Showing 123001 words to 126000 words out of 286330 words

Chapter 42 - Gidan Asali Complete Book By Hafsat Ahmad Boss Bature

05 Jun 2026

98

har sai ya mula yasha iska tukunna ya sallame ta,sannan fa take samun damar cin abincinta,Cikin lokaci ™ankani sehrish ta soma fita hayyacinta,Duk ta rame,kullum ne sai ta farka tsakar dare,ta zauna tayi ta kuka ba wanda ya sani,ita kaWae tasan irin raWaWin da take ji acikin zuciyarta,gashi in tayi kuskuren yi mashi laifi,Hukunta ta yakeyi da tsallan kwaWi,babu wanda bai fara jin tausayinta ba acikin gidan,shiru kawai sukeyi,bakomai ne ya jawo mata hakan ba fa ce rashin Hajiya azeema domin kuwa tun sati daya da yin auren,Tabar ™asar izuwa dubai inda tasaba yin harkokin kasuwancinta,Amma tayi mata al™awarin cewa bazata wuce One month ba zata dawo nigeria saboda ita kawai,Duk da haka kullum sai sunyi waya da ita,kuma tana ™ara ™arfafa mata guiwa,kullum tana kara tunasar da ita akan cewa Karta kuskura ta karaya tun yanzu,Taci gaba da hakuri wata rana sai labari,maha™urci mawadaci ne,Sannan ta dage da addu'a kuma taci gaba da kyautata mashi,sgr bai tsaya a iya nan ba,idan dare yayi dama wannan ™a'ida ne saita kai"

"mashi coffee da kayan marmari around 12,toh yanzu takai ga,sae tana bacci wuraren 1:30 na dare"

"ko biyu,ringing Win wayarshi ke tashinta daga bacci,daga ta Waga zaice mata Coffeee,yana furta hakan zai katse kiran,Dolenta ne ta tashi takai mashi ga bacci a idanunta,duk in taje part dinsa a wannan lokacin zata same shi ne yana yin nafilfilin dare,ko kuma ta same shi bayan ya kammala yin sallar yana karatun al™ur'ani,a rana ta farko data fara ganinshi yana karatun kur'ani abun ba ™ aramin Waure mata kai yayi ba,Ita duk a tunaninta babu ilmin addini akanshi,Ashe kullum saiya tashi in midnight don yayi sallar dare da kuma karatun al™ur'ani,tun daga ranar da ta fara ganinshi yana yin sallar nan,itama sai ta koma yin sallar daren da karatun al'kur'nin,saboda su dinga samun"

"ladar atare,tunda ya katse mata baccinta,"

"A 6angaren Amrish kuwa,Da™yar haroon ya samu ta amince zata koma wurin Mommynta da zama,Da kanshi ya mayar da ita gidansu,Sannan ya gargaWi mommynta akan ta kiyaye 6acin ranta,itama amrishi Win sai da yaja mata kunne akan karta ™ara yunkurin kashe kanta,da haka ya samu ya sasanta tsakaninsu,har ta koma school,Ranar da suka haWu da sehrish a makaranta kamar zasu haWiye junansu saboda tsabar farin ciki,sun sha kuka sosai,saboda sunyi kewar junansu,abun"

"ba'a magana,"

"Soyayyar junaid da jahad kuwa kullum ™ara ninkuwa takeyi acikin zukatansu,sun sha™u sosai koda yaushe suna manne da junansu,baya gajiya da Waukarta su fita shan ice cream,Junaid ya iya soyayya sosau,yaci sunanshi romeo,saboda ya iya caring,ga zumuWi kamar sabon ango,A ™agare yake da aWaura mashi aure da jahad,Bawan Allah duk safiyar Allah sai yayi shiga ta mutunci yaje gaisar da Abusufyan,hakan ba ™aramin daWi yakeyi ma abusufyan ba,tun daga haka ya gane cewa"

"junaid zai ruke mashi ´arshi dakyau duk da ™uruciyarshi,amma yana da hankali sosai,"

"A 6angaren Marshal Omar kuwa,Hosana ta tada mashi 6alli,saboda sehrish tayi aure ita bai aure ta ba,duk yadda yaso ya shawo kan hosana akan ta bashi lokaci amma yarinyar nan ta™i yarda,™arshe tace mashi in har baije anyi maganar aurensu ba,zata tona mashi asiri ne,gabanshi ya faWi ya shiga tunanin wani asiri ne hosana take ikirarin zata tona mashi,koda ya matsa mata akan ta faWa mashi abunda take 6oyewa,sae cewa tayi ae Ya ta6a yi mata fyaWe hada nuna mashi Zoben diamond W inshi daya manta a ranar,kuma tace zata sanar dasu Abbansu ne,Hankalinshi ba ™aramin tashi yayi ba,™o™arin fahimtar da ita ya shiga yi akan cewa shi fa ba fyade yayi mata ba,kawai tsautsayine yasa yayi ™o™arin raping Winta a lokacin,da™yar ya samu ya lallasheta,sannan ta ha™ura,a hakan"

