Showing 99001 words to 102000 words out of 413917 words

Chapter 34 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2711

na ganin ta haWu da Wan uwanta gabriel, ba ta son ta mutu batare data gana da shi ba, daba don shi ba da tuni ta jima da kashe kanta.


Watsa wa tayi da gudu ta nufi kofar shiga toilet dinsu ta buWe kofar ta shige taja ta rufe, tana faman jan numfashi kamar daga sama taji dirar mutun a toilet din kamar aljani haka Ya faWo mata tuni la66anta sun fara kakarwa muryarta na rawa ta soma faWin karka kuskura ka ta6ani!! kada ka matso kusa da ni, ka ?yaleni, Idan ka cutar dani dan uwana bazai kyale ka ba sai ya kashe ka..."

sambatu tadinga yi cikin rawar murya mai haWe da tsantsar tashin hankali da fargaba sam ta manta cewa giant basa ji basa gani, kallonsa take kamar dodo gaba Waya inuwarsa ta lullu6eta.

?an uwanta dake zazzaune kan gadajensu tuni zafafan hawaye sun wanke fuskokin su lokacin da suka fara jin sautin kururuwar gabriela ta cika dakinsu da wani irin azababben sautin kuka mai ?araji tamkar ana zare ranta nan take suka fahimci abun da giant din yake yi mata, ha?i?a zuciyar su ta yi matu?ar karaya.


Tsawa dattijuwar ta kwatsa masu babu digon imani aranta

"kar in kuskura in ?ara jin sautin koke koken ku, ko da tari ne bana son ji idan ba haka ba, zansa ay maku abun da akai mata" jin wannan maganar yasa sukai shiru, kukan nasu ya koma na zuci.

Tsawon mintuna goma cuf, Kafin giant din Ya fito daga makewayin sanye cikin kakinsa kamar bai aikata wani abu ba..

Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwar tayi idonta akan giant din ta jinjina masa da yatsan ta.

Kafin ta juya cikin takun izza ta nufi kofar makewayin nasu ta buWe kofar tasakai ta shiga.

A kwance ta hango ta kamar matacciya babu sutura a jikinta sai faman sakin nishin azaba ta ke yi numfashinta na fita da hucin zafi, ga wani jini dake gangarowa ta tsakankanin cinyoyin ta, baiwar Allah ko ina na jikinta Ya raunata kwata kwata bata acikin hayyacin ta, ita kaWai tasan tartsatsin azabar da ta sha, cikin fitar hayyaci take ambaton sunan Wan uwanta gabriel, yayin da hawaye ke tsastsafowa kan kincinta masu Wumin gaske, idanunta sun juye jawur kamar garwashin wuta, takasa tsaida gangar jikinta sai birgima takeyi saboda zogin azabar da gabanta yakeyi mata.

Zu?unnawa dattijuwar tayi saitin inda take, muryarta da gadara tace"bakin ki ne Yaja maki! Nayi mamaki da har kika Iya rayuwa, ay nayi zaton zanzo na same ki awargaje babu rai, amma saboda taurin kai har yanzu numfashin ki bai daina fita ba...." ta ?are maganar tare da tofa mata yawu mai yau?i kan fuskarta har cikin idanunta Ya shiga.

"FaWa da aljani ba riba, wannan somun ta6i ne, nan gaba idan kika kuskura kika sake yunkurin yi min rashin Wa'a farfesun namanki zansa ayi min shashasha kawai' ta faWa tare da kai hannu ta dam?i sarkar cross din wuyan gabriellah taja ta da karfi ta sha?e mata wuya, birgima tadingayi cikin fitar hayyaci ta soma kokarin ceton kanta sai dai ta gaza, dattijuwar bata kyale ta ba har saida taga ta daina motsi jikinta Ya saki tukunna ta ?arasa balle sarkar ta jefar da ita gefe Waya, fatar wuyanta tayi jawur saboda shakar da tai mata.....

Mikewa dattijuwar tayi fuskarta babu fara'a ta sanya ?afa ta naushi cikin gabriela tsabar rashin imani duk da ta sumar da ita hakan bai mata ba...

