Showing 387001 words to 390000 words out of 413917 words

Chapter 130 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4568

mata suje tunda dama ita ta hadata da su kuma ta san Taj yana ganin girman Aneela.

Kifa kanta ta yi gaban mirror tana shesshekar Kuka.

"Aunty Benazir" Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Zeenatu, Kasa dagowa tayi saboda bata son yanayinta ya jefa zeenatu a hali na damuwa

Shigowa dakin zeenatu tay, jikinta sanye da jallabiya fara.

Ganin Benazir zaune ta kife kai gaban mirror yasa ta nufe ta.

"Aunty Benazir, lunch is ready, we're waiting for you" ta fada tare da karasawa gaban ta.

Jin shiru bata dago ba yasa zeenatu tayi tunanin ko bacci ta ke yi.

Dafa bayanta tayi"aunty Benazir, Wake up pls, " taji tayi shiru bata tanka mata ba.

tasan in har ba magana ta yi mata ba, ba tafiya za ta yi ba, a yanzu bata son kowa a kusa da ita tafi son kadaici.


"Zeenatu! Pls ki kyale ni, basai kun jira ni ba, Ki tafi kawai ku ci abincinku,"

ras gabanta ya dan fadi jin yadda Benazir take magana cikin shesshekar kuka arude ta furta"Aunty Benazir! Meke damunki? Baki da lafiya"?

Bata san sa'adda ta daka mata tsawa ba"bansani ba, Zeenatu! Nace ki kyaleni, Ki rabu dani, bana son ganin kowa akusa dani..."

zazzare blue eyes dinta tayi, abunka ga shagwababba ta fashe da kuka ta juya ta fuce da gudu ta nufi dining area.


A lokacin Mami da Hajiya sarah tare da Dr shureim da Alhaji Ubaida suna azaune kan dining Chairs har sun fara cin abincin, Kukan zeenatu ne yaja hankulansu ga dubanta, azabure suke mike suna kallonta, Ta na karasawa ta fada jikin mommynta tana ci gaba da kuka, Hankali atashe suka dubi juna kafin suka maida idanunsu akanta.


" Zeenatu meya faru? Ina Benazir din? Wa ya tabaki"? Alhaji ubaid ne ya tambaya.

Mami tace"ki bude baki kiyi magana mana! Wani abunne Ya hadaki da Benazir dinne"?

Dago da ita Hajiya sarah tayi"Daughter, Daina kuka, Fada min meya faru"! Cikin kula tayi maganar tana share mata hawayen fuskarta
Cikin shesshekar kuka tace"Ah.. an.. aunty Benazir ce take kuka, Nace tazo muci abinci shine ta daka min tsawa tace in tafi bata son ganin kowa a tare da ita"


Dr shureim bai tsaya ya karasa sauraron maganar Zeenatu ba, Ya zame jiki Ya nufi dakin Benazir tunkafin Ya karasa shiga Ciki yajiyo sautin kukanta, gabansa na faduwa ya afka ciki Ta cikin madubi Ya hango fuskarsa sharkaf da hawaye ta zabga uban tagumi kamar wadda ta rasa gata a duniya, da sauri ya nufe arude ya furta Benazir! Lafiya kike kuka? Meke damunkin ki ne?


mikewa tayi ta nufe shi ta kwantar da kanta saman kafadar shi tana kuka, bubbuga bayanta ya somayi da hannunsa cikin sigar lallashi yace"pls ki fadamin damuwarki, Zan taimaka maki mu nemi mafita, amma kukan nan bazai amfane ki da komai ba, saima yajaza maki ciwon kai"

dakyar ta hadiye kukan tace"yaya shureim ina ma mutuwa zata zama hutu agareni wlh dana mutu na huta, nagaji nagaji da azabtarwar da zuciya keyi min akan rashin mijina da yata, yaya shureim bana jin dadin komai, hankalina ba akwance yake ba, Ina so nagan su..." dakyar ta karashe maganar..


Gaba daya a kunnan su Mami da basu dade da shugowa dakin ba, Gaba dayansu sunyi tsaitsaye cirko cirko suna sauraron maganar Benazir, tausayinta ne ya kamasu mami tuni idanunta sun ciko tab da kwalla, batasan ya zatay ba, ita kanta zataso Benazir ta hadu da bayin Allahn nan ko ta samu nutsuwar hankali..

