Showing 360001 words to 363000 words out of 413917 words

Chapter 121 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4482

ganin yadda ta fita hayyacin ta, jikinta sai kerma yake, rungumota tayi a jikinta, officers din suna ta kallon su kamar zasu hadiye su...

Bayan yan mintu, Sai ga kiran agent zahra ya shigo wayar officer din daya kira shi, bayan yai picking yace suje bakin kofar ya buWe ta.

Unaisah ta danyi mamaki jin hakan amma da ta tuna kofar tana da security sai taga ai bakomai bane may be yai amfani da computer ne gurin buWe kofar daga can inda yake.

Suna zuwa bakin kofar ta zuge da kanta, ajiyar zuciya kowannnasu ya sauke kafin suka shiga ciki baiwar Allah idanunta na akan Second floor ta dinga kallon door room dinsa dake a datse, har gizau ya dinga yi mata ta hango shi tsaye ya dafe handrail fuskarsa Wauke da murmushi, jikinta yayi sanyi lakwas zuciyarta ta karaya, gaba Waya ta shagala da kallon shi, har saida ummi tace tayi sauri ta dauki wayar suna jiran ta kafin ta nufi Bedroom dinsu Batool tabi bayanta, ummi tana a falo tana jiran su.


Suna shiga Wakin suka bazama neman wayarta, Batool tace sis ki yi kokari ki tuna inda kika ajiye ta, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace wlh na manta inda na saka ta, har zanin gado suka yaye tare da kakka6e shi duk basu ganta ba, Har closet dinsu suka duba basu ga wayar ba, suka duba under bed nan ma basu gani ba, cikin hanzari Batool ta zazzago da mirror drawer chest tana lalubawa unexpectedly hotuna suka faWo kan floor, cikin sauri ta dau?i hotunan ta kura masu ido tana kallon su farat daya ta gano inda ta ta6a ganin Faces din mutanan dake akan pics din, cike da zumudi ta furta kai Ina kika samu hoton mutumin aunty Ummi da kawarta"

Kaitsaye maganar ta daki dodon kunnan Unaisah a lokacin ta gaji da neman wayar har zata zauna gefen gado ta tsinkayi maganar Batool, mikewa Batool tay da sauri ta nufe ta tare da mika mata hotunan tace ina kika same su"? Da ruWu ta kar6i hotunan ta soma duba su tana kokarin tunano inda ta gan su sai da ta zurfafa tunanin dakyar ta iya tuna ranar da ta gansu a karkashin gado a lokacin tana cikin neman wayarta.

Numfasawa tayi kafin ta furta" ran nan ne nagansu a karkashin gadon mu shine saina boye su a cikin drawer"

"To ay mutumin aunty Ummi ne wannan" ta fada tana nuna mata hotonsa" Ita kuma wannan kin tuna ?awarta baturiya wadda sukazo airport atare wata fara sol launin idanunta blue"?

Da mamaki Unaisah ta ?ara duba hotunan dakyau tabbas ta gane fuskar baturiyar kawar aunty Ummin su, farko data fara ganin hotunan sai da tay mata kallon sani sai dai bata iya gano a ina ta ta6a ganin ta ba.

"Amma taya akai kikasan Mutumin aunty ummi ne wannan"? Ta jefa mata tambayar..

"Zan faWa maki, amma dan Allah kada ki fada ma aunty Ummi, saboda ta ta6a buga min warning, akan kar in daukar mata waya in an kira..." Unaisah tace taji ba zata fada ma Aunty ummin ba..

Nan Batool ta labarta mata ranar da ya kira video call tayi picking, abun daya Waure ma Unaisah kai ta yadda har Batool ta iya ru?e fuskarshi a karo na farko data fara ganin shi a video call.

"Kin tabbata shine"?

"Wlh shine, watakil kuma mai kama da shi ne, amma gaskiya kamanninsu ya 6aci sosai.."

lamarin ya Waure mata kai taya akai hoton kawar aunty ummi da saurayinta yazo dakinsu? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, Ta dai san aunty ummi baza ta yi gangancin kawo hoton saurayinta adakin su ba tunda har ta gargadin Batool akan daukar mata waya thats mean bataso asan komai dangane da abun da ya shafi phone dinta.


