Showing 306001 words to 309000 words out of 413917 words

Chapter 103 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4504

anan zan zauna, kuma ko wanka ma banyi ba"

?aure mata fuska yayi"Uban me Ya hana Kiyi wankan tun dazu? Ai kina sane kika boye karkashin gado, kega mai wayau ko"? Marairaice mashi fuska tayi"Dan Allah daddy, Ka ?yaleni bana son zuwa, nafison na zauna nan, Ni bazan bi su ba..."

Ganin Yana tunkarota gadan gadan Yasa Ta fara kokarin gudu, yana kokarin Cafkota, ta kufce mashi ta watsa da gudu Ta fuce daga dakin, Aguje yabi bayanta sai dai koda ya fito baiga gifcin ta ba, kamar walkiya ta 6ace ma ganinsa, Ranshi Ya 6aci ba kaWan ba.

________________________________
'?=ؔ?


Fitowa yayi daga Cikin toilet, waist Winsa Waure da white towel, motsin mutun yadinga ji acikin kunnanshi, hakan yasa shi dakatawa da tafiya, slowly yake bin bedroom Win nasa da kallo Unexpectedly eye balls dinsa suka sauka akan Curtain dakin dake motsi, alamar akwai mutun a ciki..

Yatsun kafafunta Ya hango ta ?asan labulen daya Wage sai kerma suke ...farat Waya Ya gane itace..yayi mamakin ganinta adakinsa bayan kwanakin da suka shafe batare da sun nemi junan su ba, kome ya kawota bedroom dinsa? Aransa ya ayyana hakan.

Yi yayi tamkar baisan da zamanta adakin ba, shaf shaf Ya shirya kan shi, Cikin Singlet fara da short.. kafin Ya koma gefen gadonsa Ya zauna tare da maida hankalinsa kan breakfast din da Taj yasa aka kawo mashi..

A tsanake Yake Cin abincin ta wutsiyar idanunshi Yake satar kallonta yayin da take buWe labulen Tana le?ensa ji take kamar taje garesa tayi hugging dinsa sai dai ina wani irin shakkar tunkararshi takeji, saboda maganganun data gaggaya masa marasa dadi ita kanta bata tsammaci zai dyauki tsawon kwanaki bai kula ta ba ko kiranta awaya bayayi..

Gajiya tayi da tsayuwar, ta fito daga bayan curtain din tayi tsaye tana kallon shi.

Tayi zaton baiganta ba, cikin sanyin murya tace"My man, fushi kake dani?

Banza yayi da ita hakan ba karamin karya mata zuciya yayi ba.


"Baka ga halin damuwar dana shigaba, saboda kai ko bacci bana iyayi,nasan komai ya faru laifina ne, nina ja ma kaina amma ka yi hakuri ka yafe mim, I don't know if we'll meet again, maybe this will be our last meet, duk da bansan date da zaku tafi ba, amma inaji araina yau ne, shiyasa daddyna yace mu tafi part dinsa mu zauna, ni kuma na boye saboda inason muyi bankwana kafin mu rabu..."

ta faWa idanunta cike tab da kwalla, So hana ganin laifi, duk yadda yaso Yaki jin tausayinta hakan ya gagare shi, kalamanta sun ta6a zuciyar shi.

slowly ya dubeta daga kasa Ya fara kallonta, Hankalinshi ya tashi da ganin irin ramar da tayi, daga gani bata samun isasshen bacci ko bata cin abinci yadda ya kamata ga shi babu gyara a jikinta, kamar zai zubda mata kwalla saboda matsanancin tausayinta dayaji yasan duk akan shine ta shiga halin Damuwa...

Da spoon din hannun shi ya nuna mata gefen shi, cike da rashin kwarin jiki ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya batare da ta kauda ido daga kallon shi ba..

Cup din tea Ya dauko Ya kanga mata abakinta, ganin taki buWe baki yasa shi furta"kisha" la66anta har kerma suke da sauri take kur6ar shi, nutsuwa yayi yana kallon throat dinta dake moving slowly.

sai da ta shanye shi kaf kafin ya dauki fork duk tana kallon shi Ya nannaWo noodles ya tura mata abaki, kamar yasan yunwa take ji, sakin jiki tayi ya dinga bata tana ci saida ya tabbatar taci ta koshi kafin ya aje spoon Win.

