Showing 111001 words to 114000 words out of 413917 words

Chapter 38 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2670

acikin gidan kurkukun kaddara zata neme sa da sunan bashi gudummuwar tarwatsa kurkukun ?addaraS'

Knocking kofar room dinsa akai da sauri Ya daidaita nutsuwarsa kamar wani abu bai ta6a faruwa ba...

Yayi zaton unaisah ce sai da yaje gaban kofar ya buWe karaf idanunsa suka sauka akan chief owais Ya Wauki wanka cikin shiga ta kakinsa Yayi shirin zuwa Office, from head to toe Ya kalle sa kafin Ya haWe fuskarsa bakomai Ya tuna ba face unaisah da ya gani adakinsa jiya shiyasa ya ?arajin haushin mutumin

Chief owais baibi takansa ba Ya nufi cikin dakin hannunsa ru?e da shopping bag, Ya dire masa ita kan gadon shi

A hankali Ya juyo suka fuskanci Juna

"Ba ka Iya gaisuwa ba ne"? wani Wan iskan kallo danish Yayi masa

Murmushin gefen fuska chief Yai

"Laifin me na maka kamar baka kaunar gani na"?

Shiru yayi bai tanka masa ba

Da ace chief yasan unaisah ce Silar dayasa danish Yake haWe masa rai ay da tuni Yayi masa bayanin da zai kwantar masa da hankalinsa don shi A yanzu mace bata agabansa, burinsa ya gano miyagun gidan kurkukun ?addara da kuma kawo karshen su shi ne abunda Yasa agaba

kallon shoppin bag din yai alamar yana neman ?arin bayani yaga bakon abu adakin sa

"It's a gift from Uncle Hateem. Please don't break them they're not toys," he said jokingly. tare da buWe jakar ya soma fiddo da kayan cikin ta

"suna da amfani, idan ka bani dama zan nuna maka yarda zakai amfani da su" cikin lallami yakeyi mashi magana

Ganin Yayi tsaye Yaki matsowa Ya duba kayan, Yasa chief Tunkararsa Ya ru?o hannunsa Ya janyo shi har bakin gadon

"Zuwa anjima zan ware mana lokaci in fara koya maka Yadda zakai amfani da su ko baka so"? Yai maganar Yana dubansa sai wani shan mur Yake.

Daurewa kawai cheif yakeyi amma fa ya fara hasala da halin danish kwata kwata baya sakar masa fuska kuma Ya?i magana da shi, in banda ma Yana neman alfarma awurinsa ay da bai kai matsayin da chief zai kulasa ba

Fucewa yai daga dakin Ya Bar danish a tsaye Ya kasa ta6uka komai, zuciyarsa har yanzu bata daina ambaton sunan jeremiah ba, kalaman tsohuwa Khala sun tsaya masa aransa sai yake ganin kamar amafarki ta bayyana..

zama yayi gefen gadon Ya zubawa kayan ido har cikin rashi Yaji dadin jin cewa Hateem ne Ya bashi kyautarsu, duk da baisan amfaninsu ba amma sunyi mashi kyau, bai ta6a ko Waya ba, ya yanke shawarar sai unaisah tazo zasu buWe su atare

________________________________
'?

*ANEELERH*

"Mu tafi asibitin kawai, bazan Iya jurewa ba...." gani take kamar zata rasa benazir, shiyasa ta hakura da shiga estate din
Su mahoob daman hanyar da zasu tafi suke nema, jiki na 6ari Ya buWe motar Ya zauna a driver's seat, Aneelerh ta shiga ciki, Zahra na kokarin shiga kwatsam ta hango dankareriyar motar dake tunkaro estate din dakatawa tayi saboda ranta na bata cewar Motar Hajiya saratu ce....

"zahra ke muke jira ki shigo mu tafi" acewar mahboob
"KaWan jira, naga kamar motar Hajiya saratu ce ke tunkaro estate din..." jin wannan maganar yasa Aneelerh yin hanzarin fitowa daga motar shima mahboob Ya fito duk suka ?urawa motar ido cike da sa ran ganin wanene a cikin ta

Lokacin da motar ta kusa ?a????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
rasowa dab da inda suke gudunta ya ragu slowly window glass dinta na back seat Ya zuge hakan Ya basu damar ganin na cikinta
Wata irin nauyayyar ajiyar zuciya zahra ta sauke mai haWe da annurin farin ciki
Ita kanta Aneelarh ajiyar zuciyar ta sauke haka shima mahboob duk da basu ta6a ganinta ba Yau ne rana ta farko da suka fara ganinta ido da ido
A hakimce take zaune cikin motar, ta Wauki wankan lafaya, idanunsa na a manne da farin glass ba karamin kyau yayi mata ba

Da alama su take kallo, Umarni ta ba security din dake driving dinta idan sun karasa kusa da motar su zahra yai parking, ya amsa mata da toh

Daga bayan motarsu zahra yayi parking din motar, jiki na 6ari zahra ta nufe ta, a lokacin ta bude car door din ta zuro kafarta Waya waje
Sallama tayi mata cikin girmamawa tace"sannu da zuwa mommy, ya gajiyar aiki...."

