Showing 102001 words to 105000 words out of 413917 words

Chapter 35 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2656

maida hankali akan mutumin ba sai bayan da prisoners suka bayyana tukunna Ya fara gasgata maganar mutumin da har yau baisan wanene shi ba..."

Abakin kofar dakin nasa suka dakata da yin tafiya suna kallon junansu damuwa ce ?arara akan fuskokin su kowa da abun da yake sa?awa aran shi sam sun kasa magana daga bisani suka fuce.


Chief Har ya fara nutsawa cikin baccinsa Wayarsa dake ajiye kan drawer ta fara ringing kaitsaye sautin ya daki kunnansa

A hankali yadan bude idanunsa wadanda ke lullu6e da yalwar gashi ya kalli ceilling din dakin kafin mi?a hannu ya Wauki wayar

Motsa la66ansa yai tare da furta sunan Uncle hateem.

Picking call din yai

"Uncle am sorry, jiya na shiga bedroom dinsa na taras yana bacci shiyasa ban kira ka,"

On the other hand prime minister yace"Son ka hanani ganin maganin da zai warkar min da zazzabina....."

"Sorry uncle nayi laifi ay min afwa"

"It is okey, yanzu yana ina ya farka daga bacci"?

"Yanzu zanje bedroom dinsa na duba sa"

"Okey, akwai sako da za'a kawo masa daga company.." tun kafin ya ?are maganar chief ya furta"uncle wani sako kenan"?

"Idan an kawo zaka gani, nasan idan na fada maka ba zaka bari sakon ya iso ba, zaka hana ne"

"Haba uncle, ni na isa in hanaka yin alkhairi..."

"Hakane, amma bazan fada ba" ya faWa da zolaya

murmushi chief yai"andai hanani jin menene bakomai in an kawo zan gani, bari naje na basa ku yi magana"

"Video call zamuyi zanfi jin dadin ganinsa" amsa masa yai da okey, janye wayar yai daga kunnansa Ya nufi desk ya dauko ?aramar laptop dinsa Ya sauko down babu kowa sai masu aiki dake zaryar kai abinci kan dining, ta elevator ya hau ta sauke sa second floor........

Abakin ?ofar ya tsaya yai masa knocking, shiru ba abasa iznin shiga ciki ba, yanke shawarar shiga yai a hankali ya tura kofar a zaton sa bacci yake yi, yana shiga ciki yaji alamun motsinsa a toilet, har ya juya zai fita da niyar anjima zai dawo sai kuma yaji an bude ?ofar, fitowa yayi daga ci ki jikinsa asanye da kayan baccin sa

Ganin mutum adakinsa Yasa shi cin burki ya tsaya yana kallon bayansa cike da mamakin wanene ya shigo masa bedroom dinsa...

A hankali chief Ya juyo suka fuskanci juna, nan take danish ya ?ara daure fuskarsa tamau babu annuri.

Takawa yai zuwa gabansa Ya mi?a masa hannu don su gaisa, ma?e hannunsa yai alamar bazai bayar ba,

"Ba ay min haka" ya fada tare da sanya hannu ya janyo danish yayi huggin dinsa kamar zai maida sa cikin sa, kamar wani mugun abu ya rungumesa sai kankame jikinsa yake yi, bayan chief ya raba jikinsa daga nasa ya soma yi masa magana.

"Barka da safiya, Ina fata ka tashi lafiya" shiru yayi bai tanka masa ba, wani kallon ?asan ido yake jifa masa da ace chief baisan halinsa ba da sai yace ya tsane sa

"Ba magana? Ko da ya ke nima dalili ne Ya kawo ni roon dinka, kar6i nan uncle dina ke son magana dakai" ?in kar6a yayi,

"Ina nufin uncle dina Hateem, mutumin dana hada ka da shi shekaran jiya, ina fata ka tuna sa" zare masa idanu danish yayi, sarai ya fahimci wa yake nufi abun da bai gane ba ta ina za suyi magana da uncle din nasa?

In a low voice ya furta"yana ina"?

