ?



a ruWe ta kalli fuskar shi, ya haWe rai kamar ba daddynta ba, ta rasa gane meke faruwa da shi ne.

Babu wanda Ya lura da abunda Ya faru tsakaninsu, Hankalin yan uwanta baya akan su
Duk da haka bata kawo komai a ranta ba, ta kuma cewa, "Daddy, Chief ya fada maka an ga Danish a cikin toilet Winsa...." banza yayi da ita tamkar bai ji maganar ba, hakan ba karamin Waga mata hankali ya yi ba.

komawa tayi cikin yan uwanta jiki a mace ta tsaya zuciyarta cike fal da tunanin sauyawar daddyn nata, fatanta Allah yasa ba wani abu ke damun shi ba.

Walking slowly yake taka stairs, da karfi Jemimah ta furta sunan Danish hakan yaja hankulansu gaba daya suka kalli stairs din bakunansu a buWe saboda tsantsar kyan da yayi, wata hadaddiyar light grey thobe ce a jikinsa ta bi surar jikin shi, ya Waure sumar kan shi with hair ties, gaba daya sun shagala da kallon shi, ?asa-?asa da murya ummi ta furta Tabarakallahu ahsanil khalikin, Allah yayi halitta..."

A second to the last step na stairs Win ya Wan dakata da yin tafiyar jin alamun kamar ana kallon shi kafin ya Wago da ido ya dube su, motsin buWe kofar falo yaja hankulan su.

Gaba Waya hankalinsu ya koma kan masu shigowa, Big guy ne ya shigo da sallama a bakin shi, kafin U.s armies din suka shigo kowannansu suit ne a jikin shi...zuba masu idanu su ka yi kamar ba su gane su ba, sun yi shiru suna kokwanton anya su ne? Saboda basu tsammaci zasu gan su ba.

Dakatawa su ka yi da yin tafiyar suna kallon su kusan su shida suna jira suga reaction din su, Wani irin ihun farin Ciki Gabriel Ya saki, da gudu Ya nufi Lieutenant thompson Sojan daya taimake shi a dajin evil forest saboda sarkar cross din shi, kafin Ya ?araso thompson Ya bude mashi hannayen shi ya fada jikin shi yayi hugging din shi gaba daya suka fashe da dariya.

Wayyo Allah daWi da wani irin farin ciki sauran ex-prisoners suka nufe su kafin su ?araso suka mi?a masu hannuwansu don su yi hugging din su, aiko suna ?arasawa ?an matan suka ?i bari su yi hugging Winsu sai dai suka yi shaking hands, in ka cire jemimah da ta ma?al?ale Commender har saida ya Wauke ta, mazan cikin su suka yi hugging dinsu Waya bayan Waya, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki, sunyi mamakin zuwan bazatan da suka yi ma su.

Da tsantsar mamaki Unaisah ta furta"Commander James! Captain Lewis! Major Smith! Jackson Lee! Canal Harry! Lieutenant Thompson! What an astonishing reunion! Is this really a chance encounter?"

Dariya suka saki gaba dayan su, da fara'a commender james ya ce, "Indeed, it's us! We hope you're overjoyed to see us. We've come specifically because of you, and we hope you'll welcome us with open arms." (Yeah mu ne, muna fata kunyi farin cikin ganin mu, munzo ne saboda ku, fatan zaku kar6e mu hannu biyu..." )

bai ?are maganar ba suka haWa baki gurin furta, "We welcome you, most warmly! We're truly elated to see you!"

DaWi ne Ya lullu6e sojojin, sai kallonsu sukeyi gwanin ban sha'awa sunji dadin sauyin da sauka samu sun kuma jinjina ma Chief, su Hibba da basu san su wanene ba sai faman baza masu na mujiya su ke yi cike da son sanin su wanene su Win.

Captain lewis ne ya nuna su da hannunshi cikin harshen turanci ya ce, "waWannan sune sauran yan uwan naku"? A tare suka haWa baki gurin furta Eh, Tambayar sunayen su yayi Sajeed ne ya gabatar masu da su..

Yana zuwa daidai kan Deeja Commender Ya dubi Haris, "Is she your sister cos you look alike"

Yana murmushi yace Eh sister Winsa ce.

"She's the cause of his heartbreak" Unaisah ta faWa da zolaya, dariya sojojin su ka yi.

