Showing 312001 words to 315000 words out of 413917 words

Chapter 105 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4586

a lokacin hajjaty tana adakinta tare da sauran yan aikin gidan sun hadu suna shirya mata kayanta, Baiwar Allah sai kuka take yi su kansu kukan sukeyi na rabuwa da ita, bayan sun kammala shiryata Hajjaty da Abla suka daukota sauran masu aikin na abiye dasu A harabar ajiye motoci su ka iske mutanan gidan sun hallara domin yi mata bankwana.

A lokacin bakowa marwa ke kallo ba face pravin dake ta kashe mata ido yana sakin wani dan iskan shu'umin murmushi duk idan ya fakaici idon mutane, marwa tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda bakin cikin zata tafi batare da ta tona asirin wanda yai mata aika aika ba..

har suka shigar da ita cikin mota bata daina gunjin kuka ba, haka ta dinga bugun window glass din motar da hannayenta kamar zata fasa shi.

babu wanda ya fahimci mai marwa take nufi, gaba daya sunyi tunanin zafin rabuwa dasune yasa take yin haka, har alkawari hajjaty tayi mata akan kullum zata dinga kiranta awaya sosai ta kwantar mata da hankali, bayan sunyi mata bankwana Akan idonsu Motar ta fuce daga gidan bayin Allah sunyi kukan Rabuwa da marwa.

Pravin kau ranshi fari tass Kamar ya zuba ruwa ?asa yasha Hankalin shi ya kwanta baida sauran damuwa, Ya kira zaid awaya yayi masu albishiri na tafiyar marwa, Ya kuma labarta masu maganar tafiyar da zai yi tare da baba obie, sannan Yace su dawo gida Yana son ganinsu kafin su tafi.

Bayan dawowar su twins, murna awurin hajiya saratu kamar ta shekera bata gan su ba, cos tayi kewarsu ko kaWan batai masu fadan zaman su a hotel ba, haka shima Uban saima tarairayarsu da ya ke yi.

Wuraren ?arfe shabiyu na yau, gaba daya Yan family din dake a estate din suka yi ma baba Obie rakiya zuwa Airport kamar wanda zai bar kasar, hada Owais da su Senate Lateef kowa da kowa, kamar karsu rabu da shi saboda kaunar da suke ma mahaifin su.
________________________
'?

(After One Day, Bayan kwana Waya)


Yana tsaye gaban Dressing Mirror, har ya kammala shirin xuwa Office, jikin shi sanye da kakin shi, fuskarshi kwata kwata babu walwala tamkar bai ta6a dariya ba, saboda matsananciyar damuwar data yi mashi ?atutu a zuciyarshi, Ga rashin isasshen baccin da baiyi ba jiya idanun shi sunyi ja sun Wan kumbura.

Har ya mi?a hannu zai Wauki watch daya daura gaban mirror kamar ance ya Wago da idanun shi ya kalli mirror Unexpected ba Ya hango shi tsaye ta cikin madubin Ya goya hannayen shi akan kirjin shi, Jean da t.shirt ne a jikin shi.

wani irin faduwar gaba yaji saboda bai tsammaci zaiga mutun adakin shi ba! Taya akai ma ya shugo bayan kofar tana da security? Zuciyarshi ce ta bashi amsa da cewa ka manta sihirin dake ajikin shi? A sukwane ya juyo tare da kallon shi..

Yadda kasan wanda Ya ku6uto daga gidan mahaukata, Sumar kanshi ta yamutse, Fuskarsa ba annuri kamar bai ta6a dariya ba.

hankalin Chief ba karamin tashi yayi ba, ganin yanayin da Danish Ya faWo Wakinsa, ya rasa meke damun shi? Yayi rashin lafiya ne? Kai daga ganinsa ba lafiya ba.


muryar shi da ruWani Ya furta"Danish? Meke damunka? Baka da lafiya ne"? Ya faWa akagare da son jin amsar shi.


Cikin sanyin murya yace"zan baku haWin kai, and I will lead you to the Prison of Destiny, I will help you fight them"

kamar amafarki yaji kalaman Danish saboda mamakin daya mammaye shi, hannu yasa ya Wan murza kunnan shi don ya tabbatar ba makuwa yayi ba yace"dagaske kake ko wasa"?


