Showing 237001 words to 240000 words out of 413917 words

Chapter 80 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4470

ya Wauko ya buWe ya kalli ruwan dake a ciki, yakai hancin shi ya shinshina da sauri ya kawar da kanshi gefe saboda zaurin daya buso hancin nashi.

Hankalin hajjaty ba karamin tashi yayi ba ganin yadda ya haWe rai sosai, Waya bayan Waya ya buWe murfin robobin cikin matsanancin tashin hankali ya juyo a sukwane ya kalli hajjaty dake ta zare idanunta

"Ya akai haka"? Ya faWa yana dubanta

Muryarta na rawa tace"meya faru shiekh? Ban gane me kake nufi ba" haWe rai yai tamkar ba sheikh imam ba, da kakkausar murya yace"wanene ya canza ruwan maganun dana baki"! Rass taji gabanta Ya faWi ta fara zare na mujiya, jikinta ya hau yin kerma abunka ga matsoraciya kamar wata mara gaskiya sam takasa bashi amsar tambayar da yayi mata.

Hakan ba karamin bata mashi rai yai ba"baki ji ina magana bane! Wanene Ya canza ruwan maganin? Saboda ni ba haka na baki shi ba, gaba Waya an canza ruwan cikin shi, bayan ni a iya sanina launin ruwan maganin baya canzawa..." A fusace ya fada yana binta da kallon tuhuma
Hankalin ta idan yai dubu toh ya tashi, Gabanta ya dinga faduwa gaba daya tabi ta rude, ta rasa amsar da zata bashi, wlh kwata kwata bata lura da hakan ba, sai da yayi maganar ta tuna da lokacin da Wan aiken shi ya kawo mata maganin tabbas da ta buWe tana dubawa taga launin ruwan ya banbanta.

Wahalallan yawu ta haWiya cikin rawar murya ta furta"wallahi na rantse da wanda raina yake a hannunsa bani na canza ruwan maganin ba! Wlh bani bace, bansan wanene ba, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un..." gaba Waya tabi ta ruWe wata irin zufar tashin hankali ce ta wanke fuskarta, gani take kamar shiekh imam yana zargin ta.

Girgiza kai shiekh imam yayi"kin bani mamaki! Meyasa zakiyi mata haka? Ko dan kin gaji da jinyarta ne? Ni fa ban tursasa maki ba, aikin lada ne tun lokacin dana bukaci wanda zai kula da ita da kin fadamin bakiso ay da ba haka ba"

Runtse idanunta tayi, wasu zafafan hawaye suka wanke fuskarta, kalaman sheikh imam sunyi mata tsauri, taji Wacin su azuciyarta.

"ka yarda dani, wlh ni ba muguwa bace, bazan iya cutar da marwa ba, ina da zuciyar imani, ko kiyashi bazan iya cutarwa ba, balle Wan adam, wlh bani na canza ruwan maganin ba, na shiga ukuna"

ta fada tare da dafe goshinta da hannu daya.

tunda sheikh imam yaga yadda ta rikice nan take ya fahimci ba ita bace, dama da biyu ya furta


"Ya Isa haka, Na yarda bake bace, amma wanene toh? Dole akwai yarda akai aka canza ruwan, kuma koma wanene mutunne, lokacin da dan aikena ya kawo maki maganin a ina kika ajiye shi"? Waro ido waje tayi murya na rawa tace"a dakina"


Sheikh imam yace"hakan na nufin anan aka canza ruwan maganin kenan? To wanene? Akwai wanda ke shiga dakin ki ne"? Shiru tayi jim gabanta na faduwa da matsanancin karfi, hankalinta ya tashi, kwata kwata bata kawo ma ranta pravin ba, tasan bazai ta6a yi mata hakan ba, me ma zai kaishi canza maganin marwa? Har abada ba za ta bari wani yasan akwai alaka tsakaninta da pravin ba.


