Showing 363001 words to 366000 words out of 413917 words

Chapter 122 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2662

ya furta"nagode da shawarwarinku, in sha Allah zanyi abunda kuka ce, amma Yanzu nafi bukatar wanka, zan shiga ciki, idan na fito zanci abincin.."

yana faWan hakan Ya mi?e cike da rashin kuzari Ya nufi part dinsa.
Yana shiga Ya faWa kan gado Idanunsa na fuskartar ceilling, komai daya faru a gurin Ya?in Ya fara tariyowa Hannunsa daya dafe da saitin Zuciyarshi, Yafi jin Danish Fiye da kowa sai kuma amininsa Omar wanda a halin yanzu yana agadon asibiti rai hannun Allah As a result of his brain injury, ya shiga coma ba lallai ma ya dawo da cikakkiyar lafiyarsa ba, a bayanin da docs su ka yi ma shi kenan.


abu na biyu da ya kwallafa rai akai Shine Elders, Alwashi ne ya daukarwa kanshi Elders ba zasu kai karshen watan nan ba batare daya gano su ba, abun da Yafi tada mashi hankali tsohuwa Khala matar ta tsaya mashi aranshi! Kalmar data fara furta mashi "owais kaine ka girma haka"? Meyasa yake jin kamar ya san muryarta? Meya faru da ita? Hakika tsohuwa Khala tayi masu kokari, ba wai iya makamai ta taimaka masu da shi ba, ta taimaki fursinonin da suka ku6utar, shi Kanshi ya jinjinama jarumtakarsu Ita da Danish sun cancani a yaba masu, don shi ji yake da ace Danish yana raye ba abun da zai hana Ya sauke mukamin shi na director general Ya dam?a mashi saboda ya cancan ta.

A hankali siraran hawaye suka wanke fuskar shi ya Wan numfasa tare da lumshe idanun shi yana jin wani irin yanayi mara dadi a tattare da shi


aranar da suka kwana a sansani kasancewar a masauki daya suka zauna kafin suyi bacci sun dan ta6a fira da shi har ya dan bugun cikin shi yace ya fada mashi meke a tsakanin shi da Unaisah kar yai tsammanin yana sanya masu ido ne, kawai Ya lura da yadda suke kaunar junansu, a lokacin har saida yai murmushi kafin yace ma shi ya dauka Unaisah bugun zuciyar shi ce, yana tunanin mutun zai iya rayuwa batare da zuciyarshi tana bugawa ba? Dariya chief yai ya girgiza kai yace a'a bama zai ta6a yiwuwa ba, yace mashi toh haka Yake jin Unaisah, a lokacin Chief ya sake tambayarsa ya fada masa wani buri yake so ya cika masa idan suka dawo bayan sunyi nasara, ya danyi jim kamar yana nazari kafin yace baya bukatar komai, kawai shi abunda yake so yai masa alkawarin koda bai rayu ba idan sukaje kai farmakin Ya ruke Unaisah da mahaifinta da sauran Yan uwan shi yabar mashi amanar su ita kadaice alfarmar da zai nema agurinsa.

Bayan ya dawo daga duniyar tunanin daya lula A hankali ya Kife kanshi jikin pillow, fuskarsa ta 6aci da hawayensa..

_______________________________
'?

"Dan Allah ku faWa mana ina dan uwanmu Danish meya faru daku"? Batool ce ta kuma tambaya...

Cikin sanyin murya Commender Haroon yace"ku kwantar da hankalin ku, Danish bai mutu ba, saboda bamu shaida mutuwarsa ba"

A takaice Ya labarta masu abunda Ya faru a ranar da suka kai farmakin bai boye masu komai ba"

Canal herry yace"munyi babban rashin na har abada ba zamu ta6a warkewa daga radadin da muka ji ba na rashin Danish, zai yi wuya asamu jarumi irin shi a duniyar nan" Ya fada tare da saddar da kan shi ?asa.

