Showing 147001 words to 150000 words out of 413917 words

Chapter 50 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2673

jiki na rawa na shiga toilet, dama a kagare take data bar gidan kodan ta nisanta da shi, watakil ta samu relief din radadin da heart dinta keyi mata.

Bayan ta fito shaf shaf ta shirya cikin abaya, ta dauko kaya kala uku ta cusa a backpack dinta, ta goya jakar abayanta, ta zura takalmanta kafin ta dauki wayarta, babu wanda Yasan da zancen tafiyarta, harta fuce daga gidan.....

Cikin sauri take tafiya kamar zatayi tuntu6e, a parking space ta hango daddynta tsaye, ya sanya face mask a fuskarshi
Kallo Waya yayi mata ya fahimci har yanzu akwai sauran damuwa atattare da ita
Baisan ya zaiyi da ita ba, taki fada masa damuwarta, buWe mata murfin motar yayi, wani sanyayyan kamshin turarene Ya daki hancinta, nan take ta gane kamshin wanene da sauri ta dago ta kalli daddyn nata
Murmushi ya sakar mata kafin yace"ki shiga mana"
"Wanene a ciki"? Ta jafe mashi tambayar
"Chief ne, tare da shi zamu tafi" jim ta Wanyi kafin ta kutsa kai ciki, har saida gabanta ya dan fadi lokacin da ta sauke idonta a kanshi, yana daga zaune ya Wauki wankan shadda blue sky tayi bala'en yi mashi kyau, laptop dinsa ce akan laps dinsa, ya dan lumshe idanunshi....
Bata san ya akai ta tsinci kanta da jin wani irin sanyi acikin zuciyarta.

Sai da ta zauna gefen shi kafin ta samu kwarin gwiwar yi mashi sallama tare da gaishe da shi...
Calmly ya amsa mata...
Nutsuwa tayi idon akan glass din motar da bai karasa rufewa ba, tana iya hangen filin gidan....
"Zamu Iya tafiya" chief ne Ya faWa, security din dake zaune a driver seat Ya tada motar, A hankali Ya fara driving dinsu, motarsu big guy tana abiye da bayansu su biyu aciki tare da daddynta, sai motar jami'ansu dake abiye da su....

Lokacin da motocin suka haura kan titi, ajiyar zuciya ta sauke tare da kwantar da kanta, ta lumshe idanunta, bakomai take tariyowa ba face abunda Ya faru tsakanin ta da danish, tayi fatan ace mafarkine ba gaske ba..........bata san sa'adda hawaye suka gangaro takan kuncin ta ba, kwata kwata ta manta da chief acikin motar,

Ranta ne ya bata ana kallonta, a hankali ta buWe idanunta waWanda suka kaWa jawur, karaf idanunsu suka shiga cikin na juna.....
Daga ita har shi sun kasa sarrafa kansu, wani irin kallo suke bin juna da shi mai wuyar fassaruwa
?amshin turarenshi ba karamin kashe mata jiki yayi ba..."

Tsananin tausayinta ne Ya kama shi, har yau yana mai mamakin kananun shekarunta da kuma irin wahalhalun rayuwar da ta fuskanta, shi tunda yataso rayuwarsa baisan menene wahala ko rashi ba.

"I don't want to see your tears..."

*
'DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE
'?*

*Mu haWu Jibi, Idan Allah yakaimu da rai da lafiya, Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: __________________________________
'?



EPISODE

Sai da yayi mai isarshi kafin A hankali chief ya raba jikinsu daga na juna ya tallabo fuskarshi da tafukansa, kwata kwata babu kuzari a jikin shi kamar lagwanin fitila, fuskarshi ta 6ace da blood dinsa, idanunsa sunyi nauyi dakyar ya iya buWe su ya kalli chief yana faman jan numfashi, wani irin tausayin shi ne ya kama shi ga tsananin ?aunar yaron da yake ji, duk da baisan meke damun shi ba, a sambatun da yayi, chief ya fahimci sun samu sa6ani ne tsakanin shi da Unaisah! Shiyasa jiya a mota ta dinga yi mashi kuka, har tayi mashi karyar bata jin dadin jikin ta, yanzu kuma ga Wan uwanta yana sambatu akanta har yana yunkurin halaka kan shi, hakan na nufin akwai wani abu daya shiga tsakaninsu wanda yayi silar jefa su halin da suke ciki?! Abun ya daure mashi kai.!