Tayi zurfi cikin tunaninta muryar sheikh imam ta katse ta"kinyi shiru baki bani amsa ba? Wakike tunanin ya canza ruwan maganin? In har baki fadamin gaskiya ba, zanje in fada ma baba obie abunda ke faruwa"

a firgice ta zare mashi dara daran idanunta, wani irin faduwar gaba ta ji daram kamar ana mata lugude a kirjin ta, arude ta girgiza mashi kai"kayi hakuri sheikh, wlh bani da masaniya, amma nayi maka alkawarin zan binciko koma wanene" jinjina kanshi yayi"kinyi alkawari? ?aga mashi kai tay"in har kika sa6a hmm kinsan sauran, keda baba obie ne" matse kwalla tayi, cikin sanyin murya tace"in sha Allah ba zan saba ba, amma sheikh meyasa kake tunanin wani ne ya canza ruwan? Baka tunanin bakaken aljanun jikinta ne sukayi mata hakan don kada ta samu sauki? In ba haka ba taya za'ay wani ya canza ruwan? Akan wani dalili"? Ta faWa tana kallon fuskar shi.

Murmushi shiekh imam yayi tare da dan girgiza kanshi kafin yace"ba al'janu bane suka canza ruwan, mutunne, dole akwai yadda akayi, ki zauna kiyi tunani ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????dakyau..."

Cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh,

"Sannan sheikh, akwai wani abu da marwa takeyi min, ni dai nagaza fahimta, duk in na shugo dakin zan bata magani, sai ta dinga goga hannunta a kasa, taita yunkurin yi min magana idan taga na kasa gane me take nufi saita kifa kanta jikin pillow...." bata ?are maganar ba sautin tarin marwa ya katse hanzarin su, sam sun manta da ita dakin, maganganunsu su ne suka farkar da ita

Atare suka kalle ta, tana a zaune kan mattress din, ta jingina kanta jikin bango, idanunta suna rufe ga siraran hawaye dake zarya kan kuncinta, gwanin ban tausayi


"Marwa"! Jin muryar sheikh iman yasa tay saurin bude idanunta.

tana ganin shi ta fara kokarin yin magana donta gaishe da shi sai dai takasa.


"Basai kinyi min magana ba, na fahimce ki," ajiyar zuciya ta sauke, idanunta sun kaWa jawur da su
Zukunnawa yai agaban katifar yana dubanta yace"Hajjaty ta faWa min da akwai wani abu da kike yi mata nuni da hannu ta kasa gane menene ko zaki nuna min in gani"?


da sauri ta Waga mashi kai, jikinta na kerma ta matso bakin kafitar, ta daura hannunta akan floor ta dinga goga su tana kallon sheikh imam cike da sa ran zai fahimce ta, ita dai hajjaty sai faman zare ido takeyi fatanta Allah yasa shikeh imam ya gane menene marwa ke son fada mata abun yana damunta.

A kalla marwa ta kwatanta mashi yafi sau biyar ganin kamar baigane ba yasa ta fara matsar kwalla.

zurfin tunani ya shiga can yace"wani yana zuwa dakin nan? Girgiza mashi kai tay alamar a'a"

"Ko ana tsoratar dake ne"? Still ta girgiza mashi kai, shiru yayi yana kara hasasowa can yakuma cewa"kodai kina son kiyi rubutu ne.. "Ga mamakin sa sai yaga ta daga mashi kai alamar eh hada Wan murmushin ta.

Hajjaty tayi mamakin jin hakan sosai, da sauri ta nufi drawer din marwa ta fara neman littafi dakyar ta zakulo wata jotter tare da pen, ta dawo bakin katifar ta buWe mata jotter din ta ajiye agabanta, ta zira mata pen din dakyar ta matse biron da hannayenta, ta soma kokarin gogawa paper din, lamarin ya daure masu kai, daga hajjaty har sheikh imam din, sun kagara da suga me ta ke son rubutawa.

Duk yadda taso ta rubuta sunan wanda yayi mata aika aikar takasa, biron yaki zama a hannunta duk ta cakalkala paper din akarshe ma ta yayyage, jefar da pen din tayi kasa ta fashe da kuka tare da kifa kanta jikin pillow, gaba daya jikinsu yayi sanyi, zuciyarsu ta raunata da tausayinta.

Cikin sanyin murya shiekh imam ya ce"kiyi hakuri, na fahimce ki, akwai wani abu da kike son fada mana, amma kin kasa, abunda nakeso dake ki kwantar da hankalinki, in sha Allah nan badajimawa ba ciwonki zai zama labari, zamu tayaki da addu'a sannan zan canza maki wasu magungunan.


tun tana shesshekar kuka hartayi shiru ta hakura musamman da taji maganar sheikh imam hankalinta ya Wan kwanta, har taji zata iya hakura har zuwa time da zataji sauki tunda bata da mafita.

