Showing 24001 words to 27000 words out of 413917 words

Chapter 9 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4454

"Har hotunan shi ka ajiye awayarka, lokacin da naje tada ka daga bacci naga hoton shi da kake kallo a wellpaper na wayar ka, mijina anya kuwa kana da lafiya?
Ta faWa fuskarta da tsantsar Al'ajabi
Lumshe idanun shi yayi bai san amsar da zai bata ba
"Akan yaron da bakasan ko wanene ba kake nema ka rasa sarrafa zuciyarka? What kind of crazy love is this? Na ruWe please ka fahimtar dani' ta fada tana zare mashi kyawawan idanuwanta

"You don't know who he is, you have no connection to him, so why would you cause yourself so much pain for loving him" Cikin tausasa murya tayi maganar, bawan Allah yayi shiru yana sauraranta ya rasa abun fada.

"Hankalina ya tashi hubby, kwara mubar kasar nan tunkafin In rasa kanka, Maybe if we distance ourselves from him, you'll be able to forget about him.... " cikin karyayyar murya tai maganar, fuskarta duk ta yamutse.

"Idan ma akan rashin haihur Wa namiji da baka samu bane yasa kake son shi, nayi maka alkawarin zan dage da addu'a akan Allah ya bani ciki na Wa namiji nima na haifa maka ko hankalin ka ya kwanta, zan kira mahaifina in fada mashi yasa ayi min addu'a...." tuni idanunta sun cicciko tab da kwalla, nan fa hankalin shi ya tashi don ko kadan baison 6acin ran gimbiya mujeedat gaba Waya yake rasa sukuninsa, da sauri ya janyota jikin shi.

ya rungumeta sosai yana lallashinta,
"Na gane kuskure na, ki yi hakuri gimbiyata, nima bayin kaina bane bansan ya akai na kamu da kaunarsa har haka ba, amma tun da baki so na daina, zanyi kokarin mantawa da shi arayuwana....' lallashinta yaci gaba da yi har sai da yaga ta dan saki jikinta kafin ya Wago da ita.

chain mask dinta Ya gyarata mata ganin ya karkace, bayan ya gama suka kalli juna lokaci Waya suka saki murmushi, yatsun hannun ta ya ru?o ahankali ya daura mata soft lips dinsa hadi da sumbatar su, ya kuma dagowa ya sumbaci forehead dinta, sai da ya tabbatar ya faranta mata almost 15 mins, tukunna ya mayar da rigarsa, kafin Yaja hannun ta suka nufi kofar fitowa daga room din, Jami'an dake a bakin door suna jiran su, ganin sun fito yasa suka take masu baya.

Suna gab da zasu ?arasa ga mazaunin su, ba zato ba tsammani Hasken Hall Win Ya Wauke gaba Waya duff ko'ina Yayi duhu sai hasken candles din dake a kunne, Hankalin jama'a ba karamin tashi yayi ba, Kowa Ya ruWe sautin muryoyin su Ya cika hall din Kowa sai tambaya yake yi ya akai aka dauke wutar hall din ko an samu matsala ne
"Jama'a wai meke faruwa ne? Meyasa za'a Wauke mana hasken Hall? Ba'aji ina magana ba ne"! Hajiya saratu ce take ta faman surfa masifa Sautin muryarta yafi na kowa
Faryat Har ta fara Fasa masu ihu saboda lalurar dake gare ta na rashin son duhu gaba Waya take firgicewa ta dinga kuka tana iface iface, Jazz na jin sautin ta jiki na bari ya shiga laluban ta cikin duhu cikin sa'a Ya cafko hannunta ta ?an?ame shi tana kuka....

"Wannan wani irin rainin wayau ne za'abar mutane cikin duhu? Hajiya laurat ce ta faWa atsiwace ran kowa Ya harzu?a, Hankalin zahra ba karamin tashi yayi ba fargaban ta kada ace Aikin decoration dinsu ne Yajawo matsalar, tuni ?an hanjin cikin ta suka kaWa ido ya raina fata, harta fara tunanin zuwa prison.

