Showing 153001 words to 156000 words out of 413917 words

Chapter 52 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4467

uku ke raba su lokacin sallah, lokacin zuwan chief wurin aiki da kuma lokacin bacci, wani lokaci har ?arfe shabiyu na dare suna kaiwa adakin danish harya fara koya mashi yadda zaiyi rubutu da yadda zaiyi amfani da waya harma da laptop, saboda yana son su fara making phone call da prime minister hateem, su big guy har mamaki sukeyi idan suka ga chief da danish suna magana cos basu ta6a tsammanin yaron zai iya sakar ma wani jiki acikin su har haka ba, bawan Allah Danish dannewa kawai yakeyi ba dan chief yana kokarin lallashinsa da debe mashi kewa ba da tuni ya jima da zaucewa, saboda rashin ganin unaisah ba karamin illa yakeyi mashi ba, duk daren Allah sai ya farka da radadin rashin ta, shi kadai yake haukanshi kafin Allah ya kawo mashi sau?i, bai ta6a bari chief yaga gazawarshi ba tun da ya fahimci mutumin baya son damuwarshi kuma yana bashi kyakkyawar kulawa...

Idan muka koma 6angaren Benazir jikinta yayi sau?i sosai, tana samun kulawa a wurin mutane ukun nan da suka tsaya mata, dr jzz, hajiya layla da kuma unaisah, cikin ?an kwanakin nan ta dawo hayyacin ta sai dai babu wanda Ya lura da hakan kuma bata nunama kowa ba, ita kanta tasan dalilin ta nayin hakan, dagangan take yin pretending, kusan kullum ne sai su anila sunzo dubata, haka zalika Alhaji ubaid da shureim basa gajiya da zarya wurin zuwa asibitin, har ila yau Alhaji ubaid bai haWu da unaisah ba, ba su ta6a cin karo ba, duk lokacin da zaizo tana a toilet, ko tana bacci, itama Hajiya sarah tana kokarin zuwa asibitin duk da ayyukan office da suke yi mata yawa, sau Waya suka ta6a haWuwa da unaisah har suka gaisa da junan su wani abu daya daurema unaisah kai muryar matar tayi shige data cousin din aunty pretty da ta ta6a kira, aikuwa aranar har jaraba kiran layin aunty pretty tayi saboda ta tuna da ita, sai dai kash ba'a Waga kiran ba, saboda wayar ta koma hannun zeenatu dr shureim ne ya bata donsu dinga gaisawa, ita kuma dama bata cika ruke waya a hannunta ba, sai ta wuni bata dauketa ba sai in ta tashi kiran dr shureim tukunna take daukarta..

Alhaji musa tun zuwan da yayi sau Waya, bai ?ara zuwa asibitin ba, ko awaya baya kira balle har yasan wani hali suke a ciki, gashi har dr ya fara tunanin sallamar su saboda taji saukin jikin ta sosai..


*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE
'?*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: lumshe ido tayi ya nutsu yana kallon eye lashes dinta da suka ji?e da ruwan hawaye ita kaWai ta san me take ji, zaro hanky yai daga pocket dinsa a hankali ya soma share mata tears Winta, jin saukar hannunsa akan fuskarta yasa ta yi saurin buWe idanunta ?iris ya rage karan hancinsu ya gogi na juna, hatta numfashin su kokawar haWewa yake.
Kasancewar chief na bala'en kama da Danish sai ta dinga ganin kamar shi ne a tare da ita, shima haka yake nuna damuwa akanta ya bata kulawa amma sai gashi rana Waya ya karya mata zuciya, duk irin burin da taci akan shi na son ganin sun mallaki juna.

Tuna wannan yasa ta fashe da kuka duk yadda taso ta haWiye kukan ta kasa, da sauri chief ya kwanto da ita kan kirjin shi, hankalinshi ba ?aramin tashi yayi ba, hatta agent din dake driving Winsu saida yaji sautin kukanta...."

"Sir meke faruwa ne?" Ya faWa tare da satar kallon su ta mirror, wani shock yaji cos bai ta6a ganin chief yayi hugging Win macen da ba muharramarsa ba.