Mikewa yayi tare da kallon hajjaty,

"ki zubda ruwan maganin dake a cikin robobin, zan kawo maki wani amma fa dole kiyi takatsantsan, kada ki kuskura ki bari wani yasan inda kika boye su ko kuma wani yasan na canza mata maganin nan daga ni sake wannan maganar, In kuwa kikai gangancin da wani ya sani har aka sake samun matsala to ki kuka da kanki domun kuwa bazan kyale ki ba...." a kausashe yayi mata maganar saboda ta Wauki maganar shi serious, baiwar Allah duk tabi ta rude jikinta har kerma yakeyi sai taji dama bata kar6i aikin ba saboda bata son abunda zai hana ta kwanciyar hankali.

Sallama shiekh imam yayi mata, ya fuce yabarta da jimami

________________________
'?

Zaune yake a gefen gadon shi, jikinshi sanye da voile fari, tafukan hannayenshi tallabe da qur'ni, Ya tattara dukkan nutsuwarsa akan kira'ar da yake yi, acan kasan zuciyar shi damuwa ce cunkushe baya jin dadin zuciyarshi saboda halin da Benazir take a ciki ya damu ita, yana matukar jin tausayin ta.


Yana tsaka da yin kira'ar, sautin knocking Ya katse shi


?aga murya yayi"wanene"?


"Ya shureim ni ce, Ina son yin magana dakai" jin muryar Benazir yasa shi saurin mi?ewa ya ajiye kur'anin Ya nufi kofar ya buWe mata, A hankali ta shigo ciki, jikinta sanye da abaya, tayi rolling veil akanta, hannun ta ru?e da yar purse dinta, ga wasu highhill da ta saka a kafarta, aruWe yake kallon ta ganin hada make up akan fuskarta.

"Ina kwana ya shureim ka tashi lafiya..."

"Lafiyalou sister, Ya jikin naki"?
"Naji sauki sosai" shiru sukayi fargaban shi kada tace yakaita gurin azeezaty ya san halinta in rigimarta ta motsa.


"Lafiya? Naga kamar kinyi shirin zuwa anguwa,"?

Murmushi ta sakar mashi
"Eh, gidan su anila nake son zuwa, jiya munyi waya da ita, ta fadamun yaronta baida lafiya, ashe shiyasa bata kira ta yi min ya jiki ba.." tun da tafara magana shureim ke kallonta gani yake kamar karya ta shirga mashi don ta samu yakaita gidan.


Ganin irin kallon da ya ke yi mata ne yasa tai saurin furta"wallahi dagaske nakeyi maka, bari in kira maka anilan ku yi magana" tay maganar tare da kai hannu ta buWe purse dinta, ta curo wayar ta kira layin anila tana fara ringing, ta mi?a mashi fuskarta dauke da murmushi.

"Assalamu alaikum, Anila barka da safiya"!

On the other hand tace"ya shureim ina kwana ka tashi lafiya? Ya jikin benazir din? Wlh junaid ba lafiya shiyasa ban samu na kira naji ya ku ke ba ashe ma har an sallame ta" ajiyar zuciya ya dan sauke.

"Lafiyalou anila, Benazir taji sauki, itace ma ta kira min ke, tace tana so tazo duba junaid, ubangiji Allah ya bashi lafiya, in sha Allah yanzu zamu zo"

"Allah Ya kawo ku lafiya, ngde" sallama sukayi ya mika ma Benazir wayar

"Ki bari sai anjima muje, yayi wuri yanzu" girgiza kai tay haWi da Waure fuskarta"ya shureim itafa ta nuna tana son inje yanzu"

"Naji, amma dan Allah idan mu ka je gidan, kada ki yi mata maganar yarinyar nan Azeezaty, nasan hada hakan yasa kike zumudin zuwa gidansu, kiyi hakuri Benazir yarinyar nan ba yarki bace idan kika sa hakuri in sha Allah kema zaki ga taki yar.."

dukar dakai kasa tay, idanunta suka ciko da kwalla.

