Showing 150001 words to 153000 words out of 413917 words

Chapter 51 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4479

yanayin fuskarta ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, gani take kamar yawancin iyaye mata basu da tausayin ya'yansu shiyasa suka watsar da su bayan sun haife su.

"Benazir ki shiga kiyi wankan, babynki zata jiraki anan" jikin ta na rawa ta mike ta shiga toilet din, tun zuwansu hajiya layla ke taimaka mata tayi wanka saboda rashin nutsuwar da bata da ita, amma yau da kanta tayi wanka abun ba karamin dadi yayi ma hajiya layla ba, atare suka zauna da angel ta fara bata abinci abaki tana ci sai dadi take ji, ita ma ta dauki spoon ta debo ta sanya ma angel abaki hajiya layla nata kallon su gwanin ban sha'awa bayan sun kammala cin abinci, dr jazz ya shigo duba lafiyar benazir shi kanshi ya fahimci nasarar da suka fara samu don alamu sun nuna takusa regaining hankalin ta....yau ko allura ba'ayi mata ba, magungunanta kadai suka bata tasha.

Kafin dr jazz yabar dakin saida Ya kira unaisah, suka ke6e a kofar dakin ya tambayeta meke damunta? Chief ya fada mashi bata da lafiya..." murmushi tayi masa kafin tace"ba abunda ke damuna, lafiyata qalou.." lallashinta ya dinga yi yana lalla6ata duk don ta fada mashi amma ta nace akan ita lafiyarta qalou, yace toh shikenan idan akwai wani abu da kike bukata ki sanar dani, chief ya bani amanarki bana son ganin damuwa atare dake, har cikin ranta taji dadin maganarshi, tace in sha Allah zan baka hadin kai dr, nagode da kulawarka agare ki, bayan tafiyar jazz ta juya zata shiga dakin har saida suka bangaji juna ita da benazir, taji shiru bata ganta ba shine tabiyota kada asace mata babynta, murmushi unaisah tayi tare da ruko hannunta suka koma cikin dakin, daga jiya zuwa yau wata irin shakuwace mai karfi ta shiga tsakaninsu, duk wani motsin unaisah akan idon benazir ta hanata sukuni tana a ma?ale da ita ko toilet bata son ta shiga, tafi son taji dumin jikin ta anata, haka itama unaisah ko tari Benazir tayi saita nuna damuwarta akanta.

Wuraren karfe 12 dr shureim da Alhaji ubaid suka zo asibitin, a bakin kofar dakin jami'an dake sanye da fararen kaya suka dakatar da su suka ce ba abada iznin shiga ciki ba, hankalin dr shureim ba karamin tashi yayi ba saboda baisan da dokar za'a hanasu shiga room din ba, Alhaji ubaid yace bazai yiwuba babu yadda za'ay su hana shi ganin yar shi, tun da harya tako yazo dole ya shiga ya duba lafiyarta, ganin dagaske ba zasu bari su shiga bane yasa dr shureim kiran layin hajiya layla, bayan ta Waga ya sanar mata zuwansu, fitowa tayi daga dakin sanye da hijabi, wani irin annurin farin ciki suka gani akan fuskarta, bayan sun gaisa Alhaji ubaid Yace"ya mai jikin? Ina fata jikin nata da sauki. " murmushi hajiya layla tayi"mai jiki Alhamdulillah, benazir ta fara samun lafiya, shureim bai fada maka abun farin cikin daya faru jiya ba"? Murmushi alhaji ubaid yayi"ya fada min, wlh naji dadi nayi murna naso ace na gana da iyayen yarinyar don inyi masu godiya"

labari ta fara basu na abunda ya faru da safen nan ta ?ara da cewa"yarinyar tana da wayou, baka ganta ba kamar benazir dince ta haifata sunyi kama, abunda yafi daure mun kai shakuwar su baka ga yadda suke tarairayar junansu ba. " wani irin dadine Ya lullu6e dr shurem da Alhaji ubaid