Bakomai ya jawo hakan ba face tausayinta daya rufe shi gani yake kamar kanwarsa ce Hindu take kuka...
A hankali ya zagayo da hannayansa ta bayanta, cikin sigar lallashi yake Wan shafa shi, wani irin relief taji tuni ta nemi kukan da ta ke yi ta rasa, nutsuwa tayi akan chest dinsa ta lumshe idanunta, tana jin wani irin yanayi da bata ta6a jinsa ba, at same time heart dinsu take beating rapidly, tsit kake ji babu mai magana a cikinsu, Cheif bai ta6a tsintar kanshi a irin wannan yanayin ba yana jin wani irin feelings a tare da shi,
da?yar ya samu ?warin gwiwar, raba jikin shi daga nata
ya tallabo gefen fuskarta da hannun shi, sam ta kasa buWe idanunta wani irin nauyin shi da kunyarshi take ji.
Sexy voice dinsa ce ta ratsa kunnanta"Tell me, meke damun ki? Me yasa kike kuka" la66anta na kerma ta ce"ba abunda ke damuna, lafiyana lou" ta rasa ya akai take jin muryarshi kamar ta Danish hakan ba ?aramin karya mata zuciya yake yi ba,

"Ban yarda ba, kuka baya zuwa saida dalili! FaWa min ko dai baki son zuwa asibitin ne? Daddynki ne Ya tursasa maki"? da sauri ta ce "ina son zuwa, ba shi ya tursasa min ba, kawai bana jin dadin jikina ne, bansan meke damuna ba...." gaba Waya idanunsa na akan pinkish lips Winta sun ji?a da hawaye sunyi taushi...
Ya fahimci akwai abunda ke damunta, bata son faWa masa ne, kuma bai son ya takura mata hakan yasa shi furta "Okey, ki daina kuka, Idan muka isa asibitin, zanyi magana da likita ya duba min lafiyarki..." wani irin sanyi taji ya ratsa zuciyarta, still bata buWe idanunta ba ta amsa mashi da toh, gyara zamanshi ya yi zuciyarshi cike fal da tausayinta ya maida hankalinsa akan laptop Winsa, yayin da Unaisah ta ?urawa glass din motar ido tana kallon motocin dake zarya kan titi, ?o?ari take ta kauda tunanin Danish a ranta amma abun ya faskara.....=ؔ?


_________________________
'?

Su Aneleerh suna zaune a hospital courtyard kan kujeru su uku ita da Zahra tare da Dr. Shureim sun ?i tafiya gida kowan nansu ya ?wallafa rai da son ganin haWuwar Unaisah da mamanta, duk bayan Wan lokaci sai a
Anila ta duba agogon hannunta,

Zahra harta fara gyangyaWin bacci..

"Anila anya zasu zo? Naji shiru har yanzu.." Dr. Shureim ne ya yi maganar, fuskar shi ayamutse daga gani ya gaji ba kaWan ba,
"In sha Allah zasu so, mu Wan ?ara hakuri, ina ji araina sun kusa ?arasowa..." ta faWa tare da kallon zahra dake gyangyaWi
Da zolaya ta ce, "Zahra kada fa kiyi mana bacci anan, kinsan dai ba iya Waukarki zanyi ba, sai dai ko Dr. Shureim ya taimaka mini" murmushi ya yi tare da kallon ta, idanunta sunyi ja muryarta da kasala tace "na gaji ne, ga yunwa ina ji, ga bacci..."
"Ki zo na sauke ki a gida." girgiza kai tayi, "a'a Ya Shureim kaima nasan ka gaji, bana son ma na tafi, hankalina bazai kwanta ba, in har banga haWuwar Aunty Benazir da Azeezaty ba.." har cikin ranshi yaji dadin yadda suke nuna damuwarsu akan yar uwarsa....

Kafin wani ya ?ara furta kalma a cikin su, sautin horn Ya karaWe kunnuwansu, kusan atare suka kai dubansu ga enterance gate din asibitin, a jere motocin suka kunno kai da matsakaicin gudu suka nufi parking space....

"Ina tunanin sune suka ?araso" a cewar Anila, mi?ewa sukayi tsaye suna kallon su cike da sa ran ganin sune.

Tun kafin motocin su ?arasa yin parking, Md Dr.Jidenna ya fito daga cikin asitin babban mutunne ya fara manyanta, gashin kanshi duk hurhura, Dr. Jazz na abiye da shi, already sun san da zuwan Chief, shiyasa suka fito don su tarbe shi....