Kafin wani ya ?ara furta kalma daga cikinsu suka jiyo muryar Ummi daga waje tana fadin Wai har yanzu baku ga wayar ba ne.


Cikin sauri Unaisah tace ma Batool kada ki fada mata komai dangane da hotunan, nima bazan faWa mata ba, inaji araina hotunan nan akwai wani abu atattare da su, zanyi kokari insan daga inda suke"

kafin Ummi ta shigo Wakin su ka yi hanzarin mayar da kayan cikin drawer din, hotunan ma cen cikin wasu notebook dinta dake qasan drawer din ta boyesu.

Adaren ranar basu koma part din daddynta ba, bayan da taga wayar officers suka ce su fito su koma part din daddynta, aikuwa ta sanya masu rigima akan bazata koma ba anan takeson kwana, ganin dare ya nutsa sosai yasa suka kyale ta, taso ta kwana adakin Danish sai dai takasa bude room door dinsa saboda an kulle kuma bata san code din kofar ba, adole ta hakura suka kwana adakinsu ita da Batool, Ummi kuma ta kwana adakinta.


Morning

Zaune suke su Uku akan dining Chairs, sun tasa Abincin breakfast din da aka jere masu kan table agaba sai dai sun kasa ci, saboda rashin kwanciyar hankali tun kayan baccin jiya ne a jikin su babu wanda Ya cire nashi.

"Unaisah, ku ci abinci mana" ummi ce ta faWa tana kallon su, kamar wadanda sukayi amai da gudawa duk sun faWa, sai uban kasusuwan wuya..

In a cool voice Unaisah tace "Aunty Ummi, wlh abincin ma bayayi min dadi, turawa kawai nake yi.."

Batool tace"kamar kin shiga zuciyana wlh nima dai babu dadi..." shiru ummi tayi cike da damuwa take kallon su to ita ma dindai ba dadin abincin take ji ba, turawa kawai takeyi..

"Yau tsawon sati guda Aunty Ummi, babu labarinsu, kullum da zullumi muke kwana, tunanin mu meya faru da su? Sunyi nasara ko kuwa? Tayaya zamu sani Aunty Ummi? Ko awaya babu wanda Ya tuntu6e mu...." dakyar ta ?are maganar saboda kukan dake kokarin 6alle mata, dakyar ta haWiye shi.

"Jiya har mafarkin Danish nayi, da daddyna, Amma mafarkin baiyi min daWi ba, shiyasa ban ma baku labari ba..." ta faWa arauna ce, dafa kafadarta Ummi tayi"mu kara hakuri Unaisah, tun da bamusan meya tsayar da su ba, amma wani jinkirin Alkhairi ne In sha Allah zasu dawo cikin koshi lafiya..." yamutsa fuska tayi batare data furta kalma ba,

Wayar Ummi ce tayi Ringing daga cikin aljihun wandonta, zaro wayar tayi tare da duba sunan me kiranta, kamar mara gaskiya ta dago suka hada ido da su Unaisah har suna hada baki gurin furta"Daddy ne"?


Girgiza kai tay"ba shi bane, Friend dina ne" kafin tay picking call din ya katse mayar da wayar tayi cikin aljihu kafin ta maida dubanta gare su.

A fakaice Unaisah ta kalli Batool suka hada ido batare da ta lura ba, gaba Waya sun fahimci bata son yin waya agabansu in har ba daddyn Unaisah ne ya kira ba ko big guy.

"Guys yanzu dai mu daure mu ci ko rabin abincin ne kada ay almubazzaranci"..." matsa masu tayi dakyar ta samu Suka ci kaWan.

mikewa Unaisah tayi daga kan dining din ta nufi dakin su.

