Showing 279001 words to 282000 words out of 413917 words

Chapter 94 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4509

cike da zumuWi ta mi?e, ta Wauko wayar Benazir ta fara laluban layin Azeezaty, sam ta kasa ganowa saboda batasan sunan da Benazir tay mata serving ba, amma da ta tuna Benazir ta fada mata jiya ta kira layinta bata samu ba, hakan yasa ta shiga call logs, lambar farko da akai ma saving da God Gift ta danna Call almost 3 times tana kira baya shiga, ba dan ta so ba ta hakura.

Lokacin da Benazir ta ?araso Garden Win tunkan ta ?arasa idanunta suka hango mata mutun uku zaune kan lallausar darduma kowannan su shadda ce a jikin shi.

bata iya tantance su wanene ba, saida ta isa wani irin burki ta ci ta dafe ?irjinta da hannu Waya da tsantsar mamaki ta furta, "ZAKI!"

Yana Jin muryarta da sauri ya Wago ya kalle ta, zumbur ya mi?e tare da ambaton sunan ta "Benazir!"

Hawaye ne suka ciko idanunta, tayi mamakin ganin shi, kuma tayi farin cikin ganin bawan Allahn nan ba zata ta6a manta halaccin da yayi mata ba..

Gaba Waya hankalin Sir mubarak, da na Alhaji musa ya dawo kan su, Sir mubarak na ganin Benazir a ranshi ya ayyana yanzu ya gane dalilin da yasa Zaki ya ruWe akanta, da alama dai Sir Mubarak ya yaba da kyanta.

Jinjina mashi kai tayi, "Yayana ni ce,"

Cikin sanyin murya ya ce, "Benazir baki kyauta min ba, kinsan irin tashin hankalin dana fuskanta saboda rashinki a kusa da ni.. " bai kare maganar ba, Sir Mubarak ya yi mashi gyaran murya atare suka kalle shi.
Cikin sauri Zaki Ya gabatar mata da Daddynsa, Cike da jin kunyarshi ta gaishe da shi, fuskarshi a sake ya amsa mata, tare da yi mata fatan alkhairi.

"Benazir, ki shiga da shi ciki." Alhaji Musa ne ya faWa fuskarsa a sake kamar ba shi ba, amsa mashi ta yi da toh, bata yi aune ba ta ji ya ru?o hannunta a cikin nashi kamar yadda ya saba yi lokacin da suna tare.

Fita su ka yi daga garden din, yace mata ba zai shiga gidan ba, yafi so suyi magana a cikin motarsa, ya buWe back seat na motar shi yace ta shiga, ji ta yi bazata iya yi mashi musu ba hakan yasa ta shiga ta zauna bayan shima ya shiga ya datse car door din, suka ?urama juna ido kamar yau suka fara haWuwa, sunyi kewar junan su sosai.

"Da ranki da lafiyarki Benazir, baki neme ni ba, kamar kin manta dani a rayuwarki, baki yi tunanin damuwar da zan shiga ba, kin tafi kin barni da kewarki kullum zullumina kina ina? Kin isa gidan iyayenki lafiya ko kuwa?"

Siraran hawaye ne suka wanke fuskarta, bata ji dadin halin da ta jefa shi ba, tasan sha?uwar dake tsakaninsu dole ya damu da ita..

"Ka yi hakuri Yayana na kaina, wlh kana a raina, ban manta da kai ba, kamar yadda ka damu da ni nima haka na damu da kai..." katse ta ya yi, "Amma meyasa ba ki neme ni ba?

"Ka manta wayata tana a hannunka?"

"Ba hujja bace Benazir, kin riga da kinsan wanene mahaifina a ?asar nan, kinsan family estate dinmu, why baki je can kin neme ni ba in har dagaske kin damu dani?"

Fuskarshi a yamutse ya yi maganar, kwarjini ya yi mata ta sunnar da kanta ?asa, tasan bata kyauta mashi ba..

"Me nayi maki dana cancanci hakan daga gare ki? Ko kin daina ?aunar yayan naki ne?" Yanayin yadda yake magana ba ?aramin karya mata zuciya yake yi ba, ga kamshin turarenshi da ya kanainaye hancin ta.