Da sauri Jami'an Isod suka fara durowo daga kan motarsu sanye cikin kakinsu, qugunansu na a soke da kananun bindigu,

Cikin zafin nama suka buWe masu murfin motar, A hankali chief ya fito kafin Unaisah ta fito idanunta akan katafaren asibitin, a ranta ta jinjina ma haWuwar shi, su Aneleerh na ganinta farin ciki ya lullu6e su kasancewar akwai bulbs light daya mamaye ko'ina tamkar da rana..

"Yaya Shureim sune muje mu tarbo su" Anila ce ta faWa da sauri suka nufi gurinsu, tunkan su ?araso Unaisah ta hango su wani irin farin ciki ne ya lullu6eta da sauri ta nufo su, kafin ta ?araso Anila ta buWe mata hannu suka rungume juna, Dr Shureim tun da ya kafe ta da ido ya kasa ?yaftawa wani irin faWuwar gaba ne ya dirarsa masa, ya ?ura mata ido kamar zai lashe ta, ita ko ta ?an?ame Aunty Anila kamar karta saketa,

"Sannu da zuwa my Azeezaty, tun Wazu muke sa ran ganin ku..." Anila ta faWa tare da Wago da fuskar unaisah, "Ga Yaya Shureim ku gaisa, Wan uwan mara lafiyan ne" sai lokacin ta lura da shi ita kanta da ta kalle shi saida taji gabanta ya Wan faWi, cikin sanyin murya ta ce "ina wuni? Ya mai jiki?"
Murmushi ya sakar mata, "Mai jiki Alhamdulillah, Malama Azeezaty, ina fata bamu takura maki ba, zamu Waura maki Wawainiyar jinya," murmushi tayi "Babu takura, ni naji zan iya, kuma ni abun farin ciki na ne, fatana Allah ya bata lafiya" ba ?aramin burge shi tayi ba, yarinyar ta shiga ran shi lokaci guda sai yaji inama ace yarinyar Benazir Winsu ce da sai yafi kowa farin ciki.

"Aunty Zahra" mi?a mata hannu Unaisah tayi suka gaisa da juna, Zahra na murmushi ta ce "Na ji dadin sake ganinki, Azeezaty tamu, mai mutunci" murmushi kowan nans u yayi.

Taj dake a zaune cikin motarsu Ya nutsu Yana kallonsu Aneelerh, fuskar shi kwata kwata babu walwala.

"Pls ka tashi mu fita mana" girgiza kai ya yi ba tare da ya kalli Big guy ba yace "ba inda zanje, tunda na bada Unaisah babu bu?atar in shiga ciki, ka tafi zan jira ku anan",

"Wai duk akan me kake fushin nan? Saboda baka son ganin ex-wife Win ka?" Banza yayi dashi bai tanka mashi ba,

"Meye na damuwa? Matar da bata acikin hayyacinta, kuma in banda abunka wazai san kaine? Mu da zamu 6adda kama da face mask"?

A takure ya ce"Don Allah ka kyale ni! Nace ba zan je ba, ka tafi mana..."

gyaWa kai Big guy ya yi, yasa hannu ya gyara mask din fuskarsa ya fito daga cikin motar, ya nufi wurin su Chief dake atsaitsaye suna gaisawa da su Dr Jidenna.

?aya bayan Waya ya mi?a masu hannu sukayi musabaha kafin ya Wan russina saitin kunnan Chief cikin muryar raWa yace"Sir taj yace bazai shiga ciki ba!" juyawa Chief yayi har zuwa bakin window glass din motar yayi kncoking din ta,

"Taj, ka sauke glass" zuge shi yayi,
Du?owa chief yayi suka haWa ido da shi "Haba mutumina, mun riga da munzo asibitin shiga ciki ne zai gagare ka uhuym?"

Fuskarshi a yamutse ya ce "Sir pls, bana son shiga ne, nafiso kubarni anan..."

"No taj, ban amince ba," ba don ya so ba, ya Wauko backpack din Unaisah da ya kar6a a wurinta, ya sargafo hannun jakar a kafaWarshi, kafin ya fito daga motar,

Ru?o hannun shi Chief ya yi suka nufi su Dr Jazz atare suka haWu suka dunguma zuwa cikin asibitin, su Anila suna a biye da bayansu ta ru?e hannun Unaisah a cikin nata, kamar wani yace zai ?wace mata ita.