"Kiyi hakuri idan maganata batayi maki dadi ba" girgiza kai tay'na fahimce ka, in sha Allah bazanyi mata maganarta ba, ay na hakura tuntuni" ajiyar zuciya ya sauke "haka nakeson ji, Kin fada masu mommy zaki fita" girgiza kai tay"a'a yanzu in zamu tafi sai mu gaya masu" amsa mata yai da toh

Kafin ya juya ya shiga ciki ya Wauko carkey dinsa Ya fito suka jera atare suka nufi dining room, mutanan gidan duk suna azaune suna yin breakfast, mutumin ya haWe fuska sai shan kamshi yake kamar iska tana mashi wari, abincin ma da aji da izza yake cin shi tamkar baya son tauna shi..

A fakaice hajiya layla take aika mashi harara kamar zata rufe shi da bugu, shi dai Alhaji ubaid ya nutsu Yana cin abin cin shi, yayin da zeenatu take fuskantar mommyn ta, sam takasa cin abincin ruwan lemu kawai take ta aikin durawa cikin ta, hankalinta da tunaninta suna akan Azeezaty, jiya har mafarkinta tayi, bata da burin daya wuce su haWu da ita, don ta tambayeta wacece Unaizah mai kama da itaS'

Takun tafiyar su shureim ne yaja hankulansu ga duban su,

Bayan sun karaso cikin girmamawa suka gaishe da su kowa ya amsa masu banda Alhaji musa hakan bai dame su ba, sun riga sun dan halinshi

mami ta dube su"ina zuwa haka shureim"?
"Zamuje gidansu anila ne, yaronta baya jin dadi" hajiya sarah tace"Allah sarki, itace kawar benazir wadda suke zuwa asibiti dubata ko"? Benazir ta amsa mata da eh"Allah ya bashi lafiya" mami tace"ay da kun fada min tun dazu dana shirya mun tafi atare, amma idan kun isa gidan ku kirani dan Allah" suka amsa mata da toh, Alhaji ubaid yace"ku gaishe min da mutanan gidan, ace ma anila inayi mata yamai jiki, Allah ya bashi lafiya, idan na samu lokaci zan shigo gidan" ya amsa mashi toh.

"Ya shureim zan biku dan Allah" zeenatu ce tayi maganar, har zata mi?e Alhaji musa ya jefa ta da wani kallo tuni tasha jinin jikin ta, muryarta na rawa ta furta"dan Allah daddy ka bari su tafi dani, mommy kice ya shureim ya tafi dani inaso in bi su" atsawace Alhaji musa ya furta"karki kuskura ki ?ara magana! " a tsorace taja baki tayi shiru, idanunta akan fuskar shureim dake kallon ta, wani irin tausayinta ne ya kama shi, yana so su tafi da ita sai dai yasan daddynta bazai barta ba.


"Musa ka barsu su tafi da ita tunda tana son zuwa..." Alhaji ubaid ne yai maganar,
Banza yayi da shi tamkar baiji abunda yace ba, hakan ya sosa zuciyar Alhaji ubaid musamman layla ranta ya 6aci, harara ta galla mashi akan idonshi, ita day hajiya sarah tayi shiru batace komai ba.


"Shureim ku tafi, Allah ya tsare hanya.." ta fada tare da yi masu alamar su je, ruko hannun Benazir yayi suka kama hanyar fita daga falon yana jiyo sautin shesshekar kukan zeenatu, har waiwayowa yayi sai kallon shi takeyi duk sai yaji ba dadi amma idan ya tuna abunda alhaji musa ya fada mashi sai yaji kwara zamanta agidan duk da shi baiga amfanin hakan ba saboda yayi imanin cewa Allah shi yake tsare bawansa aduk inda yake.

Har suka shiga mota, bai daina tunanin zeenatu ba, ta tsaya mashi aranshi yana jin tausayin rayuwarta

Tsawon mintina kafin suka karaso anguwarsu anila, motarsu ta na shigowa layin gidan suka hango anila atsaye cikin shiga ta abaya fara ta goya baby junaid abayanta, hannunta ru?e da wayarta..

Tunkafin su karaso ta Waga masu hannu alamar su tsayar da motar, agabanta yayi parking, ta nufi backseat ta buWe ta shiga ta zauna kafin ta warware goyan junaid ta kwantar da shi kan kirjin ta.

Dr shureum yayi zaton gidan zasu shiga har zai tada mota benazir ta ru?e hannun shi ya dubeta da mamaki"ba ciki zamu shiga ba, Anila ki faWa masa inda zamuje"

Cikin sanyin murya tace"ya shureim obie estate zaka kaimu" aruWe yake kallonsu da mamaki yace
"Bangane ba, me zakuyi acan? Anila fada mun ina fata dai ba gidan iyayen yarinyar nan zakuje ba"?