"Bansan meke damunka ba! banji dadin yadda kake kokarin illata kanka ba! Meyasa ba zaka nemi taimakon mu ba uhyum?

Cikin kulawa yayi mashi maganar, shiru Danish bai tanka mashi ba saboda wani irin jiri jiri da yake gani a idanun shi

Ru?o hannun shi chief yayi da niyar su fita daga toilet din don Ya duba lafiyar shi, da sauri Danish Ya fuzge hannun shi, dakyar sautin voice dinsa ke fita

"I don't want to see anyone! Just leave me alone! ka tafi kawai..."

"No bazan iya ?yale ka ba, Idan kai baka damu dakanka ba, Ni na damu dakai, Please, Danish, let's go treat your nosebleed."

Girgiza kai Danish yayi"bana so, lafiyata qalou, zan kula da kaina, kawai ka tafi ni bana son ganin ka.. "

"Ni kuma ina son ganinka, ba inda zan tafi, in kaga nabar dakin nan to ka samun sau?in abun da ke damun ka ne" babu wasa a fuskarsa yayi maganar tare da harWe hannayensa kan kirjin shi, kallon kallon suka fara jefawa junan su, chief ya rasa yanda zaiyi da shi, yaron yafiye taurin kai ga kafiya, da ?iwuya kamar yaron goye ...

?wara ya lalla6a shi su wanye lafiya, idan ba haka ba zai iya illata kan shi..

Cikin sigar lallashi Yace"pls Danish, ka bani damar da zan baka kulawa, ba cutar dakai zanyi ba, bana jin dadin ganinka a halin da kake a ciki, na damu dakai Danish, ina jinka tamkar Wan uwana, A shirye nake dana taimaka maka wurin ganin mun shawo kan abunda ke damun ka."

tun da chief ya fara magana cikin sanyin murya, Danish ya nutsu yana sauraron shi kamar yana fahimtar shi.

"Nayi maka al?awarin ba zaka ta6a dana sanin yarda dani ba...." bai ?are maganar ba, raunanniyar muryar danish ta katse mashi hanzarin shi"bazan ta6a yarda dakai ba, ?an uwana kadai na yarda da su, amma ku ba abun yarda bane! duk halin ku Waya, kuna da son zuciya, ba ku da tausayi, Tun ina jariri na taso rayuwata a gidan kurkukun ?addara, bansan komai dangane da duniyarku ba, saboda an tauyemin hakkin rayuwata, ina da ciwon zuciyar abun da iyayena suka aikata min, bansan wani jin dadi na duniya ba, unaisah itace farin cikina......." wasu zafafan hawaye ne suka wanke fuskarshi, zuciyar chief ta karaya, baisan sa'adda hawaye suka cika idanun shi ba, sambatun Danish sun ta6a zuciyar shi, shi kanshi baisan Yana furta kalaman ba, rashin Angel ya fara zautar da shi, dama kuma abun ya jima yana ci mashi tuwo a kwarya.

Da sauri chief Ya ?ara huggin dinshi tighly a kirjin shi, kamar zasu koma mutun Waya, a hankali yake shafa bayanshi da tafukan hannayen shi cikin kwantar da murya ya soma yi mashi raWa a kunanshi

"Danish ba duka muka taru muka zama Waya ba, ina rokon alfarma a wurinka, ka jarabani nayi maka alkawarin zan sanya farin ciki acikin rayuwarka, inaso na samu kusanci dakai, saboda na share maka hawayenka in kuma baka kulawa, bayan haka zanyi kokarin sasanta tsakaninka da ?ar uwarka unaisah duk da bansan meya faru atsakaninku ba"

Cikin sanyin murya ya furta"tayi fushi dani, ta daina sona, nasan ban kyauta mata ba, amma bayin kaina bane, ina so na bata hakuri koda ba zata cigaba da kula ni ba, ni burina ta yafe min kada ta ruke ni a zuciyarta, hukuncin yayi min tsauri bazan iya jure ba...ka taimaka min dan Allah..." a karo na farko da Danish Ya ambaci sunan Allah, ba tare da shi kanshi Ya lura da furucinsa ba, lumshe ido chief yayi, wani irin sanyine ya ratsa zuciyar sa, har lokacin suna a rungume da juna, yaji dadin damar daya samu dama burinshi yaja shi a jikin don su samu abunda suke so, yanzu ya samu mafita, ya riga daya gane lagwonsa wato Unaisah, yayi imanin badan sun samu sa6ani atsakaninsu ba, da bazai ta6a samun damar da har Danish zai kula shi ba, murmushin gefen fuska ya saki aranshi ya furta yanzu wasan zai fara=?%?