Da ?yar ta furta, "Na kar6i laifina, ban kyauta maka ba, amma ka yafe min, bazan ?ara maimaita kuskuren da nayi ba." Lumshe idanunshi yayi tare da sake buWe su kan fuskarta, matsawa yayi dab da ita da sauri ta ja da baya, har saida ya ?ureta jikin murfin motar .

Shafa fuskarta ya yi da tafin hannun shi, yana kokarin haWe bakinsu ta yi saurin kauce mashi, hakan ba ?aramin Waga hankalin shi yayi ba, saboda ta sauya mashi.

"Kin canza min, meyasa?" Muryarta na kerma ta ce, "Yayana ka yi ha?uri, ba halina bane, ko a lokacin da nake amince ma hakan bada son raina bane, sai don bani da mafita ne, kewar mijina ne yasa nake biye maka saboda in samu relief..." wani irin kishi ne ya ziyarci zuciyar shi, idanunshi suka kaWa nan da nan suka fara yin ja...

"Kin haWu da mijin naki?"

?aga mashi kai ta yi alamar eh,

Hankalin shi idan yayi dubu toh ya tashi, damuwa ce ?arara kan fuskarshi, ita kanta ta sha jinin jikinta da ganin yadda numfashin shi ke fita..

"Tayaya akai ka gano inda nake?"

Da ?yar ya furta, "Uncle Winki, abokin Daddyna ne,..." ta yi mamakin jin hakan.

A takaice ya bata labarin tun farkon dawowarshi abunda Ya faru har zuwa lokacin da Sir Mubarak ya kira Alhaji musa ya fada mashi lokacin da zasu zo ganin ta ..."

?iris Ya rage ta fashe da kuka saboda tausayinshi da ya kamata, bata ta6a sanin yana sonta ba sai yanzu da ya ke faWi mata, tayi mamakin zurfin cikin shi...

Ru?o hannayenta ya yi acikin nashi.

"Ki taimaki rayuwana, ban saba da wahala ba, bansan menene so ba, sai akan ki, ke shaida ce, mata basa a gabana, aikina kawai nasa a gaba, wlh bazan 6oye maki ba tun rana ta farko da na fara ganin ki naji na kamu da ?aunarki, shiyasa koda kika faWamin kina so ki yi nesa da kowa naki ban yi maki faWa ba, saima nayi maki hanyar da zamu bar ?asar atare saboda idanuna sun makance akan sonki, a ranar da kika faWamin kina da aure, ban runtsa ba saboda hankalina ya tashi kuma duk da sanin hakan ban ji son ki ya ragu ba saima ?aruwa...."

dafe kanta ta yi da tafukan hannayenta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daWi, kalaman Zaki sun tsuma zuciyarta da tausayin shi, ba dan Taj ba da ba abunda zai hana ta amince mashi saboda gayen ya haWa komai da mace zata bu?ata a gurin namiji, sai dai kash bata jin zata iya rabuwa da Uban ?arta.

Muryarta na rawa ta ce,"kai ne ka tura ma mijina sa?on ya sake ni?"

Girgiza kai ya yi, "Ba ni bane, bazan iya aikata hakan ba." numfashi ta Wan ja, kafin ta runtse idanun ta, ya zuba mata ido yana kallonta kamar zai hadiyeta saboda tsantsar son da yake yi mata...

"Daddyna ya bani goyon bayan in nemi soyayyarki, In har kika amince min zai yi magana da iyayenki, on friday za'a Waura mana aure, Next week zan koma dake Canada, na yi maki al?awarin ba zaki ta6a danasanin aure na ba, kin riga da kinsan wanene ni kin san halina, kuma ko bayan auren bazan hana yarinyarki ta zo inda kike ba, har shi kanshi ex-husband din naki bazan raba zumuncin dake tsakanin ku ba..."

Kuka ne ya kubce mata, hakan ba ?aramin Waga hankalinshi ya yi ba, bazai juri kallon hawayen ta ba, da sauri yayi hugging dinta, halin da take a ciki ya hana ta kwace kanta daga gare shi.