Fucewa tayi daga toilet din, ta ba giant umarnin ya dauko gabriellah, yan uwanta na kallo ya fito da ita zindir babu kaya ya ratayata kan kafadarsa suka fice daga dakin, kamar jira suke su tafi gaba daya suka rushe da kuka mai cin rai, ha?i?a sunji zafin abunda Ya faru da gabriela saboda suna sonta, tana taimakon rayuwarsu wurin kwantar masu da hankali idan damuwa ta addabe su sai gashi yau sun gaza taimakonta sunaji suna gani anci zarafinta an wulakanta rayuwarta.

Allah kadai Yasan Ina zasu kaita? Zata rayu ko ta mutu?

________________________Gabriel=???

A firgice Ya farka daga bacci, hannunsa dafe da saitin zuciyarsa dake harbawa da karfi da karfi, fuskarsa ta ji?e sharkaf da gumi.

La66ansa na kerma ya soma ambaton inna lillahi wa inna ilaihirraji'un.

zuciyarsa ce batay masa dadi, kuma yana ji aransa wani mugun abunne ya faru da yar uwarsa dake acan gidan kurkukun ?addara, saukowa yai daga kan gadon su, yakai hannu ya kunna switch din dakin haske ya gauraya ko'ina, idanunsa sun cika da kwalla, gaba daya ya rasa meke masa daWi.


A hankali yake yin tafiya kamar wanda aka zarewa laka sam babu karsashi a jikinsa, toilet ya shiga bayan ya fito ya nufi closet dinsu ya canza kayan jikinsa da jallabiya, kafin ya tsaya kan darduma ya fara jera nafilfili saboda yai mata addu'a.

Bayan ya kammala jiki asanyaye ya Waga hannayensa sama ya fara addu'o'i hawaye na wanke fuskarsa

Shesshekar kukansa ce ta farkar da naufal, tunkafin ya bude idanunsa kunnansa suka soma jiyo muryar sajeed Yana fadin"Ya Allah kada ka bari acutar min da ita, Ya Allah ka kare min ita daga sharrin duk wani abun cutarwa...

Da wata irin kasala naufal ya sauko daga kan gadon yaje gefen prayer mat din Ya zu?unna Yana dubansa.

"Sajeed meke damunka ne naga kana kuka"?

Idanunsa jawur ya kalle sa"Naufal bana jin dadin zuciyata, ina ji araina wani abu Yana faru da gabriela, kwata kwata banyi bacci mai dadi ba"

Dafa kafadarsa naufal yai cikin kulawa da nuna tausayawa yace"meyasa baka ta da ni munyi sallar atare ba"?

"Bana so na takura maka" girgiza kai naufal yayi"babu takura, nima yar uwata ce sajeed, zan iya hana idona bacci don muyi mata addu'a"

Kallonsa kawai yai ba tare daya ce masa wani abu ba.

"bro ba ka tunanin Danish zai Iya taimaka mana? Da alamun ruWu sajeed ya furta"bangane me kake nufi ba"

Naufal yace"ina nufin me zai hana mu nemi taimakonsa akan ya Wauko mana yar uwarmu, tun da yana da ?arfin da zai iya yin hakan"

"tayaya zai iya zuwa gidan kurkukun ?addara Ya taimake ta? ni bazan Iya tunkararsa da maganar nan ba, saboda bana so ya sake shan wahala, Za su Iya cutar da shi idan Yaje......." Ya faWa Yana faman matse kwalla, kafin wani Ya kuma furta kalma sautin motsin buWe kofar dakin su Yaja hankulansu ga duban door room din, kusan a tare ?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? suka zabura suka mike tsaye suna kallon shi babu wanda Yayi zaton shi ne, saboda bai ta6a shigowa bedroom din su ba, watakil Yana Wan zagaye gidanne Ya jiyo sautin muryoyin su shiyasa ya shigo dakin na su

Har suna baki wurin gaishe da shi cikin girmamawa.

Bai amsa masu gaisuwar ta su ba, gaba daya hankalinsa na akan fuskar sajeed, farar jallabiya ce a jikinsa ta kamasa.