"Zan taimaka maka in sha Allah, zanyi iyakar bakin kokarina gurin ganin kun sasanta tsakaninku, amma fa sai ka yi hakuri ka cire damuwa aranka, yanzu muje ayi maka treatment na bleeding dinka"

"Bani bu?ata, zan iya gyara kaina" ya fada tare da raba jikin su daga na juna, ya sanya hannu ya matse hancin shi, nan take jinin ya daina Wiga.

"Inason zanyi wanka" fita chief yayi daga Wakin, ya tsaya a bedroom dinsa Yana jiran shi, tufka da warwara ya fara dangane da yadda zai ja shi a jikin shi , yaso yaji meya faru atsakaninsu sai dai ya fahimci baya son sanar dashi, kamar yadda itama unaisan taki sanar da shi, bai damu da hakan ba, saboda shima baison yaji abun da zai hana shi runtsawa kwara atafi ahaka yana dai kyautata masu zato.

Kafin fitowar Danish Ya kira landline na kitchen Ya isar da sakon Yana bukatar breakfast a kawo mashi a dakin Danish

Within 10 mins chef Ya shigo hannun shi ru?e da tray na kayan abinci har saida gabanshi ya faWi ganin jinin dake agaban jallabiyar chief bai dai tanka ba, tun da ya gaishe shi Ya sauke masu akan table kafin Ya fice daga dakin.

Harya fara gajiya da tsayuwa, jin motsin buWe kofa Yasa shi saurin kai idon gare shi, Ya fito fess dashi kamar wani abu bai ta6a faruwa ba, towel ne Waure a waist dinshi, tun da ya fito chief yake kallon shi, bai ji dadi zanan tatttoo din da akai mashi ba, daga bayan shi har gaban kirjin shi da damtsen hannun shi zanan waWannan halittunne masu zako zakon akaifu, launin ja da ba?i bawai don baiyi mashi kyau ba, hasalima kyau zanan yayi mashi sai dai abun da yake jimawa ranar daya musulunta dole yaji ba dadi saboda haramunne zanan tattoo kuma daga gani permanent ne nashi irin wanda bai gogewa, sau?in shi Waya Idan ya musulunta bashi da zunubin komai.


har saida ya nufi closet kafin chief ya kau da ido daga kallon shi, ?arnin jinin ne Ya fara takura mashi fucewa yayi daga dakin Ya nufi dakin shi, ya canza kayan jikin shi ya sanya wata jallabiyar kafin ya dawo dakin danish.

A zaune ya same shi akan mirror chair ya sanya short da singlet a jikin shi, ya zabga uban tagumi da hannun shi biyu, har yanzu ba yaji shi daidai.

"Danish bismilla, taso muyi breakfast, nasan baka ci komai ba" cikin kulawa yai mashi maganar
In a cool voice Ya furta"bana iya cin komai, Unaisah nakeson gani..." ya yi maganar tare da mikewa Ya nufi kofar fita daga dakin, da sauri chief yasha gabanshi...
"Unaisah bata nan, ko kaje dakin su ba zaka ganta ba"
Hankalin shi atashe ya furta"ta gudu saboda tana fushi dani ko"? Ya fada idanunsa cike tab da kwalla"
Girgiza kai chief yayi"ba abunda kake tunani bane, muje mu zauna I'll explain everything to you.."

ya ruko hannun shi suka zauna daga gefen gado suna fuskantar junansu..
Calmly chief ya zayyana mashi komai dangane da zuwanta asibiti, bai boye mashi komai ba ...." bawan Allah har cikin ranshi yaji dadi da unaisah ta haWu da mamanta, sai dai yana jin tsoron ta juya mashi baya tun da ta samu iyayen ta..."