"ma sai da yayi mata al™awarin cewa za'a daura masu aure,"

"lokacin da Haroon Ya ji Auren Sehrish da sgr,tamkar zai zauce saboda tsabar tashin hankalin daya shiga,don shi dagaske son Sehrish yake yi,daga baya ne ya gano cewar Auren Nasu na wata uku ne,tunda yaji hakan sai hankalinshi ya kwanta,Kuma yaci alwashin cewa Sai ya samu soyayyar Sehrish,in ba haka ba sai yabi duk hanyar da zai bi wurin ganin ya biya bukatarshi da ita,don ya"

"jima da kwaWayin son kasancewa da ita,tashin hankali,"

Wannan kenan

"A ranar wata Juma'a ne,Allah yayi ma modibbo rasuwa,Mutuwarshi tayi matu™ar girgizasu gaba W"

"ayansu,Musaman Ammi kamar zata zauce don kuwa har suma saida tayi lokacin da sa™on"

"mutuwar nashi ya isar masu,Rashin lafiya yayi na rana Waya kuma Allah ya kar6i abunshi,Sunji mutuwarnan kamar kamar me,Ashe babu rabon komawarshi saudiya,duk da yaci nasara akan abunda ya kawo shi nigeria ya haWa kan zuri'arsu,ya ™ulla zumunci mai ™arfi atsakaninsu,Allah"

"ya ji™an Modibbo,"

"Gaba Wayansu suka shirya zuwa Damaturu domin halartar jana'izarshi,Banda su sehrish saboda Exams da sukeyi a school ta Second term,amma matasan gidan dukansu abbansu ya tattarasu sun tafi can,gidan ya rage daga Azmee sae su sehrish,ba™aramin daWin tafiyar sgr sehrish taji ba,Duk da ranta na bata cewar da™yar zai wuce 1 week bai dawo cikin gidan ba,ta dan samu hutu,Kullum daga taji dirar mota jiki na rawa zata je ta le™a ta window taga wanene ya dawo,Fargabarta kar ace shine ya dawo,da zarar taga bashi bane,DaWi take ji,duk da tayi kewar shi sosai,Ko bacci takeyi sai ta dinga jin muryarshi acikin kunnanta yana cewa""Oya kneel down"" har mafarkinshi takeyi,d'"

"Yau Ya kasance wata Waya cuf da yin aurensu,batare da sgr ya soke yarjejeniyar ba,yanzu kwana biyar"

"kenan da tafiyarsu Damaturu,dama abbansu yace sai sun zaga dangi,tunda sun jima basu je sun sada"

",zumunci ba"

*Boss Bature*

d'

"Wuraren ™arfe 3 na rana,sehrish na kwance saman gadonsu,tayi nisa acikin baccinta,baiwar Allah ba ™aramar gajiya ta kwaso ba,Yau suka kammala Exams Winsu,tunda suka dawo daga school Ko Uniform Win jikinta bata samu ta cire ba,ga yunwa na cinta amma ahaka ta kwanta saboda baccin"

"da take ji,"

"Jahad kuwa tana a garden suna video call da junaid,tun bayan da suka tafi,kullum ne saiya kirata video Call,idan suka fara wayar nan sai sunyi fiye da one hour suna magana,Idan da daddare ne kuwa ya kirata suna kaiwa har wurin asuba,basu runtsa ba,Soyayyarsu ba ™aramin burge sehrish takeyi ba,wani sa'in sai taji dama itace take samun irin kulawar a wurin sgr,Wan tahalikin nan tunda suka tafi kullum ne saita tura mashi Text message amma babu reply,bai ta6a mayar mata da amsa"

"ba,kuma hakan baisa ta daina tura mashi ba,"

"Cikin bacci ta dinga jin jiniyar motoci acikin kunnanta,A firgice ta farka tana faman zare ido,tsoranta kada ace Sgr ne yadawo Cikin gidan,Sai da tadawo cikin hayyacinta sosai sannan ta gane cewa ashe wayarta ce ke ringing,Wata irin nauyayiyar ajiyar zuciya ta sauke,Hannu takai tare da Waukar wayar dake ajiye saman pillow,sae hamma takeyi saboda yunwar da take ji,duba screen Win wayar tayi,Sunan Daddy ne ya bayyana,Murmushi ta Wan saki tare da answer kiran,ta kara wayar a kunnanta,"