mikewa Unaisah tayi kamar bata acikin hayyacinta kafafunta sai kerma sukeyi ruko hannun ta Taj Yayi"My angel, zauna muyi magana, bafa mutuwa yayi ba, ni nasan zai dawo ne da kanshi In ma bai dawo ba zamu koma ne"

gaba daya hankalinsu Commender na akanta, ta runtse idanunta sosai, jikinta kakarwa yakeyi kamar wadda sanyi ya kama, dakyar ta furta"daddy, Danish Yana acikin rijiya ta gidan kurkukun kaddara tare da evil giant me hadarin gaske? ku ka tafo ku ka baro shi!, sannan Elders basu mutu ba sun yi nasara kenan? ta faWa tare da dafe goshinta tana huci tace"shiyasa nace ku tafi dani, ni dama saida raina ya bani wani mummunan abu ya faru ashe mafarkin da nayi gaskiya ne"

"Unaisah, Ki fahimta bamu da yadda zamuyi ne, Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan, bamu isa mu canza mashi kaddarar shi ba, yakamata ki godema Allah Unaisah baki yi farin ciki ba? Saboda sadaukarwar da Danish yayi Mun ceto rayukan Yan uwanku dake a kurkukun kaddara yanzu haka suna a asibiti a karkashin kulawar likitoci, bayan haka mun ku6uta da ranmu da ba don shi ba da tuni mu kanmu mun rasa rayukanmu"

Bata jira karashen zancen shi ba, ta zame hannunta daga Nashi Cikin sauri ta nufi dakinsu ta shiga ta fada toilet, ta kunna shower da faucet don kada sauti Ya fita, da hannu biyu ta daddafe kanta dake sara mata, Ta daddaga ta fashe da wani irin kuka mai cin rai kamar ranta zai fita, ihu tadinga Yi tana hauka hauka gaba daya shatun jijiyoyin goshinta Ya fito rudu rudu kan fatarta, hatta wuyanta shatun jijiyoyinne, wani irin mahaukacin zafi temperature din jikinta Ya dauka, Idanunta suka kaWa jawur kamar garwashin wuta, kamar ana rura wuta Cikin zuciyarta saboda bala'en radadin da takeyi mata, sau uku tana buga kanta Jikin sink, har saida fatar goshinta ta faffashe jini ya wanke kyakkyawar fuskarta, nan take Hancin ta ya fara bleeding, lokaci daya tafara jin wani irin azababben ciwon kai mai azabar radadi, juwace ta kwasheta gaba daya ta yanke jiki ta faWa kan floor, wani irin duhune Ya mamaye ganinta, Ji take kamar ta tsaga kirjinta ta ciro zuciyarta ta jefar saboda tafarfasar da ta ke yi.

Maganganunshi ne suka fara dawo mata acikin kanta ..

_"Angel, baki damu dana mutu ba? Ina kaunar da kike mini? Kin za6i da naje na bada raina"?_

_"Abu Waya da nakeso Kiyi min al?awari shine, Ko bayan tafiyana kada kiyi kukan rashina, kada kiki cin abinci, ko ki hana idonki bacci saboda ni, sannan koda ban dawo ba, kiyi hakurin Jure rayuwa batare dani ba..."_


"Meyasa zaka yi min haka? Ta fada acikin ranta

"Don nace ka bada ranka ba ina nufin ka mutu ba, taya kake tunanin zan iya rayuwa batare dakai ba? Na rasa farin cikin rayuwata, me rage min? ya Allah Ka dauki raina in huta"

Lokaci Waya ta fara tariyo farkon haduwarsu agidan kurukukun kaddara, at sight da sukayi tozali da juna sai da ta razana da ganin kyawun shi...In har Danish bai dawo ba, to kuwa tabbas zata dawwama da bakin ciki arayuwarta.....=???

Tana jiyo sautin bugun kofar da suke yi mata, sama sama muryoyinsu ke yi mata yawo akai Unaisah ki bude kofa, pls ki bude, wai baki ji Ina magana! Ba zaki bude ba"?

ko yatsanta bata iya dagawa, saboda halin da ta shiga...

Lokaci Waya ta fara jin matsanancin ciwon kirji, hudojin fatar jikinta suka fara fitar da gumi ta ko'ina zuface Ke tsatsafo mata kamar an yayyafa mata ruwa, numfashinta yayi karanci dakyar take Jan shi bata kara sanin inda kanta yake ba=???