"I'm serious..." tsabar farin Ciki yasa chief zubewa kan gwiwowinsa yayi sujjada domin nuna godiyarsa ga Allah.

a daren jiya ya raba dare yana yin Nafilfili akan Allah ya shiga lamarinsu ya kawo masu hanya mafi sauki da zasu farmaki Elders sai gashi cikin ikon Allah yau da safe Allah ya kar6i addu'arsa.


Lokacin daya Wago daga sujjadar tsantsar farin cikine akan fuskarshi, mi?ewa yayi tare da nufar Danish yayi hugging Winsa tighly kamar zai maida shi cikin shi saboda faranta masa da yayi bai ta6a jin masifar kaunarsa ba irin na yau.


Dagowa yayi tare da dafa kafadunsa suka fuskanci juna.

"Danish, bazan Iya misalta maka farin ciki da nake a ciki ba, Ka faranta min raina, amma kai da kanka kayi ra'ayin ka bamu hadin kai ko wani ya tilasta maka? Saboda yanayin ka ya nuna kamar bada son ranka ba"

Girgiza mashi kai yayi ba tare daya furta kalma ba.

"Kamar baka da lafiya"? Ya kuma tambayarsa

"Lafiyana lou, just ask me anything you want to hear from me, and I'll tell you."

abun nema ya samu da sauri chief ya ruko hannun shi ya zaunar da shi gefen gadon shi.


Kafin ya dauki wayarsa Ya kira landline din kitchen Ya isar da sakon akawo mashi breakfast Winsa da baiyi niyar ci ba, amma saboda suji dadin tattaunawa da danish shiyasa ya umarci akawo mashi.

Ba'afi mintuna biyar ba, kuku ya shigo hannayenshi ruke da wooden tray sha?e da kayan abinci ya aje masu kan table kafin ya fuce daga Wakin.

"Nasan kana jin yunwa, mu fara yin breakfast, kafin mu fara tattaunawar tamu" girgiza mashi kai yayi"bazan iya cin komai ba.." bai ?are maganar ba chief ya katse shi"pls kada muyi haka dakai, ko kaWan ne ka ci"

matsa mashi yayi dakyar chief ya shawo kanshi, bayan sun kammala yin breakfast Win, Chief ya cire Coat dinsa Ya rage daga shi sai vest, babu zancen zuwa Office, zuwan Danish Yafi komai mahimmanci a halin yanzu.

A tsakiyar gadonshi suka zauna suna fuskantar juna kamar malami da dalibinsa, sai da ya fara kunna audio recording din wayarsa, kafin ya tattara nutsuwarsa da hankalinsa akan Danish


*Daga Al?alamin Boss Bature=?%?
'?*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 & 08103884440*
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: __________________________________=???
'?=??????=???



a ruWe ta kalli fuskar shi, ya haWe rai kamar ba daddynta ba, ta rasa gane meke faruwa da shi ne.

Babu wanda Ya lura da abunda Ya faru tsakaninsu, Hankalin yan uwanta baya akan su
Duk da haka bata kawo komai a ranta ba, ta kuma cewa, "Daddy, Chief ya fada maka an ga Danish a cikin toilet Winsa...." banza yayi da ita tamkar bai ji maganar ba, hakan ba karamin Waga mata hankali ya yi ba.

komawa tayi cikin yan uwanta jiki a mace ta tsaya zuciyarta cike fal da tunanin sauyawar daddyn nata, fatanta Allah yasa ba wani abu ke damun shi ba.

Walking slowly yake taka stairs, da karfi Jemimah ta furta sunan Danish hakan yaja hankulansu gaba daya suka kalli stairs din bakunansu a buWe saboda tsantsar kyan da yayi, wata hadaddiyar light grey thobe ce a jikinsa ta bi surar jikin shi, ya Waure sumar kan shi with hair ties, gaba daya sun shagala da kallon shi, ?asa-?asa da murya ummi ta furta Tabarakallahu ahsanil khalikin, Allah yayi halitta..."