Corridor din da zai sada su da emergency ward suka nufa, cikin girmamawa Nurses da Docs suke gaishe da Chief...

Sau Waya Taj ya saci kallon Dr. shureim, ba su ta6a haWuwa da juna ba, lokacin daya auri Benazir Dr shureim Win ba ya a ?asar ya koma Egypt da zama, sau Waya suka ta6a gaisawa a waya lokacin da ya kira ya dam?a mashi amanar ?ar uwarshi..."

Lokacin da suka ?araso gaban Medical room Win da Benazir take sai kowannansu Ya dakata da yin tafiya.

Kasancewar kofar ta glass ce suna Iya hangen Benazir dake a kwance tana bacci, Dr Adam Yana a tsaye bakin gadon Yana ?ara duba ta,

Knocking kofar Dr. Jazz ya yi, da sauri Dr Adam Ya juyo ya dube su, aiko da ganin su Chief jiki na 6ari ya fito cikin girmamawa ya mi?a masu hannu suka gaisa..

Fitowa hajiya Layla tayi daga dakin jikinta a sanye da hijabi bakinta washe ta fara gaishe da su, suka yi mata ya mai jiki ta amsa masu.

tunda Taj Ya kalleta sau Waya ya kau da idon shi gefe, ba zai ta6a mantawa da irin wula?ancin da Hajiya Layla tayi mashi ba, hakanan ta Waura mashi karan tsana saboda yana son yarta, har faWi take in banda haWama irin na Wan talaka ina shi ina Benazir? waye ubansa a kasar? Da aikin Jarida zai ciyar da ita? "Wama ya sani ko asiri kayi mata shiyasa ta nace saita aureka .." murmushin takaici ya saki ta cikin face mask Winsa...,

Dr Adam Ya ce, "ina yarinyar ne?" da yake basu lura da ita ba duk ta takure bayan Anila kamar tana jin tsoron wani abu,

"Azeezaty, zo nan mana" Biy guy ne ya kira sunanta, fitowa tayi idanunta na kallon ?asa ta tsaya a tsakiyar su, gaba Waya ta tsargu da kallon da su ke yi mata, Hajiya Layla ta kasa rufe bakin ta saboda mamakin ganin yarinyar, sai taga kamar sunyi kama da Benazir Winta, sai lokacin Dr Jazz ya lura da ita sun Wan ruWe da kyawunta, musamman Dr. Adam har dai ya gaza jurewa ya ce "Tabarakallahu ahsanul khalikin..." bai ?are maganar ba, Dr jazz ya yi saurin yi mashi raWa a kunne"kallon ya isa haka! Future wife Win babban yayanmu ce, wlh ka shiga taitayinka" da sauri Dr Adam ya rufe bakin shi da tafin hannu.

"Azeezaty, ina fata anyi maki bayanin abunda ya kawo ki nan?" Waga mashi kai tayi alamar eh,
"Okey, abunda muke so kaitsaye ki shiga Wakin wurin patient Win, ki yi hugging Win ta sannan ki kirata da sunan Mommynki" amsa mashi tayi da toh, kafin slowly ta juya ta nufi Wakin zuciyarta na dakan uku uku wani irin faWuwar gaba take ji, gaba Waya sun nutsu suna kallon ta...
Duk taku Waya idan tayi sai gaban ta ya faWi rass, ta rasa gane dalilin shigarta yanayin da take a ciki.
Tunda ta zura ?afarta a Wakin idanunta suka sauka akan mara lafiyan dake a kwance tana bacci, walking slowly ta ?arasa ta tsaya daga bakin gadon tana kallon ta, tun daga kan fararen kafafuwanta har zuwa kan fuskarta, sumar kanta ta lullu6e gefen fuskarta daga gani ba ?aramin hauka tayi ba kafin a samu ta runtsa.
Wata irin kasala ce ta baibaye Unaisah gaba Waya ta kasa ta6uka komai sai kallonta takeyi kamar zata haWiyeta.....