"Meke faru ne"? Ya jefa masu tambayar, da sauri naufal Ya nuna sajeed da yatsa"shi ne ke kuka"

takawa yayi a hankali Ya karasa gaban sajeed yakai hannu ya dafa kafadarsa

"I'm sorry nayi maku la6e, ba hali na ba ne, na fito ina zagaye gidanne sai najiyo voices Winku kuna magana, bakomaine Yaja hankalina ba, face sautin kukan ka, fadamin meke damun ka" da wata irin sanyayyar murya mai haWe da kasalar bacci ya furta maganar

Sajeed bai 6oye masa komai ba, dangane da Sister dinsa, ba zato ba tsammani yaji chief Yai huggin dinsa da hannu biyu kamar kaninsa, tuni yaji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarsa kamar an yaye mashi damuwar shi, a hankali chief ya daura hannu daya kan bayan sajeed Yana Wan bubbuga masa bayan cikin sigar lallashi muryarsa kasa kasa kamar tameyin raWa ya furta"ka cigaba da yi mata addu'a, Allah Yana atare da su, kuma Yana sane da duk wani hali da suke a ciki, in sha Allah komai yazo karshe, In har sister dinka nada tsawaicin kwana zata rayu ne kamar yadda kuma kuka rayu bayan wahalar da kuka fuskanta....." daWaWan kalamai chief ya cigaba da furta masa, ko a mafarki ba su ta6a tunanin chief zai shigo bedroom dinsu balle har ya rungumi Waya daga cikin su, sun kara ganin darajarsa da kimarsa a idanun su, sunyi mamakin hakan sosai, mutumin ya ?ara siye zuciyoyin su.
Sai da ya tabbatar Ya kwantar masa da hankali kafin ya raba jikin su daga na juna.

Fuskarsa da damuwa ya furta"time din sallar asuba yayi, ina jiranku a falo ku shirya mu tafi masallaci, ku sanar da sauran yan uwanku maza" amsa masa sukai da toh, gently ya juya har Ya kusa fita daga dakin muryar sajeed ta ratsa kunnansa.

"Nagode chief, kamar yadda ka faranta min rai, kaima Allah Ya faranta maka naka"

Ba tare daya juyo ya kallesa ba Ya furta"Ameen, but ku kira ni da sunana Owais, zanfi jin daWi"

Murmushi suka saki atare suka hada baki wurin furta"Yaya Owais" jinjina kansa yai kafin Yasakai Ya fuce daga dakin, wayyo Allah dadi kamar jira suke Ya fita, da sauri Sajeed Ya ruko gaban rigarsa ya soma shinshina kamshin turaren chief.

"Naufal shinshina kaji" shinshinawa naufal yayi sai dadi suke ji
"Wallahi baka ji dadi ba daya rungune ni, sai naji kamar an wanke min damuwana, mutumin Yana da mutunci sosai komai nasa yana burgeni....." santin chief suka cigaba dayi.

Kafin daga bisani naufal yace"yana fa jiranmu zamu tafi masallaci, mu yi sauri mu shirya"

=???UNAISAH ANGEL=???

kiran sallar asubahin farko, wayarta ta fara ringing kamar zata fasa kunnuwan su, cikin duhu ta farka tare da laluba hannu ta dam?o wayar dake ajiye kan nightstand ta Wago da ita ba tare da ta duba sunan mai kiranta ba tai picking

"Unaisah! Ina kika shiga inata jaraba kiran layinki bana samu" wata irin zabura tayi aWan ruWe saboda bata gane wacece ba.

"Nasan baki gane mai magana ba, Aunty pretty ce"

Ajiyar zuciya ta sauke muryarta da kasalar bacci ta ce "Yanzu na gane, Ina kwana kin tashi lafiya"

"Ki yi hakuri na katse maki baccin ki, na damu da son jin awani hali kike a ciki kwana biyu ba ki neme ni ba"

Muryarta adidashe Tace"ba komai, nima kina araina"

"Ban yarda ba, meyasa baki kara kirana ba? Ni ay fushi ma nake dake, kin manta dani" muryar benazir da alamun 6aci rai tay maganar.

"Ba haka bane wallahi ban manta dake ba, nayi rashin lafiya ne amma yanzu naji sau?i, wayar ma bata a hannu na sai jiya na kar6e ta"

Tana jiyo sautin muryar aunty pretty tana zabga salati gaba daya ta ruWe jin bata da lafiya

"Inna lillahi! Yanzu ya jikin naki? da sauki?

