Showing 357001 words to 360000 words out of 413917 words

Chapter 120 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2702

kurkukun nan ake ?era su, na daWe ina tara su a 6oye saboda burin da nake dashi na ganin na kawo ?arshen zaluncin su."


Ta Wan dakata tana mayar da numfashi kafin ta daura da cewa, "Makaman dake a hannunku ba za su yi tasiri akan su ba, amma in har kukayi amfani da makaman nan cikin sau?i zaku kashe su"

Farin Ciki ne Ya cika su, a hanzarce Salsabeel da Danish suka kwance buhunhunan, sun yi mamakin ganin yawan makaman, Wu?a?e ne da adduna, harda takubba da kibiyoyi, ga gatari da manyan gudumomi, nan kowan nansu ya Wauki makamin da ya kwanta masa arai, bayan sun kammala Wauka, ta ce, "Ku fara kokarin ceto rayukan fursinoni dake a ciki kafin su ankara da shigowarku, Danish da Salsabeel kuyi masu jagora zuwa da?unan da fursinoni suke." suka amsa mata da toh.

Ta ?ara da cewa, "Duk yaran da kuka taimaka, ku kawosu nan, zan taimaka masu su fita daga kurkukun..."

With respect suka amsa mata da toh.

Akwatinan ?arfen ta nuna masu, "Kakin giants ne a ciki, na tanadar maku sune saboda kuyi 6adda kama ku saje da su, duk da naga kakin ku sunyi shige da nasu."

Ta kuma nuna masu kayan Matsafan da ta kashe, "Ga wasu kayan nan ma."

Big guy yace, "Ba dukkanmu keda irin kakin ba, akwai sauran tawagar sojojin da zasu ?araso, in yaso sai wasu daga cikinsu suyi amfani da kayan." Jinjina kai ta yi, "Hakan yayi, zaku iya tafiya, Ina yi maku fatan nasara" Har cikin ran su sunji dadin taimakon da tsohuwar tayi masu, yaune karo na farko da suka fara ganinta amma ta kwanta masu a rai.

(Kunji yadda akai suka ?araso Cikin gidan kurkukun ?addara)

Suna cikin tafiya suka ci karo da wani bene mai kanannaWa, Kwata kwata babu fargaba a tare da su, suka hau benen ya 6ula da su cikin wata hanya mai tarin kofofi, har zasu gifta ta wani Wakin kwatsam wani gabjejen Giant ya fito sanye da lab coat fara a jikin shi gaba Waya suka sha jinin jikin su..

Da farko da ya kallesu yaso ya ruWe amma sai ya ji a jikin shi ba Giants din su bane.

"Su wanene Ku?" Da wata irin ?atuwar murya ya yi maganar, Yan hanjin cikinsu ne suka kaWa aka rasa wanda zaiyi mashi magana acikin su..

kamar yaso ya Wago su amma sai yayi azan daga cikin ba?insu ne da suka zo.

?arfin Hali Chief ya yi wurin furta, "Daga cikin ba?in kune, muna ?arewa ginin kallo ne" Maraba ya yi masu tare da nuna masu ?ofar dakin da ya fito ya ce, "?akin fiWa ne, zamu iya shiga ciki idan kuna neman ?arin bayani dangane da yadda muke gudanar da aikin mu."


Ya faWa tare da buWe kofar dakin ya shiga suka bi bayanshi, sun yi matu?ar girgiza da ganin fursinonin dake a kwance kan gadajen Wakin, Hada mata masu ciki, jikinsu sanye da fararen kaya, Ga wasu gungun Gigantes medici dake tsaka da yin aikin fiWa a gaban gadon fursunan da suka farke cikin shi, har sannu da aiki suka yi masu, giant doctor din da ya shigo dasu ya gabatar dasu ga sauran yan uwansa likitoci kafin yace masu su ?arasa ciki, Ya nufi gaban wasu manya-manyan furizozi Ya bubbuWe su, sun razana sosai da ganin sassan jikin mutanan da suka feWe masu yawan gaske..

Hankulansu sun tashi matu?a sai dai basu yi gangancin da zai sa a gano su ba, bayani ya fara kora masu game da yadda suke feWe mutun su cire sassan jikin shi da yadda suke amfani da shi har safarar sassan suke yi zuwa wasu ?asashen su siyar da su.