Fuskarta da fara'a ta furta"lafiyalou daughter, zuwan bazata akai mana? Amma ya akai naganku a waje..."
Zahra kamar zatai mata sujjada tsabar yadda take magana cikin ladabi da biyayya

"Masu tsaron gate din ne suka hana mu shiga sunce dole sai an basu izni, har layinki na kira baya shiga nasan kin shiga busy ne..."

"Eyyah! Na sanya wayar a silent lokacin da zan shiga meeting...' tai maganar tare da kai dubanta ga su aneelerh"su wanene? Ina fata dai lafiya? Ta fada cike da son jin karin bayani

"Auntyna ne da ?anina mahboob, wani abune mai mahimmanci Ya kawo mu .."
da sauri Aneelerh da mahboob suka karaso bakin motar hajiya saratu cikin girmamawa suka gaishe da ita, fuskarta asake ta amsa masu wato sunci albarkacin zahra shiyasa ta sakar masu fuska

"Pls kuyi hakuri sun shanya ku arana, Yanzu ku shiga motar, mu tafi. " wani irin dadi Ya lullu6e su, da sauri suka nufi motarsu, bayan sun shiga a jere motocin suka nufi cikin estate din babu wanda yayi gigin dakatar da su cikin securities din sai ma gaisuwar da suke mika ma hajiya saratu wadda ko kallo basu ishe ta ba.

Bayan sunyi parking, kowan nan su Ya fito, Aneelerh sai faman satar kallon katafaren estate din takeyi kamar a dubai, Inaga mahboob wanda Yake ta jinjina kai aranshi Yace"Wai dama haka daular obie estate take? Gari guda, TabWijan Daga gani anyi almubazzaranci wurin ginasa, Mutane kamar bazasu mutu subar duniya ba? Yo ni Allahna na tuna ko amafarki ban ta6a ganin katon gini irin wannan ba! Kai jama'a..sai faman santi yakeyi acikin ranshi
Gaba hajiya saratu tayi da sauri suka bi bayanta, zahra hada kar6ar handbag dinta ta ru?e mata ita, irin fadancin nan
Ashe mahbbob baiga komai ba, suna shiga falon kiris Ya rage ya zabga salati saboda ganin makurar kayan alatun da aka baje ta ko'ina...har wani zazzabi yake ji ajikin shi
Ga masu aiki dake kai komo cikin uniform
"Bismillah ku zauna, Ku Wan bani mintina kaWan, Yanzu zan fito..' amsa mata sukai da toh, ta nufi daki zahra tabi bayanta don ta kai mata handbag dinta..
Ya rage saura mahboob da Aneelerh, zama sukai akan tamfatsa tamfatsan royal sofa din falon...
"Karshen duniya yazo aunty aneelerh" ya faWa yana kishingiWa bayansa jikin sofa, duk da halin damuwar da Aneelerh take aciki sai da Wan murmusa jin abunda Mahboob Yace, ita kanta ta girgiza da ganin katafaren ginin
"Alhamdulillah Ya Allah.."ta furta aranta"Ya Allah kamar Yadda ka bamu ikon shiga gidan nan lafiya, Ya Allah ka bamu ikon ganin Yarinyar nan cikin sa'a ba tare da mun sha wahala ba" har cikin ranta wani irin sanyi takeji, fatanta Allah Yasa su dace
Kallon mahbbob tayi wanda ke ta bin ko'ina da kallo baki asake kamar lehen sakarai
"Mahboob! Pls kaja aji mana, kada kai mana kauyanci, duk fa abinda suke da shi mu ma muna shi agida...." tashin Farko Ya ce"muna da lifter..? murmushi aneelerh tayi"a'a amma ai akwai stairs ko"?
Girgiza kai yai"ba irin wannan ba duba fa kiga ni har hawa uku, ga yan aiki ta ko'ina..." murmushi tayi tana kallon shi" nifa aunty aneelerh bawai kyawun gidanne Ya ruWe ni ba, no kawai almubazzarancin da akai wurin ginasa shiyafi komai 6ata min rai, Allah ba karamin mai imani bane zai zauna agidan nan kuma yaci gaba da yin sallah..." yar dariya Aneelerh tayi
Kafin wani Ya ?ara magana sofia ta nufo wurinsu hannunta ru?e da tray na cool drinks tare da snack ta ajiye masu kan table
"Inayi maku barka da zuwa" amsa mata sukai da yawwa
"Hajiya saratu ce, ta bada umarnin akawo maku drinks, idan akwai abun da kuke bukata ku sanar dani..." har suna haWa baki furta"a'a mungode,
Bayan ta bar wurin Mahboob Yace"munci darajar Zahra wlh da ko kallo bamu ishi matar can ba, daga ganin ta zatai ji da kai..."