""",Assalamu Alalikum daddy"""

"Muryar abusufyance ta amsa mata da cewa""Wa'alaikum salam,Daughter ya kike?tun Wazu inata jaraba kiran wayar jahad line busy,ke ma kuma na kira wayarki kusan sau biyu tana ringing ba'a W aga ba,dafatan kuna lafiya,"""

"Bacci nakeyi ne shiyasa banga kiranka ba,Jahad kuma tunkafin na kwanta,ta sanar dani cewa junaid """

""",ya kirata,nasan yanzu haka dashi takeyin waya a garden "",Okey,hosana fa?tana ina ne?itama na kira layinta a switch off"""

"Daddy hosana fa,bata amfani da wayarta,tun ranar daka siya mana su bata ™ara bi takanta ba,tafi """

"_"",mayar da hankali akan laptop Winmu,yanzu haka ma kallo takeyi acikinta "",Abusufyan yace""Na kira ne dama don inji ya ku ke"

"?""Murmushi tayi kafin tace""Alhamdulillah daddy,muna lafiya,fatan kaima haka"

"?ina lafiya nima,Ya Exams Win taku?kunyi abun kirki ko"".."

"dariya ta Wanyi tare da cewa""Yau dai muka kammala,Result muke jira yanzu,amma fa daddy kasan a ™urarren lokaci muka koma school,duk an wuce mu a karatu,duk yadda kaga result Winmu kawai kayi "",shiru da bakinka,ka sanya mana albarka"

"Tana jiyo muryar abusufyan ta cikin wayar yana dariya,bayan ya tsagaita da yin dariyar yace""Oh,kina "",nufin cewa ba kuyi abun kirki ba ko?oh ni abusufyan kada ace ´a'´ana basu da ™o™ari"

"A'a daddy ae ba laifinmu bane,yakamata ayi mana uziri,saura fa two weeks a fara exam ka mayar "" "",damu school"

"?""Abusufyan yace""hakane kuma fa,baki tambayeni yaushe zan dawo ba?ko bakiyi missing Wina bane Muryarta da ´ar shagwa6a tace""I really missed u alot daddy,kamar na janyoka ta cikin wayar nan,inyi "",hugging Winki"

"Dariya yayi sosai kafin yace""this Week zamu dawo ae,zuwan bazata zanyi,kuma a washe garin ranar da nadawo zamuje kano,Zan Wauki Waya daga cikin ku mu tafi kano,saboda inaso muje gidan"

?makwabtan nan naku ya ma sunansu

"?""Da sauri tace""gidansu maman sadeeq"

"Yace""eh nan nake nufi,zamu je ne domin munyi bincike akan mahaifiyarku,Nasan zamu samu ™arin "",bayani a wurinsu"

"Wani irin farin cikine ya bayyana akan fuskar sehrish,fuskarta dauke da murmushi tace""daddy inaso "",dan Allah ku tafi tare dani mana"

"?""Kina tunanin cewa Babban yayanku zai bari na tafi tare dake ne"""

"Shiru tayi tuni idanunta sun ciko da kwalla,muryarta tamkar zatayi kuka tace""Amma daddy,ni ya "",kamata a tafi tare dani,saboda zanfi gane kwantancen gidan nasu"

"Shikenan idan har kinason mu tafi tare dake,toh ki fara sanar da babban yayanku,idan har ya amince "" "",zamu tafi atare,in kuwa ya hanaki zuwa sai dai ki ha™ura mu tafi tare da Jahad"

",Jikinta ne yayi sanyi harma ta fidda rai don kuwa tasan cewa Da™yar ne sgr ya barta ta tafi kano Cikin sanyin murya tace""Shikenan daddy,zan jaraba tambayarshi idan ya dawo,Allah yasa "",yabarni,wlh dana ji sosai"

"Sun jima suna waya dashi kafin sukayi sallama,ajiye wayar tayi asaman side drawer,sannan ta sauko daga saman gadon,direct ta wuce toilet domin yin wanka,within mins ta fito jikinta sanye da"

",bathrobe,ta saki gashin kanta a bayanta,yanzu tsayinshi yakai har mid back Winta"

"Gaban mirror ta tsaya,tare da ru™e qugunta,bakowa bane ya faWo mata a ranta ba fa ce Sgr,a duk lokacin daya sanya bathrobe Winshi ba ™aramin kyau rigar take yi mashi ba,yadda kasan donshi akayi"

",rigar"