Chief da Big Guy sun harzu?a matu?a, jikinsu sai tsuma yake yi saboda tsabar fusata kamar su rufe shege da bugu.

Kwatsam yana tsaka da kora masu bayani Taj ya yi su6ul da baka gurin furta, "Amma dai baku da imani" kaitsaye maganarshi da dira cikin kunnan Giant doctor din.

Nan take ya dakata da kora masu bayanin da tsantsar ruWani Ya furta,"Who are you?" Shiru suka yi, hakan ya ?ara ?arfafa zarginsa akan su.

Wata irin gigitacciyar tsawa ya daka masu tamkar zai fasa dodon kunnansu da karfi ya ce,"baku ji ina tambayarku bane? Su wanene ku huh?" Maganar da yake yi ce ta janyo hankulan sauran Giant doctors
din dake aikin fiWa, suka ajiye tiyatar da suke yi gaba Waya suka zagayesu kamar zasu rufe su da bugu, safunan hannayensu jaga jaga da jini..

Jin sunyi shiru sun ?i basu amsa ne yasa Waya daga cikinsu ya kai hannu zai cire Mask din dake akan fuskar Chief, bai kaiga ?arasa cirewa ba, Danish Ya zaro addarsa azafafe Ya datse hannunsa ya 6alle biyu jini ya dinga tartsatsi, koda ganin hakan sauran giants Win suka harzu?a matu?a, suka afka masu faWa ya kaure atsakanin su, sun ci wahala kafin suka yi nasarar kashe su gaba daya suka zubar da gawarwakinsu akan floor.

Sai haki suke suna nishi, Big guy ya dubi Taj da ya dafe cikin shi, "Next time kada ka ?ara maimaita kuskuren da ka yi, yanzu da ka ja mun rasa rayukanmu." da?uwa Taj ya yi masa batare da ya furta kalma ba.

Fursinonin dake a kwance kan gadajen suna ganin abunda ke faruwa saidai sun kasa tashi zaune saboda alluran da suka banka masu sun kashe kuzarinsu, kwayar idanunsu ce kadai ke motsi..

"Ya zamuyi dasu"? Big guy ne ya tambaya.
Salsabeel Ya dubi Danish, "ka yi wani abu pls" duk suka maida hankali kanshi, shi kadai yasan me ya yi masu sai gasu sun mi?e kan ?afafunsu.

Basu tsaya 6ata lokaci ba, wasu daga cikinsu suka tafi da fursinonin...

Fitowa sukayi daga Wakin fiWar, Suka faWa dakin dake akusa dashi, nan fa suka ga abun da ya ?ara Waga hankulansu, jarirai suka gani a cikin containers, kamar bakwaini gwanin ban tausayi...Taj har ?walla saida ya zubda masu, Big guy ya ce, "ya zamu yi da su?"

"Dan Allah mu taimaka masu, kada mu barsu anan" Taj ne ya faWa.

Salsabeel ya bashi amsa da, "Bazai yiwu ba, don ta yanzu, mu barsu kawai Allah yana atare da su."

Fucewa suka yi daga Wakin suka shiga Wakin dake a gaba, rasss! gabansu ya hau faWuwa ganin Warurrukan kwarangwal na mutane sagale jikin igiyoyi ga wasu nan zube a ?asa har jikin bangon Wakin ko'ina su ne na mutanan da suka kashe, wa'iyazubilla zuciyoyin su sun karaya ba kadan ba. Wata shari'ar dai sai A lahira wallahi.

Kusan zagaye kurkukun suka yi sa?o da lungu suka dinga shiga, sune har cikin treatment rooms din kurkukun, anan suka ga majinyatan fursinonin da suka kwantar, sun ci ba?ar azaba a hannun masu jinyar su wurin yin faWa dasu, da ?yar suka kashe su kafin suka ceci majinyatan suma.

Saida suka gama kwashe fursinonin, kafin suka dawo baya, har sun kusa 6ula ground floor din da ake shagalin Chief Ya dakata da yin tafiya, kallon shi su ka yi, duk da basu san me ya hana shi cigaba da yin tafiyar ba, sun fahimci kamar Yana jin fargaban yaga wani dangin shi a cikin matsafan, dama da zargin mahaifinsa aransa ga kuma abun da ya faru tsakaninshi da tsohuwa Khala na furucin da ta yi akanshi.