Bayan wasu ?an mintuna, Hajiya saratu ta fito har ta canza kayan jikin ta, wata hadaddiyar abayace ta sanya, zahra na abiye da bayanta har suka karaso, zama tayi kan sofa tana fuskantarsu, itama zahra ta zauna.

?ara gaisawa sukayi kafin ta ce"Zahra ta faWa min abune mai mahimmanci Ya kawo ku! ina sauraronku..." cike da dattako tayi maganar.

Gyara zama Aneelerh tayi cikin nutsastsiyar muryarta ta fara kora mata jawabin abun da Ya kawo su...

bayan ta kammala hajiya saratu tayi jimm na Wan wani lokaci kafin ta dubeta"kun tabbata Yarinyar ce? Shiru sukayi ta kuma cewa" Bana so asamu matsala! Ba ku tunanin ko mai kama da ita ce..."?

Duk da ?warjinin da hajiya saratu tay wa aneelerh hakan bai hanata Yin karfin halin furta"muna sa ran itace, saboda ni tamkar uwa nake agareta, Yau shekara shida zuwa bakwai da 6atanta kamar Yadda na fada maki, kuma sunan yarinyar Unasah kamar yadda itama yarinyar da shi owais din yake ru?o sunanta unaisah, amma muna kiran ta da Angel sunan da daddynta Ya sanya mata..." da kwarin gwiwa Aneelerh tayi maganar don ji take zata iya komai akan yarinyar nan
Numfasawa hajiya saratu tayi abunka ga mace mai izza, bata son abunda zai jawo raini tsakaninta da chief gani take kamar zubda girmane ta nemi alfarma awurinsa shiyasa take jinjinawa lamarin da suka zo mata shi, duk da tana son taimaka masu.

"Ina hoton Yarinyar, Ina son ganin shi" cikin sauri zahra ta buWe mata hoton awaya ta mu?a mata.

Bayan ta kar6a ta kurawa hoton ido nan take ta gane fuskar yarinyar cikin yaran da owais yazo da su wurin dinner.....

"Ina hoton ita Yarinyar ta wurin ku"? Ta faWa tana kallon Aneeelerh, yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin saurin curo wayarta daga cikin handbag ta buWe hoton Angel ta yunkura taje gaban hajiya saratu ta mi?e mata wayar

Bayan ta kar6a ta jera wayar zahra da aneelerh akan table din gabanta, a tsanake take nazarta hotonan ita kanta ta gasgata abunda suke hasashe komai iri Waya, banbanci ita yarinyar da uwais Yake ru?e ta fi angel dinsu girma amma duba da tazarar shekarun da yarinyar ta 6ace zai iya yiwuwa itace ta?ara girma...

Gaba daya hankulansu Aneelerh akan hajiya saratu duk sun kagara da son jin me zatace masu..

Bakomai take jinjina mawa ba face ta yadda zata zubda girmanta wurin yiwa owais magana, saboda basa jituwa tun time da ta fahimci bai kaunar mijinta, kuma tana jin haushin Yadda ake nuna wariya tsakanin Twins dinta da shi

"Dan Allah ki taimaka mana kamar yadda Allah Ya taimake ki, wallahi baki ga halin da mahaifiyar yarinyar take a ciki ba, yanzu haka tana agadon asibiti kwata kwata bata a cikin hayyacinta, sunan mijin ta da yarta kadai ta ke Iya ambato..."

muryar Aneelerh ce ta katse mata zancen zucin nata

"Meya same ta ne? Ko kina nufin tsawon lokacin da yarinyar ta 6ace bata a cikin hayyacin ta..." ta jefa mata tambayar cike da sonjin karin bayani
Labari aneelerh tafara bata tun guduwar benazir da kuma dawowarta har izuwa kan abun da Ya faru jiya

Jinjina kai hajiya saratu tayi da alama abun Ya tsuma zuciyarta duk da bata nuna ba.