*Bayan Wani Lokaci*

*OIH*

Da matsakaicin Gudu Motar su ta shigo asibitin tunkafin suyi parking, Nurses suka fito a gaggauce hannayensu ruke da Stretcher agaban motar suka aje, Jikinshi na rawa ya fito daga backseat na motar, Ya zura hannu Ya dauko Unaisah dake a rungume Jikin Ummi, kwata kwata babu Numfashi a jikinta, Batool sai kuka takeyi kamar ranta zai fita, da kanshi Ya kwantar da ita kan Stretcher din, Nurses suka gungura ta zuwa Emergency ward yayin da Su ummi ke abiye da bayan su.


A waiting Area Ummi da batool suka tsaya Suna jiran tsammani, Chief yana a zaune kan seat Ya dafe forehead dinsa da tafin hannunsa, idanunsa sun kaWa jajur saboda tashin hankalin da yake fuskanta.


Bayan yan mintuna, Motar Us armies da ta Senior agents ta karaso asibitin, visitor din dake kai komo a harabar asibitin sai kallonsu sukeyi, gaba daya suka fito daga Cikin Motocin hada Taj wanda gaba daya fuskarsa ta jike da hawaye kamar karamin yaro yayi kuka sosai, ga shi ba koshin lafiya gare shi ba, dama ko sallamar shi ba ay ba Ya matsa lamba akan a sallame shi saboda yar shi, dakyar ya samu Chief ya sanya hannu suka sallame shi acan inda aka kwantar da su a (Combat support hospital)


gaba dayansu babu wani mai kwanciyar Hankali, Sun rasa ina zasu sa ransu suji dadi a duniyar nan, Na hannun daman Chief suka kewaya batool da Ummi suka fara lallashinsu da kwantar masu da Hankali, Shima Taj haka suka dinga tausarshi yana azaune kan wheelchair dinsa ya sadda kan shi kasa, Kasa jurewa yayi a karshe ya gungura kujerarsa Ya koma bakin Kofar dakin da aka kwantar da ita, Kasancewar Kofar ta glass ce yana iya hangen Docs din da suka kewaye gadon ta, sun dage damtse suna ta kokarin ceto rayuwarta, leken ta ya dinga yi tana a kwance kan medical bed Sai jan numfashi take duk da sun sanya mata Oxygen mask akan fuskarta.

Addu'o'i Ya dinga yi mata acikin zuciyarsa akan Allah ya bata lafiya..=???

Wunin ranar suna asibiti Har lokacin likitoci suna aiki akanta, Kafin marece docs din suka kammala bincike sakamakon ya nuna tana fama da severe depression and Heartbreak Syndrome, She's in a critical situation, dealing with two major issues simultaneously, docs din ma sunce in har ba'ay kokarin shawo kanta ba, Zuciyarta zata bugawa ne, amma zasuyi iyakar bakin kokarinsu don ganin ta samu lafiya.

Hankalin su Ya tashi matu?a sun shiga matsananciyar damuwar abunda ke damun Unaisah, duk wannan abun dake faruwa Danejo da sauran Yan uwansu dake agida basu sani ba.

(Get well Soon Unaisah Angel)


*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?=?%?=?%?
'?*


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: =?%?=???=???=???=???=???>???
~_______________________________~


Jikinta yai tsauri har tsawon kwana Uku batasan inda kanta ya ke ba, abu daya da take iya furtawa sunan My man da yaki barin bakin ta, sai da takaiga kullum sai docs sun banka mata Sedative injections saboda bugun barazanar da zuciyarta keyi mata ta hakanne kadai suke Iya sarrafa ta har su samu tayi bacci, duk da karfin allurorin da sukeyi mata hakan bai hana ta yin sambatu akan shi ba, saboda shi ne aranta, su kansu docs din dake duba lafiyarta sun tausaya mata matu?a sun kumayi mamakin kaunar da takeyi ma shi, a cikon kwana na hudu ne ta dawo hayyacin ta sai dai bata iya magana kamar kurma sai dai tabi mutane da ido, saboda bakar azabar ciwo data sha har rama tayi, kwana uku kamar wadda tayi shekara Tana jinya saboda fadawar da tayi, har addu'ay tay Allah ya dauki ranta ta huta ko ta huta da radadin da zuciyarta keyi mata, bata ta6a dasanin bata masa rai da ta dinga yi ba sai yanzu da babu shi duk in ta tuna rayuwarsu a kurkukun da jan shi fada data dinga yi yana kyaleta tayi azaton baida karfi tsoronta yake ji ashe yana da karfin da zai iya ramawa amma saboda kaunar da yake yi mata ya dinga kyaleta saboda baya son ya cutar da ita, Ya Ilahi tay babban rashin da har abada ba zata ta6a samun madadinsa ba=?-?