Murmushi unaisah tayi jin yadda ta ruWe"ay na fada maki da sau?i yanzu"

Tana jiyo sautin ajiyar zuciyar ta
"Har naji sanyi araina, Allah ya ?ara maki lafiya, wallahi baki ji yadda naji ba saboda na damu dake, dan Allah Idan nan abuja kuke da zama, ki bani dama inzo gidan ku, dama yau nakeson fita anguwa"

waro idanu unaisah tayi da sauri tace"a'a ni ban ma ta6a zuwa abuja ba, a kano mu ke"

"Allah sarki, kinyi min nisa, in sha Allah wata rana zan kawo maku ziyara"

"Nagode da kulawarki a gare ni" sun jima suna waya kafin daga bisani su ka yi sallama, ta ajiye wayar tana faman sauke ajiyar zuciya, ita kanta tana son haWuwa da matar sai dai tasan ba abune mai yiwuwa ba, na farko batasan wacece ita ba? Idan har dagaske number da take amfani da ita ta sajeed ce me zai biyo baya?

da wannan tunanin ta sauko daga kan gadon ta kunna hasken dakin nasu

a hankali ta sauke idonta kan Deeja dake bacci tana jan minshari kwatsam taga ta fara mirginawa zata faWo ?asa daga kan gado, cikin zafin nama ta yi hanzarin tallabota a hankali ta wurga ta kan mattress din

Murmushi ta dan saki kafin ta juya ta shiga toilet, har yau tana mamakin jinin daya dauke mata tun bayan da ta sha bakar wahala bai dawo ba, har cikin ranta bata ji dadi ba, saboda taji ance alamun girma ne ga mace, kuma idan tanayi boobies Win ta zasu kara cukowa sannan hips dinta zai ?ara faWaWa komai ma na jikinta zai canza ta zama cikakkiyar budurwa, a gaban sink ta tsaya tana lalubar wurin don taga idan za'a samu ko da alamunsa ne sai dai bata ga komai ba...." fuskarta ayamutse ta kalli mirror kamar zata fasa ihu haka take ji, ita da take son ta zama house wife idan har bata fara wadannan abubuwan ba ina ita ina iya zama matar aure? ta faWa aranta, kafin ta sa hannu ta zame wuyan rigar baccin ta, ta soma le?en kirjin ta, murmushi tayi ganin sun ?ara girma ba laifi, wani irin dadi ne Ya lullu6e ta, har yau bata bari danish ya gan su ba, saboda kullum in zata sanya kaya sai ta Waure su tamau don karsu fito.

jujjuyawa ta yi agaban mirror din tana kallon qugunta, ni dai na rasa me angel take ma zumudi, da alama batasan meye ake azaman auran ba.

Gaba Waya matasan gidan sun tafi masallaci, bayan sun kammala sallah shiekh imam ya zaunar da su don suyi karatun da yake biya masu kullum.


Fitowa yai daga bathroom, waist dinsa daure da towel fari, gaban dressing mirror Ya tsaya zuciyarsa cike fal da tunanin halin da sajeed ke aciki, saboda Ya damu da yaran musamman wadanda ke acan gidan kurkukun ?addara sun tsaya masa a zuciyarsa, ayanzu baya da wani buri da ya wuce su kai masu Wauki, shaf shaf Ya shirya kanshi cikin dark jeans tare da v neck shirt ta Wame fatarsa.

Hayewa yai kan gadonsa ya daura kansa bisa pillow, hannunsa ruke da wayarsa, layin Boss Ya danna ma kira bayan yai picking suka gaisa da juna

"Inason ganinku, tare da salsabeel a room dina" amsa mashi boss yayi da toh"

Bayan wasu ?an mintuna, wayarsa tai alert, unclock Ya danna a hankali kofar ta buWe suka shigo su uku, cikin girmamawa suka gaishe da shi ya amsa masu

"Have a seat" ya fada Yana nuna masu couch, zama sukai suna fuskantar sa... Ya Wan dauki lokaci kafin ya dan bude idanunsa dake a lumshe ya dubesu daya bayan daya kafin ya tsayar da idanuna akan salsabeel

"me yakamata mu yi? bana son abun yadau lokaci, ko dan saboda sauran yaran dake fuskantar barazana da bu?atar mu kai masu dauki....." babu wasa akan fuskarsa yai maganar


Calmly Salsabeel Ya fara magana"yalla6ai, ni bani da hanyar da zan iya jagorantar mu zuwa gidan kurkukun ?addara, saboda garkuwar sihirina ta karye kuma ina da tabbacin daga wajen su ne suka yi min hakan, amma nasan Wan uwana zai Iya taimaka maku, shi kadai ne yasan hanyar da zai shigar daku Gidan kurkukun ?addara amma fa dole mu bi komai asannu kada muyi gaggawa saboda gidane mai hatsarin gaske, wani irin kurman ginine idan har baka da ilmi akansa kai kuskuran shiga kwakwalwarka zata iya ta6uwa"

Jin wannan maganar daga bakin salsabeel Yasa Taj da big guy suka kalli junansu da alamun rudani.