"Allah ya bata lafiya" suka amsa mata da ameen.

"Zan nema maku alfarmar ganinta, amma kafin nan ina bukatar ku bani zuwa gobe, kunsan yanayin aikinsu na jami'an sirri, kuma yaran kamar suna bincike kan case dinsu ne, ganinsu zaiyi wuya, dole sai na fara yin magana da shi....."

Aneelerh taso ace ta kira chief din awaya sunyi maganar nan take amma dole ta hakura tunda su ne ke nema awurinta dole su yi biyayya
A tare suka haWa baki wurin yi mata godiya.

har bakin motarsu hajiya saratu ta rakosu ta ?ara jaddada masu gobe zasuji daga gareta

Lokacin da motarsu ta haura kan titi, shiru babu mai magana a cikinsu,

"Wani jinkirin Alkhairi ne, muyi hakuri" zahra ce ta fada ganin damuwa na neman rikita auntynta
"Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa" suka amsa mata da ameen
Dai dai motarsu ta kusa shiga tankameman gate din asibitin saiga motar dr shureim tana fitowa daga ciki, kasancewar window glass din abude Yake da sauri aneelerh ta kwala masa kira Ya shureim...
Ya na ganinsu Ya samu wuri Yai parkin din motarsa, fitowa tayi da sauri ta nufi motar ta Wan zukunna bakin glass din tana kallonsa
Duk sai taji wani iri ba dadi ganin yadda fuskarsa tayi jawur idanunsa sun kumbura
"Yaya shurem Ya jikin benazir din?
"Da sau?i, amma har Yanzu bata tashi daga bacci ba...
"Allah Ya bata lafiya
"Ameen..." shiru sukai kafin tace"naga ka fito ko gida zaka koma ne..."
"Bani zan koma gida ba, zeenatu zan maida..." sai da yai maganar idonta Ya hango mata zeenatu dake zaune a backseat ta kifa kanta bisa gwiwowinta yatsun hannunta sai kerma suke daga gani babu nutsuwa atare da ita
"Ina fata badai wani abu Ya same ta ba"!

"Daddynta ne Yace amaida ta gida, shi ne take kuka"

"Allah sarki baiwar Allah...." cikin nuna tausayawa tayi magnar, zeenatu duk tana jinsu saidai bata jin zata iya dagowa saboda gaba daya fuskarta ta ca6e da ruwan hawaye..

"Ya ake ciki game da Yarinyar kun samu ganin ta..."? Ya jafe mata tambayar saboda abun na aransa
Nan Aneelerh ta sanar da shi Yadda sukai da hajiya saratu
Jinjina kai yai"in sha Allah gobe idan ta kiraku awaya tare zamuje estate din....ko su mami ban sanar mawa ba saboda bana so su sanya rai har sai mun tabbatar in itace....

"Shikenan Yaya shureim Allah Ya kaimu lafiya amma zaka dawo ko"?
"Ay dole na dawo aneelerh, Daga na kaita zan juyo..." Allah Ya dawo dakai lafiya

