Showing 210001 words to 213000 words out of 413917 words

Chapter 71 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2664

ne Ya motsa? Kada fa ta hau ta da bugu tun ba hankaline da ita ba..tuni tasha jinin jikin ta, tana faman haWiyar yawu kutt murya na rawa ta furta"am..um.. mamana! Tun yaushe kika farka"? Dakyar ta kare maganar ganin yadda Benazir tayi mata rumfa kamar zata danne ta, babu alamun zata tanka mata tayi shiru tanata kallon ta...babban tashin hankalin unaisah hajiya layla bacci takeyi balle ta kawo mata Wauki, tuni ido ya raina fata.
"Dan Allah na ro?e ki, ki daina kallona haka, babaynki ce fa, ki na bani tsoro. .." sai da tay wannan maganar, Benazir ta saki murmushin gefen fuska har dimple
dinta ya lotsa...
"Babyna ne"? La66an unaisah na kerma tace"ni ce, dan Allah kada kiyi min komai..." ?ar dariya benazir tayi, wani irin nishadi take ji..
Shafa sumar kanta tayi har wani kyafkyafta idanu take Yi kamar wata mara gaskiya
Unexpected ta ji ta manna mata sumbata kan kuncinta, kafin tayi wani yunkuri ta kara mata wani kan la66anta, runtse idanu tayi kamar zata fasa ihu ta furta"na shiga uku, tawa ta same ni"! dariya benazir tayi kafin ta janye jikinta daga na unaisah ta koma kan gadonta ta kwanta idanunta na fuskantar ceilling..." wasu zafafan hawayene suka wanke fuskarta da sauri ta cusa kanta jikin pillow,
Satar kallon ta unaisah tayi, ta rasa gane meke damun matar, ta fara tsorata da lamarinta, kwanakin nan ta canza mata, ba kamar farkon da tafara jinyarta ba, ko meyasaS'

Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta sauko daga kan gadon, ta lalla6a cikin sanWa take tafiya, backpack dinta ta buWe ta curo wayarta ta nufi toilet ta shige ciki,

Text message ta tura ma daddynta

"Daddy, barka da dare, daddy ni dai nagaji da zaman asibiti, gida nakeso in dawo" tana tura mashi text din jim kaWan saiga kiran shi, tayi mamaki saboda batasa rai zai bata amsa ba kusan karfe shabiyu na dare, tayi zaton yayi bacci.

Picking call din tayi tare da kara wayar a kunne"My daughter! Me kike yi har yanzu baki kwanta bacci ba? Wani abu ya faru ne"?

Cikin muryar raWa ta furta"ba abun da ya faru, kawai bana jin dadin yawan kallona da matar takeyi, duk in na farka tsakar dare saina ganta akaina ta tsare ni da idanunta"

Sautin dariyar shi ce ta ratsa kunnanta aiko ta haWe fuska kamar tana agabanshi tace

"Daddy dariya kake yi min?

"Sorry daughter, maganarki ce ta bani dariya, but ki ?ara hakuri Anila ta fada min next tomorror za'a sallame ta"

Shagwa6e fuska tayi, ko tsoro bata ji ita kadai a toilet


"daddy ina yan uwana? Yau banji muryoyin su ba"

"Suna nan cikin koshin lafiya, basu da wata damuwa"

Shiru sukayi na wani lokaci, zuciyar ta sai azalzalarta takeyi akan ta tambaye shi ina Danish amma ina takasa furtawa...

Kamar taj ya karanci abunda ke zuciyarta sai taji yace"Daughter, labari me dadi, dan uwanki Danish ya fara koyon rubutu da karatu a wurin chief, abun saiya baki mamaki yana da kaifin basira, kamar ke lokacin da kina ?arama, kwakwalwarsa tana ja, abun burgewa sun shaku sosai da chief in kika gansu kamar ?an uwan juna, tare sukeyin komai......." batasan ya akai ta tsinci kanta da sakin murmushin gefen fuska ba, har cikin ranta taji dadin jin labarin nan da daddynta ya bata..