Cikin shesshekar kuka ta ce,"In har da gaske kana so na kuma kana son farin cikina, to ka barni in rayu da mijina, wallahi bazan iya rayuwa da wani Wa namiji in ba shi ba, ba dan ?addara ta raba ni da shi ba, babu abunda zaisa na juya mashi baya, ko dan darajar ?ar dake tsakaninmu bazan Iya rabuwa da shi ba..."

kusan suman zaune yayi jin maganar ta, raba jikinta ta yi daga nashi, fuskarta ta ji?e sharkaf da hawaye taci gaba da cewa, "Ka taimaki rayuwana, ka rufa min asiri, in har taimakon da kayi min kayi ne don Allah, toh ka ha?ura da ni, mu cigaba da zumunci har ?arshen rayuwarmu, amma maganar aure babu ita tsakanin mu..."

Maganganunta sun karya mashi zuciya, wani irin zafi ne ya mamaye jikinshi, duk da sanyin A.c din motar hakan bai hana shi fitar da gumi ba.

kifa kanshi ya yi kan kafaWarta yana ambaton Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan min ha..." sambatu ya ci gaba da yi kamar ya fara zaucewa..

Tasan irin radadin karya zuciya ba kowa ke iya jurar shi ba, fargabanta kada tayi silar da Zaki zai rasa rayuwarsa amma ya zata yi? Bata da mafita da ya wuce ta lallashe shi taci gaba da bashi hakuri...

"Yayana nakaina, matsayinka bazai ta6a canzawa agurina ba, bazan ta6a juya maka baya ba, ina jinka tamkar Wan uwana na jini, ina mai takaici ?in amsa bukatarka, bawai don baka kai in aureka ba, wlh kowace mace zata yi burin ta auri namiji jajirtacce nagari irinka, saboda ka haWa duk wasu kyawawan dabi'u da halaye wanda zaisa mace ta so ka, sai dai kash Allah bai kaddara kaine mijina ba, muyi ha?uri mu rungumi kaddara, zan tayaka da addu'a Allah ya baka mace tagari, wadda zata maye maka gurbina...." cikin karyayyar murya ya furta, "Benazir bazan Iya rayuwa batare dake ba, zan ro?i Allah ya dauki raina in huta da radadin rasa ki da nayi" da sauri ta ce,"In sha Allah bazan zama silar da zaka mutu ba, sai dai in zama silar farin cikin ka na har abada, zan tayaka da addu'a Allah ya baka ikon cinye jarabawar soyayyata, Allah ya cire maka sona acikin zuciyarka..." cikin rawar murya ta ?arashe maganar.

shiru yayi bai ?ara magana ba, sai bugun zuciyarsa da take ji a jikinta.

"Alfarmar da zan ro?a a gurinka, don darajar manzon Allah SAW, ka rufa min asiri yayana nakaina, kada ka faWama Daddynka komai da ya faru tsakanin mu, saboda zai iya sanar da Uncle Wina shi kuma zaiyi min dole ne, nasan bazaka so abunda zai 6ata raina ba..." wani irin zazza6i ne ya lullu6e jikin shi, kamar ya fasa ihu haka yake ji, So bala'ene, duk maganganunta akan kunnanshi sai dai ya kasa furta kalma.

Shafa sumar kanshi tayi da tafin hannunta cikin sigar lallashi ta ci gaba da kwantar mashi da hankali maimakon yaji sau?i a ranshi saima yaji kamar tana ?ara rura wutar sonta a zuciyar shi..

Tayi fatan ace zata iya share mashi hawayenshi ta aminta da auren shi sai dai kash bazata Iya ba, kamar yadda yake jin azabar sonta itama haka take jin azababbiyar soyayyar Taj, duk namijin da zai aure ta sai dai ya auri gangar jikinta amma ruhinta yana agurin Taj.

Bayan wani lokaci, ta fito daga cikin Motar, da gudu ta nufi cikin gidan tana shiga daki bata iske Zeenatu ba, saman gado ta faWa ta rushe da matsanancin kuka tamkar ranta zai ita.

Hanky ya zaro daga front pocket dinsa ya share fuskar shi, saboda baisan daddynsa ya gano abinda ya faru da shi, saboda yayi mata alkawarin zai rufa mata asiri, ka ji masoyi na gari samun irinsu zaiyi wuya aduniyar nan.

Zaki mutum ne mai ha?uri ga tawakkali.

Bayan ya goge fuskar shi, Ya rufe murfin motar, ya zaro shades ya sanya ma idanunsa.