Bayan tafiyarta Batool ta dubi aunty Ummi"yaushe zamu koma part din daddy, kada suji mu shiru"

Ummi tace"nima abun da nake tunani kenan, Bari na kira Danejo awaya in fada mata don ta kwantar masu da hankali" ta fada tare da zaro waya ta danna ma Danejo kira.


zama tayi gefen gadon Su hannunta ruke da iphone dinta data dauko, messages ta shiga ta buWo Sakonnin daya ta6a tura mata, nutsuwa tayi tana karanta su fuskarta Wauke da murmushi, bayan ta gama karanta sakonnin ta shiga gallery ta bude hotunan da ta ta6a yi mashi batare da sanin shi ba, yayi mata kyau a pics din har wani lumshe idanu takeyi idan tana kallon su, ta kosa ya dawo ko dan ta cika mashi burin shi, idan ta tuna alkawarin daddynta dayace in har ta bi umarninsa zai bari ta auri zabin ranta sai taji wani dadi ya lullu6e zuciyarta, fatanta Allah yasa suyi nasarar ruguza kurkukun kaddara su dawo cikin koshin lafiya.

Kira ne Ya shigo wayarta, murmushi ta dan saki ganin sunan mommyna ya bayyana akan screen din wayar, picking call Win tayi tare da kara wayar a kunnanta..

"Haba my baby, kin daga min hankali kullum saina kira bana samun ki, Almost a week?! Meke damun ki ne? sautin muryarta da damuwa ta tambaya.

"I'm sorry mommy, school ne ya boye ni, bayan haka wayar ma ta samu matsala sai jiya aka gyara min ita"

On the other hand, Benazir kiris Ya raga ta sanya dariya, ta rasa gane meyasa Unaisah take son yi mata karya, bayan ba halin ta bane, since last week ta riga da ta gane itace Unaisah yarinyar da ta kira wrong number tay mata karyar a kano suke yanzu kuma tace tana school bayan a labarin da Aneelerh ta bata Unaisah bata zuwa School.

basarwa tayi tare da cewa"Okay, kada ki damu, nima bazanso na takura maki ba, am babyna Ina daddynki ne? Almost a week bana ganin shi a online.." su6ul da baka tay What's your connection with him?"

yar dariya benazir tayi"son shi nakeyi, tun ranar dana fara yin tozali da shi, don ma ya?i kulani ay da tuni mun yi maki ?ani..." waro idanu Unaisah tayi can kuma tadan saki dariya, har cikin ranta taji dadin maganar Benazir don kuwa time da ta fara ganin ta saida tayi ma daddynta sha'awar auranta, tadaiyi shiru ne saboda tana kokwanton ko tana da aure bayan haka bata son yayi ma Danejo kishiya ga kuma aunty Aneelerh da take burin ya aura saboda kaninta junaid ya samu Uba nagari.

tayi zurfi a tunaninta muryar Benazir ta katse ta"kinyi shiru babyna, kin san nima na rasa mijina da yata, ina maraicinsu, Aneelerh ta fadamin baya tare da mommynki, shiyasa nakeso nazo na maye gurbinta, ko bakya son in auri daddynki"

murmushin ya?e tayi kamar tana agabanta tace"inaso, amma bata faWa maki yana da au..." bata ?are maganar ba, sakamakon dirar motocin data jiyo acikin kunnanta, rejecting call Win tayi tare da jefar da wayar Kan gado, ta fito da gudu ko Mayafi bata Wauka ba ta nufi hanyar fita daga falon jikinta sai kerma yake tsabar zumuWi, kafin ta ?arasa Ummi da Batool suka bi bayanta da Wan gudun su.

At same time motocin su ka yi parking, a gaggauce Officers dake tsaron gidan suka Yi masu kawanya tare da yin hanzarin buWe cardoors, Adai dai lokacin Unaisah ta zuro kofarta waje wani burki Taci idanunta azare take Kallon motocin Cike da fargaban wa zata fari gani.

CO ne Ya fara fitowa cikin hanzari ya zagaya bayan motarsu ya buWe boot ya cure folding wheelChair ya ajiye ta kasa ya fara kwancewa sai da ya daidaita wheelchair din kafin Ya furta"zaku iya fitowa da shi"

Wani irin faduwar gaba taji gaba daya tabi ta rude jin ya furta za'a iya fitowa da shi ko wanene? sai faman rarraba idanu takeyi akan motocin, lokacin da idanunta su kayi mata tozali da mutumin da SA suka rurruko daga backseat na Waya daga cikin motocin, jikin shi sanye da patient uniform blue yar riga ce mai tsayi, Cinyar kafarsa Waya gaba dayanta a nannaWe take da bandage daga gani aiki akayi masa a tsakiyar cinyarsa, A hankali suka zaunan dashi kan wheelChair din sai nishi yake yana fitar da numfashi mai huci daga gani babu lafiya atattare da shi.