"Daddy, na taya shi murna, kuma naji dadi wlh, Allah ne kadai zai iya biyan chief, yayi mana hallacci arayuwar mu, ina jin dadin kyautatawarshi agare mu, Allah yasaka mashi da mafificin Alkhairinsa....." addu'o'i ta cigaba da yi mashi daddynta yana amsa mata da ameen

Kafin daga bisani yace"daughter, ki koma bacci, bana so ki makara sallar asuba, kiyi addu'a kafin ki kwanta sannan ki kula min da kanki"

"Toh daddy, kaima ka kwanta kayi bacci, ka kula min da kanka" bayan sunyi sallama da juna, kasa motsawa tayi daga cikin toilet din, wani irin yanayi take jin kanta mara misaltuwa, tanaji aranta kamar tayi missing din wani abu da zuciyarta take muradin son gani, ta wani bangaren taji dadin labarin cigaban da danish ya samu sosai har wani dan murmushi ta saki

Lumshe idanu tayi tare da jingina bayanta jikin wall na tsawon mintuna kafin ta juya ta buWe kofar, cikin sanda take tafiya tana satar kallon gadon benazir, ta lullu6e jikinta da bargo da alama ta koma bacci, hakan ba karamin dadi yayi ma unaisah ba..
Kan gado ta haye ta kwanta tare da jan duvet tayi covering jikin ta wani baccin ne ya kuma daukarta...

_________________________________
'?

*Hajjaty*

Tun da sanyin safiya bugun kofa Ya farkar da ita, tana tsaka da jin dadin baccin ta, da wata irin kasala ta mi?e ta sauko daga kan gadon tayi mi?a haWi da yin hamma, ?ar rigar bacci ce a jikin ta, sai da ta fara daukar hula ta lullu6e kanta kafin ta nufi kofar tana tambayar wanene"?

Daga waje tajiyo muryar sofia cikin tashin hankali tace"Aunty ni ce sofia, ki buWe min kofa" da sauri hajjaty ta buWe kofar ta le?a kai tana kallon sofia wadda gaba Waya babu kwanciyar hankali atare da ita ..tunkafin taji me zata faWa mata gabanta ya fara faWuwa.

"Sofia! Meke faruwa ne? naganki kamar ba lafiya"? Yarfa hannu safiya tayi murya na rawa tace"marwa! Aunty mun shiga uku, kizo kiga abunda ke faru ! Marwa ta kuturce. .." aruWe hajjaty ta ce"bangane me kike nufi ba? Meya faru da ita? Wata irin kuturta . "? Bata jira hajjaty ta kare maganar ba, taja hannunta da sauri suka nufi dakin marwa dake anan corridor din da Wakunan house maids din gidan su ke..

Shigarsu ke da wuya hajjaty tayi arba da ?an aikin gidan gaba dayansu, sun hallara, fuskar kowan nansu sharkaf da hawaye cikin tashin hankali suke sallallami idanunsu akan marwa.

Suna ganin hajjaty suka buWe mata hanya don taga abun tashin hankalin da suke kallo,
Lokacin da ta sauke idonta kan marwa dake nannaWe kan katifarta rass taji gabanta yayi mata wani irin mahaukacin bugu na tashin hankali, ta waro idanu waje, agigice ta daura hannayenta biyu saman kanta, ta zabga salati tana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'u!!

la66anta na kerma ta furta"Mar..marwa! Meya faru dake? Ya akai kika koma haka? ta faWa tana kallon yatsun marwa da suka dunkule irin na kutare ga wani ruwa mai yau?i dake gangarowa ta tsakaninsu,, la66anta sun shafe babu hudar baki kamar ba'a ta6a halittarta da shi ba, wani irin nishi take saki, idanunta sun kaWa jawur ga zufa data wanke jikin ta baiwar Allah ita kadai tasan azabar da take ji, sai faman zare na mujiya takeyi jikin ta nata kerma.