A second to the last step na stairs Win ya Wan dakata da yin tafiyar jin alamun kamar ana kallon shi kafin ya Wago da ido ya dube su, motsin buWe kofar falo yaja hankulan su.

Gaba Waya hankalinsu ya koma kan masu shigowa, Big guy ne ya shigo da sallama a bakin shi, kafin U.s armies din suka shigo kowannansu suit ne a jikin shi...zuba masu idanu su ka yi kamar ba su gane su ba, sun yi shiru suna kokwanton anya su ne? Saboda basu tsammaci zasu gan su ba.

Dakatawa su ka yi da yin tafiyar suna kallon su kusan su shida suna jira suga reaction din su, Wani irin ihun farin Ciki Gabriel Ya saki, da gudu Ya nufi Lieutenant thompson Sojan daya taimake shi a dajin evil forest saboda sarkar cross din shi, kafin Ya ?araso thompson Ya bude mashi hannayen shi ya fada jikin shi yayi hugging din shi gaba daya suka fashe da dariya.

Wayyo Allah daWi da wani irin farin ciki sauran ex-prisoners suka nufe su kafin su ?araso suka mi?a masu hannuwansu don su yi hugging din su, aiko suna ?arasawa ?an matan suka ?i bari su yi hugging Winsu sai dai suka yi shaking hands, in ka cire jemimah da ta ma?al?ale Commender har saida ya Wauke ta, mazan cikin su suka yi hugging dinsu Waya bayan Waya, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki, sunyi mamakin zuwan bazatan da suka yi ma su.

Da tsantsar mamaki Unaisah ta furta"Commander James! Captain Lewis! Major Smith! Jackson Lee! ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Canal Harry! Lieutenant Thompson! What an astonishing reunion! Is this really a chance encounter?"

Dariya suka saki gaba dayan su, da fara'a commender james ya ce, "Indeed, it's us! We hope you're overjoyed to see us. We've come specifically because of you, and we hope you'll welcome us with open arms." (Yeah mu ne, muna fata kunyi farin cikin ganin mu, munzo ne saboda ku, fatan zaku kar6e mu hannu biyu..." )

bai ?are maganar ba suka haWa baki gurin furta, "We welcome you, most warmly! We're truly elated to see you!"

DaWi ne Ya lullu6e sojojin, sai kallonsu sukeyi gwanin ban sha'awa sunji dadin sauyin da sauka samu sun kuma jinjina ma Chief, su Hibba da basu san su wanene ba sai faman baza masu na mujiya su ke yi cike da son sanin su wanene su Win.

Captain lewis ne ya nuna su da hannunshi cikin harshen turanci ya ce, "waWannan sune sauran yan uwan naku"? A tare suka haWa baki gurin furta Eh, Tambayar sunayen su yayi Sajeed ne ya gabatar masu da su..

Yana zuwa daidai kan Deeja Commender Ya dubi Haris, "Is she your sister cos you look alike"

Yana murmushi yace Eh sister Winsa ce.

"She's the cause of his heartbreak" Unaisah ta faWa da zolaya, dariya sojojin su ka yi.

Major smith Ya ce,"Dear Angel, where is that handsome young man, mai nauyin bacci ban gan shi ba ko baya nan .." bai ?are maganar ba Thampson Ya ce, "nima abunda nake so na tambaya kenan, Ina Danish"? da yatsa Unaisah ta nuna ma su shi, yayi tsaye kan stairs, idanunsa na akan su, gaba Waya suka kai duban su gare shi Commender ya ce, "Har yanzu yana nan da ?yuiyarsa?"

ganin kamar baida alamun zuwa gurinsu ne yasa Unaisah yin saurin cewa,"may be bai gane ku ba ne," major ya sake cewa, "Mun riga da munsan halin shi ai, Ya bacci har yanzu yana yi ko ya daina?

Dariya suka saka gaba Wayan su, da ido Unaisah tayi mashi alamar ya zo gurinsu ganin kamar sun damu da son ganin shi.