Cike da tashin hankali ta zare idanunta, la66anta na kerma ta furta"inna lillahi wa'inna Ilaihirraji'in! Daddy"! Da karfi ta furta sunan shi, bawan Allah a firgice Ya dubi inda take har rama yayi saboda azabar ciwo, suma Jami'an suka maida hankali akan ta..

watsawa tayi da gudu tana karasawa gaban shi a slow ta zube kan gwiwowinta, ta fashe da matsanancin Kuka tamkar ranta zai fita Cikin shesshekar kuka ta furta nashiga ukuna! daddy Meya faru dakai? Meya faru da kafarka?

tsantsar tausayinta ne Ya kama shi, Ummi da Batool sun kasa motsawa saboda tashin hankalin da idanunsu suka gane masu, daya bayan daya sauran dake acikin motocin suke fitowa, Chief owais ne jikin shi sanye da Singlet fara sai short, gaba Waya goshinshi bandage ne, fuskokin su duk sun 6aci da tabonnin raunukan da suka ji, Wa'iya zubilla, dafe kirji ummi tayi cike da tashin hankali ta furta"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Batool kuwa Fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita musamman data lura babu Danish a cikin su, daga cikin sauran da suka fito daga cikin motocin U.s armies din da suka rage ne su Biyar, babu cikon Wayansu, sai wasu daga cikin na hannun daman Chief wadanda ba'aje Kai farmakin da su ba.

Akace labarin zuciya atambayi fuska, tunkafin suyi masu bayani suka karanci komai daga yanayin su, Dakyar Taj yai karfin halin janyo Unaisah Ya rungumeta akan kirjin shi, tare da shafa sumar kanta yana faman sauke ajiyar zuciya, har cikin ranshi yaji dadi da Allah yasa ya rayu ashe da rabon zai sake ganawa da yarsa? sai dai abu daya da yake ma fargaba.

hannun Ummi ruke dana Batool suka karaso Gurin su Chief, Fuskokinsu sharkaf da hawaye Murya Na rawa Batool ta furta"Ina Danish din mu"? Shiru sukayi don basu shirya komawa asibiti da wanin su ba.."dan Allah ku faWa min Ina danish? Meyasa bangan shi ba..." cikin shesshekar kuka tayi maganar, Sunyi shiru suna kallon ta, Chief ma Hankalinsa baya akan su, saboda matsananciyar damuwar data mamaye zuciyarsa.

Unaisah data kwantar da kanta a kirjin daddynta, Hankalinta Idan yai dubu toh ya tashi, tin da taji muryar Batool tana tambayar Danish ta fahimci babu shi su ka dawo! Babu!!babu!! Hasbunallahu wa'ni imal wakeel, acikin zuciyarta ta dinga maimaita duk wata addu'a datazo cikin bakin ta.

Ummi kuwa Jikinta yagama mutuwa Cikin sanyin murya ta wanda Ya kara tayi masu Chief barka da dawowa da tambayar ya jikin su, fuskokin su kwata kwata babu walwala suka amsa mata, Kafin Commender james ya nemi su shiga ciki saboda majinyatan jikinsu da suka jigata, dakyar Chief yake Tafiya saboda rashin kuzari, bawan Allah shi kadai yasan me yake ji a cikin zuciyarshi bazai ta6a mantawa da Danish ba Har abada ya kafa tarihi acikin zuciyar shi, gaba daya abun da suke jima fargaba yadda yan uwan shi zasu kar6i abunda zasu fada masu saboda su sunsan irin kaunar da suke ma Junansu komai zai iya faruwa idan suka ji cewa Danish ya mutu.

"Commender pls, meya faru ne? Hankalina Ya tashi, Ina son nasan Ina Danish ne? Ina Omar? Ina Major"? Suna Ina"?

Girgiza kai commender yayi cikin rauni murya da harshensa na turanci ya furta"Ummi, muje ciki zamuyi maku bayani"

yana fadan hakan yabi bayan Su Chief suka nufi ciki.

mutun uku ya rage a harabar, gaba daya suka zukunna Agaban Taj, Cikin rauni na murya Unaisah ta furta"daddy, Ina Danish"?cike da fargaban amsar da zai bata tayi maganar, tare da dago kanta daga kirjinshi, fuskarta ta 6aci da hawayenta, gwanin ban tausayi ya ke kallon ta.

