Showing 252001 words to 255000 words out of 413917 words

Chapter 85 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4455

kuke? Motar waye naga ta fita yanzu? Kallon ta su ka yi ba tare da sun furta kalma ba

"Ba ku ji Ina magana bane"?

Ajiyar zuciya suka sauke atare Unaisah tace"bamu san motar wanane ba, muma yanzu muka fito"

"Daga ina"? Kallon juna su ka yi
"Kamar baku da gaskiya, ku fada min mana daga ina kuke" ta fada tana jifansu da kallon tuhuma.

"Mun je part din daddyna ne, daga can muke" ba dan ta yarda da su ba tace"shine ko ku fadamin ay dana shirya mun je tare, gaskiya baku kyauta min ba" ta fada tana jifar su da harara dariya sukai atare..

"Ku wuce mu shiga ciki," gaba tay suka bi bayan ta hannun su ruke cikin na juna

*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?=؋?*


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*


Assalamualaikum inayiwa kowa ftn alkhairi

Bayani xamuyi amfani d wannan dama domin bayani akan wannan business din Mai tarin albarka da Kuma hanyar daakebi a samu kudi acikin sa =ص?=ظ?>?p?Abu na farko dai shi kasuwancin metaforce kasuwacine halattacen a musulunci sanan Kuma harkace ta crypto currency bayan haka Kuma decentralize project ne duk abunda akace decentralize to ba platform bane bakuma abune da xaa tafi d kudinka ba sannan a tsarinshi ba abune daaxace kasaka Abu kaza xaka kwashi kaza ba AA
Kamar yanda kukaji na fada shi wannan business ne yanada tsare tsare xaki samu kudade a cikinsa maxajen kudade matuqar kinbi tsarin wannan kasuwanci yanda ya dace matuqar kinyi register da wannan tsari na META FORCE xaki amfana fiye da tunaninki Yar uwa bake kadaiba harta da Yan uwa ki da abokanan arxiqi duka xasu amfana Dake insha Allah ammanfa idan kinyi register d wannan tsari Mai albarka insha Allah kada na cikaku d surutu bari mushiga Kai tsaye domin Jin yanda tsarin kasuwancin yake>??? B&?>??? B&?=؃??s?>?s?>?s?<؉?<؉?<؉?=?B?<؉?<؉?


Hanya ta farko akwai referral daga lokacin da kikayi idan kikaci damara kika dage da kawo referral toh tabbas company xata biyaki =د? percent Kuma xata biyaki da dollar gwargwadon level din da mutum yayi register a qasanki metaforce wannan dadi=؃? A misali kika kawo mutum uku a level 1 sukayi registration a kasanki company xata baki 5 dollar
Idan kika kawo mutum na 4 company xata baki 5 dollar
Idan kika kawo mutum na 5 company xata baki 5 dollar idan kika hada duka kinka kinsamu 15 dollar kin maida kudinki sau 3 =؃??s?>?s?>?s?
Bayannan samun spillover tana daya daga cikin hanyoyin da ake samun kudin da wannan business na metaforce matuqar ana aiki a team dinki xaku dunga samun spillover wannan kyautace d company ke bayarwa ga Wanda ke d rabo=؃??s?>?s?>?s?<؉?<؉?<؉?<؉? me kika mantane hajiya kixo kiyi register tun lokaci bai kure maki ba
Hanya ta gaba bayan kinyi registration akwai kyauta d company ke bayarwa na TR shi Kuma wannan kyautace da nan gaba xaki amfana da ita nan gaba kadan wannan coins din da xasu baki yanada daraja shiyasa akeso kiyi babban level tun kafin adaina badata>?p?>?p?>?p?

Abu na gaba akwai force coins wannan coins ne Mai daraja Wanda sai kinyi register da METAFORCE =ز?=ز?=ز?
Sannan xaki samu damar mallakarsa Wannancoin din ana sa ran nan gaba idan ya shiga kasuwa duniya xaiyu kudi fiye d Bitcoin saboda irin yanda tsarinsa yake tun ynx Wanda suka mallakeshi sun fara gani
Alhmadulillah da xuwan META FORCE =؃? Yar uwa da wannannanne nake kiranki d babbar murya daga ranar da kikaci karo da wannan typing din nawa kisa a ranki arxiqine ya kwankwasa maki kofa saboda da akwai alkhairi Mai tarin yawa a META FORCE ga wandanda suke da buqatar yin registration suna iya tuntubata a wanan lamba=?G? 09016713233

Ko ku yi Joining Group=?G?

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FN9GrQXqIoCGNwJ8xhSpWO
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun dadi
*Zuzeam empire* takawo muku babbar gara basa
Duka akan 5500 ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa =????=????=????=??<؁?=؃? ?