Ya ruko yatsun hannayenta a cikin nashi, bata ta6a jin kunyar hada ido da shi irin na yau ba, saboda rashin mutuncin data zazzaga mashi, sunnar da kanta kasa tayi

Cikin nutsastsiyar muryarsa ya ce"Ni ban ru?e ki a zuciyata ba, baki min komai ba, amma yanzu kin min abunda banji dadin shi ba..." a rude ta kalle shi

"Meyasa zaki takura kanki akaina"?

Cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri, nasan nina tursasa maka akan kaje aman wallahi ni kadai nasan radadin da zuciyata keyi min saboda zullumi da fargaban mezai biyo baya idan ka tafi, wallahi bana so na rasaka, kuma wallahi bada son raina na gaggaya maka magana ba, nayi ne kawai don in fahimtar dakai amma kaima kasan irin son da nake maka zan iya rayu wa dakai ahaka yadda kake, koda kuwa zaka makance ne ka kuturce, ka gurguce wlh zan rayu dakai bazan ta6a canza maka ba"

bata kare maganarba, ya rufe la66anta da yatsan shi, hakan yasa ta haWiye sauran maganar da bata amayar ba..

Nutsuwa yayi yana kallon siraran hawayen dake sintiri kan kuncin ta..


"Basai kin yi min bayani ba, na fahimce ki, ina jin abun da kike ji..." lumshe idanunta tayi tana jin wani iri aranta...


"Listen to me carefully, now I need your peace of mind because that way, I'll have the confidence to do everything, maganganun da kika gaya min tabbas banji dadinsu ba, amma ta wani bangaren sun taimakamin gurin Farfado da tunanina..." Ya Wan dakata Yana duban fuskarta, sill bata bude idanunta ba.

"Abu Waya da nakeso Kiyi min al?awari shine, Ko bayan tafiyana kada kiyi kukan rashina, kada kiki cin abinci, ko ki hana idonki bacci saboda ni, and even if I don't come back, be patient, Endure a life without me"

(sannan koda ban dawo ba, kiyi hakurin Jure rayuwa batare dani ba)

bai ?are maganar ba, ta katse shi cikin shesshekar kuka tace"Bazan iya daukar maka alkawarin nan ba, saboda bazan iya jurewa ba, bazan ma iya rayuwa batare dakai ba.."

fuskarta ya tallabo da tafukan hannayensa"meyasa zaki karaya Unaisah? Kin manta abunda kike ce? ...girgiza kai tayi"ka manta da abunda ya wuce, ba acikin hayyacina na fada ba.." murmushi takaici yayi

"Ki sama ranki zan dawo da raina da kuma Lafiya na, Nayi maki alkawarin hakan, zan kare kaina bazan bari na mutu ba.." bai kare maganarba tay saurin furta"baka ce In sha Allah ba"? Shiru yayi bai amsa mata ba.

Gyada kai tayi"tunda ba zakace ba, ni zanyi maka addu'a, Allah ya kare mun kai, Allah ya dawomin dakai da ranka da lafiyarka, in sha Allah, ko bayan kun tafi zan raba dare na biyu, rabi inyi baccin awanni kadan rabin In tashi tsakar dare inyi maku addu'a...." har cikin ranshi yaji dadin maganarta, kuma, Har time din bata buWe idanunta ba.

Batai aune ba, Taji safkar Yatsunsa agaban rigarta, a firgice ta bude idanunta, wata irin kunyace ta kamata ganin Yana maida mata front buttons Win rigarta, sakamakon gudun da tayi Wazu gaban rigar ya buWe batare da ta ankara ba, tun da yafara bata abinci yake ta kokarin gyara mata rigar saidai ya kasa saboda gudun masifarta.

Sunkunyar da kanta kasa tay, tasan yaga abun da take 6oye masa..

"Ranar dana dawo, what will you do when you see me?"

Ya fada tare da zame yatsunsa daga gaban rigarta ya maida tafukansa kan shoulders din ta kamar kanwarsa.

"I can't imagine how happy I'll be, I'll cry for joy and hug you tightly"

ha6arta Ya Wago da hannun shi"shi kadaine abunda zaki min"? Jinjina mashi kai tay,

"That won't be enough for me.."