Zeenatu dake kuka kalaman benazir sun karya mata zuciya, wani kukan takuma fashewa da shi.

"Benazir, Kiyi hakuri, Ki kara jurewa dan Allah, Na roke ki, sanya damu arai bazai haifar maki da komai ba, saima ta fama maki raunin dake a cikin zuciyarki, bana so a koma yar gidan jiya, dan Allah Benazir kiyi hakuri zamu tayaki da addu'a kema ki dage in sha Allah zasu bayyana"

Hajiya sarah ce ta yimaganar cikin sanyin murya.

Girgiza kai Alhaji ubaid yai shi kanshi abun na damun shi.

"Kinga kukan Ya isa haka, Kiyi shiru, in sha Allah Idan Uncle dinku ya dawo zanyi magana da shi ya taimaka yasa a yi cigiyar su agidan jaridu watakil adace..."


gaba daya tunaninsu har yanzu babu labarinsu ita kadai tasan Da zaman su..


A hankali ta dago daga kan kafadar dr shureim Idanunta sun kada jawur ta dube su ji take kamar ta fada masu Taj da Unaisah suna nan kuma tasan inda suke, ko dan ta samu su tayata neman yafiyarsa.


Girgiza kai tayi"nagode da kulawarku agareni, Amma basai an yi cigiyarsu a gidan jaridu ba, Aneelerh ta fada min sunyi iyakar bakin kokarinsu gurin yada hotunansu a social media da Gidan jaridu amma har yau babu labarinsu...." ta dan dakata kafin ta daura da cewa"dan Allah kada ku damu da halin da nake a ciki, bawai don banyi imani da kaddara ba, wlh nayi kokarin In manta da su a cikin zuciyata amma abun Ya faskara..."

ta faWa tana matse kwalla.
Kallonsu Dr shureim yayi"pls Ku barni da ita, ku je ku ci abincinku, Zan yi mata nasiha" Alhaji ubaid yace"yawwa shureim pls kayi kokarin shawo kanta, bana so ciwonta ya tashi" amsa mashi yai da toh, fita su ka yi ya rage saura su uku

Kallon zeenatu yayi, Tana atsaye bakin kofar sai shesshekar kuka take.

"Calm down your mind, Ki kawo min lunch din ta a daki" ta amsa da toh ta juya ta fuce..

Ruko hannunta yai suka zauna kan gadon ta.

Nasiha ya farayi mata cikin kwantar da murya har saida taji zuciyarta ta dan lafa da radadin da takeyi mata.


Sai da yaga ta samu nutsuwa sosai kafin yace"akwai inda ke maki ciwo" girgiza ma shi kai tay"a'a ya shureim, lafiyana lou"

"Okay, " ya fada tare da sauke ajiyar zuciya.

Shigowa zeenatu ta yi cikin dakin, hannayenta ru?e da tray mai dauke da lunch ta mika ma dr shureim Yasa hannu ya kar6a yadago ya dube ta"thanks, yanzu sai hankalin ki ya kwanta, tunda auntyn naki ta daina kuka" murmushi tadan saki.


"Ki je ki ci abincin ki"

Cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh.


Bayan fitar Zeenatu daga dakin Ya maida hankalinsa akan Benazir, A baki ya soma bata abincin tana ci, sai kallon shi takeyi har saida Ya tsargu da kallon Yace"Akwai wani abu ne"?
"Yaya shureim dan Allah ka taimaka ka kaini gidansu Anila Inason ganinta."

"Da yaushe"?
"Ko yanzu kace sai in shirya mu tafi"
"Kin fada mata ne"?
Shiru tayi jim don rabon da suyi waya da Aneelerh kusan two weeks babu wanda ya tuntubi wani amma saboda tana son Taje din yasa tay mashi karyar sunyi waya harma ta fada mata zasu zo

Yace toh idan sun kammala Cin abincin zai kai ta.

Dadine Ya lullubeta bayan sun gama cin abincin, Ya fita don yaje ya shirya.


Jikinta na rawa ta dauki waya ta danna ma Anila kira, don ta sanar da ita batun zuwansu, almost 3 times tana doka mata kira ba'a picking a karshe ta hakura da kiran nata ta fada toilet don tayi wanka.



*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?
'?*



*Game bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: =?%?=???=??? &?=???=???>???