Idan muka koma bangaren Elders, sun shagala suna kallon karawar da matsafan su ke yi a tsakar fili, kowani matsafi ya zage damtse gurin nuna ?arfin sihirin shi, dambe ne na fitar shari'a suke yi kamar zasu kashe juna, idan bala'e yayi bala'i har rikiWa suke yi su koma dodanni su cigaba da dambatawa a tsakanin su.

Saida aka zo zagaye na ?arshe a wasan, Elders suka ji shiru ba'a zo da prisoners ba babu su babu alamar su...

Da yatsa Elder Ya yi ma Waya daga cikin Evil giant din dake bayan shi alamar Ya matso kusa, sunkuyar da kanshi yayi saitin fuskar Elder...

Cike da bada Umarni Ya ce, "Ka yi ma Giantesses magana, suzo da yaran da sauran kayan da aka tanada Yanzun nan...!" da buWaWWiyar murya Giant din Ya amsa mashi da angama sir, daga Inda Yake bai matsa ba ya 6ace ma ganin shi.

Bai dira a ko'ina ba sai a hall din da suka tara prisoners, Nan Ya ga abunda Ya tada hankalinsa, gawarwarkin da ya gani baje ?asa na female giants dinsu, Ga Gawar tsohuwa Inno...aruWe da yana yi na mamaki Evil Giant din Yake bin Wakin da kallo kamar a mafarki, Fitowa yayi daga Hall din saboda dakakkiyar zuciya irin nasu, neman waWanda suka kawo masu hari ya shiga yi, don Ya aika su lahira.

Yana Cikin tafiya suka bangaji juna shi da wani giant, tun daga yanayin yadda yayi tangal tangal zai faWi Evil giant din Ya gane ba nasu bane saboda giant basa bangazar juna.

Da kakkausar murya ya furta"Wanene kai?" Rasss ya ji gabanshi ya faWi, yan hanjin cikin shi suka kaWa, baima san ubanda ya janyo shi wurin ba shi kaWai batare da kowa ba gashi sam ya kasa yin wani yunkuri don ya ce ci kan shi, ware faffaWan tafukansa evil giants Win ya yi da niyar Ya tarwatsa ?o?an kanshi sai dai kafin ya yi hakan baiyi aune ba Yaji dirar Zarto saman kan shi, kwatsa kwatsa Ya faffasa kan nashi Kafin Ya ?wal?walo idanunshi yabar gangar jikin shi yashe a ?asa, ajiyar zuciya Taj ya sauke wlh har ya fidda rai da rayuwa badan Allah Ya hankaWo Danish ba da tuni evil giant Winnan Ya aikasa Barzahu.

Duk da bawani sabawa suka yi da juna ba saida yaji kaunarsa ta shiga ranshi, cikin sanyin murya ya furta, "Thanks" Jinjina mashi kai ya yi tare da nuna mashi hanya, "Zamu iya tafiya." Bin bayanshi Taj yayi suka nufi sauran jami'ansu da sukai Basaja..

Jin shiru Evil giant din da suka aika bai dawo bane yasa Elder Sake tura wani, a karo na biyu yaji shiru bai dawo ba, wasa wasa har giant biyar suka aika basu dawo ba, lamarin ya Waure masu kai, Mi?ewa elder ya yi Jan Wuya ya ce, "Ina zaka je?"

"Ina so naje na duba Hall din, tayaya zamu aika mutun biyar shiru basu dawo ba, kada a yi abin kunya!"

Girgiza kai Jan Wuya ya yi, "Ba kai yakamata ka je ba, bari na je na duba.." ya faWa tare da mi?ewa cikin takun ?asaita ya fuce daga filin taron, bayan tafiyarshi, Elders suka Ji shiru shima bai dawo ba, hakan yasa Jan Harshe ya mi?e Ya tafi neman shi, shiru shima bai dawo ba, har saida ta kaiga gaba Waya Elders sun bar filin shagalin, Fitarsu keda wuya kwatsam! ba zato ba tsammani wata irin kururuwar Fashewar bamabamai ta karaWe gidan kurkukun, Gaba Waya taron matsafan da ke a gurin shagalin babu wanda Ya tsira da ranshi, saboda mamayarsu aka yi sihirinsu bai amfane su da komai ba, Haka wuta ta dinga balbali tana Cin naman jikinsu, suka run?a sakin wata irin kururuwar radadin azaba mai amon gaske.