Saukowa down ya yi ya nufe su, commender ya mi?a mashi hannu, "Danish, come here, I'm thrilled to see you! I hope you're safe and sound," ya faWa tare da yin hugging Win shi, In low voice ya furta, "I'm fine, ina yi maku barka da zuwa" ya faWa tare da raba jikinshi daga na commender ya bi sauran yayi hugging Winsu tare da yi masu barka da zuwa hakan ba ?aramin daWi ya yi ma su ba.

Big guy ne yace da su, "Mu shiga ciki, ku zauna ku huta." Hannayen su ru?e dana prisoners suka nufi falon, kafin su ?arasa Taj dake tsaye yana kallon su, Ya matso kusa da su suka gaisa da junansu, big guy ya gabatar masu da Taj a matsayin mahaifin Unaisah sun yi murnar jin hakan sosai, duk budurin da ake Ummi tana can gefe Waya tana yin waya har sai da commender ya hangota yana ganin bayanta ya gane itace, nufar ta yayi yana isa ya rungume bayanta, a Wan firgice ta juya don ta ga wanene ta haWe rai amma koda ganin commender James sai ta waro idanu cike da mamaki ta ambaci sunan shi, "Sir James, is that you? I'm surprised," ta faWa tana yar dariya

Sir james ya ce, "It's me, dear. Yesterday when we called, I hid the point of my coming because I wanted you to be surprised."


Murmushi ta sakar mashi, "I welcome you wholeheartedly I'm at a loss for words to express my happiness and how much I've missed you."

"I've missed you too, dear one. I'm overjoyed to see you." Ya bata amsa.

Ya yi zaton za ta yi hugging na shi amma sai ya ga akasin hakan, Taj da Big guy kuwa tun rungumar farko da commender yayi mata suka kalli juna, dama sun san za'a rina tun da su dabi'ar su ce yin hakan, a kan sofas suka zauna gaba dayan su, nan fa ex-prisoners suka fara cika su da surutu suna basu labarin abubuwan da suka faru bayan dawowar su Nigeria, suna tsaka da yin fira Chief Ya sauko down shima ya kimtsa tsaf cikin suit nasa, suna ganin shi suka mi?e da sauri commender ya nufe shi suka rungume juna a mutunce suka gaisa ya yi mashi barka da zuwa, kafin ya nufi sauran sojojin ya mi?a masu hannu suka gaggaisa.

Kowa na gidan tun daga kan Gate security Officers har Chefs na kitchen saida suka shigo falon domin yi ma ba?in Chief barka da zuwa, hakan ba ?aramin faranta ransu yayi ba ganin yadda kowa ke Wokinsu sai girmama su ake.

Batare da bata lokaci ba, Chefs suka shirya masu dinner a dining, duk girman table Win saida suka cika shi da kayan abinci kala kala.

Yau gaba Wayansu su ka yi dinner a tare da ba?in su, gwanin ban sha'awa su commender sun ji daWin karramawar da akai ma su, abun da yafi burge su yadda prisonsers suka saki jiki da su kamar irin sun haWa ala?a ta jini da su, hakan yasa suma suka samu walwala kamar suna a gidajen su na America, ga jemimah da ta yi ta basu nishaWi da surutunta, ta maida commender kamar kakanta, har abinci take bashi a baki, ta yi kane-kane akan laps din shi, Danish kuwa hankalinshi na akan Unaisah ya lura kamar akwai wani abu dake damunta saboda yadda take cin abinci kaWan kaWan kuma hankalin ta yafi karkata akan daddynta saboda shine damuwarta.

Bayan sun kammala cin dinner Win, wata sabuwar firar ce ta 6arke a tsakanin sojojin da su Chief har kusan ?arfe goma kafin Big guy ya raka su masaukin da za su zauna, duk yadda Unaisah taso ta gana da daddynta a daren ranar abun yaci tura tana ta jiran zuwan shi tasan ya saba duk in yana gidan dare yayi sai ya zo dakinsu yayi mata sallama kafin ya tafi amma yau taji shiru, koda ta fito bata iske kowa a falon ba, shima yayi tafiyar shi, da damuwa ta kwana a ranta.


Gidan Kurkukun ?addara=?%?
_____________________________
'?