"Alhamdulillah, ubangiji Allah Yasa yarinyar ta zama silar warakarta. " suka amsa mashi da ameen
"Yanzu ba zamu samu ganin Benazir din ba"? Alhaji ubaid ne yayi maganar,
Hajiya layla tace"ba zasu bari ku ganta ba, kuyi hakuri kawai har zuwa lokacin da zasu salleme mu"
Dr shureim Yace"gaskiya ni bazan iya hakura ba, ina son ganin yar uwata..Alhaji ubaid yace ni bansan dalilin kafa dokar ba, in ma za'a hana wani ya shiga ay dai ba a hana ni ba, ni da nake mahaifinta.." kiri kiri jami'an suka hana su shiga ciki gashi sun kwallafa rai akan son ganin su, zuwan dr jazz ne Ya sama masu maslaha, da farko yayi kokarin fahimtar da su dangane da dalilin dayasa suka hana shiga, Yace iyayen yarinyar ne basa son wani abu ya samu yar su, shiyasa suka sanya tsaro a asibitin bayan haka basu san wani abu da zaisa ita benazir din ta gane ba mamanta bace" Alhaji ubaid yace su dai a taimaka abarsu su ganta.."_ ganin ya kafe ne yasa dr jazz ya kira chief a waya ya sanar da shi dangane da zuwansu Alhaji ubaid, shiru yayi jim yana nazari dama don saboda Alhaji ubaid suka kafa dokar amma daya tuna yadda taj ya fada masa ya yi ma unaisah bayani akan ko wani ya nuna ya santa kada ta nuna ta sanshi, ya dai san in suka hadu idan ta ganshi zata iya gane shi tun da yarinyar da wayon ta amma bai kamata su hana family din mara lafiyan ganin ta ba zasu iya zargin wani abu, hakan yasa chief furta"Jazz ku bar su su shiga, amma kada su Wauki lokaci, sannan ka sanya ido akan su bana son fira mai tsayi ta shiga tsakanin su da yarinyar .." amsa mashi yayi da toh, bayan sun gama wayar ya sanar da su Alhaji ubaid sun samu iznin shiga amma kada su wuce mintuna biyar, lokacin da suka shiga unaisah ta shiga toilet, bata samu ganin su ba, ta dai jiyo muryoyinsu a dakin suna magana, sunyi jiran fitowarta amma har time ya cika ba ta fito ba, sai bayan da suka fita daga Wakin kafin ta fito daga ciki.


Around karfe 3 na rana su Anila suka zo tare da su mami hada abie, bayan sun gaisa sukayi ma hajiya layla ya mai jiki tace masu, ay tama fara samun sau?i sosai, har labari taba anila na irin shakuwar da sukayi, ba karamin dadi taji ba, su kansu sun lura da cigaban da aka samu na lafiyarta, saboda tana gane kowa dayazo wurinta, har sunayensu take kira, Unaisah taji dadin zuwan aunty Anila, har tambayar baby junaid tayi anila tace mata ta yi hakuri school yake zuwa kuma sai marece yake dawowa cikin gida, bata ji dadi ba saboda ta kwallafa rai akan son ganin shi, lallashinta anila tayi tace kada ta damu zatayi kokari koda cikin weekend ne zata kawo mata shi, sun jima a asibitin kafin daga bisani suka tafi

_________________________________
'?



Bayan sallar magrib, Unaisah tana zaune gefen gadon benazir dake akwance tana bacci ta ru?e hannunta acikin nata don kada a sace mata babynta,
Hajiya layla tana zaune kan darduma hannunta ru?e da cazbaha tana ja,..."

Baiwar Allah duk dauriyar da takeyi sai da tagaza jurewa duk bayan ?an mintuna sai ta shiga toilet ta yi kuka, tayi kokarin cire shi aranta ta kasa, zuciyarta sai azalzalarta takeyi akan shi, bata bari hajiya layla ta gane halin da take a ciki ba ....