Mi?a masa laptop din yai" anan zakuyi magana da shi ta video call"

wani kallon rainin wayau danish yai masa arude ya furta"tayaya zanyi magana da shi ta wannan abun" Wan zaro ido chief yayi, can kuma ya saki fuskarsa tunawa da wanene shi

"Oh okey na fahimta lemme show you yadda zaku yi magana" bayan ya kira hateem video call fuskarsa ta cika laptop screen din, juyama danish ita yayi"look at him ku yi magana"

har saida danish Yaso Ya firgita lokacin da ya sauke idonsa kan laptop screen din ganin fuskar hateem mai Wauke da murmushi, muryarsa cike da nishadi Yace"my baby boy danish, ka tashi lafiya? Ya ka kwana jiya? Ka yi kewana kuwa ko kuwa ka manta dani" yatsun hannun sa na kerma Ya kar6i laptop din daga hannun chief Ya kura ma hateem ido yana kallonsa batare daya furta komai ba, shi mamakinsa tayaya har ya bayyana akan wannan abun?

"Ka zauna ku yi magana" chief ne Ya fada tare da nuna masa gefen gado, jiki na bari yaje ya zauna yaci gaba da kallon hateem dake ta faman sakar masa murmushi

"Ka yi shiru baka tanka min ba, ko dai kamanta dani ne? Fadamin sai in tuna maka" shiru yayi bai masa magana ba, mamakin duniya ya cikasa

Chief dake atsaye ya harWe hannayensa kan kirjinsa sai kallonsa yake yi zuciyarsa cike fal da tausayin rayuwarsa baiyi tunanin tsayawa ya kammala wayar ba sai ya juya ya fita daga dakin.

"Bazan damu ba, kallon da kake yi min ya tabbatarmin da ka gane wanene ni, shekaran jiyama da muka fara haduwa sai da nasha wahala kafin Ka yi min magana" ya faWa yana murmushi.

"Nakasa jurewa ka tsareni da wadannan kyawawan idanun naka please ko da zagina ne kayi ni dai burina naji muryar nan taka mai kwantar min da hankali, chief bai fada maka nayi zazzabin rashin ka ba"? Ya fada yana marairaice masa fuska alamar zaiyi kuka...

Yana faman furzar da numfashi Ya dan motsa la66ansa kamar baison furta maganar yace"ina son ganin ka"

"Ba ga ni kana gani na ba" girgiza kai danish yai alamar a'a

"Ka fito kazo nan dakina"

"No bazai yiwu ba, ay bana kasar yanzu ina canada kai kuma kana nigeria, sai na hau jirgi tukunna zan iya zuwa wurin ka" hankali atashe danish Yace"a'a ni dai kawai kazo ka fito daga wannan abun ina son ganinka" waro idanu hateem yai da alamun ruWani akan fuskarsa.

"Ba yadda za'ae na fito, laptop ce fa, baka ga ?arama bace taya ni da nake babban mutun zan fito ta cikin ta" kamar zai sanya masa kuka yace"ni dai kazo ina son ganinka" ya fada yana shafa laptop screen din a kokarinsa naya gano kofar da zai buWe wa prime minister Ya fito waje.....

Chief owais Na awaje Yajiyo sautin fashewar wani abu daga dakin danish....



*Daga Al?alamin Boss Bature=???
'
'?*


*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: _*~
'=???BOSSLADIESWRITERS=???*~_



3,F 'DB/=???=?%?=???


~Takun ?arshe=?%?~



Dedicated to Aunty Kubra=???=???



B5) -( 1HE'F3J) :J1 9'/J) (JF 'D3,F'! E9 *7H1'* E9B/)=???=???=??


An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists d'=???=???




Daga al?alamin Boss Bature=???
'






Chief na waje ya ji yo sautin fashewar wani abu daga dakin danish, a hanzarce ya tura kofar ya shiga kwatsam ya taras da abun da banyi tsammani ba

Gaba Waya ya fasa laptop din, ya raba ta gida huWu, hakan bai masa ba sai da Ya zu?unna a gaban pieces Win Ya sa hannu Yana tatta6a su kamar wani zararre komai ya kwance masa

Chief Ya jinjina ma lamarin, abun ya Waure masa kai tamau, ta inda ya gode ma Allah laptop ba wadda ya ke aiki da ita ba ce, da kuwa yaja masa babbar asara.