_Kwatsam ba zato ba tsammani, A lokacin da kowa Ya gama rikicewa wani Haske mai ?yal?yali daga saman ceilling Ya soma baiyana A hankali Ya ke haskaka bakin ?ofar shigowa Hall din, gently ya dira ?afarsa kan Polished marble floor din wurin A matu?ar ruWe suka kai idanunsu kan mai shigowa yayin da zuciyoyinsu ke harbawa da ?arfi ?arfi_



(Mu hadu monday idan Allah ya kai mu da rai da lafiya in sha Allah)

*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*

*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*
[10/1, 18:57] +234 903 893 6460: _ *~
'=؋?BOSSLADIESWRITERS=؋?
'~*_



3,F 'DB/1=؋?
'=?%?


~Takun ?arshe=?%?~



B5) -( 1HE'F3J) :J1 9'/J) (JF 'D3,F'! E9 *7H1'* E9B/)=؋?=ؘ?=??


An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists d'=؋?=ؘ?



Daga al?alamin Boss Bature=؋?
'



__________________________
'?



Gently ya dira ?afarsa kan Polished marble floor din wurin A matu?ar ruWe suka kai idanunsu kan mai shigowa yayin da zuciyoyinsu ke harbawa da ?arfi ?arfi.

Lokacin daya ?arasa shigowa ciki, Gaba Waya Suke bin shi da kallo mai cike da tsantsar ruWani, idanun kowa akan zazzafar surar jikin shi, kasancewar ya sanya face mask hakan ya 6oye ainihin suffar fuskarsa, wato wata hadaddiyar Emirati thobe ce a jikin shi yar ubansu launin Black gold, yadda kasan a jikin shi aka Winka ta saboda yadda ta bi shape nasa, ta baiyanar da surar shi mai matu?ar jan hankali, Musamman sick packs din kirjinsa ya fito 6aro 6aro, da murWaWWan damtsensa, abun ka ga dogon namiji komai nashi is exraordinary, farar fatarsa kuwa har wani sal?i take tana walwali, yadda kasan namijin hurul aini tsabar kyau da daukar ido, wrist din hannun sa na asanye da agogo ?irar Rolex sai ?yalli take, face mask din dake lullu6e da fuskarshi dai dai ?asan idanunsa ya rufe kyawawan sexy eyes dinsa waWanda ke a kewaye da lallausan long eye lashes dark brown sun ?ara ?awata kyawun idanunsa, yalwatacciyar sumar kanshi kuwa tasha gyara har ?yalli take, gaba Waya gashin an tattare shi an Waure yasauka har kan gadon bayan sa, Wani irin sanyayyan ?amshin turare ne ke fita daga jikin shi mai narkar da zuciya,

Hankali fa gaba Waya ya tashi da ganin Wan tahalikin nan, tun kafin ma ya buWe fuskarshi sun gama girgiza da kyawun shi, kowannansu sake sake yake a zuciyarsa wanene wannan? Daga ina Yake?

Zuciyoyinsu ba su gama kiWima ba, sai da su ka yi tozali da kyakkyawar matashiyar dake shigowa hall Win ta bayan shi, wohoho zo ka ga yadda idanu suka koma kanta, from head to toe suke kallon ta, ta Wauki wankan Embroidery Open front baya, launin black anyi mata adon gold stone works da zanan Red flowers, rigar tayi masifar yi mata kyau, ta yi rolling mayafi akanta, itama fuskarta asanye da face mask take, ?afafuwanta kuwa Highhills ne jigunanu, Tsabar ruWani Ya hana kowa na hall din furta magana sai dai su bi da idanu kamar kurame, ko da shigowarta daga gefen shi ta tsaya, Jim kadan suka cigaba da shugowa kowan nan su da face mask, matan cikin shiga ta abaya mazan kuma Emirati thobe ne a jikin su, sai da suka cika su goma sha Waya cuff tukunna suka dakata suna kallon kallo atsakanin su da mutanan hall din, ga dukkan alamu bakin su ya mutu, saboda babu alamun zasu furta magana, lamarin ya ruWar da su, mamakin su ina aka samu wadannan matasan yan matan da samari? Daga gani dai ba yan nahiyar su bane saboda komai nasu is exraordinary, dai dai da yanayin tsayuwarsu abun kallo ne kamar a shirin drama.