A hankali ta cire hannunta daga na benazir, ta mike ta shiga toilet ta tsaya agaban sink, ta fashe da kuka da sauri ta toshe bakinta da tafukan hannayenta don kada su jiyota, fuskarta tayi jawur hatta idanunta sun kankance, damuwarta awani hali yake a ciki? Tasan halin shi yana da wuyar sha'ani ba lallai ya yarda da wani ba, zai cigaba da killace kanshi ne adaki watakil ma har zuciyarshi ta buga Ya rasa ranshi! Wa zai bashi kulawar da take bashi? Mutumin da baisan komai ba sai soyayyarta itama tasan da hakan, Itace jindadin shi na rayuwar duniyar nan...amma meyasa yayi mata hakan? ya rasa akan wa zai gwada rashin imaninshi sai akanta? Abunda yafi 6ata mata rai tana fama da radadin ciwon ciki ya nemi illata rayuwarta, duk in ta tuna yadda ya janyo kafafuwanta cikin rashin imani ya wurgar da ita kanta gado ya hambare kanta, abun Ya 6ata mata rai, sai dai har yanzu wani sashe na zuciyarta ya?i aminta da zargin da takeyi mashi saboda bai ta6a yunkurin cutar da ita ba wannan ne karo na farko daya farayi mata hakan...." runtse idanunta tayi wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makoshin cikin karyayyar murya ta furta"meyasa kayi min haka? Me nayi maka dana cancanci hakan daga gare ka? Ka rasa wa zaka cutar sai ni? Angel dinka? Mai son ganin farin cikinka me share maka hawayenki"?

Ta jima acikin toilet, sai da ta gama sambatunta, kafin ta wanke fuskarta ta fito jiki asanyaye, wayarta ce ta fara ringing, da sauri ta nufi backpack din ta curo wayar tare da duba sunan mai kiranta, tayi mamakin ganin sunan chief Owais ya bayyana, tun time da daddynta ya bata layinsa bata ta6a kira ba ta daiyi saving dinta.


Picking call din tayi tare da kara awayar a kunne cikin sanyin murya ta gaishe da shi ya amsa mata
"Ya mai jikin"?
Tace"alhamdulillah, da sauki sosai, bacci takeyi yanzu"
"Okey, ina fata dr jazz Ya duba lafiyarki"? Ya fada tamkar baisan abun da ke damunta ba..
"Eh, naji sauki ma"
"Okey, nazo asibitinne, amma ban shigo ciki ba, Ina parking a space, Yanzu zan turo ataho mun dake..." waro ido tayi jim kafin ta amsa mashi toh,
Bayan ya katse kiran ta sanar da hajiya layla game da zuwan chief

Ko minti biyar ba ay ba, sai ga agent sanye cikin ????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
kaki, da sauri ta dauko hijab ta zura a jikin ta, Allah yaso benazir bacci takeyi da kuwa ta hanata fita.

Tana fitowa daga dakin agent din Ya mi?a mata face mask, ta sa hannu ta kar6a kafin ta sanya a fuskarta, tabi bayan shi suka fito... Tunkafin su karasa harabar ajiye motocin ta hango chief ya dauki wankan suit, yana daga tsaye ya jingina bayan shi jikin motarsa, fuskarsa na asanye da mask, gaba Waya hankalinsa na akan wayarsa da yake dannawa. ...

"Assalamu alaikum..." sanyayyar muryarta ce ta ratsa kunnanshi, A hankali ya Wago suka haWa da juna da sauri ta sunnar da kanta kasa kamar wata munafuka, kunyar shi taji tunawa da huggin dinta da yayi a jiya.
Lumshe idanunshi yayi tare da sake buWe su kan fuskarta, jiya zuwa yau ba karamin jinta yake a cikin zuciyar shi ba.

"Ya kuka ?are da Sis din nawa"? Murmushi tayi kafin ta fara bashi labarin shakuwarsu.. " kallon ta kawai yakeyi daga yanayin ta ya fahimci taji dadin kasancewarta da mamanta hakan ba karamin faranta ranshi yayi ba
"Kinyi kuka ne"? da sauri ta girgiza kai alamar a'a
"Kada kiyi min ?arya, naga alamun hakan a idanunki" shiru tayi jikin ta ya fara kerma sam batason kowa yasan abunda ke damunta...
"Ina daddy na da yan uwana"? tayi mashi tambayar ne don ta mantar da shi
"Baki da layin shi"?
"Ina da shi, amma wayar babu card da zan kira shi"
"Ina wayar" da sauri ta fiddo da hannunta, ta mi?a mashi ita, bayan ya kar6a yace"ki shiga cikin motar, ki jirani" amsa mashi tayi da toh...