Meke faruwa a gidan kurkukun ?addara? Saboda gabatowar gagarumin shagalin da zasuyi na black Night, sun fara shirye-shiryen tarbar wannan dare mai daraja a gurin su, Yanzu sun dakata da yin duk wani mugun abu da suke yi a gidan kurkukun, hatta fursinonin su sun yi mamakin sauyin da suka gani, lafiyayyan abinci suke basu mai rai da lafiya har sau uku a rana, bayan haka sun tsaftace Wakunan prisoners din da makewayin su sun kuma canza masu sabbin Uniform.


Duk da sauyin da suka samu, hakan bai saka su yin murna ba, saboda sun san da wata manufa a ?asa, wata wutar bala'en ce zata kunno kai, kamar ko sun sani dalilin dayasa suka sauya masu cimarsu daga ganye zuwa lafiyayyan abinci mai gina jiki, saboda albarkatun jikinsu su cicciko suyi ?iba fatarsu tayi kyau don su ji daWin aikata fasi?anci da su, a cikin abincin da ake kawo masu hada wata kwayar sihirin da suke saka masu a cikin dafaffen kwai, kamar sha ka fashe take aiki a jikin Wan adam walau mace ko namiji, cikin kankanin lokaci Yake ciko da duk wata ramar jikin su ya ha66aka jinin jikin su.

Lallai Elders Sun shirya ma Black Night..=???


Yau gaba Waya Sun fiddo da Prisoners din dake a kurkukun zuwa tsakar prison din, ko ina ka kalla sune birjik, sun jera layi, as usual jajayen uniform ne a jikin su, a yanzu babu masu black Uniform na ?an baiwa tun daga kan su Unaisah.

A ?alla fursinonin da suka rage agidan kurkukun ?addara zasu kai kimanin Wari uku da hamsin, daga ciki harda jariran da suke raino.

Yan matan suna asanye da short gown wadda bata wuci gwuiwarsu ba, mazan kuma riga da wando ne ajikin su, babu mai magana a cikinsu kamar gumaka sun ?ame a tsaye ko motsi basa yi, Iya ?wayar idanun su ce kadai take kyakkyaftawa sai numfashinsu dake fita.

Bakomai ne yasa suka nutsu ba, fa ce Giants Win dake a kewaye da su, Wasu irin gabza-gabza masu jini a jika.

sun kasa sun tsare sai suntiri suke umarni kawai suke Jira su aiwatar.

Cikin takun Izza Tsohuwa Inno ta nufo gurinsu hannun ta ru?e da sanda, kamar kullum a cikin shiga ta red gown take, daga bayanta Giants Win dake take mata baya ne, kan matakalar benan dake fuskantar prisoners Win suka dakata da yin tafiya, ta tsaya tana bin su da ?as?antaccen kallo.

har na tsawon mintuna batare data furta kalma ba, sai da ta mula ta sha iska kafin ta fara magana a a gadaran ce

"Duk wanda na kira lamba Win shi a cikin ku, Ya koma gefe Waya" ta faWa tare da nuna masu inda zasu tsaya da sandar hannun ta..

"Prisoner no twelve, Thirteen, Fourteen...' duk wanda ta kira sunansa, Jikinsa na kerma yake fitowa daga cikin layi ya tsaya gefe Waya, daga gani masu kyawun surar cikin su take za?ulowa waWanda suka zama matured.

Kusan fursinoni arba'in da takwas ta kira, mata sunfi yawa acikin su, saida ta kammala kiran lambobin waWanda ta zaba kafin ta furta prisoner no 100 shiru ba'a amsa mata ba, da alama ta manta aika aikar dasa giant yayi mata, tsawa ta daka masu, "baku ji ina magana bane? Where is she?"

Murya na rawa wata young adult daga cikin su ta yi ?arfin halin furta, "tun lokacin da kika sa Giant Ya tafi da ita, bamu ?ara ganin ta ba"!

Shiru tayi jim sai da yarinyar tayi magana kana ta tuna abun da tasa aka yi mata.

Giant Win dake a gefenta ta kalla, "Tana raye ko ta mutu?" Cikin girmamawa da wata irin buWaWWiyar murya ya ce, "Bani da masaniya, bayan na kaita Wakin fiWa kamar yadda kika bani umarni,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0