"Hannu tasa tare da janyo gashin kan nata,ta dawo dashi ta gabanta,tana kwaikwayon yadda sgr yakeyi"

",in ya fito daga wanka,ta daure fuskarta kamar yadda yake tamke fuskarshi,a ™arshe ta fashe da dariya Tana cikin rahar nan,hosana ta turo ™opar Wakin nasu,Ta cikin mirror take hangenta,Hannunta na ruke"

",da system Winsu,jikinta na sanye da doguwar riga ta material"

""",Sehrish ga lunch Winki can a dining,Aunty azmee ta ce idan kin gama baccin lalacin naki kije ki ci"""

",Ta ™arasa maganar a yayin da take zama daga gefen gadon nasu"

"Juyowa sehrish tayi tare da kallon hosana tace""daddy ya kira wayarki a switch off,wai ina kike ajiye"

"?""ta ne"

"Yatsina fuska hosana tayi kafin tace""Oho,nima bansan inda take ba,nemanta na keyi ruwa ajallo,dan Allah ki tayani nemanta,inaso in kira Ya Omar,nayi nayi da jahad ta kira munshi amma ta™iya,dama "",kece mai Wan mutuncin"

"Harara sehrish ta watsa mata tare da cewa""Sai yau kikasan da haka?bayan kinsaba cewa nafi kowa "",tsiwa,bayan duk acikinmu ni ce innocent"

"Marairaice mata fuska hosana tayi,""pls rishi komai ya wuce,dan Allah ki bani aron wayarki yanzu dai in kira Ya omar,2 days banji Voice Winshi ba,Ni fushi nakeyi dashi ma,ko ya kira yaji ya nake,amma bai"

",kira ba,""rai a6ace tayi maganar"

""",Kada ki isheni da surutu,don nasanki bakya gajiya,ga wayar nan ki Wauka,salon ki cinyemun katina"" Cike da zumuWi hosana ta ajiye system Win asaman gadon,sannan ta Wauki wayar da sauri ta fuce daga"

",Wakin"

"Gaban wardrobe ta koma tare da buWewa,tana neman kayan da zata sanya,shirt ce ta Wauko off shoulder Ash colour tare da dogon wandon Jeans,batare da 6ata lokaci ba ta zura kayan ajikinta,bayan ta kammala sanya kayan ta koma gaban mirror, tana shafa powder,sannan ta Wan shafa lip gloss,murza"

",la66an tayi,tana cikin sharce sumar kanta,Jahad ta turo ™opar Wakin"

",Hannunta ru™e da wayarta,fuskar nan awashe sae faman sakin murmushi take yi"

"Juyowa sehrish tayi tare da kallonta tace""Sai yanzu kika kammala shan Love Win?Ni wannan soyayyarta ku tana Waure mun kai wlh,ko gajiya bakuyi,yadda kasan Romeo da juliet,kullum kuna a "",manne da juna"

""",Jahad tace""da alama ba™in ciki kikeyi mun Allah"

"In rasa dawa zanyi ba™in ciki sae dake?kin manta wa nake aure?Ni fa matar Surgeon general ce,ke "" ""...fa?Ni har kunya ma nake ji,ki rasa dawa zakiyi soyayya sae wannan shagwa6a66an"

"Tunkan takai ™arshen maganar jahad tace""Auren da yanzu saura 2 month ya mutu!dashi har kike "",tutiya"

"Gaban sehrish ne ya faWi rasss!lokaci guda jikinta yayi wani irin sanyi,yayin da idanunta suka ciko tab"

",da kwalla"

"Ita kanta jahad,bataso ta faWi hakan ba,ranta ne ya 6aci saboda ta tsani a kushe mata baby Junaid"

",Winta,Wannan ne yasa har ta faWi maganar da tayi"

"?""Jahad!ni kike faWa ma haka"""

"Da sauri jahad tace""dan Allah kiyi ha™uri,wlh bansan na faWi hakan ba,raina ne ya Wan sosu,"""

"Kinayi mun fatan aurena ya mutu kenan""? Tayi tambayar hankalinta aWan tashe"""

"Dan Allah rishi kidaina faWin wannan maganar,nace maki ba a son raina na faWi hakan ba,""tayi """

",maganar tare da ™arasawa wurin sehrish Win,ta ru™o hannunta"

"Pls kada ki bari hawayen nan sun fito daga cikin idanunki,kinsan cewa bazan ta6a yi maki fatan "" aurenki ya mutu ba,kuma wlh ban faWi hakan ba donna 6ata maki rai ba,"" fuskar jahad tamkar zatayi"

",kuka saboda tausayin sehrish"