BuWe mata murfin motar yai, kwata kwata bata lura da mutun a ciki ba, ta kutsa kai ta shuga ta zauna, wani irin ni'imtaccen sanyin A.c ne Ya ratsa fatar jikin ta mai hade da kamshin turare
Wurga idon da zatayi karaf ta sauke su akan fuskarshi, ta cikin mirror ta hango shi, kiris Ya rage ta fasa ?ara saboda ta tsorata batasan da mutun ba
A firgice ta kalle shi, yana a gefenta farar jallabiya ce a jikin shi, fuskarshi sam babu walwala, zuciyarta ta hasala ranta ya 6aci da sauri tafara kokarin bude murfin motar taji shi a gar?ame kamar taga wani mugun abu..
Hakan ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, wani irin shakkarta Yake ji
"Angel... Pls ki tsaya inyi maki bayani nasan zaki fahimce ni..." banza tayi dashi kamar bata ji me yace ba

"Nayi zaton kece mutun na farko da zaki fara yi min uziri ki fahimce ni idan na aikata badai dai ba sainaga ba haka ba, kamar bakisan wanene ni ba"? Muryarshi ba karamin kashe mata jiki tayi ba, ta haWe fuskar kamar bata ta6a dariya ba duk don kada yayi tunanin zata raga mashi...
Fashewa tayi da kuka tana fadin"bana son jin muryarka! Bana son ganin ka! Meyasa kazo"? Hawayene suka wanke fuskarshi.
"Pls ka kyaleni in rayuwata, yanzu bana bukataka, na riga na gane ba dan Allah kake tare dani ba akwai wata manufa aranka..." ta faWa tana zare mash gray eyes dinta wadanda suka kada jawur da su.
"Bazan ta6a sauraronka ba, saboda kai makaryaci, kayi min karya danish meyasa baka yarda cewa kaine ka aikata min hakan ba lokacin da nazo dakin ka"? Ta jefa mashi tambayar tana kallon fuskarshi duk yabi ya dabarbace sai lokacin ta lura da yanayin shi har rama yayi ga wata matsananciyar damuwa data gani akan fuskarshi
"Kiyi hakuri ki yafe min Angel, na aikata babban kuskure, amma ki fahimce ni bada son raina na aikata miki hakan ba, nima bana acikin hayyacina, lokacin da kikazo dakina na manta komai daya faru saboda bayin kaina bane sai daga baya nayi mafarkin abunda ya shiga tsakanin mu..." ya faWa yana haWiyar yawu mai Waci.

"Angel kinsan bani kadai bane kuma har yanzu elders suna bibiyar rayuwata ko su zasu iya shiga tsakaninmu don su rabani dake saboda sun san cewa ke daice lagona, ta hanyar shiga tsakanina dake ne kadai zasu iya cin galaba akaina.." wani irin faduwar gaba take ji, ita kanta bata son tayi silar da zai koma kurkukun ?addara, maganar tashi taso tayi tasiri azuciyarta....

Jin tayi shiru yasa shi tunanin ko ta yafe mashi ne, matsawa yayi kusa da ita, ya Wan kwantar da kanshi saman kafaWarta da sauri ta sanya hannu ta ture shi da karfi ta wurga mashi harara da kakkausar murya tace"kada ka ?ara gigin ta6ani! Idan har ba so kake inyi maka abunda baka ta6a tsammani ba! Kabarni inji da abunda ke damuna Danish! Ka nisanta kanka dani zaifi maka kwanciyar hankali"

Kamar karamin yaro haka ya fashe mata da kuka, bawan Allah Ya rasa meke yi mashi dadi a duniyar nan

"Ki tausayama rayuwata angel, ki yafe min koda ba zaki cigaba da kula ni ba, bana so kina fushi dani, na yarda na amsa laifina, ki yanke min kowani irin hukunci ne a shirye nake dana kar6e shi...."