"Ya shureim muje kawai, zamuyi maka bayani daga baya, wani abune mai mahimmanci zai kai mu can" bai musa masu ba, yayi reverse ya mi?i hanyar fita daga unguwar


"Anila ya jikin junaid din! Ko dai shima duk plan dinku ne"? Murmushi suka saki, Anila tace"a'a ba plan bane, dagaske baida lafiya, amma jikin nashi da sau?i.."

"Meke damun shi ne"? Kafin ta bashi amsa junaid ya fara mutsu mutsu kamar zai farka hakan yasa tay shiru tana kokarin lalla6a shi don ya koma baccin.

Cikin kulawa dr shureim yace"Allah ya bashi lafiya" ta amsa mashi da ameen.


*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?*



*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Assalamualaikum inayiwa kowa ftn alkhairi

Bayani xamuyi amfani d wannan dama domin bayani akan wannan business din Mai tarin albarka da Kuma hanyar daakebi a samu kudi acikin sa =ص?=ظ?>?p?Abu na farko dai shi kasuwancin metaforce kasuwacine halattacen a musulunci sanan Kuma harkace ta crypto currency bayan haka Kuma decentralize project ne duk abunda akace decentralize to ba platform bane bakuma abune da xaa tafi d kudinka ba sannan a tsarinshi ba abune daaxace kasaka Abu kaza xaka kwashi kaza ba AA
Kamar yanda kukaji na fada shi wannan business ne yanada tsare tsare xaki samu kudade a cikinsa maxajen kudade matuqar kinbi tsarin wannan kasuwanci yanda ya dace matuqar kinyi register da wannan tsari na META FORCE xaki amfana fiye da tunaninki Yar uwa bake kadaiba harta da Yan uwa ki da abokanan arxiqi duka xasu amfana Dake insha Allah ammanfa idan kinyi register d wannan tsari Mai albarka insha Allah kada na cikaku d surutu bari mushiga Kai tsaye domin Jin yanda tsarin kasuwancin yake>??? B&?>??? B&?=؃??s?>?s?>?s?<؉?<؉?<؉?=?B?<؉?<؉?


Hanya ta farko akwai referral daga lokacin da kikayi idan kikaci damara kika dage da kawo referral toh tabbas company xata biyaki =د? percent Kuma xata biyaki da dollar gwargwadon level din da mutum yayi register a qasanki metaforce wannan dadi=؃? A misali kika kawo mutum uku a level 1 sukayi registration a kasanki company xata baki 5 dollar
Idan kika kawo mutum na 4 company xata baki 5 dollar
Idan kika kawo mutum na 5 company xata baki 5 dollar idan kika hada duka kinka kinsamu 15 dollar kin maida kudinki sau 3 =؃??s?>?s?>?s?
Bayannan samun spillover tana daya daga cikin hanyoyin da ake samun kudin da wannan business na metaforce matuqar ana aiki a team dinki xaku dunga samun spillover wannan kyautace d company ke bayarwa ga Wanda ke d rabo=؃??s?>?s?>?s?<؉?<؉?<؉?<؉? me kika mantane hajiya kixo kiyi register tun lokaci bai kure maki ba
Hanya ta gaba bayan kinyi registration akwai kyauta d company ke bayarwa na TR shi Kuma wannan kyautace da nan gaba xaki amfana da ita nan gaba kadan wannan coins din da xasu baki yanada daraja shiyasa akeso kiyi babban level tun kafin adaina badata>?p?>?p?>?p?

Abu na gaba akwai force coins wannan coins ne Mai daraja Wanda sai kinyi register da METAFORCE =ز?=ز?=ز?
Sannan xaki samu damar mallakarsa Wannancoin din ana sa ran nan gaba idan ya shiga kasuwa duniya xaiyu kudi fiye d Bitcoin saboda irin yanda tsarinsa yake tun ynx Wanda suka mallakeshi sun fara gani
Alhmadulillah da xuwan META FORCE =؃? Yar uwa da wannannanne nake kiranki d babbar murya daga ranar da kikaci karo da wannan typing din nawa kisa a ranki arxiqine ya kwankwasa maki kofa saboda da akwai alkhairi Mai tarin yawa a META FORCE ga wandanda suke

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0