Har Cikin Kunnan Elders yayin da suka je hall din don su ga meya hana giants din da ake aika dawowa.

Kowa ya shiga ciki wani irin burki yake ci sakamakon abun al'ajabin da idanunshi ya gani, a haka har suka haWu su duka, Cak duk suka yi sun kasa yin wani ?wa??waran motsi, da wani irin matsanancin mamaki da al'ajabi gami da ruWanin tashin hankali suke duban junansu....ganin abunda basu ta6a zaton ga ni ba, ga kuma sautin da kunnuwansu suka jiyo masu. Wannan shi ake kira bazata!!!



*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?
'?*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: =?%?=???

~__________________________~
'?


After One week (bayan sati Waya dakai farmaki Gidan Kurkukun ?addaraS'


Hankalin Unaisah ba ?aramin tashi yayi ba, Jin shiru har tsawo sati Waya basu dawo ba, lamarin Ya Waga hankalin ta ba kadan ba, dauriya kawai takeyi kamar yadda tayi ma su alkawarin zata daina kuka, kuma bazata sanya damuwa aranta ba, sannan ba zata hana idanunta bacci da kuma cin abinci.


Abu Waya ne bata wasa da shi, Tashi Yin nafilfili takai kukanta gurin Allah, idan dare yayi, biyu take raba lokacin ta, rabi tayi bacci rabi ta tashi tayi nafila, wani sa'in in ta fara tsayuwar daren Har sai kafafunta sun fara raWaWi tukunna take dakatawa.

mafi yawan lokutta akan prayer mat bacci ya ke yin awon gaba da ita, Unaisah da Aunty Umminsu sai batool ne kadai sukasan da tafiyarsu kai farmaki sauran yan uwanta babu wanda ya sani abu daya da suka sani shine har yanzu suna shirye shiryen tafiya amma basu tafi ba, kamar yadda Unaisah ta sanar da su, tayi masu hakanne don kada su daga hankulansu yayin da ita kuma hankalin nata ba akwance yake ba, sai dai suna yawan tambayar meyasa Danish baya le?o su? kuma su an bar su anan ko nan zasu ci gaba da zama ne kuma yaushe ne zasu je kai farmakin, dakyar suke samu su shawo kansu ita da ummi, harta Danejo batasan komai ba dangane da kai farmaki ta dai san zasu je yin wani aiki kamar yadda Taj ya faWa mata, abunda yafi damunsu babu wanda ya kira su awaya balle su san awani hali suke a ciki....=???


A daren jiya ne ta farka tsakar dare da matsanancin faduwar gaba sakamakon wani mummunan mafarki da tayi, Hankalin ta ya tashi matuka jin yadda tsigar jikinta da zuciyarta ke tashi, gaba daya tarasa samun nutsuwarta saboda tana ji aranta wani mummunan abu ya faru da su, a lokacin idanunta sun makance burin ta kawai ta ganta a part din Chief don taga idan sun dawo ko basu dawo ba, hijab ta zura a jikin ta, batare da sanin kowa ba ta fito daga dakin daddyta dama anan suke kwana ita da Batool bayan tafiyar su.

Ta sauko down ta nufi main door ta falo, ta dinga ?o?arin buWe ?ofar ta kasa saboda security din dake a jiki, batasan menene password din kofar ba, har jaraba sanya numbers tayi sau biyu ana nuna mata wrong code tare da warning message.

zukunnawa tayi bakin kofar tafukan hannayenta toshe da bakinta don kada yan uwanta sujiyo ta, ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, sai da ta gama hasala can zuciyarta ta ayyana mata me zai hana ta jaraba sanya kwanan watan da aka haife ta, cos ta sani tuntana karama mahaifinta baida password da ya wuce date of birth inta, cikin hanzari ta mi?e ta danna numbers din fortunately ?ofar ta buWe batai wata wata ba ta fuce aguje ta nufi part din Chief, ko tsoro bata ji dare ne fa sosai donma akwai hasken Electricity tamkar rana.