A ?alla an shafe tsawon Mintuna ana jifar juna da kallon ?urulla, da?yar Hajiya saratu ta samu ?warin giwar buWe baki ta furta"Su wanene ku"? Ta jefa masu tambayar tana mai zare idanu

"Bayin Allah daga ina ku ke? Wanene Ya gayyace ku dinner din nan? Meyasa ku ka rufe fuskokin ku da face masks? Hajiya Madina ce tayi maganar a ?agare da son jin amsarsu

Gaba Waya mutanan hall din suka matso gab da su, kamar sunga sabbin halittu daga wata duniyar

"To ko dai mutanan boye ne? Wai ba zakuyi mana magana ba, kuntsaya kuna kallon mu kun bar mu a cikin duhu"! Da tsiwa hajiya laurat ta faWa tana tada jijiyoyin wuya.

"Anya kuwa waWannan ba mutanan 6oye bane? Nifa wlh hankali na bai kwanta da su ba, akan me zaku faWowa mutane Wakin taro babu sallama? mun tambaye ku su wanene ku kun yi shiru ba ku tanka mana ba, ko dai turo ku akayi ne don ku tarwatsa mana taron mu"! A faWa ce Hajiya saratu ta kuma yin magana, Hankalin fa kowa Ya tashi wasu sun harzu?a, su kan su tsabar fargaba ne ya hana su buWe baki suyi masu sallama, duk sun sha jinin jikin su.

Baba obie da Manyan mutanan canada sunyi kasa?ai Suna Kallon su tamkar a shirin drama, sam babu alamun sun tsorata da ganinsu saboda sun san akwai jami'an dake tsaron gurin dole akwai wanda ya gayyace su, sai dai zallar mamakin dake shimfiWe a kan fuskokin su.

?an matasan family din maza da matansu sunyi cirko curko suna kallon su, cike da son sanin su wanene wadannan bakuwar fuskan da suka faWo masu a hall!!!

Mc da ke atsaye ya ru?e mic sai mazurai yake yana fadin"ga dukkan alamu mun samu ba?i daga jinsin aljanu, suma sunzo taya mu jimamin tafiyar prime minister Hateem, wannan abun mamaki ne da al'ajabi, lallai prime minister ba karamin mai farin jini ba ne......." sai sambatu mc yake yi yana dubansu babu alamun wasa akan fuskarshi, bilhakki dagaske yake koro jawabi, su sir mubarak kuwa jira kawai suke suga iya gudun ruwan wadannan bayin Allahn da suka faWo masu bagatantan babu sanarwa.

Sannu A hankali sautin takalman prime minister ya karaWe tsakar filin, babu fargaba ko kaWan Ya nufi inda suke har ya ?arasa gaban matashin nan daya fara shigowa kafin yaci burki yana bin shi da kallo tun daga sama har ?asa, hakanan ranshi ya dinga bashi cewar yaron daya jima yana kwaWayin sanyawa a idanun shi ne, zuciyarshi ce ta soma azalzalar shi da son tabbatar da abun da yake hasashe, a hankali Ya juyo baya ya dubi chief owais dake a can gefe Waya ya goya hannayensa bisa ga kirjinsa tamkar baisan meke wakana ba
HaWa ido su kayi da prime minister, cikin sanyin murya ya furta"shi ne...?


*WAIWAYE A DON TAFIYA*

Abun da ya faru, lokacin da Chief ya dawo gidan bai samu kowa a falon ba,, har su naufal da suka zauna sun koma daku nan su, direct Ya nufi bedroom dinsa bayan shigar shi, tsayawa yayi agaban mirror zuciyarsa a cike fal da tunanin ta wace hanya zai iya taimaka ma Uncle dinsa! Saboda yaji tsantsar tausayinsa ganin irin halin da ya shiga na kaunar yaron, bai da burin daya wuce danish ya farka ko dan Ya faranta Ma daddy hateem kafin yabar nigeria....

Yayin da ya ke wannan tunanin Yana safa da marwa a tsakar Wakin sa Ya shafe kusan Mintuna ashirin, Batare daya samu mafita ba, Yanke shawarar kiran layin Waya cikin drs dinsu yayi don azo aduba lafiyarshi wata'kil adace, duk da shiekh Imam Ya ce basai sun kira likita ba saboda rashin lafiyar tasa bata asibiti bace, kawai a lokaci Ya ?osane daya farkan shiyasa ya yi deciding kiran likita.