~<><><><><><><><><><><><><><><
'?~




~___________________________________~




Sheikh Imam Malik Shahararren malamin addinin musulunci ne, kuma babban alkalin Kotun Musulunci, Haifaffen jihar jos ne, wayayyen malamin addinin musulun ci ne kuma dan boko maiji da kanshi, ga wadatar arziki da Allah ya yi mashi, sheikh Imam ya yi suna wajen yin adalci, rukon amana tausayi da jin?ai, yana da ?warewa ta fannin shari'ar musulunci, mutunne shi mai tsastsauran ra'ayi akan addininsa, kuma kaifi Waya ne In ya furta magana baya canza ta, da dama mutane masu aikata mugayen laifuka suna jin tsoron shari'ar sheikh Imam Malik saboda sun san Halinsa baya kar6ar Cin hanci, dole mutun Ya kar6i hukunci dai dai da abunda ya shuka ko Wan uban wanene, sannan yana da zuciya idan ranshi ya 6aci, sai dai duk da hakan Yana da sau?in kai ga wanda ya iya zama da shi.

Matarsa Ta farko Malama Fatima Batool wadda ta kasance Yar uwarsa diyar wan mahaifinsa mazaunin Sudan, Auren zumunci iyayensu suka haWa su, Kuma cikin Ikon Allah jininsu ya haWu soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu har takai su ga yin aure, Sunyi zama Na amana saboda Ra'ayinsu yazo Waya, Yaji dadin zama da ?????!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!?!"ita saboda kyawawan halayenta, tanayi mashi biyayya sau da kafa, A lokacin data samu ciki yayi murnar da bazata misaltu ba, baya gajiya dayi mata addu'a akan Allah ya sauke ta Lafiya, bayan data haihu ne ta koma ga Mahaliccinta yayin da tabar masa Yar jinjiran da ta haifa masa, Shiekh Imam Yaji rasuwar ta, duk irin juriyarshi da tawakkalinsa sai da ya zubda ?walla saboda babban rashin da yayi.

Rainon yarsa ya koma hannun gwaggwansa kanwar Mahaifiyarsa, A lokacin iyayensa duk basa araye, itace ta kula masa da Yarsa Har ta dan fara tasawa.

daga bisani Kawunsa na sudan ya bashi auren kanwar Matarsa Aunty Laura, a wani zuwa da yai sudan kai masu ziraya, A lokacin sheikh imam baida niyar ?ara aure saboda bai warke daga radadin rasa matarsa da yayi ba, amma saboda aunty laura ta kasance Jinin Malama Batool yasa shi amincewa da aurenta.


Bayan auransu da wata daya Rainon Aisha ya dawo hannun Aunty laura, ta rike ta da amana kamar yar cikinta, tana bala'en Son Aisha, saboda jininta ce ita uwa uba kamanninta sak dana Yayarta Malama Batool, saboda yadda take bata kulawa ba zaka taba gane ba yarta bace sai an fada maka.

hakika sheikh imam malik yayi namijin kokarin gurin tarbiyantar da rayuwar yarsa, ya tsaya mata tsayin daka don ta nemi duniyarta da lahirarta, gaba daya halayanta da dabi'unta irin nashi ne, abu daya da bata Wauko na shi ba shine Zuciya, tana da tsantsar hakuri kamar Mahaifiyarta Malama Batool, hausawa sukace kyan Wa ya gaji ubansa itama hakan ta ke Aisha tagaji mahaifinta da kuma mahaifiyarta malama Batool.


Sheikh Imam ya Waura mata burin duniya, Bai taba son wata aba kamar yarda yaso Aisha ba, ita kadai ce ?a daya tilo da Allah ya albarkace shi da ita, Babu irin gatan da sheikh Imam bai yi mata ba.

Aishatu macace mai cikar kamala, mai tsantsar kamun kai, samun matashiya mai irin baiwar ilmin da Allah ya bata zaiyi wuya a fadin duniyar nan, ta haddace alkur'ani mai girma tun tana da shekara goma sha uku a duniya, mutane dayawa suna yabonta saboda kyautatawarta a gare su, kyawawan dabi'unta da halayanta abin koyi ne ga duk wata ya mace, kuma burin kowani namiji ne ya mallaki mace kamarta.

duk wani abu da zai sabama Mahaliccinta gudun shi takeyi, tana da jin?ai da son taimako bata gajiya da hidimtawa addininta.