"Angel dina taga mamanta"? Jinjina mashi kai chief yayi,
"Kaima in sha Allah iyayenka zasu bayyana kuma zasu baka farin cikin daka rasa arayuwarka ..." yanayin fuskarshi ne Ya canza zuwa tsantsar 6acin rai.

"Bana son su, bani bukatarsu, bana son ganin su, na tsane su, ni bani da iyaye, unaisah ce gatana" murmushi chief yayi.

"Baka tunanin kaima iyayenka suna kaunarka? Think about it. zai iya yiwuwa wani ne a danginka ya sadaukar dakai ba iyayenka ba, kai da kanka kace tun kana jinjiri aka sadaukar dakai, watakil iyayenka basu san an sace masu kai ba, don ni gaskiya bana tunanin a duniyar nan za'a samu iyayen da zasu haifi kyakkyawan yaro kamar kai su suyi watsi da shi...." shiru Danish yayi baice mashi komai ba, kamar yana nazarin maganar shi, sai dai babu alamun zai fahimce shi.

Cikin dabara chief yacigaba da kwantar mashi da hankali, har ya samu suka ci abinci atare, bayan yayi mashi alkawarin zai kai shi wurin Unaisah amma ya bashi shawarar ya Wan bata tazara watakil ta sauko daga kan dokin zuciyar da tahau...yace mashi bazai iya ba, baya jin dadi in bata atare da shi, yafi son yaganta akusa dashi ko da bazata kula shi ba.. Akarshe yace mashi da anjima zai kai shi wurinta suga juna in har hankalin shi zai kwanta....

Lokacin da su Batool suka farka har yar rige rigen zuwa dakin unaisah su kayi don suga kota dawo amma suna shiga suka iske babu kowa, Hankalin su ba ?aramin tashi yayi ba, wasu har sun fara kuka, saida Ummi ta sauko down ta same su zazzaune kan sofas kowannansu Ya zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki.

Suna ganin ummi suka nufe ta"aunty ummi har yanzu yar uwarmu bata dawo ba, dan Allah ina taje ne bata fada mana ba"?
Kwantar masu da hankali tayi kafin ta sanar da su inda taje, har suna hada baki wurin fadin aunty ummi dan Allah zamuje asibitin wurinta, harma muga yar uwar chief din muyi mata ya jiki"
"Kuyi hakuri, ba za'a bari kuje ba, ku bari ta dawo kawai, in sha bazata jima ba" rigima suka sanya mata musamman jemaimah da azeeza dakyar ta samu ta shawo kansu har suka hakura.

_______________________________
'?

*OIH*

A hankali ta buWe idanunta, ta ?urawa ceilling ido na wani lokaci, kafin ta shafa jikinta da hannunta, jin babu mutun yasa ta yun?ura zata mi?e da sauri hajiya layla ta taimaka mata ta zauna, muryarta na rawa ta furta"wayyo Allah na, mami ina babyna? wa ya dauke min ita? Jiya fa na ganta da ido na, har na rungumeta a kirjina! Ko dai mafarki nayi ne..."? gaba Waya tabi ta ruWe ta Waga hankalin ta, dafa kadarta hajiya layla tayi fuskarta da murmushi tace"kwantar da hankalin ki, babyn ki tana nan cikin koshin lafiya kuma tana a tare dake" girgiza kai tayi tana faman zare ido tace"to ay banganta ba! Babu ita ko'ina, wani ya dauke min Angel dina..." ta fada tana laluba bedmattress.

tun da asuba aka canza masu room yanzu suna a privet room na asibiti, tamkar bedroom na gida haka Yake, har gado Waya aka ?ara masu saboda ya ishe su ita da unaisah.