"Ki rungumeta mana, ke muke jira" ?asa ?asa da murya Dr Adam ya furta maganar,
Numfashi ta ja kafin ta daidaita nutsuwarta, a hankali ta zauna daga gefen gadon kafin ta faWa kan ?irjinta tare da lumshe idanunta lokaci Waya ta fashe da matsanancin kuka me sautin gaske ita kanta batasan kukan Ya kubce mata ba, hankalinsu ba ?aramin tashi ya yi ba amma sai suka yi zaton tayi ne don abun ya tafi dai dai..
Sautin kukanta ne Ya daki kunnan Benazir, cikin magagin bacci ta fara sambatu tana faWin "Babyna, wayyo Allah mami! ina babyna naji sautin kukan ta, don Allah ku kawo mini ita..." yatsun hannunta na kerma ta Waura su kan bayan Unaisah, da dukan hannayenta biyu ta fara shafa bayanta taji mutun akan cikin ta, hakan yasa ta fara kokarin buWe idanunta, da?yar ta buWe su sun kaWa jawur saboda bacci,

Daga can waje Dr Adam ya ce "Nayi mamakin farkawarta, because bana tunanin allurar da nayi mata ta isa ta saketa..."
Su Anila duk sun ?agara Benazir ta karasa farkawa, gaba Waya jikinsu sai tsuma yake yi ga wani irin annurin farin ciki da ya wanke zukatansu,
Mayafin kan Unaisah tuni ya jima da zamewa, hakan yaba Benazir damar cusa hannayenta acikin sumar kanta ta cigaba da sambatu tana faWin "Babyna ne? Mami daddy kuna ina? Wanene Ya kawo min babyna? meyasa take kuka?" Sosai Unaisah ta ?an?ameta, ta ?ara cusa kanta a kirjin Benazir babu alamun zata saketa, Allah sarki jini Waya ba wasa ba, wannan unconditional love Win dake atsakanin uwa da Wanta shine yayi tasiri a zukatansu, a karo na farko da ta fara jin Wumin mahaifiyarta ba tare da sanin itace ba, aruWe Benazir ta zabura ta Wago da fuskarta ta ?ura mata ido tana kallonta, baiwar Allah Angel fuskarta tayi jawur da ita ruwan hawaye ya wanketa tass, da ?yar take buWe idanu tana kallon cikin idon Benazir, kallon kallo suka fara jefawa junansu duk hawayen Unaisah sun wanke fuskar Benazir, la66anta na kerma ?irjinta na bugawa ta furta "Mamana! Ni ce babyn ki, meyasa kika tafi kika barni? kin manta dani a rayuwarki? Nayi kukan rashin ki atare dani mamana!"

Shigowa Wakin Hajiya Layla tayi daga bakin gadon ta tsaya tana kallonsu, ?walla sun taru acikin idanunta,

"Mommy ki faWamin? Da gaske babyna ne nake gani ba mafarki nake ba? Angel Wina ne?" Kwata-kwata Angel bata fahimci sambatun Benazir ba saboda ita kanta ta Wan shiga ruWanin halin da ta tsinci kanta game da matar,

"Benazir, yarinyar ki ce Angel, ki rungume ta a jikin ki, " Hajiya layla ta faWa da murmushi akan fuskarta, fashewa da kuka Benazir tayi, da sauri ta kwantar da Unaisah kan kirjinta ta rungumeta sosai kamar zata mayar da ita cikin cikin ta.
Cikin shesshekar kuka take lallashin ta"kiyi shiru ki daina kuka, bana son ji, nasan nice na 6ata maki rai, kiyi hakuri ki yafe min bazan ?ara tafiya in barki ba, nayi maki alkawarin zan baki kulawa babyna, kinji my Angel"? Sambatu taci gaba da yi ta?i bari Unaisah ta Wago da kanta ta ?an?ame abun ta kamar wani yace zai kwace mata ita.....

Jikin Taj ba ?aramin sanyi yayi ba, da sauri ya du?ar da kan shi hawaye sun cika idanunshi, sai yaji inama ace zai iya zuwa ya haWa su duka a kirjinshi ya rungumesu,

Zahra sarkin tausayi tuni ta fara matse ?walla, ita kanta Aneleerh kukan ne ya kusa kubce mata, da hannu biyu ta toshe bakin ta don bata son ayi zargin ko yarta ce ta gaske,
Lumshe ido Chief ya yi a yayin da yake kallon su, ya jima baiga abun farin cikin da ya sanyaya zuciyarshi ba irin na yau! abun ya ta6a zuciyar shi....

Hatta Docs Win dake a tare da su saida suka ji tsananin tausayinsu, A

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0