Abun burgewa iyaye mata da matan aure suna karuwa da ita, also she's a role model for young women.

tun tana yar matashiyarta take koyawa a islamiyar Mahaifinta mai suna madarasatul Fatima Batool dake a kusa da gidan su, tana yin wa'azi ta kuma yi da'awa ga waWanda basuyi imani ga Allah ba, ta dalilin Aisha, Sheikh imam malik Ya samu daukaka fiye da zaton shi, ta kare mashi martabarshi da kirmarshi ta kuma daukaka darajar shi a idon duniya, sau dayawan lokutta baya sanin tayi wani abun, sai dai akira shi awaya ko azo har gida ayi mashi godiya akan alkhairin da Aisha tayi, yai ta mamaki farin ciki ya cika shi, sai ya kirata ya tambayeta me tayi tukunna take fada masa Alherin da take samu a gurin Gasar karatul al'qur'ani da wadanda mutane suke bata kyauta saboda dadin wa'azinta da suke ji, dama A duk lokacin da ta kawo mashi kudin don ya dauki wani abu baya kar6a, kudinne take tarawa in suka taru dayawa da su take amfani gurin tallafawa marasa karfi, tana yawan ziyartar asibitoci, gidajen yari, da gidajen marayu ta basu tallafin kayan abinci da suturu in kuma bata da kudin da zata basu zatayi masu wa'azine da nasiha mai ratsa zuciya, shiyasa sheikh imam ya ke bala'en ji da Aisha, yana matukar son Yar shi, itama bata da abu mafi soyuwa dayawuce Mahaifinta, tana yi mashi biyayya sau da kafa, batason bacin ran mahaifinta, tana kokarin yin duk wani abu da zai faranta ran shi.


Dangantar da ke a tsakanin Benazir da Ayshah da Dr shureim ta samo asali ne tun daga kan Iyayen su Maza, Sheikh Imam malik baida amini daya wuce Alhaji ubaid Wadata sun kasance makwabtan junane, Gidansu Yana a jikin na juna, Akwai zumunci mai karfi a tsakanin Iyalansu, atare suka taso tun kuruciya, kasantuwar Alhaji ubaid Dalibin Mahaifin sheikh Imam ne agurinsa yake Waukar karatun addini kafin Allah yayi masa rasuwa, Alhaji Ubaid dan babban Gidane, Family dinsu yayi shura A jihar, saboda Arzikin Mahaifin su marigayi Alhaji mu'azzam wanda akeyiwa lakabi da wadata babban dan kasuwane a zamaninsa.

Benazir da Aisha ?awayen junane kuma aminnai tun kuruciya, atare suka taso kuma atare su ka yi primary da secondry a makarantar Sheikh Imam Malik wadda Har Islamiya ake koyawa a cikin ta, abun da zai Waure ma kai, kwata kwata halin Aisha dana Benazir baizo daya ba, sun sha banban, Benazir tana da girman kai, rashin kunya kuma bata iya shigar mutunci ba, duk suturar da zata sanya sai ta matse jikin ta.

Sarai Sheikh Imam yasan da Halin Benazir Ya kuma san Gado tayi agurin Hajiya layla, mutane suna yawan kawo mashi tsegumi akan ya raba yar shi da Benazir In ba haka ba zata bata masa tarbiyar ?a, Bai ta6a Waukar maganarsu ba, saboda Shi ya yarda da tarbiyar daya ba Aisha yasan bazata ta6a bari Benazir ta rinjaye ta ba, sai dai ita ta rinjayi Benazir gurin karkato da hankalin ta don ta shiryu, bayan hakan Yayi Wa Benazir farin sani, Yasan Bata Jin magana kuma bata da kunya sai dai ita din ba Yar iska bace, bata shaye shaye, bata bin maza, Rashin Wa'arta abaki ne da kuma yanayin Shigarta, sai kuma yawon gantali da take fita a kowani dare ne sai taje Night club, gata yar hana biki maraici, kuma zabaya ce a fagen rawa, amma Sheikh bai ta6a gigin raba ?awancen su ba, saboda yana son duk wani abu da Aisha ke so.

bayan haka baya son abunda zai raba zumuncinsu da makwabtan shi.