"FaWa min me kake so"?

Kunnanta ya ruko tare da yi mata raWa bai ?are maganar ba, tay sauri toshe bakin shi da tafin hannunta, kamar wadda taji wani mugun abu, jikinta har rawa yake, His shyness enveloped her, and his sexy words made her burn with desire he also set his soul on fire, lumshe idanun shi yayi tare da ware su cikin nata, harara ta Wan watsa mashi tare da murguWa mashi small lips din ta.., kashe mata ido Waya yai tare da Wage mata gira batasan sa'adda ta saki murmushin gefen fuska ba, wato son da takema Danish irin unconditional love ne, idan tana tare da shi takan manta da komai, kamar dai yanzu da suke atare ta manta ma da hudubar da daddyn ta yayi mata kan hada jiki da sukeyi indai tana tare dashi mantawa take da komai shi kadai take gani kuma takeso ta kasance dashi.

Yana kokarin janye hannunta daga bakinshi, ba zato ba tsammani suka ji anyi knocking Win kofar, kallon juna sukayi wani irin faduwar gaba taji, sam ta sha'fa'a ta manta da daddynta da ke neman ta.

Muryarta nawa tace"nasan baiwuci daddyna bane, ni bana so naje part dinsa nafiso Inga tafiyarku tukunna, pls kada ka fada masa ina aciki, Ni zan boye..." wani irin kallo yake binta da shi, jikinta na kerma ta mike da sauri ta boye bayan curtain

Daga waje sukajiyo muryar Taj Yana fadin"Danish, Ka bude min ?ofa" mikewa yayi yaje gaban room door din Ya bude mashi.

shigowa yayi fuskarshi babu walwala Yace"Unaisah tazo nan"? Danish dabai Iya karya ba, Ya nuna mashi Curtain din da hannun shi"tana ciki" cike da takaici Taj Ya nufi labulen Ya Wage shi, wata irin gigitacciyar ?ara ta fasa kamar zata zauce, ta dinga ihu tana fadin daddy bazanje ba, Ka kyale ni, kabarni inga tafiyar ku"!


ga tausayinta yanaji amma ji yake kamar ya rufeta da bugu.

bai bata lokaci ba, Ya sungumeta kan kafadar shi, Ya juya ya nufi kofar dakin kuka ta dinga Yi tana mika ma Danish Hannu don Ya kawo mata dauki bawan Allah Yana ji Yana gani Taj Ya fuce da ita, baisan ko wannan zai kasance rabuwarsu Ta karshe ba, yana jiyo sautin muryarta daga waje cikin shesshekar take sambatu

_"I love you, Danish! I really love you, i wanna be with you for the rest of my life, I can't live without you, My heart beats for you alone, My soulmate, I'm yours, I don't want you to go and leave me! Please come back to me! don't die! I'll wait for you..."_

Zubewa yayi kan gwiwowinshi a karshe Ya yada kafadunsa kan floor.....

Yadda take a haukace, Ahaka Taj Ya nufi part dinsa da ita, sautin koke koken da takeyi ne yaja hankulan jami'an dake kai komo A compund din gidan zuwa ga kallon ta, gaba daya hankalinsu?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ya dawo kan su, Kamar mazurai haka suka zuba ido suna kallon Unaisah dake ta kokarin kwace kanta daga jikin daddynta, sun kwadaitu da ganin santala santalan cinyoyin ta, Yar rigar baccin jikinta duk ta nannade dama bata wuci gwiwarta ba...Bacin rai Ya hana Taj Ya lura da abunda ke faruwa..


*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?
'?*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: _____________________________
'?=?%? &?


Ya faWa yana ?o?arin taimaka mata don ta tuna.

Shiru tayi fuskar ta da alamun ruWu sam takasa tunawa, Girgiza kai ta Wanyi"bazan iya tunawa ba, dama hoto Waya ne akai..." bata ?are maganar ba ya katse ta da cewa"zan baki lokaci, ki nutsu kiyi tunani a ina hotunan suke, cos inaji araina akwai hotunan nan biyu da babu jikin diary din, pls ki kokarta ba karamin taimako zaiyi mana ba gurin gudanar da binciken mu"

jinjina mashi kai tayi"in sha Allah zanyi kokarin in tuna" rufe Diary dinsa yai tare da maida shi cikin drawer.