Sallama sukai ma junansu, ta tsaya tana kallon motarshi har ta 6ace ma ganinsa
Komawa tayi cikin motarsu, Mahboob Ya karasa shiga da su ciki tun kafin yayi parking yake ta faman jinjina kai Yana fadin anyi almubazzaranci wurin gina asibitin sai kace ba wurin jinyar marasa lafiya ba, komeye amfanin ?awata asibiti ...."
yana karasa yin parking suka fito da sauri suka nufi emergency ward sai da suka fara tsayawa wurin nurse's station bayan sun fada masu sunan marar lafiyar da suka zo dubawa, Waya daga ciki tayi masu jagora har dakin da aka kwantar da ita, kafin ma su isa suka hango Hajiya layla tare da Alhaji ubaid abakin kofar asitin suna magana atsakaninsu, fuskokin kowan nan su babu annuri sai tsantsar damuwa
Takun tafiyarsu Aneelerh ne Yaja hankulansu ga dubansu
"Aneelerh......" hajiya layla ta fada cike da mamakin ganin ta, ita kanta baza ta iya tuna rana ta karshe da tai tozali da ita ba.
Aneelerh na karasawa ta rungume hajiya layla batasan sa'adda kuka Ya balle mata ba
Shafa kanta hajiya layla tayi tana Wan rarrashin ta, hakika tayi mamakin ganin yadda ta kara girma rayuwa kenan andade ba'a hadu ba, tun da zumuncin su Ya watse
Tsawon mintuna hajiya layla tana lallashinta, kafin ta dago idanu jawur ta gaishe da Alhaji ubaid fuskarsa da fara'a ya amsa mata har yana Wan zolayarta
Aneelatu kece kika koma haka? ?ayanki nawa? Cikin shesshekar kuka tace Yarona dayane Yana a school,
"Allah shi raya shi,
Tace"ameen"
"Ya hakurin abun da ya faru da su Uzair"?
"Mungode Allah"
"Ubangiji Allah Ya bayyanar da su" ta amsa mashi da ameen
Hajiya layla tace"ki shiga ciki," da sauri ta shiga dakin,
Su zahra dake atsaye har suna haWa baki wurin Gaishe da su ita da mahboob suka kuma yi masu ya mai jiki
"Jikin da sauki bacci take, amma ku yan uwanta ne"?
"?a?an uncle dinta ne mu"
"Allahu akhbar kamar na ta6a ganinku da jimawa lokacin baku kai haka ba.."
Zahra tace"eh ay muna yawan zuwa joss lokacin baya..."
"Allah sarki ku shiga daga Ciki dan Allah kuyi mata addu'a' amsa mata sukai da toh
Bayan sun shiga, agaban gadon suka iska Aneelerh ta zu?unna kan gwiwowin ta, kanta akan gadon, hannunta acikin na Benazir, jikinsu duk sai yayi sanyi ganin yadda benazir ta faWa daga jiya zuwa yau har ta canza...
Har lokacin hajiya sarah na zaune kan kujera sallah kadai ke tada ta..
Gaishe da ita su zahra sukayi tare da yi mata ya mai jiki tace masu da sauki,
"Ubangiji Allah Ya bata lafiya, Allah yasa kaffarane" ta amsa masu da aneen
Gaban gadon suka tsaya kafin suka fara yi mata addu'o'i suna tofe mata jiki da su,.....
Kamar masu zaman makoki haka suka tasa ta agaba suna kallon ta.
Wureran karfe biyu da rabi ta farka kamar mai ta6in hankali haka ta dinga fusge fusge tana ambaton sunan taj da Angel, ta makance bata ji bata gani bata sauraren kowa hauka kawai takeyi masu, haka suka dinga rurru?e ta don kokari ma take ta sauko daga kan gado, su Aneelerh sun sha kuka ba kamar da ta furta"kada su bari ta mutu bata sanya yarta a idon ta ba, bata son ta mutu bata ganta ba, su taimaka ma rayuwarta....."
babu wanda bai zubar mata da kwalla ba, hatta mahboob Yaji tausayinta

Likitan dake kula da ita ne Ya shiga dakin tare da wasu nurses Ya bukaci su hajiya sarah su fita daga waje
Nan suka fito kowa Ya zauna kan waiting seat suna ta jiran tsammani

Tsawon mintuna Wuff suka daina jin sautin koke koken benazir, har sun fara fargaban meke faruwane sai ga dr adam Ya fito daga dakin tare da nurses din

Suna ganin shi kowa Ya mike suka nufe shi suna tambayar awani hali take ciki"?

Fuskarsa babu walwala Yace masu suci gaba da yi mata addu'a sannan su yi kokarin samo yarinyar da zata iya pretending amatsayin yarta daga yau zuwa gobe in ba haka ba sakamakon ba lallai Yayi masu dadi ba, don sunyi iyakar bakin kokarinsu amma abun yaci tura, Yanzu haka allurar bacci suka ?ara Yi mata....."

Hankulansu ba karamin tashi Yayi ba, nan fa suka fara shawarar Yadda za su samo Yarinyar dake kama da Angel ?ar fara mai launin ido ruwan toka..

Aneelerh tayi saurin cewa akwai wata yarinya da ta sani mai kama da unaisah, amma ko za'a same ta sai ya kai zuwa gobe...." ta fadi hakanne saboda tana sa ran gobe hajiya saratu zata kirasu inyaso koda yarinyar ba unaisah bace sai su nemi alfarmar abasu ita aro har zuwa time Win da benazir zata ji sauki...

Hankalinsu ba karamin kwanciya yayi ba, hajiya layla tsabar zumudi hada cewa me zai hana yarinyar tazo yanzu? In ma da bukatar suje gidan iyayenta neman alfarma sai suje..tace masu ay

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login