Ba irin nasihar da ummi batay mata ba akan tay hakuri ta rungumi kaddara, shima taj yana kokarin yi mata nasiha amma abun yaci tura zuciyarta ta?i bata hadin kai, azabtar da ita kawai takeyi, duk da haka basu fasa lallashinta da kwantar mata da hankali ba ta ko'ina take samun kulawa musamman docs da nurses din dake kula da ita.

A ranar da suka Cike kwana hudu Chief ya ce a sallame ta, Duk da docs sun ce lokacin sallamarta baiyi ba, ya nuna yafi son A sallame tan su koma gida inyaso sai acigaba da yin jinyarta acan, badan sunso ba suka bada sallamar Unaisah.

Abun dayasa Chief ya nemi su sallame ta saboda Hankalinsa bai kwanta da zamansu a asibitin ba, yana yawan Jin faduwar gaba aduk lokacin daya zo dubata, duk da ba ita kadai ke kwana asibitin ba shi ya nemi alfarmar Abar ummi da Batool su zauna gurinta yayin da Taj da Chief suke zuwa dubasu sau uku arana amma saboda Halin dayake shiga Na jin faduwar gaba yasa shi cewa A sallame ta, kuma hada ?arin Obie International Hospital Yana a under Suspect saboda mafi rinjayen matan family dinsu dake haihuwar yara ba araye ba anan asibitin ake kawo su idan suna Labour taya hankalinsa zai kwanta da zaman Unaisah asibitin.


~_______________________________~
'?


*

Slowly take kokarin buWe idanunta waWanda su ka yi mata wani irin nauyi ga kasala data baibaye gabban jikin ta, biji biji take ganin kamar mutane kewaye da inda take akwance sai dai bata iya tantance su wanene ba, kokarin Wago da hannu tayi don ta murza idanunta ko ta samu ganinsu dakyau sai dai kafin tay hakan taji anyi saurin dam?ar wuyan hannun nata, hakan yasa ta zare gray eyes dinta tare da wurga eye balls din ta kan wanda Ya ruke hannun nata, da farko sai ta dinga ganin kamar Danish ne la66anta na kerma ta furta"My Man kai ne"? Girgiza mata kai yai"ba shi bane Unaisah, madadin shi ne"

ras ta Wan ji gabanta ya faWi ganin Chief Owais a zaune kan kujerar dake a gefen gadon su, muryarta kasa kasa ta furta"Chief" lumshe mata idaninshi yayi cikin sauri ta dubi hannun ta daya ruke, Iv drip ne aka sanya mata, goshin ta anade yake da bandage sakamakon raunin da taji ma kanta har treatment sai da akai mata.


"Daughter"! Muryar daddynta taji a cikin kunnanta, da sauri ta wurga eye balls dinta kan fuskarshi, ta kura mashi lumsassun idanunta Yana daga zaune kan wheel chai?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? r dinsa a gefen gadon, Fuskarsa da damuwa yayi maganar...

"Sister naji dadi kin fara samun lafiya Ya jikin naki", shiru tay bata amsa mata ba, A hankali ta mayar da duban ta inda suke a zaune ita da Ummi sun kura mata ido suna bin ta da kallo mai cike da tausayawa tsawon kwana hudu rabon da suyi wanka saboda rashin lafiyarta, La66anta na rawa ta furta"Har yanzu Danish bai dawo ba"?

Sunyi mamakin jin tayi magana kuma sunyi farin ciki da hakan, Shiru sukayi aka rasa me bata amsa, lumshe idanunta tayi tana jin wani irin Waci da zafi a cikin zuciyar ta...

"Unaisah" chief ne ya ambaci sunan ta cikin sanyin murya sai ta dinga jin kamar muryar Danish din ta, kasa buWe idanunta tay, hawayen da suka taru cikin idanunta suka fara zarya kan kuncin ta.

"Ina so ki nutsu ki saurare ni" jinjina ma shi kai tay,

Still Chief bai saki hannunta ba ya furta"meyasa kikeso kiyi ma kanki Illah? Shiru tay bata furta kalma ba..