Kiran Sallar asubahin farkone Ya karaWe kunnuwansu, mikewa tayi da sauri tace"zan iya tafiya" Waga mata gira yai alamar eh..

Juyawa tayi da sauri ta nufi kofar fita, bai daina kallonta ba, har saida ta 6ace ma ganin shi.

Cikin tafiyar sanWa take taka matalar benan gudun kada wani ya ganta ta fito daga Wakin Chief a irin wannan lokacin, kamar wata munafuka.

Kwata kwata bata lura da mutun agabanta ba, sai yan waige waige takeyi kamar wuyanta zai balle Unexpectedly tayi tuntu6e da faffaWan kirjin shi.

tsabar tashin hankali kusan suman tsaye tayi tunkafin ma ta kalli fuskarshi ta riga da ta gane wanene!

Ja da baya ta Wanyi tare da sa tafin hannu ta dafe handrail ta Wago tare da kallon shi from head to toe tayi mamakin ganin sleeping dress dinsa kalar na jikinta launi Waya, idanun shi manne da shade fari ya Waure sumar kan shi ta baya, ba karamin kyau yayi mata ba sai dai ta ji shakkar yanayin shi, ya haWe rai kamar bai ta6a murmushi ba, Allah kadai yasan tun yaushe yake tsaye.

Ido cikin ido suke kallon juna batare da kyaftawa ba

tayi mamakin ganin fuskarshi a yamutse idanunshi sun dan kumbura da alamun rashin bacci atattare da su, ko me ya fito da shi a wannan lokacin? Ko dai damuwar maganarsu Salsabeel ce ta hana shi runtsawa ne"? Aranta ta ayyana hakan.


Shiru babu wanda yayi magana sai sautin numfashinsu dake fita har na tsawon mintuna biyar kafin ta katse shirun nashi da faWin"My man, me kake haryan zu ba ka yi bacci ba"?

Shiru bai tanka mata ba


"How long have you been here"?

"Tun lokacin da kika shiga bedroom Winsa" waro idanu waje tayi sam ta kasa magana sai yan kame kame ta ke yi.

"Me kike yi adakinsa? Har na tsawon awanni hudu"? He asked throwing her a suspicious look She could see the jealousy on his face

Muryarta da inda inda tace"am..um..dama Wazu ne da dare naje kai mashi backpack Win Unaizah daya bukaci yana son ganin ta saboda binciken da suke yi, shi ne da na shiga dakin na iske ya shiga toilet wanka, bansan bacci ya dauke ni ba, sai yanzu na farka..."

kasa karasa maganar tayi ganin yadda ya matso kusa da ita kamar zai rufe ta da bugu tuni tasha jinin jikin ta, bakomai yake kallo ba face kayan baccin jikinta sunyi uban squeezing kamar an kwatosu daga bakin kura, zuciya da sa?e sa?e saita dinga hasaso mashi abinda ya shiga tsakaninta da chief har wani jirin 6acin rai yake gani a cikin idaninsa.

Da wata irin kasalalliyar murya tamkar tame jin bacci ya furta"na yarda dake nasan ba zaki iya cin amana ta ba, amma meyasa zaki je dakinsa ki Wauki lokaci har haka? Ki rasa inda zaki bacci sai dakinsa"?

Dafe kai tayi da hannu Waya harta fara tunanin lallashin shi ta bashi hakuri amma da ta tuna maganar daddynta sai ta samu kwarim gwiwar cewa"Sai me Danish in nayi bacci dakinsa? Fiye da haka ma zan iyayi!" gabansa ne ya fadi cike da mamaki yake kallon ta

"Ka bani kunya my man, ka rasa wa zaka butulce mawa sai Chief? Da ya Salsabeel? i heard everything daya faru tsakaninka da Chief" ta fada tana galla masa harara

"Wai har elders kake ikirarin basu ta6a cutar da rayuwarka ba, kuma sune kake kallo amatsayin iyayenka! Are you crazy? Ko ka fara shaye shaye ne"? Ta fada tana kallon cikin idanunshi, babu alamun zai tanka mata, kamar ana tunzurata ta cigaba da cewa

"Saboda me zaka ?i ba su haWin kai? Meyasa zaka rufawa Elders asiri? Ko dai kun haWa baki da su? In ba haka ba, tayaya zaka rufa asirin miyagun da suka kaskantar da rayuwarka saboda muguwar manufarsu akanka"! Runtse idanun shi yayi gam maganarta ta daki zuciyarshi bai ta6a zaton zaiji kalaman nan daga bakin ta ba.