"Amma idan har Garkuwa ne zaiyi maku jagora shi ya san ta yadda zai shigar daku ba tare da kun sha wahala ba, amma fa da wuya danish Ya bamu haWin kai, mutum ne mai wuyar sha'ani yana da kafiya, kuma har yanzu shi garkuwar su ne zasu iya sarrafa shi daga can kurkukun, ni dai ashawarata tun yanzu ku fara jan shi a jiki kuna koya masa abubuwa masu mahimmanci kamar rubutu da karatu tun da baisan komai ba ta hakanne zai fara sakin jiki da ku har asamu abun da ake so" gaba Waya sun gamsu da bayanin salsabeel.

Numfasawa chief yai kafin ya ce"in sha Allah zamu yi ?o?arin jan shi a jiki,"

Big guy yace"ni abunda ke Waure min kai da yaron kwata kwata baya son mutane su rabe shi in ba yan uwansa ba, kuma baya son wani ya rabi yan uwansa, meyasa"? ya tambaya yana kallon salsabeel

"Rashin sabo ne, idan Ya saba da ku zai daina, amma fa da bu?atar ku guji bata masa rai, in har ya nuna baison abu to kada ayi masa in ba haka ba komai zai iya faruwa, idan ransa ya 6aci evil heart Winsa zata iya motsawa abun da bana fata" ta6e baki big guy shi dai har yanzu bai yarda da Danish ba.

Shiru sukayi na wani lokaci

"I understand that dealing with them won't be easy." gaba Waya suka maida duban su ga chief da yai maganar

"in sha Allah, zamu yi zaman tattaunawa tare da chief of army, da kuma commender na america, bayan haka za mu tuntubi rassan jami an ISOD da ke wasu kasashen, saboda taron ya shafi kowa da kowa. Dole ne mu hada kai kafin mu ci nasara a kansu. "

"Haka Yakamata yalla6ai" suka fada atare

Lumshe idanunsa yai gaba daya sun fahimci damuwar abunne ke addabar zuciyarsa

A lokacin da basuyi tsammani ba suka ji ya furta"na rantse da wanda raina ya ke a hannunsa wallahi duk wanda na kama da sanya hannunsa a kungiyar matsafan kurkukun ?addara sai ya WanWani kuWarsa ko da kuwa mahaifina ne bazan raga masa ba, ..., " yayin da yake yin maganar idanunsa sun kaWa jawur saboda tsantsar 6acin rai

"In sha Allah sir mahaifinka ba zai ta6a zama Waya daga cikin su ba..." kafin taj ya ?are maganar chief yai hanzarin katse sa yana huci yace"nima ina fatan hakan amma nasan mawuyacin abune, boss bana son na zurfafa bincike saboda fargaban kada inga wanda banyi tsammani ba, Ina jin tsoron ace akwai sanya hannun wani a family dina zuciyata zata karaya watakil ma hakan zaiyi silar da zuciyata zata buga...." ba su ta6a ganin tashin hankali tsantsa akan fuskar chief irin na yau ba, kwata kwata babu walwala atare da shi
Hada baki sukai wurin kwantar masa da hankali suna bashi baki, dakyar suka samu ya lafa yana faman sauke ajiyar zuciya ya kifa kansa jikin pillow... Bai sake dagowa ba, kamar bacci ne yai awon gaba da shi.

Mi?ewa sukai atare suka bar dakin, zuciyoyin su cike fal da tashin hankali, su kansu tsoron ranar da asiri zai tonu suke yi saboda sun san dole akwai na jininsa, a kwanakin baya ya ta6a basu labarin kiran sirrin da wani bawan Allah yake yawan yi masa akan Ya binciki danginsa akwai bara gurbi acikin su wadanda suke sadaukar da yaran family Winsu har faWa masa yai yaran da ake haihuwar su a mace ba mutuwa sukai ba suna nan da yaransu, bai ta6a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login