"Dan Allah Daddy Ka fada mana, Ina Dan uwanmu Danish"? batool ce ta fada still bata daina kukan ba...

Ummi ma tace"tun da kuka tafi, Hankalinmu ba akwance yake ba, saboda zullumi da fargaban awani hali kuke ci, gashi kun dawo ba yadda muka zata ba, babu wasu daga cikin ku, sannan ku kanku araunace kuke, that means something bad happened."?

Ta fada idanunta cike tab da kwalla, yayi shiru yana binsu da kallo...

"Daddy, pls ka fada min, yana raye koya mutu, kada kace zaka boyemin, saboda duk mun daren dadewa dole naji, kwara ka fadamin ayanzu inyi jinyar zuciyata idan ina da rabon cigaba da rayuwa, ay ma nayi imani da kaddara, in ma ya mutun Zanyi hakuri in rungumi ?addara..."

wani kallo Taj yayi mata bakomai yake tunawa ba face abubuwan da suka faru kafin tafiyarsu irin haukan da tadinga yi na zai raba ta shi, shine yanzu take kokarin yi mashi burga salon Ya fada mata Ya rasata na har abada.

ganin kallon da ya ke yi mata yasa ta kama in-ina hawaye na cigaba da tsastsafowa kan fuskarta tace"wlh daddy bazan damu ba, ka fadamin kawai.." tana kuka tana dariya tayi maganar kamar zautacciya.

hmmm baiwar Allah bashi ba, hatta ummi ta karaya da ganin yanayinta, kodan saboda Unaisah zataso ace Danish Yana raye.

Da ido tayi mata Taj alamar karya kuskura ya fada mata, don ita tasan me ta gani wlh, Shafa fuskarta yayi da tafukansa Ya kakalo murmushi kan fuskarshi"meye naga kun wani daga hankulanku"?

"Daddy taya hankalinmu bazai tashi ba, kun dawo gaba dayanku ba lafiya, kuma babu Danish da ya Omar"

jinjina kanshi yayi"hakane daugher, amma inaso ki sani dan uwanku yana nan cikin koshin lafiya.."

ba dan sun yarda da maganar ba, Tace"yana ina"? kafin ya bata amsa Ummi ta katse su da cewa"Haba Unaisah, dudufa Yanzu suka dawo, baki ga halin da yake a ciki ba, ki bari Ya shiga Ciki Ya huta mana, inyaso sai muji komai daga bakinsu," dakyar Ummi ta lallashe su suka hakura da yi mashi tambayoyin.

Unaisah da Batool ne suka gungura Wheelchair din Taj ganin ya raunata sunsan ba lallai ya iya gungura kan shi ba, suka nufi main falo din ummi na abiye da bayan su, anan suka iske su commender zazzaune kan Sofas, gaba dayansune da suka shigo, a tsakiyar sofas din Su batool suka dakata da gungura shi, kan floor suka zauna kamar masu zaman makoki, ummin ma ta zauna gefen su.

saida suka huta nutsuwa ta shige su sosai, kafin chefs din gidan suka shiga jera masu Abinci, kamar sarki haka suka dinga lallashin chief donyaci abinci yace masu bazai iya ba, ko yaci bazai ji dadin shi ba, subar shi kawai shi kadai yasan halin da yake aciki, cikin kwantar da murya commender yace"in har bakaci abincin ba, taya zaka samu karfi ajikinka balle harka Iya Karasa aikin ka"!

"What you need now is peace of mind because your brain needs rest to function, Chief worry won't solve anything, it will just lead to loss and regret, just Forget about every bad thing that happened in the prison of destiny, Strengthen your heart and face what lies ahead, that's how you'll achieve success ka fuskanci abunda kasa agaba, ta hakane zaka cimma nasara..." kalamai masu karfafa zuciya Commender james Yaci gaba da furta mashi sauran na hannun damanshi duk suka saka baki gurin kwantar masa da hankali har saida suka samu Ya Wan lafa, cikin sanyin murya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0