Fashewa hajjaty tayi da kuka, gaba daya sautin koke koken su Ya cika dakin
"Wayyo Allah! Na shkga uku! Dan Allah ku fadamun meya faru da ita? kaina ya kulle nagaza yarda da abunda idanuna suke nuna min! Jiya jiyan nan mukayi aikin dinner tare da ita lafiya lou muka rabu da ita...taya akai ta samu wannan lalurar ta kuturta? Ina bakinta yake"? Cikin shesshekar kuka tayi maganar
Abla tace"Aunty bamusan meya faru da ita ba, yau da safe mun tashi zamu fara aikin breakfast, mun ga bata fito daga daki ba, shine nace ma sofia taje tayi mata magana kada mu makara, bayan tafiyar sofia har mun fara aiki muka jiyo sautin ?ararta daga dakin marwa shine muka taho da gudu mu duka dan muga mike faruwa a nan muka tarar da marwa cikin wannan halin.. ." ta ?are maganar tana kuka
Sofia tace"wlh bansan meya faru da ita ba, Nima haka na sameta, ina shigowa dakin na isketa a nannaWe kan kafita, har ina zolayarta nace mata bana son iya shege kina ji inata ?wala maki kira kinyi shiru baki ce min komai, wlh aunty dana zo gaban katifar naga hawaye idonta gashi babu hudar baki, yatsun hannunta sun kuturce bansan sa'adda na fasa ihu ba, ni ban ta6a ganin tashin hankali irin wannan ba, Allah daga gani Aljanune suka shafe ta . ..." gaba daya duk sunbi sun ruWe, hankalin su Ya tashi, jikin hajjaty na 6ari tace"ba kallonta yakamata mu tsaya munayi ba, bari inje in sanar da mutanan gidan..." da sauri ta fuce daga dakin... .

Kafin wani lokaci gaba Waya mutanan gidan suka hallara a dakin marwa, da sauri maids din suka basu hanya don su shuga ciki, baba obie ne kan gaba jikin shi sai 6ari yakeyi, Pravin da twins suna abiye da shi, har sunyi shirin zuwa office wannan abun tashin hankalin Ya ris?e su, hada Hajiya saratu ta shigo ta zumbula buba ajikinta, sai faman raba idanu takeyi tun kafin ma taga meya faru da marwan!!

lokacin da sukayi arba da marwa gaba Waya hankulansu suka tashi, sunyi matu?ar razana da ganin yadda halittar marwa ta canza, kowa sai tambayar ba'asi yakeyi, Tafa hannu hajiya saratu tayi"La'haula walakuwata illa billahil azim! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni filmusibati.. Gaba Waya tabi ta rikice, "Ya akai Haka ta faru? Wata irin lalura ce wannan"? Ta faWa tana zare na majuya
Masu aikin suka hada bakin wurin fadin wlh bamu sani ba, haka muka same ta,
Idan hankalin su twins yayi dubu toh ya tashi, wani irin ?yan?yami da ?yamar marwa ne Ya kama su, babu wanda Ya lura suka sa6e daga dakin suka yi tafiyar su don bazasu juri ganin tashin hankalin nan ba.
Tsabar tashin hankali da kiWima Ya hana baba Obie furta kalma, dama da ?ar cazbahar shi a hannu sai faman jan ta yakeyi yana ambaton sunan Allah
Pravin dake a ru?e da kofa fuskar shi a hautsine Yana ta faman zazzare idanu kamar na kwarton muzuru har wani gumi Ya haWa muryarsa na rawa yace"yarinyar nan ba ta rasa iskokai akanta, daga gani aikin aljanune, taya za'ace farat Waya mutun ya tashi ba baki? yatsu kuma sun kuturce"?

Jin wannan maganar Ta pravin Yasa hankalin hajiya saratu yayi mugun tashi, nan fa ido ya raina fata, dama a tsorace take da lamarin, baban tashin hankalinta kada itama abun ya shafeta, tunda kwana nan suna mutunci da marwa saboda aikin le?en asirin da take yi mata, batare da kowa Ya lura ba, ta lalla6a ta fuce daga dakin marwa, jiki na kerma ta koma bedroom dinta, ta yi shirin zuwa office don ta bar gidan, saboda rashin tausayi maimakon ta tsaya su nema mata mafita tunda dai ita takeyiwa aiki
Baiwar Allah marwa ba halin Yin magana, kukan zuci take mai Wacin gaske, ga abu tana so ta fada amma takasa sai kallon hajjaty da pravin takeyi hankalin ta yafi kakarta akansu

Dakyar baba obie Ya haWiye tashin hankalin shi, Ya dubi maids din dake kuka cikin sanyin murya yace"kuyi hakuri ku kwantar da hankalin ku, ba kuka yakamata kuyi mata ba, addu'arku take bu?ata..." ya fada tare da kallon Hajjaty"ku taimaka ku dauko ta, muje asibiti aduba lafiyarta. " da sauri hajjaty da Abla suka haWa karfi wurin cuccu6ar marwa suka fito daga dakin sauran masu aikin suka bi bayansu, tunkafin su fito baba obie yayi waya da Waya daga cikin jami'an gidan, Aka fiddo da mota mai kama da bus, aciki suka shigar da ita, kowan nan su Ya samu wurin zama, motarsu baba obie da pravin tana abiye da tasu a jere motocin suka fuce kaitsaye suka nufi asibiti=??? tunkafin sukai asibitin marwa take ta kallon hajjaty kamar zata hadiyeta ita kanta hajjatyn dake aruke da ita tayi matu?ar tsorata da kallon da marwa keyi mata ga wani nishi da gurnani da takeyi=?"?