Major smith Ya ce,"Dear Angel, where is that handsome young man, mai nauyin bacci ban gan shi ba ko baya nan .." bai ?are maganar ba Thampson Ya ce, "nima abunda nake so na tambaya kenan, Ina Danish"? da yatsa Unaisah ta nuna ma su shi, yayi tsaye kan stairs, idanunsa na akan su, gaba Waya suka kai duban su gare shi Commender ya ce, "Har yanzu yana nan da ?yuiyarsa?"

ganin kamar baida alamun zuwa gurinsu ne yasa Unaisah yin saurin cewa,"may be bai gane ku ba ne," major ya sake cewa, "Mun riga da munsan halin shi ai, Ya bacci har yanzu yana yi ko ya daina?

Dariya suka saka gaba Wayan su, da ido Unaisah tayi mashi alamar ya zo gurinsu ganin kamar sun damu da son ganin shi.

Saukowa down ya yi ya nufe su, commender ya mi?a mashi hannu, "Danish, come here, I'm thrilled to see you! I hope you're safe and sound," ya faWa tare da yin hugging Win shi, In low voice ya furta, "I'm fine, ina yi maku barka da zuwa" ya faWa tare da raba jikinshi daga na commender ya bi sauran yayi hugging Winsu tare da yi masu barka da zuwa hakan ba ?aramin daWi ya yi ma su ba.

Big guy ne yace da su, "Mu shiga ciki, ku zauna ku huta." Hannayen su ru?e dana prisoners suka nufi falon, kafin su ?arasa Taj dake tsaye yana kallon su, Ya matso kusa da su suka gaisa da junansu, big guy ya gabatar masu da Taj a matsayin mahaifin Unaisah sun yi murnar jin hakan sosai, duk budurin da ake Ummi tana can gefe Waya tana yin waya har sai da commender ya hangota yana ganin bayanta ya gane itace, nufar ta yayi yana isa ya rungume bayanta, a Wan firgice ta juya don ta ga wanene ta haWe rai amma koda ganin commender James sai ta waro idanu cike da mamaki ta ambaci sunan shi, "Sir James, is that you? I'm surprised," ta faWa tana yar dariya

Sir james ya ce, "It's me, dear. Yesterday when we called, I hid the point of my coming because I wanted you to be surprised."


Murmushi ta sakar mashi, "I welcome you wholeheartedly I'm at a loss for words to express my happiness and how much I've missed you."

"I've missed you too, dear one. I'm overjoyed to see you." Ya bata amsa.

Ya yi zaton za ta yi hugging na shi amma sai ya ga akasin hakan, Taj da Big guy kuwa tun rungumar farko da commender yayi mata suka kalli juna, dama sun san za'a rina tun da su dabi'ar su ce yin hakan, a kan sofas suka zauna gaba dayan su, nan fa ex-prisoners suka fara cika su da surutu suna basu labarin abubuwan da suka faru bayan dawowar su Nigeria, suna tsaka da yin fira Chief Ya sauko down shima ya kimtsa tsaf cikin suit nasa, suna ganin shi suka mi?e da sauri commender ya nufe shi suka rungume juna a mutunce suka gaisa ya yi mashi barka da zuwa, kafin ya nufi sauran sojojin ya mi?a masu hannu suka gaggaisa.

Kowa na gidan tun daga kan Gate security Officers har Chefs na kitchen saida suka shigo falon domin yi ma ba?in Chief barka da zuwa, hakan ba ?aramin faranta ransu yayi ba ganin yadda kowa ke Wokinsu sai girmama su ake.

Batare da bata lokaci ba, Chefs suka shirya masu dinner a dining, duk girman table Win saida suka cika shi da kayan abinci kala kala.

Yau gaba Wayansu su ka yi dinner a tare da ba?in su, gwanin ban sha'awa su commender sun ji daWin karramawar da akai ma su, abun da yafi burge su yadda prisonsers suka saki jiki da su kamar irin sun haWa ala?a ta jini da su, hakan yasa suma suka samu walwala kamar suna a gidajen su na America, ga jemimah da ta yi ta basu nishaWi da surutunta, ta maida commender kamar kakanta, har abinci take bashi a baki, ta yi kane-kane akan laps din shi, Danish kuwa hankalinshi na akan Unaisah ya lura kamar akwai wani abu dake damunta saboda yadda take cin abinci kaWan kaWan kuma hankalin ta yafi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0