Wadannan dalilan ne suka sa Shiekh imam Ya amince ma ?awancen Aisha da Benazir, Amma sai da ya gindaya mata sharudda akan bai lamunta tadinga fita yawo ba, kulle ya ke mata daga makaranta sai gida, In har zasu hadu da Benazir sai dai tazo gidan su, Ko kuma In Aunty laura zataje gidan gurin Hajiya layla ta tafi da ita, sai kuma in sun haWu a school, amma sam bai yarda ta dinga bin Benazir suna fita yawon gantali ba bayan haka ya hanata kula kowani saurayi saboda akwai wanda yake burin ta aura har sa'insa su ke yi da Aunty laura akan ya hana Aisha kula samari ita ta rasa gane ma manufarsa akan Aisha kamar ba yar cikinsa ba, maganganu marasa dadi take fada masa bai ta6a biye mata ba.


Aunty laura wayayyiyar macace Yar boko kwararriya ta fannin business, ta inda suka sha banban da Imam ita tana da karancin addini akai, kwata kwata halinta ba irin na yayarta mariganya Batool bane, shiyasa basu jituwa da sheikh imam malik, sa'insa suke da junansu saboda ta tsani yadda yake zafafawa akan addini kuma A ganinta kullan da ya ke yi ma Aisha takura ce.

shi kuma yanayi ne saboda Farin jinin da Allah yayi mata, Babban abunda Ke ci mashi tuwo a ?warya yadda wasu mazan basa iya kau da maitarsu akan Aisha, saboda Dirin da Allah yayi mata, tun tana ?an?anuwarta wani irin dirin jiki ne da ita mai jan hankali, duk taku daya idan tayi sai jikin ya girgiza koda kuwa ta sanya dogon hijabi ajikinta ne sai shatun dirinta Ya bayyana wani irin farin jinin samari gare ta kuma mafi akasarinsu ba don Allah suke son ta ba sai don kwaWayin Surar ta.

wannan dalilinne yasa shi tsananta mata tsaro ko fita za ta yi dole ta sanya dogon hijab da ni?ab, daga makaranta sai gida makarantar ma shi ke kai su da kanshi In an tashi ya dauko su ita da Benazir, wani sa'in In aikin yayi mashi yawa ko zaiyi zaman shari'a Aunty Laura ce ke dawainiyar kaisu wani lokaci in ta samu damar dauko su daga school in an tashe su sai ta saci hanya takai su Shopping mall tayi masu siyayyar kayan amfanin su na mata.

Awata rana ne Aisha tana a zaune kan darduma sai ga Benazir ta shigo gidan da rawar jiki ta shigo har dakinta ta ruko hannunta da farin ciki take fada mata tazo taga Uncle musa da Yaya shureim sun dawo Nigeria, kasantuwar su dukansu A lokaci ba mazauna Nigera bane, Shi Alhaji musa harkar kasuwancin shi yakeyi a kasashen ketare yayin da Shureim ke karatu a kasar egypt can gurin ammin su ya ke da zama.

da fara'a Aisha tace meyasa bata fata mata ba, Benazir tace kawai tana son tayi suprising dinta ne, cike da farin ciki tace ta jira ta a falo zata shirya, Benazir na fita daga dakin Aisha ta soma shirya kanta cikin abaya, sai ga Aunty laura ta fito daga daki ta iske Benazir zaune kan sofa, da fara'a suka gaisa da juna har ta tambaye ta meya sanyata farin ciki nan take fada mata yaya shureim da Uncle musa ne suka dawo Nigeria shine ta zo don ta fada ma Aisha, washe baki aunty laura tayi tana fadin Ah lallai manya manyan baki, shine ba'a fada min ba? tana cikin magana sai ga Aisha ta fito sanye da dogon hijab hada nikab akan fuskarta.

fuska adaure Aunty laura tace kefa matsalata dake kenan, kamar kinfi kowa tsoron Allah, kullum cikin nikab, yanzu nan da gidan makwabtan namu sai kin saka hijab da nika..." a karshe ta korata daki tace taje ta sako Mayafi..da damuwa tace ita bazata iya ba, saboda hijab mutuncin ya mace ne, bayan haka baba ya hanata fita ba hijabi har ta soma janyo mata aya, aunty Laura ta mike rai a6ace taja hannunta suka koma daki, adole saida ta tursasa ma Aisha

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0