(Tashin hankalin da ba'a saka mashi ranaS'W')

__________________________________
'?

A zaune take kan dinning chair, ta sanya abaya dogo ajikinta, table din gabanta cike Yake da kayan breakfast ita kadai ta rage a dining, tana cikin shan tea a cup, ?amshin turaren dr shureim Ya daki hancin ta, da sauri ta Wago tare da kallon inda take jiyo sautin tafiyarshi, a tsanake Yake tafiya cikin kamala, Ya sanya shadda a jikin shi ta zauna mashi yayi wani fresh da shi hannun shi ru?e da car key,
Tunda ta kafe shi da ido sam ta kasa daina kallon shi, saboda yayi mata kyau
Karasowa yayi gaban dining din, fuskarshi dauke da murmushi Ya furta"sanyin idaniya, ina fata kin tashi lafiya"? Farfari tayi mashi da ido hadi da sakar mashi murmushi kafin tace"hubbyna na tashi lafiya, ina fata kaima haka"
Yace Alhamdulillah,
"Yaya shurem, Ka zauna mu yi breakfast, ko ka riga da kaci ne? Yau ni kaWai na rage a dining, ban iske kowa ba .."
"Bana jin yunwa, Inason zan fita ne" yanayin fuskarta ne Ya canza, kamar zata fashe mashi da kuka tace"dan Allah ya shureim kada ka tafi kabarni agida ni kadai, kaga mommy ta tafi office, daddy da uncle sun je party meeting, kullum sai ni kadai kuke bari agida bana aikin kome" ta faWa da shagwaba...
Shiru yayi yana tunanin meya kamata yayi? Shi ma baison suna tafiya su barta agida ita kadai baisan ya zaiyi da ita bane tunda bata son zuwa asibiti wurin Benazir, gashi har benazir ta fara tambayar shi ina zeenatu, itama hajiya layla abun ya fara damunta duk in yaje sai tace wai meya hana zeenatu zuwa.
Wata dabarace ta fado mashi aranshi, da sauri ya dubeta ta kura mashi blue eyes dinta masu walwali
"Zaki rakani mu tafi atare inda zanje"?
"Ina zamuje"?
"Wani wuri ne..." shiru tayi jim kafin tace"ni dai saika fadamin ina ne"
"Yawon buWe Ido" waro ido tayi kafin tace"dagaske"? Jinjina mata kai yayi alamar eh, da sauri ta mike tana fadin"yaya shureim bari naje na canza kaya"
"Okey, ki same ni a mota, but karfa ki dade" amsa mashi tayi da toh, jikinta na rawa tsabar zumudi ta nufi part dinta
Murmushin gefen fuska shureim ya saki aranshi ya furta"yau zanga meke akanki my zeenati"! Ya faWa tare da juyawa ya fuce daga falon