A firgice ta farka daga gajeran baccin da yayi awon gaba da ita tun bayan kammala sallar azhar, Hannun ta dafe da saitin zuciyarta dake yi mata wani irin bugu tamkar ana dakan sakwara, wani irin faWuwar gaba ta soma ji, Hankalin ta sam ba'a kwance yake ba, tarasa gane dalilin jin bugun da zuciyarta take yi mata da rana tsaka, kuma ita ba mafarki tayi ba, saukkowa tayi daga kan gadon su, batool dake a kwance babu alamun zata farka, Cikin sauri ta fito daga room dinsu zuciyarta na azalzalarta da taje ta ?ara duba danish dinsu don tana ji aranta wani abu ne ke faruwa da daya daga cikin su shiyasa taji wannan faduwar gaban, kuma bakowa ne ya fara fado mata aranta ba face shi din dama da tunanin shi ta wuni.

Gudu gudu sauri sauri ta nufi second floor, ko da ta shiga falon babu kowa.

Tana ?arasawa bakin ?ofar ta sanya hannu biyu ta dafe ta da karfi har sai da ta buWe kafin ta faWa a fujajen shigarta keda wuya, idanun ta su kayi mata tozali da abun da Ya figitar da ita, da wani irin faduwar gaba take kallon shimfidar shi.

Wata irin zuface take tsastsafo mashi tun daga cikin sumar kanshi take gangarowa har izuwa saman fatar wuyan shi, kyakkyawar fuskarshi ta ji?e sharkaf da gumi, hatta jallabiyar jikin shi ta manne ma fatarshi saboda ruwan zufar daya ji?e ta, muryart na kerma ta soma kokarin ambaton sunan shi.

"Dad...da..nish" bata ?are maganar ba, ganin yadda yatsun hannayensa dana ?afafuwansa suka fara kerma tamkar na wanda sanyi ya kama.

Kasa samun nutsuwa tayi, har batasan sa'adda ta haura saman gadon nashi da rarrafe ta ?arasa saitin inda kanshi ya ke, ta zuba mashi ido tana kallon shi da tsananin firgi ci.

Cikin lokaci ?an?ani, Ilahirin Jikinsa Ya ji?e sharkaf da gumin zufa, lamarin yayi matu?ar Waure mata kai.

Tsabar Yadda Jikinsa ke kakarwa Har gadon kerma yake yi ita kanta jikinta ya kama kakarwa, tun zuciyarshi na bugawa a hankali har ta fara bugawa da matsanancin ?arfi kamar zata fasa kirjinsa ta fito waje, sautin numfashinsa mai haWe da gurnani ya gauraye bedroom dinsa, da karfi Yake Jan shi tamkar babu wadatacciyar iskar da zai sha?a.
Ko wani sashe na jikin shi tuni ya soma motsawa, Unaisah dake kallon shi idanunta azazzare duk tabi ta rude ta firgice Lokaci Waya tsoro Ya cika ta, Zabura tayi da niyar ta watsa aguje gudun kada Ya cutar da ita don ta fahimci kamar baya hayyacin sa ...

Sai dai kafin tayi wani yunkuri juyawa yayi wani kwakkwaran juyi tamkar mayunwacin zaki haka Ya dam?o sumar kan nan nata daya sha gyara gaba Waya ya dawo da ita jikin sa, Yana huci ya matseta kamar zai tsinkata biyu, Ji tayi tamkar an daureta da igiyoyin kaca, hucin zafin jikinsa har anata jikin take jin shi, Zuciyarta ce ta bata shawarar ta hankaWe shi ta gudu, kafin yai yun?urin cutar da ita, Cikin ?arfin Hali ta daddage ta fusge kanta daga ru?on da yayi mata, gaba Waya ta kundumo saman tiles kanta ya daku, Harta zabura zata mike da niyar ta watsa a guje taji ya dam?i ?afarta Waya, ta ?arfi ya janyota kamar Wiyar roba ya dawo da ita saman gadon, runtse idanunta tayi da sauri tana ambaton La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin.