"Meyasa ka fasa ta? why pls ? Ko kallo bai ishe shi ba, damuwarsa akan Hateem ne da bai gani ba bayan yasha wahalar balla abun

Girgiza kai chief yayi"da ita ne zaka iya amfani wurin yin magana da shi saboda baya a Nigeria" Wagowa danish yayi fuskarsa a yamutse gaba Waya ya rasa sukuninsa, shi fa ya fasa ne da niyar ya buWe ma prime minister hanyar da zai iso gare sa.

"It is okey, koma ka zauna kan gadon ka, a hankali Ya koma kan gadon yana faman bin laptop din da kallo

?arasawa chief yai tare da kwashe pieces din ya fuce daga dakin Ya koma bedroom dinsa Yana shiga wayarsa ta fara ringing

Da sauri Ya Waura laptop pieces din kan couch kafin Ya Wauki wayar yai picking

"Owais meya faru ne? Muna cikin yin magama da shi naji Wuff ya katse kiran"

"Uncle mai kuke tattaunawa ne da shi"?

"Cewa yai yana son ganina in fito daga laptop din, nace masa bayadda za'ay amma ya matsamin shi ne fa naji shiru kiran ya katse"

"Uncle Ya 6alla laptop Win, gaba Waya ta tashi aiki, Allah Yaso ma ba wadda nake amfani da ita bane ay dayaja min asara"

Muryar Hateem da mamaki Ya furta"what? Ya fasata? Amma meyasa yayi haka"?

"Saboda ka ?i fitowa, may be yana nema maka hanyar da zaka fito daga cikin ta ne"

Kusan atare suka fashe da dariya daga hateem din har chief din saboda abun Ya basu mamaki da al'ajabi......

Dakatawa sukai da yin dariyar, kowan nan su yayi shiru na Wan wani lokaci, kwatsam sautin shesshe?ar kukan prime minister hateem Ya karaWe kunnansa lokaci Waya zuciyarsa ta buga saboda jin abun da bai zata ba, aruWe ya furta"uncle? Kuka kake yi? Ko dai kunne na ne suka ji min badai dai ba"?

Muryarsa araunace Ya furta"Ina tausayin rayuwarsa owais, ya karya min zuciyata yau, mutum har mutun baisan komai ba, da ace ya taso cikin kulawar iyayensa koda ba dan masu hali bane zai samu ilmin addini dana zamani dai dai gwargwado....." yana magana sautin na fita da alamun kuka maitsuma zuciya.

Lumshe ido chief yai kafin Ya furta"pls ka kwantar da hankalin ka uncle, zanyi iyakar bakin kokarina don ganin ya samu ilmi akansa, kamar yadda nayi maka al?awarin bashi kyakkyawar kulawa..."

"Owais idan zai yiwu ku sanya shi makaranta, Ni zan Wauki nauyin karatunsa because I want him to be like everyone else. ni wallahi da zaka bani dama zansa akawo min shi nan canada"

Cikin kwantar da murya owais yace"Uncle zuwansa canada bazai yiwu ba, akwai abun da ban fada maka dangane da rayuwar su ba, amma dan Allah kayi min Uziri uncle nan badajimawa ba zan sanar da kai komai....."

Yana jiyo sautin ajiyar zuciyarsa"Toh zan jira har zuwa lokacin, Allah yasa inji alkhairi, yanzu sai yaushe zan sake yin magana da shi saboda bangaji da ganin sa ba"

"Ka bani lokaci uncle, zanyi kokarin fahimtar da shi yadda zaiyi amfani da laptop din"

"Okey, nagode my son, sannan ina mai baka hakuri amadadinsa"

"Kada ka damu uncle, ay ba yin kansa bane rashin sani ne"

kwantar masa da hankali Yaci gaba da yi har ya samu ya shawo kanshi kafin daga bisani su ka yi sallama zama yai gefen gadonsa zuciyarsa cike fal da tunanin abun da ya faru.