Bayan tafiyar Benazir da yan mintuna Sai ga Sir Mubarak da Alhaji Musa sun fito daga garden din gidan, fuskokinsu Wauke da fara'a da alama sun ji daWin firar da suka yi.

"Naji daWin karramawar da aka yi mana, yanzu sai yaushe mahaifin nata zaizo Abujan ko mu zamu je can Jos dinne? cos ina son ganawa da shi game da zancen auransu"

Alhaji Musa ya ce, "kada ka damu, basai kunje can Win ba, tun da har ni na amince da aurensu, shima zai amince ne." murmushi Sir Mubarak yayi, "Mutumina ka faranta raina, Allah ya ?ara dankon zumunci a tsakaninmu," Ya amsa mashi da ameen.

"Ba zaka shiga ciki ka gaisa da madam Wina ba"

"Ban shirya haWuwa da surukata ba, sai zuwa na gaba in sha Allah." Ya faWa yana bin compound din da kallo yana ci gaba da yin murmushi.

Fitowa Zaki ya yi daga motar, fuskar shi da fara'a ya ce, "Daddy, mun riga da mun gama magana da ita, harma ta koma ciki."

Farin ciki ne ya lullu6e Sir Mubarak,

"Uncle, ina godiya da damar da ka bani, Allah ya ?ara girma da Waukaka" ya faWa yana kallon Alhaji musa,

Murmushin gefen fuska ya sakar ma shi, "Kada ka damu, na dauke ka kamar Wana, komai zan iya yi saboda farin cikin ka."

Bayan sunyi sallama da juna, Alhaji Musa Ya koma gidan, su kuma suka shiga motar su.

Kwata kwata Sir Mubarak bai lura da yanayin fusakarshi ba saboda shades din da ya sanya ya rufe idanun shi ya hana yaga eye balls dinsa waWanda suka kada jawur tamkar garwashin wuta.

"Bani labari mana my son, ya kuka yi da ita?"

Shiru yayi jim kafin ya cije ya ce, "ta amince Daddy, "

"Alhamdulillah, yanzu da yaushe zamu zo nema maka auren ta?"

Tamkar baison furta maganar ya ce, "Ba yanzu ba daddy, mun yi da ita sai bayan na sake samun hutun aiki zan zo Nigeria sai a Waura mana auren" farin cikine ya cika Sir Mubarak.

"Ina tayaka murna my son, ni dama nasan da wuya a samu macen da zata yi rejecting dinka, saboda kai din na musamman ne." Murmushin takaici ya ?a?alo kan fuskar shi ba tare da ya iya furta kalma ba, a ranshi ya riga da ya yanke shawarar barin ?asar gobe, kwara ya nisanta kanshi da ita in ba haka ba zai iya zaucewa.


*MEETING ROOM*


Around ?arfe 11 na safe hamsha?an motoci suka fara kurWaWowa ta entrance gate din Isod headquarter, jigunannun gaske da matsakaicin gudu suke tururuwar shigowa a jere har kusan guda shida, kowace mota tana da tinted.

A parking space motocin su ka yi parking, a hanzarce Jami'an dake sintiri su ka yi saurin ?arasawa bakin car doors Win suka bubbuWe masu kofar....


Chief Owais ne ya fito tare da Big guy, motar bayan tasu Senior agents Win su ne.

Bayan su sai Commender james Ya fito shima tare da sauran sojojin da suka zo, kowannansu yana asanye da kakinsa..

Motar ?arshe General Win sojoji ne.

A gaggauce Jami'an dake kewaye da su sukayi hanzarin buga kafa tare da sara ma su cikin girmamawa suka gaishe da su kamar zasu zu?unna masu tsabar ladabi.

Basu tsaya 6ata lokaci ba, Cikin takun dattako suka nufi Secure operation center duk inda suka gifta sai ?amshin turarensu ya gauraye da iskar gurin daddaWan gaske, kuma duk hanyar da suka bi jiki na 6ari jami'an dake a gurin ke sara masu, sai dai kawai su Waga masu hannu alamar sun kar6i gaisuwar tasu.