Dogayen yatsun hannayensa dake kerma ya Waura saman wuyanta, ya sha?eta sosai tamkar zai tsinka wuyan, radadin azabane ya ziyarce ta, ta kware baki ta fasa wata irin ?ara mai sautin gaske, sai faman kiciniyar kwace kanta take yi amma ta kasa saboda ?arfin dake gare shi tamkar zaki a haka ma don bai da koshin lafiya da tuni yajima da kashe ta cikin rashin sani. Radadin da tajine yasa ta fashe da matsanancin kuka mai sautin gaske

Adai dai Lokacin Ummi ta fito daga room din ta, don taje ta fara shiryasu ganin lokacin dinner din Ya kusa Cika

Har ta nufi stairs zata hau, kunnuwan ta suka soma jiyo mata Gunji gunjin kukan unaisah, Lokaci Waya taji gabanta yai mugun faWuwa, tsabar rudanine akan fuskanta, fasa sauka tayi cikin takun sauri take bin hanyar da take jiyo sautin kukan cike da was wasin kodai kunnuwanta ne suke jiyo mata badai dai ba

A hanzarce takarasa Bakin kofar, ta soma bubbugata tamkar zata 6alleta, muryarta da sauti mai karfi take ambaton sunanta"Unaisah!! Unaisa!! Unaisah"

Kofar tamkar an datse ta da key taki buWewa ta rufe gam, kware murya ummi tayi tana ambaton ba kowa ne akusa? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un unaisah idan kinaji na ki yi min magana! Meke faruwa dake ne'?_

Ta faWa jiki na tsuma ta zura hannu Waya ta dauko wayarta daga cikin aljihun skirt dinta.

Layin boss man ta danna ma kira bugu biyu yayi picking ko sallama babu tace"yalla6ai kazo gida an samu matsala, na fito daga daki na na ji yo sautin muryar unaisah a dakin danish tana kuka na tashin hankali, nayi kokarin buWe kofar ta datse..."

Muryarshi a ruWe Ya furta"Chief bai dawo ba"? Yarfa hannu ummi tayi "bansani ba, yanzu na fito daga daki.... bai bari ta ?are maganar Ba, Yayi rejecting kiran ranta ne ya 6ata cewar zai zo, tsayawa tayi abakin kofar Idanun ta sun kaWa jawur ta tsorata dajin ihun unaisah, lokaci daya taji shuru babu ihun nata nan fa hankalinta ya kara tashi tadinga buga kofar da hannu da kafa Tana Ambaton"Unaisah dan Allah Kiyi min magana? Danish Ya farkane? Me yake yi maki? Meyasa kike kuka, Nashiga ukuna, Unaisah kada ki bari Ya cutar dake, Kiyi kokarin kare kanki! Unaisah kina jina? Naji kinyi shiru inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." hawaye har sun fara wanke fuskar ummi saboda ta gama gigita Zuciya da sake sake gani take kamar Danish Ya kashe ta ne shiyasa tajiyo shirunta.

Kamar an jeho shi Ya faWo falon A fujajen, wuyan jallabiyar shi ma akarkace take sam baya a hayyacinsa, da gudu Ya falfala Ya haye up inda ummi take atsaye tana faman buge bugen ?ofa, yana karasawa Ya daddage da iya karfin shi na karshe Ya bangaje ta da kafadarsa nan take kofar Ta zuge kanta da gudun gaske, Tsabar saurin su shiga suga meke wakana har suna bangaje juna shi da ummin america, duk wannan budurin da ake sauran yan uwan su basu san meke faruwa ba.

Shigar su keda wuya, suka taras da abun da ya daure musu kai, Yana azaune bakin gadon Ya du?ar da kanshi kasa, Sumar kanshi Ta lullu6e fuskar Unaisah wadda kanta yake abisa cinyoyinsa' basa iya ganin fuskarta sai ?an kafafuwanta, cike da fargaba da karyewar zuciya boss Ya furta Sunan shi"Danish! Unaisa meya faru ne? Ka yi mata wani abu ne? Ha?i?a sun yi mamakin farkawarsa babu wanda yayi tsammanin zai tashi a cikin ?an kwanakin nan.

Adabarbarce ya kare maganar, tamkar yayi magana da bango babu alamun danish zai saurare su duk sun bi sun rude mutun kamar Ifritun

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0