_________________________
'?


"Deeja! Deeja" kamar daga sama taji ana ?wala mata kira, firgigit ta ware idanunta masu Wauke da bacci ta sauke su kan ceilling da alama batasan daga ina ake kiran ta ba sai faman ?yafta ?yafta idanu ta ke Yi, fuskarta ta ca6e da jan bakin ta

"gani anan tsaye ina kallon ki" wurga ido tai kan Unaisah da ke yi mata magana, tana a tsaye ta ru?e qugu da hannu Waya, wata hadaddiyar riga doguwa ta sanya a jikin ta black colour tabi shape dinta ba karamin kyau tayi mata ba, hada light make up akan face dinta, tayi rolling veil ga wani daddaWan fragrance dake tashi

Zumbur khadeeja ta mi?e zaune fuskar a jagule take kallon ta

"Sorry na katse maki baccin ki, safiya tayi tun Wazu, ga shi ko sallar asuba bakiyi ba, yakamata kije kiyi sannan ki yi wanka ko kin ji dadin jikin ki"

Yamutsa fuska Khadeeja tay"to ke din wacece ne? Kin cika ni da surutu Ina yaya salsabeel da su rubina"?

Murmushi unaisah tayi"Yar uwarki ce unaisah baki gane ni ba"? Harara ta jefa mata"ni bansan ki ba Allah, ki fadamin ina yan uwana suke"?

Zuba mata ido unaisah tayi da alama zatai kafiya, don ma tasan halin kayan ta.

"Yan uwanki suna nan a cikin gidan nan, amma waye ya kawoki Wakin mu jiya"?

Sosa ?eya tayi kafin tace"harisuna, shine Ya rakoni in kwanta"

"Okey yanzu ki tashi ki shiga ga toilet can" ta fada tare da Wan juyawa ta nuna mata kofar da hannu, saukowa tayi daga kan gadon tana mi?a tare da hamma ta nufi toilet ta shige, unaisah nata bin ta da kallo har ta shige.

"kin canzamin kamar ba deejana ba, naso ace kina acikin hayyacinki komai Ya faru nasan zakiyi farin cikin saurayin rayuwar da muka samu, Allah Ya baki lafiya my sister"

Bakomai take tunawa ba, face ranar da giant ya tafi da khadeeja da kuma lokacin da aka dawo masu da ita taje gaban gadon ta tana shesshe?ar kuka ta tada ta daga bacci taja ta suka shiga toilet har take fada mata abun da akayi mata bayan an Wauke ta

Tuni taji jikinta yayi sanyi lakwas rayuwa kenan, babu wanda yayi tsammanin zasu kai wannan lokacin araye sai gashi Allah ya raya abun shi, dama ance wuya bata kisa sai in kwana sun kare.

FaWowa Dakin Haris Yayi, fuskarsa dauke da tsantsar farin ciki sai faman sakin murmushi Yake yi, ba don komai ba sai don zumudin ganin deejansa jiya da ita Ya kwana Aransa yanzu haka yazo ne don Ya ?ara ganinta ya kuma tabbatarwa kansa ba mafarki bane abun da Ya faru Jiya.

Unaisah Na ganinsa Tace"ba sallama? Me ma Ya kawoka dakinmu da sassafe"?

Shafa sumar kansa yai"ina deejana"? AWan ruWe tay pretending"deeja kuma? Kayi mafarki da ita ne"!

Hankali atashe Yace"bangane me kike nufi ba, wani irin mafarki bayan jiya sun zo gidan nan har mu ka yi shagali, da kaina ma na rakota dakin ku da tace min tana jin bacci.

Fuska adaure tace"haris? Ko dai ka fara samun ta6in hankali ne? Meya kawo maganar deeja? Bayan ta riga da ta rasu tun a prison"? Yanayin yadda tayi magamar ba karamin kayar masa da gaba tayi ba jikin shi yai sanyi gwiwarsa ta sage

"Kina nufin mafarki nayi jiya" Waga masa gira tay"zai iya yiwuwa" shiru yayi zuciyarsa ajagule yake kallon unaisah gaba daya so take ta rikita lissafin ?walwarsa ..

"Lafiya ka tsaya kana kallona? Meke damunka ne"? ?walla ce ta ciko idanunsa muryarsa na rawa ya furta"deeja na ta mutu? mafarki nayi jiya sunzo? har ta buWe baki zata bashi amsa Kwatsam Deeja Ta banko kofar toilet din kamar an wurgo ta da karfi ta furta"Laahh! Haris kaine? Yana jin muryarta a ruWe Yakai dubansa gareta lokaci Waya ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya, da gudu Deeja Ta nufe sa ta ?an?ame shi tana fadin"wallahi jiya har mafarkinka nayi harisuna"

"Deejana Kin tashi lafiya"?