Wa.me/+2348144015291 For more information say hi =?K? Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam empire tashirya tsaff dominku=؃?=؃?=؃? muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu

*DAHUWAR KAZA*

Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato *Ni ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya*
Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt *Akwai kyauta <؁? mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya*

*INA MASU JEGO DA AMARE*
Karku bari wannan dama ta wuceku
*08144015291*
Zuzeam empire

ASSALAMU ALAIKUM Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 08144015291. 1000 kacal =?L?
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd

Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar g1da set
Mai jego set

Dadai sauransu


*=؋?BOSS BATURE
'*


Bayan ta samu ta lalla6a junaid ya koma bacci, tun da motarsu ta haura kan titi suke ta satar kallon juna tsakaninta da Benazir ta cikin mirror din motar kamar wasu munafukai, kwata kwata hankalin dr shureim baya akansu ya tattara nutsuwarsa akan driving din da yakeyi, hakanan ranshi ya raya mashi ya dubi fuskar Benazir, ta wutsiyar idanun shi ya ke kallon ta adaidai lokaci sun kura ma juna ido ita da Anila da alamun rashin gaskiya atattare da su, duk dagowar da zaiyi sai ya kama su suna kallon juna ta mirror, gyaran murya yayi masu da sauri suka dube shi.

"Ban yarda daku ba! Ku faWamin gaskiya meke faruwa ne? Meyasa kuke satar kallon juna ta mirror? Ina fa lura da duk wani motsinku acikin motar nan, kamar baku da gaskiya, ku ji tsoron Allah ku sanar dani abun da kuke boye min"!

Shiru su ka yi suna ta ?an kame kame an rasa me bude baki ya bashi amsa duk sun sha jinin jikin su.

"Da ku nake magana? Me zamuje yi a obie estate? In har baku fadamin ba zan dakata da yin driving din..." fuskar shi adaure yayi maganar batare daya kalle su ba, kallon juna suka sake yi ta mirror, kafin su yanke shawara da junan su dr shureim ya yi parking din motar a gefen titi Ya kashe ta tare da jingina kanshi jikin headrest.


"In har ba zaku fadamin abunda kuke boye min ba, to kuwa zamu kwana anan ne.."

yawu Anila ta hadiya tare da kallon benazir da hankalinta ya gama tashi,

Cike da fargaba benazir tace"yaya shureim..dama ummm gidan su Azeezaty zamu je..." Dakyar ta ?are maganar ganin ya juyo dakai ya kalle ta tuni ya hade rai, annurin fuskarshi ya gushe rai a6ace yace"meyasa baki jin magana ta? Har nasiha nayi maki nace ki yi hakuri tun da yar nan ba taki bace ki hakura mana, ni dama tun da naga take takenku raina ya bani gidan su yarinyar nan zaku je, to wlh bada ni ba, da nasan gidan su azeezaty zamuje da ban biye maku ba." kallon juna sukayi hankalin su atashe damuwa ce ?arara akan fuskokin su.

Juyawa yai tare da kallon Anila cikin sanyin murya yace"haba anila! Meyasa zaki biye mata? Ni nasan bada son ranki ba, itace ta matsa maki, Benazir bata da hakuri ta fiye kafiya da naci, ba irin lallashin da ban yi mata ba akan ta hakura da yarinyar nan amma ta?i jin maganata"

kifa kai Benazir tayi jikin seat din da take azaune ta fashe da kuka tana fadin"yaya shureim na hakura da ita, nasan ba yata bace na yarda da hakan, Anila tayi min bayanin komai dangane da ita kuma na fahimce ta...." ta ?are maganar tana shesshekar kuka, kafin yayi magana Aneelerh ta riga shi cewa"ka yi hakuri yaya shureim ban nemi shawararku ba nayi gamon kaina, saboda ina tausayin halin da Benazir take a ciki" ta fada tana kallon fuskar shi"shekaran jiya ta kirani awaya take faWa min ita fa tun a asibiti ta fahimci yarinyar nan ba yarta bace kun ce mata taj ya dauketa sunje mall shiru basu dawo ba kun hana tasan gaskiya kun boye mata saboda baku san 6acin ranta, ni kuma abunda nayi tunani duk daran dadewa dole Benazir tasan gaskiya tun da gashi harta kirani awaya ta fadamin tagane ba yarta bace shiyasa kawai na faWa mata gaskiyar zance, sannan na kwantar mata da hankali nayi mata nasiha nace tayi hakuri da boyen matan da akai munyi hakanne saboda gudun kada mu rasa ta"!

tun da ta fara magana dr shureim yayi shiru yana sauraronta, jikinshi yayi mugun yin sanyi zuciyar shi ta karaya.