Cikin sanyin murya ya soma yi mata nasiha mai ratsa zuciya, yace a matsayinta na musulma wadda tayi imani da kaddara mai kyau da mara kyau, wata irin jarabawace bata shiga ba kuma Allah yakubutar da ita, sbd haka tayi hakuri ta rungumi wannan jarabawar, har yanzu bamu shaida mutuwarsa ba, don haka kada ki yanke kauna da rahamar Ubangiji, ni'imomi nawa Allah yayi maki Unaisah, bayan kadddara ta rabaki da mahaifinki kin taba tunanin zaku rayu harku Sake hadu? Bama wannan ba, Kin taba tsammanin zaki fada gidan kurkukun kaddara harki hadu da shi Danish din da sauran yan uwanku? Allah fa shiya hadaki da shi bakisan da zaman shi ba, don a yanzu ya raba ki dashi sai ki nemi butulcewa? meyasa bazakiyi hakuri ki rungumi kaddara ba? Unaisah ki cire damuwa aranki, Kiyi hakuri dukkan tsanani yana tare da sauki, komai mukaga ya same mu da sanin ubangiji shi yasan dalilin dayasa abun ya faru da mu.

Nasihar Chief ta karya zuciyarta, Jikin ta yayi sanyi sosai, Taj yaji dadin yadda Chief ke kokarin shawo kan Unaisah, Hankalinsa Harya kwanta, Ummi da Batool sun nutsu suna sauraron Nasihar chief sun kasa kunne har mamaki sukeyi jin yana magana sosai a yadda sukasan shi da miskilanci.


"rashin lafiyar ki ta haifar mana da rauni a cikin zukatanmu, hankalinmu ba akwance yake ba taya kike tunanin zamu samu kwanciyar hankalin da zamu gudanar da bincikenmu akan Elders? Ko kina so ki mutune batare da kin cimma burinki ba? Girgiza kai tay cikin shesshekar kuka tace"in..ina so na rayu ko dan na daukar masa fansa"

"Good, Docs sun fada mana, Ciwonki kwanciyar hankali da nutsuwa yake bukata, dole ki cire damuwa aranki ki dauki dangana ki fawwalawa Allah komai, In sha Allah zaki ga ribar hakurin da ki kai, yanzu Tsakaninmu da Danish addu'ace kawai"

Cikin shesshekar kuka ta furta"ay ba musulmi bane, ya mutu bai yi imani da Allah ba..."

Kafin chief ya bata amsar maganarta Ummi ta kar6e da cewa"Allah mai rahama ne kuma mai jin kai ne, ba zamu yanke mashi hukunci ba, saboda gaba daya rayuwarsa bayin kan shi bane, hakkinsa ya rataya akan wadanda suka tafiyar da shi, Allah ne kadai yasan menene makomarsa..."

maganar Ummi ta kwantar mata da Hankalinta har taji sanyi aranta..


A hankali ta dan buWe idanunta akan fuskar Chief

"Akwai inda keyi maki ciwo"? Girgiza mashi kai tay"No, I'm feeling better now."


"Okay, the doctor will continue coming here for regular check-ups, your aunt will take care of your treatment plan" ya fada tare da nuna Ummi

"Ga daddynki akusa and your sister Batool, Komai kikeso ki fada masu, zasuyi maki in sha Allah, We are all here for you, a shirye muke da mu taimaka maki gurin ganin mun ya?i abun da ke damun ki har sai kinji saukin jikin ki, In sha Allah zamu share maki hawayenki In har kika bamu hadin kai"

Har cikin ranta taji dadin Kalamai Chief ya faranta mata sosai, ko dan saboda yarda ya nuna damuwa akanta zatay kokarin faranta masu

Ummi ta ce"Ciwonki Yana bukatar kulawa sosai, Dole sai kin cire damuwa aranki in ba haka ba zaki rasa tunaninki ne, Ga mahaifinki nan bashi da koshin lafiya, Ciwonki yana kara jefa shi cikin damuwa, Yakamata kodan saboda shi ki jure Unaisah..." idanunta cike tab da kwalla ta furta"in sha Allah, Chief nagode sosai da kulawarka agareni.." ta fada tana kallon Cikin idanun shi, jinjina mata kai yai batare daya furta kalma ba


Ajiyar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login