"Hmmm, dama nasan ba zaka ce komai ba, saboda baka da gaskiya Danish! I have been suspecting you for a long time since we were in prison baka ta6a faWamin komai dangane da kurkukun ?addara ba, ni ban ma ta6a sanin me ake aikatawa a cikin kurkukun ba sai da karanbani na yakaini na gani da ido, meyasa ka boye min a lokacin uhyum"?

Bata jira amsar shi ba ta daura da cewa"Bayan haka ranar da Giants suka zo daukar Batool da hannunka ka mi?ata, ta rayu ko ta mutu, baka damu ba, hakan na nufin kaima da sa hannunka ake akaita komai, watakil ma Wan le?en asirin su ne halan...." kasa karasa maganar tayi sakamakon bugun handrail da yayi da tafin hannun shi, saboda zafin maganarta dayaji, buWe idanunshi yayi sun kada jawur ita kanta sai da taji gabanta Ya faWi amma ta dake ta jajirce don ta harzu?a shi tayi karfin hali cigaba da magana

"Ka sha faWamin kai garkuwane agareni, mai bani kariya, zaka iya komai dan farin cikina, Danish Ina son na tabbatar da son da kake min, shin zaka Iya sadaukar da farin cikin ka saboda nawa" ta fada batare da ta kau da ido daga kallon shi ba..

Jinjina mata kai yai alamar eh, murmushin gefen fuska ta dan saki kafin ta haWe fuskarta tamkar bata ta6a dariya ba.

"Danish, Inaso ka yi masu jagora zuwa gidan Kurkukun ?addara..."

bata kare maganar ba Yai hanzarin furta"bazan Iya ba, pls kada ki tursasamin inyi abunda banyi niya ba..." a rude yake maganar

da kakkausar murya tace"nasan zaka Iya ne shiyasa na umarce ka da kaje, saboda ni nasan wanene Man dina, kada ka bani kunya, bansan ka da tsoro ba.."

"Bazan je ba, bana son duk wani abu da zaiyi silar raba mu, suma ina jiye masu haWarin da zasu jefa rayuwarsu, Ja da Elders ba abune mai sau?i ba, basu da karfin da zasu iya farmakarsu please understand me..."

fuskarsa ayamutse yayi maganar

"Danish Idan har bazaka je ba, to inaso ka sani zan yanke duk wata ala?a dake a tsakanin mu! Saboda bazan ta6a auran ragwon namiji ba, matsoraci wanda bazai iya jefa rayuwarshi cikin hadari don ya ceci rayukan Al'umma ba ya kuma kawar da masu aikata zalunci a doron ?asa.."

waro idanunshi waje yayi tamkar kwayar zata faWo ?asa.

"Chief yafika jarumtaka, yana da zuciyar imani da tausayi, baisan mu ba, bai hada alakar komai damu ba, amma saboda kyakkyawar zuciyarshi burinshi Ya taimaki rayuwarmu data sauran yaran dake agidan kurkukun kaddara sannan ya kawar da miyagu a cikin al'umma bai damu daya rasa ranshi ba! a shirye yake da ya sadaukar da ranshi saboda ya ceci rayuka kaifa? Ta jefa mashi tambayar shiru yayi bai tanka mata ba

"Saboda kai na hakura da burina na ganin na auri attajirin mai kuWi mai asali Wan babban gida, mai ilmin addini dana zamani, naji zan iya rayuwa dakai ahaka saboda kaunar da nake maka, amma meyasa kai ba zaka iya hakura da ra'ayinka akan nawa ba"?...dakyar ta ?are maganar saboda hawayen da suka kubce mata tana mai jin takaicin tilasta masan da take kokarin yi.

"Danish baka da komai, in banda kyan da Allah yayi maka, If I marry you, how will I be proud of you"? Cikin shesshekar kuka ta faWa

"Ace na auri ragon namiji mai tsoron zuwa yaki? Ko

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0