Benazir ta Waura da cewa"Yaya shureim bayan Anila ta fadamin gaskiya, nayi kokarin cire azeezaty araina saboda a lokacin na hakura da ita, nasan inda rabo wata rana nima Allah zai bayyanar min da ?ata Angel, amma wallahi nakasa ya shureim Inason Azeezaty, Allah Ya jarabce ni da kaunarta, kai shaida ne akan irin Son da nake mata, ko bayan dana gane ba ?ata bace, ina sane nake yi maku pretending saboda kada ku rabani da ita, shiyasa ko bayan da muka dawo gida na Waga hankalina sosai saboda na fahimci kun rabani da Azeezaty" ta Wan dakata da yin maganar tana kallon dr shureim dake kallon ta,

numfasawa tayi kafin taci gaba da cewa"jiya batare da sanin kowa ba, na kira Aneelarh awaya na fada mata halin da nake a ciki na rashin azeezaty, na ro?e ta akan ta taimaka min ko sau daya ne in ganta, saboda na kasa cire ta araina, shine tace min in jira zata yi magana da iyayen yarinyar idan sun amince muje gidan zata sanar dani, sai yau da safe ta kira ni ta fadamin tayi waya da daddyn azeezaty yace muzo gidan mu ganta, har ce mata yai ita ma yarinyar tana son ganina tun bayan data koma gida kullum sai ta yi maganata kaga itama kenan tana jin abun da nake ji agame da ita, ko da bamuje gidan ba, zata sa daddynta ya kawota gurina ne saboda itama ta damu dani"

Muryarta adisashe tayi maganar tana kallon dr shureim, ajiyar zuciya ya sauke har cikin ranshi yaji dadi da Benazir ta hakura abunda ya kara kwantar mashi da hankali jin cewa da sanin iyayen yarinyar zasuje gidan dama shi abun da yake jima fargaba kada su kwasa su je gidan ba tare da sanin iyayen yarinyar ba, benazir ta sanya masu rigima akan su bata ?arta, tun da ba hankali gareta ba, yanzu kuma yaji daga bakinta tasan me takeyi ashe dagangan takeyi masu pretending don kada su raba ta da yarinyar, baiyi mamakin jin hakan ba, cos ya riga da ya san halin Benazir tun tana ?aramarta idan ta kwallafa rai akan abu har aljanun karya take yi masu don ta Waga masu hankali kan abun.

yayi zurfi acikin tunanin shi, Benazir ta katse shi cikin rauni na murya tace"ya shureim dan Allah ka taimaka ka kai mu gidan, nasan me kake tunani, in sha Allah bazan bamu matsala ba, nayi maka alkawarin hakan, Ni kawai burina inga Azeezaty, kona samu kwanciyar hankali"

nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, tare da lumshe idanun shi yayi shiru jimmm yana nazari kafin ya buWe su akan fuskar Anila"ba ki yi laifi ba Anila, kinyi abunda ya dace ne, bansan da wasu kalmomi zanyi amfani gurin yi maki godiya ba saboda naji dadin yadda kika damu da Benazir, wlh kin faranta min rai, saboda kwanakin nan dakyar nake bacci saboda damuwar halin da Benazir take a ciki, amma yanzu kin sama mana maslaha atsakanin mu da ita, ubangiji Allah yasaka maki da mafificin alkhairinsa."

Ajiyar zuciya Aneelarh ta sauke, fuskarta dauke da murmushi tace"ameen ya shureim, ay ba godiya atsakaninmu, mun riga mun zama Waya, zan iya yin komai saboda farin cikin ku" har cikin ransu sunji dadin maganar Aneelerh.

Kallon Benazir yayi suka haWa ido da juna, fuskarta tayi jawur saboda kukan da tayi"kiyi hakuri kinji, ki share hawayenki, yanzu na fahimce ku, kuma naji dadin yadda kika Wauki dangana, in sha Allah kema zaki gana da yarki wata rana, zamu ci gaba da yi masu addu'a ubangiji Allah ya bayyanar mana da su" suka masa mashi da ameen


Daga bisani ya tada motar ya cigaba da yin driving dinsu, Hankalinsu Ya kwanta sosai, Yanzu basu da sauran damuwa, har yanzu junaid bai farka daga bacci ba, maganganun da sukayi baisa ya farka ba, wani irin bacci yake yi mai nauyin gaske.

_________________________________
'?

*UNAISAH ANGEL=ؓ?*

Tana a zaune tsakiyar Bedmattress dinsu, kayan baccin jiya ne a jikinta riga da wando da alama ko wanka batayi ba, gaba daya hankalinta na akan notebooks din da ta jera kan katifar, ta sanya farin glass a idanunta kamar wata malaman makaranta, ta ru?e red pen a hannunta, ta nutsu tana dudduba notebooks din data kar6a a hannun su Parveen, Assignment Win da ta basu jiya shine yau take dubawa, ta rasa gane me suka rubuta, duk jagwalgwalo ne, wani rubutun kamar na ?an china wani shigen na thailand, tun da tafara checking note books din fuskarta Wauke da murmushi wani lokacin saita kwashe da dariya hada kifawa kan katifa ba karamin nishadi suka sanyata ba, ta fahimci kwata kwata basu gane abunda take koya masu, kwakwalwarsu bata daukar karatu, bayin Allah sai taji ta karajin tausayinsu da kaunar su.