"Tuni hawaye sun shiga wanke mata fuskarta,cikin sanyin murya ta wanda ya karaya tace""kin faWi gaskiya jahad,bai kamata inyi prouding da aurenshi ba,Ni sam na manta ashe yau saura 2 month ',babban yaya ya sake ni,ni nama ™osa ya sake ni in huta"

"Hannu jahad tasanya tana share mata hawayenta""in sha Allah Babban yaya bazai ta6a sakin ki"

"ba,banayi maku fatan rabuwa da junanku,Nafison ku kasance atare na har abada,Daso samu ne kawai wani abu ya shiga atsakaninku,Ana saura sati daya auren ya mutu,aga kina amai kinga shikenan babu zancen saki,Sae dai a fara tanadin suna,""cike da zolaya jahad tayi maganar,aikuwa nan take sehrish ta"

",fashe da dariya"

"Ganin tafara dariya yasa jahad taci gaba da tsokanarta""gaskiya na™osa in ganki da ciki,cikin ma na babban yayanmu,Wayyo Allah na bansan wani irin farin ciki zanyi ba aranar,zanso naga babynku,wlh "",ba ™aramin kyau zaiyi ba,idan ya biyo kowannanku"

"Fuskarta Wauke da murmushi tace""Najima ina burin wannan ranar,bazan 6oye maki ba jahad,inaso "",inga nima na haifi Wan babbyna,Amma nasan ba yanzu ba"

"Dont worry ur self,Very soon zaki haifa ma babban yayanmu twins ko triplet,tunda muma triplet """

",ne,nasan acikinmu baza'a rasa wadda zata haifi ´an biyu ba ko ´an uku,""Acewar jahad"

"Shiru sehrish ta Wanyi tana murmushi,duk da tasan abune mai wuya amma taji daWin maganar nan ta"

",jahad"

""",Inaso naje naci abinci,yunwa nake ji"""

"Ta ™arasa maganar tare da kama hanyar fita daga Wakin,Bin bayanta jahad tayi da sauri tare da ru™o"

",hannunta cikin nata"

""",Mu tafi atare,nima ae banci abincin ba"""

"Dining suka nufa,Wuri suka samu asaman dining chairs Win kowa ya zauna,Tray ne mai faWi azmee ta ajiye masu asaman dining Win,Warmers ne guda biyu babba da ™arama ta miya ajiye asaman shi tare da"

",plate,sae drinks data Wauko masu"

"Da yake mutanen gidan duk basu nan shiyasa bata girka abinci dayawa ba kamar yadda ta saba,ita"

",kanta ta Wan samu hutu yanzu"

",Munyi waya da daddy,""sehrish ce tayi maganar a yayin da take ™o™arin buWe warmer Win"""

"_?""Ya faWa maki ranar da zasu dawo ne"""

""",A'a bai faWamun ba,sai dai yayi mun albishir mai daWi"""

"?""Cike da zumuWi jahad tace""Wani albishir kenan"

",Murmushi ta Wanyi a lokacin ta kammala buWe warmer Win,wainar shinkafa ce acikinta"

"Ya sanar dani cewa da zarar sun dawo daga damaturu,A washe garin ranar zasu tafi kano,wurin "" "",nemo oumman mu"

",Maimakon taga farin ciki akan fuskar jahad,sai taga idanunta sun Wan ciko daa kwalla"

"?""Meyasa bakya farin ciki ne"""

"Sehrish farin ciki fa kika ce?Bana Farin ciki,Idan har kika ga nayi farin ciki,toh An samu oummaan "" mu ne da ranta kuma da lafiyarta,ina fargabar abunda zaibiyo baya,idan suka je nemanta,Kinsan yadda oumman mu take tsananin son mu sosai,Amma lokaci guda aka nemeta aka rasa,tsorona kada ace ya sayyadi ne yayi mata wani abun,dama yasha faWin cewa zai kashe ta idan har bata daina bin"

",™wa™™wafin da takeyi mashi ba. ""dakatawa jahad tayi da yin maganar,jikinsu duk yayi sanyi"

"Addu'a yakamata muyi mata akan Allah yasa su samota,Amma nikaina ina fargabar a wani hali zasu "" "",same ta"

"Duk sunsha jinin jikinsu,zuba masu wainar tayi acikin plate,sannan ta buWe ™aramar warmer"

",Win,Miyar ganye ce,taji ganda lu6u lu6u acikin,Tuni ™amshinta ya gauraye wurin"

",Da™yar suke iya cin abincin,kamar waWanda akayi ma dole suci"

*HAROON*

"Fitowarshi kenan daga cikin bedroom W inshi,yana ™ okarin barin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login