"Mommy wlh bata nan, ta 6ace, wani ya sace min ita, nama san taj ne Ya gudu da ita saboda yana jin haushina...." saukowa tayi daga kan gadon ta durkusa tana le?en karkashin gadon sumar kanta duk ta rufe fuskarta da bayanta...
"Benazir me kikeyi anan ki tashi mana, nace maki yarki tana atare dake yanzu zata fito, Ki zo ki sha maganin ki, ga breakfast an kawo mana..." ta faWa tare da ruko hannunta, fashewa tayi kuka tana fadin"wayyo Allahna mami, wlh babu ita, na shiga uku na bani na lalace, baby ta 6ace..." duk yadda hajiya layla taso ta shawo kanta abun Ya faskara gaba daya nema take ta zauce...
Motsin buWe kofar toilet ne Ya katse mata kukan nata, a firgice ta juya tana kallon kofar tana faman zare dara daran idanunta, tundaga kasa ta fara kallon kafafuwanta dake asanye da slippers farare tas da su, da sauri benazir ta wurga idanunta kan fuskarta, harsaida ta lumshe su saboda wani sanyi daya ratsa zuciyarta, fitowarta kenan daga wanka, doguwar riga ce a jikin ta pink colour tayi wani fresh da ita kamar babu damuwa atare da ita.


?urawa juna ido sukayi batare da kyaftawa ba, hajiya layla dake kallon su tsabar murna bakinta ya?i rufuwa yadda kasan gonar auduga.


Cikin sanyin murya unaisah ta furta"mamana! Kin tashi lafiya! Ya jikin naki? Kin farka baki ganni ba am sorry na shiga toilet yin wanka ne..." wani irin bugu zuciyar Benzar tayi yanayin fuskarta ya nuna kamar tana kokarin dawowa hayyacin ta ne.

Murmushi Angel ta sakar mata har dimple dinta suka lotsa, kamar ta samu tv haka ta ?ura mata ido tana kallon ta.

"Benazir baki gane ta ba? Babyn da kike nema ce, Kije wurin ta..." jikinta na 6ari kamar mazari ta mike ta nufi unaisah, tana karasawa ta zube kan gwiwowinta ta sanya hannu biyu tayi huggin dinta tightly akan kirjinta, wani irin yanayi suka tsinci kansu mara misaltuwa, kusan a tare heart dinsu ke bugu da karfi da karfi, tuni kwalla sun cika idanun kowan nan su.

"Babyna ne"? Ta fada tare da tallabo fuskar unaisah ta ?ura mata ido tana faman zare mata idanunta har saida gaban angel ya fadi tarasa gane meyasa take jin ta kamar mahaifiyarta.

"Kinyi shiru baki amsa min ba! Baby na ne? Ke ce? Ta fada tana Wage mata eye brows dinta.

Jinjina mata kai unaisah tayi"ni ce mamana" yawu benazir ta haWiya kafin ta furta"taj ne Ya kawo min ke uhum? Yana ina"? Rass gaban Angel Ya faWi ta zaro ido tare da kallon hajiya layla wadda ta kura masu ido tana kallon su gwanin ban sha'awa.

Lamarin ya daure mata kai, meyasa take ambaton sunanta da sunan daddynta? To kodai itama sunan yarta ne da mijinta hakan? Abun da daure kai, tayaya akai sunan su yazo Waya"? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsar ta, ranta ne ya raya mata ay ba ita kadaice me irin nickname dinta ba suna dayawa, shima sunan taj din ba daddynta kadai ke da shi ba, hakan yasa ta saki jikin ta.

Jinjina mata kai tayi"daddyna ne Ya kawo ni, shima yana nan zaizo wurinki amma sai kin kwantar da hankalinki..." cike da zumudi tace toh toh zan kwantar da hankalina..."
Huggin dinta unaisah ta karayi wani irin dadi takeji, ta dade batayi bacci mai dadi irin na jiya ba, bata ta6a zaton zata iya runtsawa ba saboda halin damuwar datake a ciki na abun da ya faru tsakaninta da Danish amma cikin ikon Allah silar baiwar Allahn nan jiya tayi bacci mai nauyi kuma ta samu relief na radadin da zuciyarta keyi mata.

"Mamana, Ki shiga toilet, kiyi wanka zaki ji dadin jikin ki, Idan kika fito dakaina zan baki abinci abaki .." wani irin dadine Ya lullu6e benazir, da sauri ta kalli hajiya layla idanunta cike tab da kwalla tace"mommy tana sona sosai, dama nasan bazata guje ni ba, saboda ita jinina nace, kuma tasan bada san raina na gudu nabarta ba..."

rass gaban angel ya fadi maganar benazir ta jefata arudani, lokaci daya brain dinta tafara tariyo mata labarin mamanta data gudu tabarta a kwamin wanka, tuni

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login