Motsin buWe toilet door ne Yasa ta Wago dakai ta dubi kofar, Batool ce ta fito daga ciki, ta sanya bathrobe kafafuwanta sanye da slippers, ta nannaWe sumar kanta da farin towel, dakatawa tayi da yin tafiya ganin irin kallon da Unaisah ke yi mata duk saita sha jinin jikinta, da sauri ta bi kanta da kallo don ta ga ko tayi wani abu badai dabai ba, ganin lafiyalou babu wani aibu yasa tace"Sister, meyasa kike kallona? Akwai wani abu ne"? Murmushi ta Wanyi tare da girgiza mata kai"bakomai wlh, You look so gorgeous, like a pearl" kayataccen murmushi Batool ta saki har dimples dinta suka lotsa, taji dadin yabon da unaisah tayi mata.


"tun dazu nake jira ki fito nima in shiga inyi wankan," ta faWa tare da saukowa daga kan gadon ta fara tattara notebooks din ta Waurasu kan bedside drawer.

"ki zauna ki jira ni, idan na fito zan za6a mana kayan da zamu sanya, har make up zamuyi" dadine ya lullubeta"amma pls kada ki daWe"
"Toh" da sauri ta nufi mirror chair ta zauna tana jiran fitowar ta.


Tsawon mintuna kafin ta fito daga toilet din, tayi Waurin gaba da towel fari, ta naWe sumar kanta da towel kamar yadda Batool tayi...tsayawa tayi tana kallon batool ganin ta daura kanta gaban mirror idanunta arufe alamar bacci takeyi da alama taji dadin wankan da tayi shiyasa ta 6uge da bacci


Karasawa tayi gaban mirror din ta Wauko hairdryer ta jona ta a socket, takai hannu ta tum6uke towel din da batool ta Waure kai da shi, ta saita hairdryer din akanta iska ta fara busowa buuuuu a firgice Batool ta farka tana kokarin buge dryer din hannunta.


Dariya Unaisah tayi"Sorry na katse maki baccin ki, inaso na gyara maki gashin ne naga kin wanke shi, ajiyar zuciya ta sauke tare da jingina bayanta jikin kujerar ta dafe saitin zuciyarta da hannu"kin bani tsoro sister, wallahi nayi azan wani mugun abunne"

Still fuskar Unaisah da murmushi ta cigaba da cakuWa sumar kanta tana busar mata da ita


"Duk in na tuna farkon haduwar mu a prison, sai inji na kara kaunarki a zuciyata, saboda kin so ni a lokacin da kowa ke guduna, bakisan wacece ni ba, amma ki ka kirani da sunan sister dinki, duk da irin ?yarar da nake maki hakan baisa kin juya min baya ba, har saida kika dasa min kaunarki a cikin zuciyata"

Murmushi Batool tayi"nima har yau idan na tuna farkon haduwarmu sai inji na kara kaunarki, abun da ya daure min kai a lokacin ya kuma bani mamaki, irin masifar son da nake yi maki, wallahi ko yan uwana da muka taso atare da su tun kafin mu mallaki hankalin mu ban yi masu irin son da nake maki ba, Allah ya jarabce ni da kaunarki a zuciyata..." ta fada tare da runtse idanunta.
Unaisah dake kallonta ta cikin mirror, tuni taji kwalla ta cika idanunta wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta..
Shiru sukayi na wani lokaci kafin batool ta ce"sister akwai wani abu dake damuna"!
"Menene"? ta tambaya tana kallon fuskarta
Cikin sanyin murya ta furta"Danish, wallahi na damu da shi, bansan meyasa ya canza mana ba, ba kamar lokacin da muna a prison ba, gaba Waya, baya son kowa yaje kusa dashi, ko magana nayi mashi dakyar yake amsa mini, har tambayar shi nayi meke damun shi yace min bakomai..." yanayin yadda tayi maganar tamkar zata fashe da kuka..
"Hatta su Haris sun fahimci baya son suna zuwa dakin shi, shiyasa suka janye jikin su, ni so nake naji idan wani abu muka yi mashi sai mu bashi hakuri ya yafe mana" shiru unaisah tayi batare data iya furta komai ba, Dama tasan dole su damu da halin ko in kulan da yake nuna masu, batasan meyasa yake takura rayuwarshi ba, kwata kwata baya son kowa ya ra6e shi in ba ita ba, yanzu da suka samu sa6ani atsakanin su abun Ya ?ara ta6ar6arewa,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0