Tana faman Washe Baki tace"lafiyalou wlh, nima muryarka najiyo ina ga daga Cikin toilet, Har na fara alwala na katse ta"

Unaisah dake kallonsu tana dariya gaba daya mamakin ?aunarsu ya gama cikata, wani abu daya Waure mata kai yadda deeja Ta yarda dashi bayan jiya sukai ta fama da ita akan ta tuna shi amma ta?iya sai gashi da yake kaunar tasu a jini take har sun sha?u jiya izuwa yau

"Sister kada ki sake yi min irin wannan wasan, zuciyata zata Iya bugawa Allah" Yai maganar idonsa akan Unasah

"Naji romeo, bazan ?araba, Yanzu sai kabarta ta koma ta karasa alwalar ko fa salla batai ba" Harara deeja ta watsa mata"waike ina ruwanki dani in ma banyi sallar ba, ay ni ba kullum nakeyi ba sai na ga dama, Ko su hawwa basu min dole balle ma ke da bansan wacece ba' muryarta da shagwa6a take magana hakan bakaramin dariya ya basu ba

Lalla6ata haris yayi"rabu da ita, kishi takeyi da take don taga kinfi ta kyau, " washe baki tayi jin Yana yabonta

"Yanzu ki koma ki karasa alwalar in kin gama ki yi wanka sai ki fito muje muyi breakfast" amsa mashi tayi da toh da gudu ta juya tana fadin Kada ka tafi harisuna ka jira ni in fito Yana murmushi ya amsa mata da toh har ta shige bai daina kallon ta ba

Da zolaya unaisah tace"Hankali Ya kwanta Haris, deeja Ta dawo, No more heartbreak " dariyar farin Ciki Ya saki" ba zaki gane ba, wlh daren jiya bayan na rakota dakin ku ta kwanta dana koma dakinmu har nafila nayi saboda in nuna godiya ga Allah daya sake hadani da ita, Ina son deeja Allah Yabar mun ita har abada, in ma mutuwa zata dauke ni ta dauke mu atare" idanu abude Unaisah ke kallon shi aranta tunani take tsakanin deeja da haris da kuma ita da danish suwaye sukafi son juna tsakani da Allah? anya idan danish Ya rasata zaiyi ciwon zuciya kamar yadda haris yayi akan deeja? Ko kuwa ita idan tarasa shi zatai hauka? tabbas A yanzu bata iya ganewa tun da wani bai ta6a rasa wani a cikin su ba, kuma bata fatan abun da zai raba ta da muradin ranta, her eternal lover

"Haris Ina tayaka murna, Allah Ya nuna mana ranar auranku mu sha biki" da mamaki ya maimaita kalmar aure" yar dariya tay"cikar burin masoya kenan idan time yayi basai na maka bayani ba" murmushi kawai yayi duk da baisan me akeyi a auranba but maganarta tasa shi fara jin son ganin auran nasu.

?arfe tara daidai agogo ta buga, Waya bayan Waya suke fitowa daga dakunansu zuwa dining Room kowan nan su yayi wanka Ya shirya sunyi kyau daga ganin fuskokinsu zaka shaida Anyi kwanan farin ciki daren Jiya....

Da wani irin Waukin junansu suka fara ?an rungume rungumen juna, gwanin ban sha'awa, ?aunar su a jini ta ke, harta chefs din dake a dakin cin abincin kallon su sukeyi saboda sun siye zuciyoyin su.

Mutun ukune ke babu acikin su, ummi da batool sai Danish, su kadai ne ba su kaiga ?arasowa ba.

Sun cika dining room din da surutu Ko zama sun kasa yai,

Gyaran murya chef Yai masu Hankalinsu Ya dawo kan shi

"Barkanku mu da safiya yan mata da samari, ina fata kun tashi Lafiya" a tare suka amsa mashi da lafiyalou

"Yawwa, Yanzu ba lokacin surutu bane, lokacin bama ciki hakkinsa ne, nasan kunyi kewar Juna amma Ku Wanyi hakuri ku zauna mana"

murmushi Kowan nan su Ya saki,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login