Bata ta6a ganin tashin hankalin akan fuskarsa irin na yau ba, taji tausayin shi amma in ta tuna irin rashin imamin daya yi mata adaren shekaran jiya sai ta ji ta?ara jin tsanar shi, akan me zataji tausayin shi bayan shi bai tausaya mata ba? kalaman auntyn ummi ne suka fara dawo mata cikin kanta, idan har tabari namiji yana ta6a ta zata samu ciki, wannan maganar ta Waga mata hankali, tabbas in har ta cigaba da bashi fuska zaicigaba da kokarin kusanta kanshi da itane, wannan dalilin ne yasa tace"Zan yafe maka, amma abisa sharaWi Waya"? Jikinsa na kerma yace"wani irin sharaWi ne"?
"Kayi min alkawarin zaka yi komai nace"? Waga mata kai yayi alamar eh
"Daga rana irin ta yau bana so ka kara kusanta kanka dani...." kafin ta kare maganar yace"bazan iyaba angel..." da sauri ta daura yatsanta kan la66ansa da ruwan hawaye suka ji?a tsit yayi yana sauraronta
"Idan har dagaske kai garkuwa ne agareni mai bani kariya daga dukkan abun cutarwa toh inaso kabani kariya daga sharrinka danish! Ka nisanta kanka dani, in har kana son farin cikina, saboda ganinka da nakeyi a yanzu raina yana 6aci..." wasu zafafan hawayene suka kara wanke fuskarshi
"Baka da mafita data wuce wannan! In har kayi min hakan zan yafe maka.." runtse idanunshi yayi yana jin wani irin kunci da takaici kamar ya binne kanshi haka Yake ji, bakomai ya fado mashi aranshi ba face kalaman chief, dayace mashi ya bata tazara kada ya tursasa mata saboda ayanzu tana akan dokin zuciya!
Numfashi Yaja kafin a hankali ya buWe idanunshi a acikin nata, har saida gabanta ya fadi ganin yadda suka kaWa jawur tamkar an watsa mashi barkono a cikin su, kyakkyawar fuskarshi ta 6aci da ruwan hawayen shi har cikin ranta tana jin kamar bata kyauta mashi ba.
Cikin rauni na murya yace"na amince in har hakan zaisa ki yafe min, bazan ?ara takura maki ba" dakyar ya kare maganar, kafin ya kifa kanshi saman laps dinshi
"Danish! Ta ambaci sunan shi bai amsa mata ba,
"Bana so wani yaji abunda ya faru atsakaninmu! Koda chief ne! Duk da bansan ko ka riga da ka faWa masa ba" muryarshi kasa kasa yace"ban fada masa ba" ajiyar zuciya ta Wan sauke, da sauri ta share hawayen ta kafin ta kuma cewa"don na yanke alakar dake atsakaninmu hakan ba yana nufin bana sonka ba! Kawai bana son ka akusa dani ne, sannan bana son hukuncin da na yanke ya shafi rayuwarka! kada ka hana idon ka bacci saboda dani, kuma kada ka ?i cin abinci, idan kayi hakan bazan ji dadi ba..." tana magana hawaye na kara wanke fuskarta, kasan hijab din jikinta ta sanya ta share hawayen kafin ta daidaita nutsuwarta.



Kafin Takai hannu ta zuge window glass Win motar, tayi ma chief magana don ya buWe mata car door Win da ta gaza buWe wa, dagangan Ya datse kofar motar shiyasa ta gaza buWe, yanzu daya tabbatar sun gama magana, da kanshi ya buWe mata, ta fito idanunta cike tab da kwalla dakyar ta haWiye kukan da take ji, haWa ido sukayi cikin na juna, muryarta ?asa ?asa ta furta"mun gama magana inaso zan tafi" bata san hawayen da take 6oyewa sun fara sintiri kan fuskarta ba, hanky ya zaro mika mata"ki share hawayenki"! Kar6a tayi a hankali ta fara share kwallar
Iphone dinta dake a hannun shi ya mi?a mata"na sa maki card, zan kira anjima zamu yi magana, ki koma ciki yanzu" amsa mashi tayi da toh nagode, kamar karta tafi haka take ji tana tafiya tana waiwayon motar zuciyarta cike fal da tunanin shi....

*AFTER SOME DAYS*

(Bayan wasu kwanaki)

tun daga ranar da chief Ya kawo danish asibitn bai ?ara matsa mashi akan ya kawo shi ba, daga shi har ita unaisah din sunji jiki ba kaWan ba daurewa kawai sukeyi, sau?in su Waya kowannansu Ya samu abunda Yake Webe mashi kewa, chief ya zama tamkar abokinshi baya barin shi acikin damuwa, sai da yasan ta yadda yai harya samu kar6uwa a wurin danish, kullum suna atare abinci ma atare suke cin shi, abu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0