Fitarta keda Wuya Batool ta farka sakamakon fitsari daya matseta Bayan ta fito daga toilet din ta dawo dakin Sai lokacin ta lura babu Unaisah, hankalin ta ya tashi tana fitowa ta hango ?ofar Falon abude kasancewar Unaisah bata datse ?ofar ba, nan take ranta ya bata fita tayi cikin sauri ta nufi kofar harta kusa Isa kwatsam Ta tsinkayi muryar Ummi cikin Kunnanta.

"Babe Ina zuwa" cak ta tsaya da tafiya, Ummi ta nufo ta cike da mamaki take duban kofar falo data gani a???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?buWe.

"Ina zaki haka da tsakar dare ko mayafi babu akanki? Wanene kuma Ya buWe kofar nan? Ko wani ya shigo ne?

cikin rawar murya ta fada mata babu Unaisah adaki, Da jin haka Ummi ta ruko hannunta suka bi bayan Unaisah, fitarsu keda wuya kofar falon ta datse silar bangazar da sukai mata..

Suna fitowa suka hango Unaisah tsaye agaban Security officers din gidan ta ru?e qugu, ashe sun ganta lokacin da take gudu tana kokarin karasawa ga kofar shiga bangaren Chief.

a hanzarce suka kewata suna tambayarta ina zataje da tsakar daren nan? Gaba daya sun fahimci bata acikin hayyacinta sai haki take muryarta na rawa ta furta wurin Chief zataje.

Officers din sukace mata ay basu dawo ba, don haka ta koma inda ta fito, ta fashe da kuka tana fadin ba inda zataje, ita ta gaji da zama cikn fargaba kawai su kaita inda suke.

rigima ta saka masu duk yadda suka kaiga zare mata ido da yi mata tsawa akan ta koma takiya har takaiga wani Soja yai kokarin kai hannu da niyar ya Wauke ta aikuwa ta gartsa mashi cizo har saida ta fasa mashi fata, ranshi ya 6aci matu?a harya daga hannu zai kwasa mata mari cikin zafin nama officer din dake a gefen shi Ya dam?i hannunsa da kakkausar murya yace"karka kuskura, In har ba so kake ka rasa aikin ka ba"

Yana huci Ya fusge hannun shi ya juya yabar wurin, lallashin ta suka cigaba dayi don su samu ta koma tace masu in har suna so ta koma su bude mata kofa ta shiga ta dauko wayarta data bari, Officer din yace ta fada masu inda ta ajiye wayar zasu kawo mata zuwa gobe yanzu dare yayi taje ta kwanta, kin fada masu tayi tace itama batasan inda ta ajiye wayar ba sai ta shiga zata duba, kuma a yanzu take son wayar"

Ba yadda suka iya da ita adole suka kira Layin Agent zahra saeed daya daga cikin na hannun Chief amintattunsa, saboda ba wanda zai iya bude kofar idan ba su din ba.

Saboda rigimar Unaisah yana bacci tare da iyalinsa yayi recieving call din su, bayan sun sanar da shi abunda ke faruwa yace su dauke ta su mayar part din, Officern yace mashi yalla6ai ba fa yadda zamuyi da ita, abokin aikinmu da yai gigin ta6a ta cixo ta gartsa mashi har saida ta fasa Fatar shi, yana can yana jinyar kan shi" da jin hakan agent zahra yace"tafi karfin ku ne? wai ma wacece acikin yaran" kallon ta officern yayi meye sunanki" muryarta ashake tace Unaisah..

"Sir sunan ta Unaisah, tana launin ido ruwan toka" da jin hakan okay yace su jira shi.

Adai dai lokacin su ummi suka karaso tayi mamakin ganin Unaisah tsaye gaban Security Officers, Hijab din jikinta ta jike sharkaf da gumi ta hade rai kamar bata ta6a dariya ba, tambayarsu tayi meke faruwa ne, anan officers din suka sanar dasu komai daya faru, batai mamaki ba ta riga tasan halin kayanta in taso abu kamar zawo take bata da uziri ko kaWan.

Batool ta tausaya mata sosai,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login