After some mins, Yana zaune a driver's seat, Ya dan jingina kanshi jikin headseat, har ya lumshe idanun shi Yaji motsin buWe car door, A hankali Ya kalli zeenatu dake kokarin shigowa ciki, wani irin sanyayyan kamshin turarentane Ya ratsa hancin sa, kamar wadda zataje gasar miss world, wata hadaddiyar emirati abaya ce ta sanya launin yellow, abunka ga jinsin turai ta fito fara fess rigar tayi mata kyau, ga wani veil da tayo rolling, hannunta ru?e da wayarta, kafarta kuwa wasu highhills ne masu tsini, harta zauna dr shurem bai daina kallon ta ba...
Farfari tayi mashi da ido voice dinta da shagwa6a tace"yaya shureim wannan kallon fa" kayataccen murmushi ya sakar mata, tare da kai hannu ya shafa sajen shi, key yai wa motar, ya Wanyi reverse kafin Ya fara driving slowly Ya nufi katafaren gate din gidan, tunkafin Ya karaso waWannan Samudawan security office din suka yunkuro kamar zasu rufe motarshi da bugu ba don komai ba sai don saboda Ya dauko zeenatu...
Ba arziki yayi parking motar, ya sauke glass din Yana kallon su
da kakkausar murya daya daga cikin su Yace"da iznin wa zaka fita da ita.. " saboda karfin hali na dr shureim Ya wani hade fuska Yace"daddyn ta ne Ya bani izni" arude zeenatu ta kalle shi wato taji ya shureim yayi karya agabanta
"Amma mu bai fada mana ba"!
"Ku kira shi awaya sai kuji" ya fada yana ?ara tamke fuskar shi
Kiran alhaji musa sukayi wayar tayi ta yin ringing ba'ayi picking ba, dr shureim Allah Allah Yake kada Alhaji musa ya Waga, kai hada addu'a yayi a zuciyar shi, cikin sa'a bai Waga ba..
Muryar zeenatu na kerma tace"ku kira mommy ku tambayeta, ay itama tasan da zancen fitarmu, daddyne ma yace ya tafi dani..." ba suyi ?asa a gwiwa ba suka kira hajiya saratu bugu uku kafin suka samu ta Waga...
"Ranki ya dade, da izninki dr shueim zai fita da zeenatu"? Kallon juna zeenatu da dr shureim sukayi duk suka sha jinin jikin su, fargabansu kada hajiya sarah ta kwafsa masu

"To amma shi yalla6ai yasan da fitar su?
Hajiya sarah tace"eh ya sani, kawai ku barsu su tafi"..kusan atare dr shueim da zeenatu suka sauke ajiyar zuciya.. munafukan gate officers din ba don sunso ba suka basu hanya, dr shurem Ya ?ara wa motar gudu Ya fuce daga gidan....

Lumshe idanu zeenatu tayi tana dariya tace"ya shureim kasan Allah da ace daddy ya Waga kiran nan da sukayi mashi wallahi bazai bari ka fita dani ba, ni narasa gane dalilin dayasa yake kullena kamar wata matar aure..."
"Mommynki ta rufa mana asiri wlh, naji dadi my zeenatu, kinga yanzu zamu sakata mu wala..." yai maganar hankalinsa na akan driving din da yakeyi, A hankali ta daura hannunta saman dayan hannunshi gefe tare da lumshe idanunta, har satar kallon ta sai da yayi kamar wata jinjira komai nata burge shi yakeyi...

________________________________
'?

Gaba Wayansu sun shirya tsaf, zasu ziyarci gidan uncle abdallah, tun daga kan mami, ummi, zahra, abi, da uncle Wan iya, kowannansu ya Wauki wanka na mutunci namu na hausawa, mutun biyu ke babu a cikin su, mahboob wanda tun safe ya tafi kai baby junaid school, har yanzu bai dawo ba..
A tare suka fito daga falon gidan, suka nufi harabar ajiye motocin su,
Mami tace"yau dai Allah Ya nufa zamu cika mata alkawari, baiwar Allah mun saka mata rai, kullum ayta za'aje za'aja amma shiru.." ummi tace"nasan zatayi farin ciki idan taganmu kwanmu da kwarkwatarmu don ma babu junaid, ay da sai tafi jin dadi munzo mata da Wan jikallan ta..." .murmushi kowannansu Yasaki,
A bakin motocin suka dakata da yin tafiya, suna jiran Aneelerh da zahra su fito,
Abie Yace"wai zaman me sukeyi agidan? Kwalliyar ce har yanzu ba'a gama ba?
Uncle Wan iya yace"da rabon mu tafi mu barsu agidan sun taho daga baya, dama tafiya indai da mata za'ayi ta to fa sai an 6ata lokaci, su komai nasu da nawa babu karsashi..." ya faWa yana haWe fuska....

Acan cikin gidan kuwa, fitowa zahra tayi ta dauki wankan atampa, an yafa veil a kafada, hannu ruke da jaka, ta ca6a uban ado, dakin aneelerh ta nufa, kafin takaiga kofar dakin sai ga Aneelerh fito cikin sauri, wata hadaddiyar lafaya ta laga a jikin ta,launin orange mai adon stones, ta fito Wass abunta, itama ta ruko handbag din ta, zahra na ganinta taci burki tana fadin"Aunty aneeleeh! kinga yadda kikai kyau? Meyasa baki fadamin lafaya zaki sanya ba nima ay saina sanya nawa" ta fada tana hade fuska, murmushi Anila tayi"kai zahra ay kin ma fini kyau, kinga su abie suna jiranmu, mu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login