Bayan sun hau lift ta sauke su a third floor, A bakin awani Katafaren Meeting room (Wakin taro na sirri) wanda gaba Wayan shi a kewaye yake da zallar glass launin blue sky, wanda ke a waje bazai iya ganin na ciki ba, bayan haka bangon gilashin Wakin soundproof ne irin wanda ke hana sauti fitowa waje, duk wani abu da za'a tattauna iya cikin Wakin sautin ke tsayawa na waje bazai ta6a iya ji ba..

Gaba Waya sun nutsu suna jiran kofar ta buWe ma su, biometric authentication ce sai ta tantance mutun kafin ta bashi iznin shiga..

Tafin hannu Chief ya Waura kan saitin na'urar ta yi screening din shi ta haska kwayar idanun shi kafin ?ofar ta fara sliding slowly har ta ?arasa zuge kanta..

Walking majestically suka fara shiga Waya bayan Waya cikin katafaren Meeting room din, U.s armies din dake a tare da su sai faman jinjina kai suke saboda ?awatuwar dakin taron yayi matu?ar burge su, cos ba su tsammaci zai kai haWuwar meeting room Win su na America ba, wata irin ni'imtacciyar iskar A.c ce mai fita da Wumi ta fara ratsa hudojin gashin jikin su irin mai sanyaya zuciyar mutun ta kwantar masa da hankali yaji shi a wata duniyar daban.

Wani katafaren zunguraren table ne a tsakiyar Wakin shape Winsa kamar rectangle ya ke iya jikinshi abun burgewa ne sai sal?i da daukar ido yake, ga wasu high-end Chairs kewaye da shi ga wasu haWaWWun Microphones da Laptops a gaban kowace kujera, bangon dake fuskantar table Win wani tafkeken large screen ne.


Komai na yin meeting an tanade shi a Wakin.

A tsanake kowannan su ya ja kujera ya zauna, suka fuskanci junan su, bayan sun daidaita nutsuwarsu Wakin yayi tsit na Wan wani lokaci, kowa da abunda yake sa?awa acikin zuciyar shi...

Abu na farko da suka tsara yi ma junansu barka da zuwa da kuma gabatarwa..

Dakin taron ya yi tsit a daidai lokacin da Chief Owais ya mi?e daga kan kujerarsa tare da tawagarsa, domin fara gabatar da kan shi cikin dattako ya fara magana yana duban kowannansu....

"Good morning everyone, i'm director Owais Sharafudeen Obinna, the Chief of Isod, With me are my team members," ya faWa tare da yin nuni da su,

"Deputy Director General Omar Musa Wadata, Chief of Operations Ahmad Hassan, Chief of Intelligence Commander Haroon, and Senior Agents Dr. Zarah Saeed, Agents Ethan Kim and Jabeer Osman."

yanayin yadda yake gabatar da su ba ?aramin burge su yayi ba komai nashi cikin aji yake yin shi, duk wanda ya ambaci sunanshi zakaga ya saki ?ayataccen murmushi kan fuskar shi..

"Muna yiwa kowa barka da zuwa" ya fada tare da komawa kan kujerarsa ya zauna suma duk suka zauna.


The next person General Noah ne wani bayerabe ba?i mai jiki ya mi?e yana gyara necktie Winsa,

"Hello everyone, nice to meet you all, I am General Noah the General Officer Commanding the Nigerian Army, It's an honor to be here today." ya faWa fuskar shi da murmushi kafin ya koma ya zauna.

Cike da kwarin gwuiwa Commender James Ya mi?e tare da tawagarsa su shidda,


"Hello everyone, I am Colonel James, the U.S. Commander of the Joint Task Force. I am joined by my team.." ya faWa tare da nuna U.s armies din dake gefen shi,

Ya fara zayyana sunayen su,

"Major Smith, Captain Lewis, Canal herry and Lieutenant Thompson tare da Jackson lee, munayi ma kowa barka da zuwa, mun ji daWin gayyatar mu da ku ka yi" gaba daya sunji dadin gabatarwar da yayi bayan sun zauna Wakin yayi shiru na Wan wani lokaci.


Kafin Chief ya numfasa calmly ya cigaba da kora jawabi, "Thank you, everyone, Let us proceed with the agenda, we are gathered here today to discuss a grave and urgent matter, already mun riga da mun san abun da ya tara mu, dangane da yaran

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0